Showing 21001 words to 24000 words out of 110329 words
Chapter 8 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
sanda ya ji shi fuk ya fadi kasa ba ya gwara kai da bango. Shin taba ta din da yayi shine ya fadi kasa ko kuwa fuskarta ce ta bashi tsoro ya fadi da kansa don razana? Oho! Fuskar Iman ta razana Suhaif ya sake gwala ido yaga lallai Iman ce duk da fuskarta ta canja zaka iya hango kamanninta. Idota jawur, jan kyalle a wuyanta jan kyalle a gashinta, jajayen kyalle a daure a hannunta da kafafuwanta. Suhaif ya gyara zama cikin fidda rai da sake yin numfashi a duniya ya ce "Iman da gaske ne abin da mutane suke fada kenan? Ta nuna masa kofar fita da hannu alamar ya tashi ya fita da sauri. Suhaif ya mike yana layi kamar zai fadi ga zafin da keyarsa take yi masa inda ya fadi ya doka kai a jikin bango, ya juya zai fita kamar daga sama yaji muryar Iman ta ce "Suhaif! Suhaif!! Suhaif!!! Da karfi ya juyo da sauri ya dubeta. Ta ci gaba da cewa "Ina baka shawara yau kada ka yi bacci ka kwana kana addu'a, ka kwana kana sallah, ka nemi tsari daga makiya, munafikai da shaidanu. Suhaif ya tambayeta cikin mamaki "Kamar yayafa? Ta daka tsawa ta ce "Kada ka bincikeni, kada kaki bin umarnina, kada ka karyata ni, kada ka shagala da barci ka ki yin addu'a idan ba haka ba zaka mutu a daren yau. Ba na son ka mutu don kana da kirki. "Mutuwa? Waye zai kasheni? Ya sake tambaya. Ta yi kara mai tsanani ta ce ya fita ya bata waje. Suhaif ya fice hawaye na zuba a idanuwansa yana nanatawa a zuciyarsa abu kamar wasa ashe da gaske mutane suke. Wannan lamari na Iman ya caja masa kai, har ta kai ta kawo hankalin iyayensa ya tashi sun ga Suhaif kamar mahaukaci yana tafe yana magana. Sai mahaifinsa ya kirawo wani malami bayan sallar isha ya zo yasa Suhaif a gaba yana tofe shi.
Bayan Malamin ya tafi sai Suhaf ya yi alwala ya ce zai je Masallaci acan zai kwana. A'a hauka ta bayyana sai *yan uwa suka dau kuka. A kayi-akayi ya dawo yaki dawowa ya shiga Masallaci yayi ta sallah yana addu'o'i. Cikin gida mata da *yan uwa da ubansa suma addu'a suke yi Suhaif ya tabu. Shi kadai yasan dalilinsa na kwana sallah da lazumi. Sai karfe tara na safe aka samu Suhaif ya fito daga masallaci suka nufo gida da mahaifinsa da Najib suna wani sashi a tsakiya wai dan karya koma Masallacin tunda suna tunanin aljanar Iman ita take kaishi Masallaci sai dariya ta kubuce masa idan ya ga sunyi wani abun. Dan shi da hankalinsa ras suke tunanin bashi da hankali. Idan yayi dariya sai su sake razana sun dauka haukar dariya ce ta kamashi. Sun kusa isa gida sai ga wasu motoci guda uku bus biyu da motar *yan sanda biyu ta zo ta wuce. Wani yaro ne ya rugo yana fadawa abokansa cewar Maigari da jama'arsa ne suka je Dutse suka shaidawa Gwamna abun da yake faruwa game da maganar Iman, cewar a kawo musu agaji annoba ta sauka a garin Doko a zo a fitar musu da ita shine aka ciko motoci biyu da malamai da kuma *yan sanda. Idan bata fito ba za'a saka mata tiyagas ko a kona dakin.
Ai kafin yaron nan ya rufe bakinsa Suhaif ya arta da gudu inda Iman take, Najib da Mahaifin Suhaif binsa suke a guje suna "Jama'a ku tare mana shi. Suhaif ya isa kofar gidan ya iske cin-cirindon mutane da Maigari da *yan fadarsa, ga *yan sanda na kokarin hada tiyagas zasu jefa cikin dakin. Malamai na bin katanga suna tofa addu'a. Amma an rasa mai shiga ciki saboda an riga an fada musu irin bala'in da suke cikin dakin. Suhaif na isa wajen, mutanen gari suka ce "Yauwa ga mai iya shiga wajenta. Suhaif ya ce "Ku dakata zan shiga in fito da ita karku saka mata tiyagas. Kafin su Mahaifinsa su iso Suhaif ya shige dakin sai suma suka tsaya a gefe suna kallon ikon Allah. Ya shiga ya iske Iman zaune tana duban bakin kofa amma jajayen kyallayen nan babu a jikinta. Ya karasa gareta yayi mata sallama bata amsa ba sai ya durkusa a gabanta ya fara mata bayani akan ta fito zasu tafi wani gari. Ta bude baki ta bashi labarin abunda ke faruwa a waje ta ce "Babu garin da zamu tafi. Malamai da *yan sanda ne zasu fita dani daga garin, kaje ka basu labarin bazan fita ba sai dai su kasheni. Mutuwa nake so. Mutumin daya kashe hukuncinsa a kashe shi nafi so a kasheni. Hawaye ya kwararo daga idanuwanta, sai Suhaif ma ya fashe da kuka ya tashi ya fita wajen jama'a ya shaida musu sakonta. Wani Malami daga cikin Malamai ya ce "Kaje ka ce mata ta fito za'a kasheta in har an bincika hukuncin kisa ya hau kanta.
Suhaif kuka yake haikan ya koma cikin dakin da Iman take ya shaida mata ta fito sun ce zasu kasheta. Wannan karon murmushi ta yi. Suhaif ya dauko mata hijabinta ya ce ta saka saboda akwai maza da yawa a waje. Iman ta girgiza kai ta ce "Ni da za'a kasheni maye abun saka hijabi? Ba zan saka ba. Suhaif ya girgiza kai don tausayi ya cukuikuye hijabin ya dauko mata jakar kayanta da takalmanta. Iman ta mike, tafiyarta da kamanninta sun dawo dai-dai ta dubi Suhaif ta ce "Har yanzu ni Musulma ce idan aka kashe ni aimin wanka, a yimin sallah, a yi min sutura irin ta addinin Musulunci ina son Musulunci. Sai hawaye ya zubo daga idanuwansu su duka "Suhaif ya ce "To naji amma ki saka hijabinki sai kifi kama da Musulma sai su yadda muyi miki Sallah. Ta karba ta saka hijabin suka fito. Jama'a sunyi mamakin Iman sanye da hijabinta a nutse yadda take da, *yan sanda da Malamai sai jikinsu yayi sanyi suna fadin yarinya nutsattsiya haka ace mata mayya? Watakila ma bakin ciki ne yayi mata yawa ta shiga wannan hali. A gindin katuwar bishiya aka shimfida tabarmi da kujeru aka ce ta zauna za'ayi hira da ita ayi mata tambayoyi kafin a kasheta din. Iman taki zama ta ce ita dai kawai a kasheta babu hirar da za'ayi ta gaji da duniyar.
Malamai suka ce babu yadda za'ayi su kasheta basu ji wa da wa ta kashe ba, don sai wanda ya kashe wani sannan a kashe shi. Da kyar Suhaif ya lallasheta ta zauna akan wata tabarma Suhaif ya ajiye jakar kayanta yazo ya zauna a kusa da ita. Mutanen gari mata da maza suka dinga diddukowa, a ciki harda Goggo dasu Naja'at. Kuka kawai Iman take ta kasa magana. Anyi mata tambaya kala-kala tayi guda ASHIRIN DA HUDU taki amsawa tamkar da GANGAR JIKINTA ake magana Ruhinta baya wajen. Ba karamin yi da baki aka yi ba kafin Iman ta bude baki ta fara magana.
LABARIN IMAN...........
Wash gaskiya na gaji da shige da fice dan ganin na kawo muki labarin nan.
clap 4 me.... Kunsan na cika jarumi da har nabi bayan Suhaif na ambalo muku abin daya faru tsakanin su. Su wa'e ko Oho. Lolx...
Reedwan Suraj Isma'il
>>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA
____CI GABAN LABARIN
_LABARIN IMAN_
Ta ce "Makasudin shigata wannan mummunan hali na dangantashi da Iyayena. Su suka jamin wannan bakar rayuwa. Tun kin maganar Allah da abinda Annabi ya zo dashi sai bata, sai kuma kuncin rayuwar duniya da lahira.
Mahaifina mutumin Gombe ne bafillatani ne gaba da baya kallo daya zaka yi masa kaga kamannin Fulani. Fari ne tas dogo sosai sunan Mahaifina Lamin kuma shine babba a gidansu sai kannensa mata guda biyu Hajara da Gambo, mahaifinsu ya rasu tun suna kanana Mahaifiyarsa ce kawai take kula da su sunanta Fatima. Sun sha wuyar rayuwa kasancewar duk dangin mahaifinsu basa kulasu, sun bar Mahaifiyarsu da wahalarsu. Ta jajirce sai sunyi karatu musamman mahaifina ganin shine babba namiji babu abunda zata masa irin ta bashi ilimi gara ma matan dake su aure zasu yi shine ya kamata yayi karatu ya sami babban aiki ya riketa ya rike kannensa. Ta sayar da shanunsu ba adadi da gona don Lamin ya sami ilimi. Allah cikin ikonSa ya gama sakandiren dai-dai lokacin yayi nisa a karatun alkur'ani gashi da hazaka a duka bangarorin biyu. Ya sami admission a Jami'ar dake Bauchi wato ATBU suka bashi Engineering course din masu kwazo da kokari. Haj. Fatima Mahaifiyarsa ta hada masa duk abunda zai bukata na makaranta ya tafi.
Mahaifiyata kuwa sunanta Patrica ba Musulma bace. Mahaifiyarta Inyamurace mutanen Onisha, Mahaifinta kuwa bature ne jar fata. Yazo nan ya ganta suka yi aure daga karshe ya tafi da matarsa can kasarsu Maziko acan Allah Ya basu haihuwa suka haifi Mahaifiyata Patrica. Ai dole tayi kyau don ta biyo Mahaifinta sak farinsa da gashinsa da hancinsa, idanuwanta ne irin na Mahaifiyarta dara-dara duk da Mahaifiyar ma farar Inyamura ce tas amma farin Patrica kana gani kasan na farar fata ne. Mahaifiyata na shekara uku Mahaifinta ya rasu. Cikin dare Mahaifiyarta ta saceta suka gudo Nigeria don taga alama dangin mijinta na kokarin kwace mata *yarta.
Mahaifiyata na da shekara tara Mahaifiyarta ta rasu a garin Onisha sai kaninta ya dauketa mai suna Uncle Sunday. Aiki ya kaishi garin Jalingo wato Taraba State nan Mahaifiyata tayi karatun sakandire dinta ta samu admission ita ma a nan ATBU Bauchi inda Mahaifina yake suka bata courst din Architecture wato zane da tsara gine-gine. A lokacin Mahaifina yana shekara ta uku wato lebel 3 Mahaifiyata ta shiga label 1.
Allah cikin ikonSa tun sanda Mahifina yasa ido akan Patrica yaji duniya babu wacce yake so sai ita. A hankali suka saba musamman a lokacin Jarabawa wajen karatunsu daya, kasancewarsu su duka masu nacin karatu ne har yake koya mata abun da bata sani ba. Bayan sun saba sai ya fito mata da bukatarsa cewar yana sonta kuma da aure. Abunda ta fara nuna masa ya za'ayi yace zai aureta bayan YARENSU da ADDININSU ba daya bane? Ta nuna masa tayi zurfi a addininta, uwa-uba kawunta murikinta babban mukami yake dashi a wajen bautarsu sune masu bin kauyuka suna kira azo cikin addininsu. Ta ce tayi nisan da babu wani abu da zaisa ta canza addininta. Mahaifina ya nuna duk wannan mai sauki ne shima bazai bar Musulunci ba ya dawo addininta ba, don shima yayi nisa a addininsa amma zasu iya aure kowa yayi addininsa. Ta nuna masa wannan abu ba mai yiwuwa bane ya bar maganar kawai. Yaran da zasu haifa fa ai zasu iya shiga addininsa. Yayi mata alkawari duk yaran da zasu haifa ya yarda subi addininta idan sun ga shi suke so. Tambayar da tayi masa ita ce "Ka yarda da *ya*yanka su bi ADDININA kai kaki yarda ka bi ADDININA meye dalilinka nayin haka? Ya kasa amsa mata wannan tambayar. Amsar ita ce idonsa ya rufe yaga wacce yake so baya tunanin rayuwar *ya*yansa yadda zata kasance nan gaba. Wanne irin bacin ran Mahaifiyarsa da danginsa zasu shiga idan suka ji ya auri wacce ba Musulma ba?
Patrica a kullum tana nunawa Lamin bata son wannan soyayyar tasu domin abune mai wuya musamman idan aka koma bangaren Iyaye. Iyayensa da nata ba zasu yarda ba don haka su hakura su auri wadanda YARENSU DA ADDININSU yake daya. Amma Lamin ya makale shi dai yaji ya gani ba gudu ba ja da baya. Tayi masa wulakancin da ko kare bazai dauka ba don yaji haushi ya rabu da ita, duk da tana tsananin sonsa itama amma tana tunanin gara su hakura domin ita babu mutanen da ta ki jini irin Musulmai da addinin Musulunci. Lamin ya gama karatunsa ya tafi bautar kasa ya bar Patrica a ATBU ita bata gama ba. Allah cikin ikonSa aka turashi Jalingo garin su Patrica acan yake bautar kasarsa. Lokaci-lokaci yake zuwa ya gaishe da kawunta marikinta ya shaida masa shi abokin Patrica ne a makaranta. Wani weekend Patrica tazo gida ta iske Lamin da kawunta har sun saba hira suke haikan. Tayi matukar mamaki ya aka yi Lamin ya nemo gidansu harya shisshigewa kawunta haka suka saba? Bayan ya gama bautar kasarsa ma saiya nemi aiki a garin saboda abar kaunarsa Patrica. Duk inda take yana biye da ita, duk sanda ya shiga Gombe garinsu sai ya karasa Bauchi wajenta haka idan aka yi hutu ta dawo jalingo Lamin yana Jalingo kullum saiya zo gidansu Patrica.
Abun ya fara bata tsoro don kawunta ya fara fuskantar akwai soyayya a tsakaninsu ba kawance bane. Tasan abune marar yiwuwa tunda tun tana yarinya yake yi mata fada tasan kawayen da za tayi a makaranta ban da Musulmai domin zama da Musulmai zasu dinga saka mata wata akida har wataran taji tana son addinin Musulunci. Amma me? Sai taga kawunta da kansa yake nuna mata ta kula Lamin tabar wulakanta shi, don yaro ne mai hankali da nutsuwa. In har yace zai aureta ta yarda ta aure shi.
Patrica ta tsorata da maganar kawunta. Ya za'ayi da bakinsa zaice ta auri musulmi. Ya fada mata manufarsa ita ce watarana zasu iya jan hankalin Lamin ya shigo addininsu. Tunda ya nace yana matukar sonta kamar ransa, har ya yarda *ya*yansa su bi addininta shima zai iya canjawa. Patrica ta yarda da zancen kawunta daman kuma tana matukar son Laman sai ta sakarwa Lamin fuska suka yi ta tafka soyayyarsu. Aka tsayar da lokacin aure da zarar ta gama karatunta sai tayi bautar kasa a dakin mijinta.
Duk wannan shirye-shirye tsakanin Lamin da Patrica da iyayenta ne kawai ake yi, Iyayen Lamin basu taba sanin akwai wata halitta a duniya ba wai ita Patrica balle zancen aure a tsakaninsu. Don su a bangarensu har sun tanadar masa wacce zai aura a dangi. Yarinya mai kyau *yar Fulani Hauwa'u sunanta ta gama Sakandirenta a F.G.C Azare tana kiransa. Sai hanya-hanya yake yi musu har ta kai ta kawo ya fara dauke kafarsa daga garinsu don ana damunsa da maganar auransa da Hauwa'u. Idan mahaifiyarsa ta tuntubeshi game da zancen aurensa sai yayi ta hanya-hanya yana cewa a jinkirta akwai wasu shirye-shirye a gabansa yana so ya kamala. Haka mahaifina yayi ta shammatarsu har lokacin aurensa da Patrica, suka yi bikinsu ba tare da danginsa sun sani ba. A nan garin Jalingo ya samo wasu tsofaffi suka shige masa gaba aka yi aka gama. Amarya ta tare a gidan angonta a cikin Jalingo wata unguwa da gidajen ma'aikata suke wato G.R.A.
Mahaifina yayi ta nuku-nuku ya kasa shaidawa mahaifiyarsa da danginta cewar ya auri wacce ba musulma ba amma duk daren dadewa abun boye zai fito fili haka duk nisan dare gari zai waye. Wani dan uwansa ne yazo Jalingo kuma aka fesa mata labari cewar Lamin fa ya yi aure tuntuni wacce ya aura kuma ba Musulma bace kuma taki Muslunta. Bai yi wata-wata ba ya garzaya garin Gombe ya shaidawa Kakata da danginta halin da dansu Lamin yake ciki. Aka ce Mahaifiyarsa faduwa tayi fuk ta suma. Dangi gaba daya kuka suke yi tamkar gidan mutuwa. Ko da labari yakai kunnan Lamin cewar yazo maza-maza a gida ana nemansa sunji labarin auren da yayi sai yaki zuwa garinsu kwata-kwata. *yan uwansa da yawa sun zo sun iske shi har Jalingo suyi fadansu su tafi babu abunda ya ragu a jikinshi don shi yanzu ya fara zama da matarsa babu mai rabasu.
Allah Ya albarkacesu da samun haihuwa suka haifeni ko ban fada ba kunsan nayi kama da Mahaifiyata ne tunda jama'a da yawa suna mun kallon farar fata ce *yar kasar jajaye. Duk da idan ka karemun kallo zaka iya ganin ina kama da Babana amma nafi kama da Mahaifiyata. Ta radamun suna RUFKATU. Mahaifina kuma ya tara Musulmai ya yanka rago ya radamun sunan Mahaifiyarsa Fatima. Nan aka sha rigima da mahaifiyata wai ita babu mai kiran *yarta da sunan Musulmai Fatima. Shi kuma ya ce ba zai kira *yarsa da suna Rufkatu ba. Mahaifina yana kirana da Fatima. Mutanen gari suna kirana da Prety ma'ana mai kyau. Kowanne suna ina amsawa, amma da aka sakani a makaranta Rufkatu Lamin Mahaifiyata tasa ake rubutawa.
Ina da shekaru hudu aka haifi kanina kamarmu daya aka saka masa suna Bobby, mahaifina ya rada masa suna Abubakar. Bayan ya shekara biyu aka haifi *yar autarmu, mahaifiyata na kiranta da Rebecce Mahaifina yasa mata sunan kanwarsa mai binsa Hajara. Bacin rai sosai ya dasu a zuciyar mahaifiyata danme mahaifina yake yanka mana rago yake rada mana sunayen Musulmai baya kiranmu da sunayen data radamana. Bayan dashi aka yi yarjajjeniya *ya*yansu zasu bi addininta, ya ce ya yarda. Me yake nufi kuma yanzu? Fadan safe daban na rana daban. Ya shaida mata shi ba wai yana nufin *ya*yansa dole sai sunyi sallah ba, amma shi abun kunya ne wataran su shiga danginsa aji sunayensu bana Musulmai ba. Mahaifina yana ta aike a nemar masa gafara wajen Mahaifiyarsa, ace ta yafe masa yasan yayi mata laifi. Dakyar ya samu ta aiko masa da magana mai dadi ta ce ta yafe masa kuma tana masa fatan Allah Ya shirye shi ya kare shi daga barin addininsa kamar yadda ya yarda ya haifi arna a cikinsa. Da ya dauki hutu a wajen aiki, Mahaifiyata ma tana aiki a banki itama ta dauki hutu mu ma aka yi mana hutu a makaranta saiya cika mu a mota muka nufi Gombe muje muga danginsa, dangi kuma su ganmu.
Munsha wulakanci, munga takaici iri-iri domin baro-baro ake nuna mana tsana da zafuta da hantara. Ko randar Kakarmu muka je muka bude muka sha ruwa sai an fasa randar an sayo wata wai marasa tsarki sun saka mata najasa. Bamu isa mu zauna akan tabarmarsu ba balle abun sallarsu sai ayi ta yayyafa ruwa koma a wanke gaba daya. Mahaifiyata taji haushin wannan wulakanci da ake yi mata da *ya*yanta sosai, tasha alwashin har abada ba zata sake zuwa Gombe ba. Mahaifina ma baiji dadin yadda aka yi mana ba, amma ya kasa tarar danginsa balle yajawa kansa. Muka har-hado muka dawo gidanmu Jalingo.
Yaren Fulatanci shine yaren da yawancin *yan garin suke yi don haka fulatanci Mahaifina yake yi mana. Mahaifiyarmu ma haka amma