Showing 54001 words to 57000 words out of 110329 words

Chapter 19 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt

22 Feb 2025

7477

irinsa ba. Mafarki nayi na ganni a wani gari, mutanen garin gaba dayansu suna sanye da hijabai a jikinsu. Sahun sallah sahu-sahu anata sallah, wasu kuma suna karatun kur'ani. Ina tsaye ina kallonsu, a mafarkin sai wata mata ta saka min hijab ta ce "Fatima shigo cikinmu muyi sallah, mu karanta littafi mai tsarki sai muyi addu'a Allah Ya yaye miki bakin cikin dake damun ki. Sai na ganni tare dasu muna salla, ban iya karatun kur'ani ba sai karatun salla kadai, amma a mafarkin na ganni ina karatun kur'ani babu gargada manyan surori nake ja. Dai-dai nan na farka daga barci, a lokacin ana kiran sallar asuba. Na bude ido na tabbatar mafarki nake, nayi farat na tashi zaune naji jikina yayi karfi. Na daina ciwan kai, zuciyata tayi fari tas. Na tsinci kaina ina farin ciki, babu abinda ya lullube min zuciya sai in tashi in tafi neman wannan gari da ake addinin Musulunci, in nemo ilimi in tsayar da Sallah da azumi.
Na yankewa kaina hukuncin gara in raba rigima tsakanin uwata da ubana in bar garin, tunda haka rayuwata ta kasance, bani da sha'awar karatu a rayuwata ba zan iya ba, ganin yadda ta kasance daga zuwana Jami'a, kawayena sun rasa rayuwarsu, nima kuma na fada hatsari da masifa kala-kala. A sanadiyyar karatu aka samu yaron da bai san komai ba ya zo ya fada maraici da rashin gata ga rashin asali. Na fada a baiyane bazan auri Micheal ba, bazan tafi jami'a ba. Ba aure, ba karatu, dole ba zaman gidanmu. Kuma idan na zauna a gidanmu bani babu addinin Musulunci. Zuciyata ta ce min "Tashi maza-maza shirya ki gudu ki bi hanya madaidaiciya. Nayi wuf na mike daga kan shimfidata na nufi bandaki da sauri na dauro alwala na rufe kofar dakina, na gyara labulayen wundo, na kashe fitilar dakin kada wani ya zo ya riske ni ina salla. Na dinga jero sallolin da banyi ba jiya na ramasu kakaf, na idar nayi addu'a sosai akan Allah Yasa karshen damuwata ce tazo barina gaban Iyayena. Na shiga bandaki nayi wanka na wanke bakina da brush, na hada sosona da brush dina a leda na daure na fito da su. Na dauko jakar zuba kayana na saka a ciki. Na zabi kaya kala uku atamfofi na zuba a jakar. Sannan na saka wani leshi pink sai dai matsalar bani da gyale babba bare hijab da zan saka in saje da Musulmai a garin Musulunci. Salla ma dakyar na harhada kananan Mayafaina nayi. Babu komai idan naje can zan samu in siya insa.
Af na manta, nan fa matsalar take da na tuna bani da kudin motar barin garin. Amma sai na tuna akwai wata tsohuwar sarkata ta gwal da ta tsinke tuntuni dan kunne daya ya fadi, Mahaifiyata ta ce in ajiye zata karba ta canzo min wata. Na lalubota cikin akwatina da warin dan kunnanta, na saka a jakar kayan tafiya. Na dauko biro da takarda guda biyu na zauna na fara rubuta wasiku, daya ta Maman daya kuma zuwa ga Babana. Na basu hakuri kuma na nemi gafarar su yafe min. Na shaidawa Mahaifiyata tayi hakuri ni Musulma ce bana bin addininta yanzu haka na tafi neman ilimin addinin Musulunci. Na bata labarin rayuwata da su Harriet da yadda aka yi na samu jaririn, amma ban fada mata jaririn bai mutu ba, nace idan Micheal ya zo su fada masa jaririnsa ya mutu. Na shaidawa Mahaifina yayi kuskure babba da ya bar addininsa na Musulunci addini gaskiya. Don haka bazan iya zama da su ba, na tafi wajen *yan uwana Musulmu. Na rokesu da kada su damu kansu su wahalar da kansu su bazama nemana, baza su iya gano inda nake ba don taka maimai nima kaina bansan garin da zan nufa ba, mai yiwuwa ma in bar kasar gaba daya. Bazan fada hannun halaka ba ko mugaye, ko karuwanci tunda Allah Yasan zuciyata da izininsa zai kareni. Na ce su kara hakuri da rashina nima ina cikin tsananin bakin ciki da takaicin rabuwa da su, da kuma kannene dole ce tasa zan tafi don ba yadda zanyi. Ina gama rubuta wasikun sai kuka ya kece min. Na jera wasikun akan katifata a bude yadda suna shigowa zasu gani. Jikina yana karkarwa na yafa dan karamin gyale na rufe jakar kayana na rataya na fito gami da tura kofar dakin na rufe kamar ina ciki na fara sanda don kar suji karar bude kofar falon, na fice na mayar da kofar falon na rufe.
Misalin karfe shida na safe ne don haka garin bai gama wayewa ba. Mai gadinmu mijin Mama Tabita bai fito wajen gadi ba yana gidansa shima. Na iske get din a datse da kwado, gashi ban san inda ake ajiye mukullin ba, amma wannan ba matsalata bace duk girman bishiya da tsawon get zan haura, saboda tun ina yarinya ni da kawayena Mumuyawa mun saba hawan bishiyoyi kala-kala. Ina jefa jakata waje, sai na nade siket dina na kama get na haura. Na dauki jakata na kara gaba. Kicibus nayi da Mahaifin Hamma Huzaifa ya dawo daga Masallaci. Nan da nan na kawar da fuskata gefe na rufe da gyale don kada ya gane ni, amma yaso ya gane ni sai kallona yake har da waiwaye cike da mamaki. Na san dalilin da yasa bai tsayar dani ba, yasan babu yadda za'ayi in ce ban tsuguna na gaisheshi ba. Na wuce shi da sauri dan kada ya tona min asiri.
Ina isa bakin titi na tsayar da achaba na haye, yana tambayata ina zan kaiki nace muje kawai. A hanya nake shaida masa wuraren zuwan nawa da yawa. Na farko ina so ya kaini duk inda yasan ana sayan gwal zan sayar, sai kuma ya wuce dani tashar da zan tafi wani gari. Yayi murmushi ya ce "Akwai wata Hajiya tana zuwa Saudia tana sana'ar gwal zai kaini yasan zata siya, sannan wanne gari zanje dan yasan tashar da zai kaini? Nayi shiru can na ce "Garin da kasan suna Addinin Musulunci. Ya tuntsire da dariya ya ce "Lallai yarinya nan baki ma san wanne gari zaki ba, ko dai guduwa zaki yi daga gidan Iyayenki, ko gidan mijinki? Nayi caraf na ce "Na yi maka kama da mai guduwa ne? Kawai tambayarka nayi don inji yadda nake zato din gaskiya ne. Shine garin da yafi kowanne gari Musulmai. Ya nisa ya ce "Wanne gari kika dauka yafi kowanne musulmi? Na ce "Kogi state. Dan acaba ya ce "Inah ai yarinya baki canka ba Kano yafi Musulmai. KANO TA DABO TUMBIN GIWA KO DAME KAZO AN FIKA. Na maimata "Kano? Ya ce "Kwarai akwai Malamai, a kwai Makaranta addini, ga masu arziki da suke taimakawa addini da dukiyoyinsu. Ke duk *yan garin Musulmai ne sai dai bakin da suke zuwa zaka samesu da wani addini. Nayi wuf na ce "Ashe nayi gaskiya nima Kanon na nufa sai na bugi cikinka na tambayeka. Ni da shi duka muka tuntsire da dariya.


Yakaini kofar gidan Hajiya mai sayar da gwal, saina kafe a bayan babur naki sauka, na ce sai dai in bashi ya shiga ciki ya sayar mun idan ta ganni yarinya zata ki saya ta ce na sata ne, shi kuwa babba ne zata siya. Bai yi musu ba ya kashe babur na debo su daga jakata na hada da zoben dake hannuna na mika masa. Ya aika yaro cikin gidan akayi masa sallama da ita suka tsaya a zaure suka yi ciniki ta shiga gida ta dauko masa kudin. Ina kallonsa bayan matar ta shiga cikin gida sai ya debi wasu kudin ya zuba a aljihunsa ya fito daga zauren ya nufo inda nake, ban nuna na ganshi ba ya mikomin kudin na karba nayi godiya. Ban damu da cutar da yayi mun ba ganin kudin cunkus ya bani. Ya buga babur muka tafi. Na sake mamaita masa "Ka kaini tashar Kano yace "An gama *yan mata.
Muka isa tasha na sauko daga kan babur na dauko kudi mai yawa na bashi, ya sani, nima nasan yafi kudin aikin da yayi mun. Yana ta godiya muka yi sallama na nufi wajan motoci shi kuma ya buga babur dinsa yana mai matukar farin ciki shikam ranar kamar danshi na sayar da gwal dinnan, saboda kudin da ya samu.
Nayi tambaya ina zanje in hau motar Kano? Aka nuna mun, kwarai kuwa gaskiya ne, Kano garine na Musulmai da Musulunci. Domin matan dana iske a layin yankar tikitin shiga mota sun burgeni gaba dayansu sanye suke da hijabai har kasa wasu harda abun lullube fuska wato (nikaf) nabi layi nima a bayansu. Kamar yadda naga suna yi duk wacce ta mika kudinta aka yankar mata tikiti sai ta dauki jakar kayanta ta shiga cikin zungureriyar mota. Layi yazo kaina na tambayeshi nawa ne? Ya fada mun na zaro kudin na bashi ya bani tikiti saina dauki jakata na shiga mota. Na shiga cikin mota ina ta baza ido ina neman wajan da zan zauna, kasancewar motar tana da kujerun zaman mutane bibbiyu ne a layi-layi. Kowanne layi ya cika da mutane. Hankalina ya tashi ganin zan rasa wajen zama kuma kowa abokin tafiyarsa yake tanadarwa kusa dashi, ni kuwa ni kadaice bansan kowa ba. Amma zuciyata tayi sanyi hankalina ya kwanta ganin kowacce na hada ido da ita sai tayi mun murmushi tace mun "Salamu alaikim. Na wuce can karshen motar saina iske wata mata ita kadai, koda taga na tunkaro wajenta nan da nan ta dauke jakarta ta nuna mun kusa da ita ta ce in zo in zauna. Ina zama a kusa da ita saita mikomun hannu gami da cemun "Salamu alaikim". Muka gaisa. Nayi ajiyar zuciya na ce a zuciyata "Addinin Musulunci kenan, Musulmi suna son *yan uwansu Musulmai.
Mota ta cika aka rufe kofar mota, direba ya shiga ya kunna mota ya ja muka fara tafiya, yayin da hawaye ya kece mun. Matar da ta ke kusa dani ta lura da kuka nake sai ta shiga yimun tambayoyi meya sameni nake kuka? Duk ta damu ta rikice tana tambayata. Na rasa amsar da zan bata na goge hawayena na hau murmushin dole. Ta fara mun nasiha tana jawomin aya tana bani musalai da rayuwar da sahabbai suka yi, daman duniya kurkukun mumini ce sai lahira zaiji dadi dan haka duk yawancin masu holewa a duniya su sha giya, suyi zina, suyi sata, su suke jin dadin duniya lahirarsu kuwa tamkar kurkukunsu ne. Nan ma naji na karu da abunda ta fadamun na rike a zuciyata. Sai na fara tambayarta ita *yar Kano ce ko *yar Jalingo ce? Ko da yake naji ta iya Hausa sosai daga dukkan alamu *yar Kano ce. Sai ta ce mun ita *yar Kano ce aure ya kawota Jalingo, amma duk shekara tana zuwa Kano. Na sake tambayarta ganin gida take zuwa. Sai ta ce "Bama ganin gida kawai ba, kinsan wannan watan Azumi ne duk gomar karshe muna shiga Ittikafi a Masallaci har sai ranar sallah muke fitowa muna Masallaci muna ibada. Nayi shiru na kasa magana tunda bansan har an fara azumi ba an yi kusan ashirin. Sai dai duk sanda na shiga gidansu Huzaifa sai suce min suna azumi, bansan Ramadan bane koma na sani ai ba damar inyi a gidanmu. Ina mata tambayoyi tana amsamin duk yadda suke yi. Ta nuna min sauran tawagar tafiyarta ta ce haka suke yi duk shekara a Masallacin BUK old site suke zama har kwana goma suna sallah cikin dare suna addu'o'i. Nan danan na ce mata nima zan bita inje mu kwana goma. Ta dube ni cike da mamaki sai ta tambayeni "Kin fadawa iyayenki sun yadda? Na Marairaice na fara hawaye na ce "Ai ni marainiya ce, aikin wanke-wanke da shara nake a Jalingo suka koreni, shine zan taho Kano ko zan samu wani aikin. Sai naga ta kuramin ido tana min kallon kurilla daga ni har kayan jikina. Da alama taga babu wahala a tare dani, sai ta shiga wani tunani mai zurfi. Dana ga haka dan karta gane ni sai na hau tsarata yadda zata yadda da ni na ce "Sun rike ni amana a gidan aikin tamkar *yar gida tun ina karama, sun saka ni a makaranta, to tun lokacin da mai gidan ya ce yana sona matar gidan ta tsaneni ta kore ni. Nan da nan matar ta gaskata abunda nake fada mata ta ce "Eh kwarai dole ta kore ki karki aure mata miji, to Allah Ya kyauta. Ta yi shiru bata sake cewa komai ba muka ci gaba da tafiya, Jalingo da Kano akwai nisa. Duk inda muka tsaya salla sai matar ta siya mana abubuwan ciye-ciye kona roketa ta bari in siya da kudina sai ta ki. Ganin duk suna azumi nima sai in ajiye in ki ci ina jiran sai an sha ruwa. Amma ta lura bana azumi sai ta ce min "Zan iya ajiye azumin saboda ni matafiya ce bayan sallah sai na rama azumin. Na ce "A'a azumi nake nima. Sai daf da zamu shiga Kano aka kira sallar Magaruba, dukkan mu muka yi buda baki da abubuwan da muka siya. Mun isa Masallacin BUK ana kiran sallar isha'i.
Mun iske mata da yawa masu zaman Ittifaki, haka wasu da yawa sun zo bayanmu. Na sha mamaki dana ga wasu harda kayan abincinsu danye da rusho din dahuwa kamar a gida. Sunan matar da muke tare da ita Maman Aisha. Tana da kirki sosai kamar yadda ya kamata, tana kaunata tamkar jininta, naji dadin zama da ita kamar yadda taji dadin zama dani. Ta bani hijab dogo har kasa haka duk wasu ayyuka da suka taso da rawar jiki zan tashi inyi bana barinta ta wanke ko cokali. Muna zaman lafiya da kowa, *yan uwa Musulmi masu neman ladan ciyarwa a cikin wannan watan mai girma na azumi suna ta tururuwar kawo abinci sadaka cikin Masallaci, don haka akwai wadatar abinci kuma idan wasu daga cikinmu suka dafa suna kiran kowa da kowa a taru aci saboda Allah.
Muna yini ibada, mu kwana ibada, bayan sallolin farilla da muke bin jam'i, daga karfe sha biyun dare mata suke tururuwa su taru a Masallacinmu ana cika taf har wasu a waje saboda cika. Maza kuma a bangaransu babu mai ganin wani idan aka fara salla har asuba. Allahu Akbar! Lallai Musulmi su suke ibada tukuru da jikinsu kuma duk mulkinka da kudinka. Na sha wuya kafin in saba dare da rana sallah, ga yunwar azumi amma zuciyata a dake take na sawa raina son Musulunci, kafin kwana gomar nan harna saba na daina gajiya. Ba shakka wannan shine mafarkin da nayi, sahun sallah sahu-sahu sannan ayi karatun kur'ani. Ina nacewa Maman Amina tana biyamin karatun kur'ani na kuwa fara koya yadda ya kamata.
RANAR SALLAH. !!!


ALLAH YA KARA DAUKAKA MUSULUNCI DA MUSULMAI AMEEN


Reedwan Suraj Isma'il




*************** YAREANA ADDININA
___CIGABAN LABARI


RANAR SALLAH !!!
Ranar da muka kwana goma, ranar ne ake sauke azumi, ranar ne kuma ranar Sallah. Bayan Sallar Idi sai naga matan da muke tare suna harhada kayansu suna shirin tafiya. Na tambayi Maman Amina ina zasu tafi naga suna hada kaya? Sai ta sanar mun ai yau kowa zai tafi gidansa tunda azumi ya kare. Gabana ya fadi, hankalina ya tashi bani da inda zan nufa, sai jikina yayi sanyi. Maman Amina ta lura da halin da na shiga yanzun nan, sai ta fara mun tambayoyi taji ra'ayina. Ta ce min "Yau nima zan je gidan Iyayena ayi bikin sallah dani sai sati na sama in koma Jalingo. Ke fa Fatima wacce unguwa zaki tafi ne? Hawaye mai yawa ya zubo nace bani da kowa, ban san Kano ba, ban taba zuwa ba bani da dangin uwa babu na uba. Sai na rushe da kuka na fada kan cinyarta ina cewa "Maman Amina ki taimakeni.
Hankalinta ya tashi, tana lallashina idonta ya cika da kwalla ta ce min, "Fatima yi shiru kada jama'a su taru kinga sun fara tambayata meya sameki zan taimakeki kamar *yar cikina, Fatima Allah ne Ya hadamu. Naji dadin maganarta sai hankalina ya fara kwanciya ta share mun hawaye ta ce "Zaki yarda ki bini gidanmu na nan Kano idan sati ya zagayo zan koma Jalingo mu tafi tare, ki zauna tare da ni da marayun *ya*yana su Amina? Nan fa daya ai bani ba komawa Jalingo, nayi shiru. Can naji ta sake ce wa "Zabi zan baki, ko kuwa kinfi son in nemar miki gidan aiki anan garin? Nayi sauri na ce "Eh ki samar min gidan aiki anan garin saboda inason garin akwai addini. Tayi murmushi ta ce "Jalingo ma akwai Musulunci sai dai kice akwai yare daban-daban da wasu addinai, ba kamar Kano ba Hausawa ne kuma Musulmai ne dukkansu. Mu duka mu kayi dariya. Wadanda muka saba suna ta zuwa inda muke muna zaune acikin Masallaci suna yi mana sallama, muna musu fatan alheri da fatan Allah Ya hadamu a wata shekarar.
Muma muka tashi muka hada kayanmu Maman Amina tayiwa *yan tawagar da muka taho tare sallama cewar ita ta tafi cikin gari sai wani satin zata je Jalingo su kuwa yau zasu koma Jalingo nima nayi musu sallama muka fito. Bana barin Maman Amina ta dauki tsinke idan muna tare dan haka da jakar kayana dana kayanta na dauka muka fito get din makarantar BUK. Naga ta tsayar da tasi ta ce masa TUKUR ROAD zai kaimu. Su kayi ciniki muka shiga. Muna tafiya a hanya take sanar dani zata kaini gidan aiki ne da farko sannan ta dawo cikin gari kusa da gidan Sarkin Kano nan ne unguwar gidan Iyayenta. Ta ci gaba da yi mun bayani, ta ce gidan da zata kaini bama Hausawa bane balle ayi gutsiri tsoma da kananan maganganu. Larabawa ne, larabawan Egypt. Mace da Mijinta sai dansu guda daya. In har zan zage in yi musu aiki ba ha'inci in kular musu da dan karamin yaronsu to lallai zasu rikeni tamkar *yarsu, zanji dadi in huta, gida ne tamkar aljannar duniya. Kamar yadda ta karanci halina dan zaman da muka yi tasan babu matsala halina yana da kyau zamu dai-daita, don haka ne ma taga ya dace ta kaini

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login