Showing 72001 words to 75000 words out of 110329 words

Chapter 25 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt

22 Feb 2025

7485

(S.W.A). Suhaif ya fada yayin da ya sulale ya zauna dan murna da mamaki, lallai wannann shine arziki a dare daya.
Allah mai azurta duk wanda Yake so a duk lokacin da Ya so. A cikin shekara daya Allah Ya azurta Suhaif fiye da tunanin mai karatu. Kwangilolin da yayi ta yiwa port Authority ake biyanshi akan lokaci ya sami makudan miliyoyi. A shekara ya kama hadadden gidan haya duplet a unguwar manya (victoria island) wanda kudin hayar ma kadai zai iya siyan wani gidan. Kafin ya samu a hankali ya binciko inda zai sayi fili ya gina gida irin wanda ya keso, a garin da ya keso, da unguwar da yake so.
A lokacin Suhaif ya canja mota kirar zamani wacce ake tsakiyar yayinta a lokacin. Nan fa Suhaif yaga ikon Allah da abunda yafi karfin idonsa, wato cincirindon *yan mata da suke sonsa HAR DA SU WA'E . Shi kuwa basa burgeshi ko daya baya son su, soyayya bata gabansa har yau har gobe Iman ce a zuciyarsa.
Ya hado tara ta arziki ya zo ya gaishe da Iyayensa, a Kano ya sauka. *yan gidan sun sha mamakin yadda Suhaif ya zama a shekara guda. Duk da bai yi kiba ba amma yayi fari, kallo daya zaka yi masa kasan yana cikin daula, ni'ima da wadata. *Yan gidan gaba daya sunyi farin ciki da zuwan Suhaif, saboda sun dade basu ganshi ba. Yana musu gizo kamar ba shi ba. Gara Baba na Kano, Baba na Doko da Najib sunje Lagos sun ganshi kwanakin baya, amma Mama, Goggo, Naja'at da Zubaida shekara guda cur kenan basu ganshi ba. Shima farin cikinsa baya musaltuwa dan haka nema ya sakarwa kannensa fuska ya daina musu muzurai. Har a kwano daya suke cin abinci shi da Naja'at da Zubaida, bayan zama akan kujera daya ana wasa da dariya har yana tsokanarsu wai ina samarinsu, bayan manya-manyan leshina daya siyo musu, mamaki ya ishi Zubaida da Naja'at ganin yadda Suhaif ya sauko wanwar.
Kwanan Suhaif biyu a Kano sannan ya shirya ya ce zai je Doko ya kwana biyu. Najib ya so su je tare amma shi yanayin aikinsa na Banki ke hana shi sukuni. Wata raba har asabar da lahadi ma sai sun je banki.
Suhaif cikin dandatsetsiyar motarsa ya isa kofar gidansu na Doko. Tuni kafin ya fito daga mota matukar mamaki ya rufeshi a lokacin da ya yi ido biyu da motar Zubaida a kofar gidansu. Yana fitowa direban gidansu Zubaida ya taso da sauri ya zo ya karbi jakar hannun Suhaif gami da yi masa sannu da zuwa. Cikin fara'a Suhaif ya tambaye shi "Malam Dauda yaushe ka zo, ba dazu-dazun nan na ganka a zaune a kofar gida ba a Kano? Malam Dauda ya yi dariya ya ce "Ranka ya dade ai kana fitowa mu ma muka fito muna binka a baya, sai kayi hanyar cikin gari mu kuma muka zarto nan. Isowarmu kenan Allah Yaja zamaninka. Suhaif ya ce "Kai dawa ku kazo? Malam Dauda ya ce "Ai Hajiya Zubaida na kawo, ai da niyyar makaranta zan kaita muka fito sai kawai ta ce in kawota nan ta fasa zuwa makarantar. Suhaif ya yi shiru mamaki ya rufeshi ya yi minti biyar bai motsa ba, ya kurawa kofar gidansu ido kawai yana tunani yana tambayar zuciyarsa. "Shin me Zubaida ta zo yi Doko da rana tsaka ba tare da ta fadawa kowa ba? Kada fa a ce zancena ta zo yi, son da take yi min bata hakura ba? Malam Dauda ya katse masa tunanin da ya ke, ya ce "Ranka ya dade a shigar da jakar nan ciki? Suhaif ya yi ajiyar zuciya ya ce "Ka kai ciki ka ce musu zan je in gaishe da Hajja Kakata zan dawo yanzu. Malam Dauda ya amsa ya nufi cikin gida. Abokan Suhaif, *yan uwa da yaran unguwa suka zo suka kewaye shi suna kwasar gaisuwa gami da taya shi murnar sayen wannan dalleliyar mota. Sun cika da mamakin ganin yadda Suhaif ya zama gagarumin mai arziki a shekara guda, tare da sha'awar dama sune Suhaif ganin yadda yayi kyau yana kyalli shi da kayan jikinsa.
Suhaif baya kyamarsu, baya daga musu kai ko dan saboda yayi kudi, kamar yadda suke da, haka suke hira suna musabaha. Ko wannensu da irin nasa kokekoken da suke kawowa Suhaif. Wannan ya ce matarsa ta haihu bashi da ragon suna. wancan ya ce gidansa ya burma, katanga ta dare. Wadansu basu da na cefanu ga iyali ga yara kanana. Suhaif ya amsa musu da cewa da izinin Allah zai taimaka, amma ba yanzu ba su dawo gobe tunda yana gari har kwanaki uku. Da yawa suka shige motarsa wai zasu rakashi inda zaije. Suka dunguma suka nufi gidan Hajja. "Oh *yar Hajja ke har yanzu babu ci gaba a tattare dake balle ki waye kina nan jiya iyau. Suhaif ya fada tun kafin ya fito daga mota. Ya na fitowa daga cikin motarsa ita kuma tana kofar gida tana suyar wainar fulawa ta sayarwa. *yar Hajja ta bude baki tana kallon motar da mai motar dan bata gane shi ba har yanzu. Ta zabura ta tashi da sauri ta ce "Lah Babangida kaine? Haka ka zama? Ba'sabanba, kudi kayi? Suhaif ya tuntsire da dariya ya ce "Ni fa nasan kullum a rana sai kin ambaci kudi yafi sau dari saboda tsabar son kudinki. Ta zura cikin gida da gudu ta shaidawa Kakarta cewar ga Babangida ya zo. Suka yo waje su duka, Hajja tayi murna da ganin jikanta har da kukan dadi. Suhaif ya jawo hannun Kakarsa suka shiga gida. *yar Hajja kuwa jikinta na rawa taje ta kashe wutar wainar, tasa yara suka tayata ta shigo da kayan cikin gida. Ta fasa wainar tunda taga Babangida dole zai bata kudi, ko bai bata ba zata warta.
Bayan sun gaggaisa, Hajja tayi masa fada bai kamata ba ya tafi Lagos ya shekara guda cur bai zo gida ba ganin Iyayensa da *ya uwansa, musamman ita tsohuwa wacce ake saka mata ran mutuwa yau ko gobe. Ta bashi shawara ya rage fushi da zuciya da zafin rai irin nasa, ya yi hakuri da rayuwar duniya. An bani labarin duk yadda akayi Babanka ya koreka, amma tunda Baban naka yayi nadama yaje har Lagos din ya ce ka zo gida ai sai ka zo. Anan Mahaifiyarka take zuwa ta zauna, ita kuka ni kuka tana cewa ita Lagos din zata bika idan shekara ta cika baka zo ba.
Suhaif ya amsa laifinsa kuma yayi mata alkawarin zai yi amfani da shawarar da ta bashi. Albishir na farko daya fara fadawa Hajja shine ta shirya da ita da *yar Hajja da su za'ayi aikin HAJJI bana in Allah Ya so. Kuma idan *yar Hajja ta sami miji ayi masa magana ko tsinke kada wani ya saya shi zaiyi komai na aure. Sannan kafin su dawo daga Hajji zai sa a rushe wannan gidan nata na kasa a mayar da shi na siminti. *yar Hajja ta daka tsalle ta dira tana murna, Hajja kuwa sai ta rushe da kuka tana godiya. Nan dai Suhaif ya fito ya barsu sun rikice kamar zasu suma don murna. Da kyar ya samu ya lallashi dinbin jama'ar da suke jiransa a kofar gida sun kewaye motarsa, ya basu hakuri akan yanzu ya shigo garin amma su sameshi da daddare a gida. Ya shigo mota ya nufi gidansu. Ya iske babu motar Zubaida a kofar gidan, babu Malam Dauda da alamar sun tafi. Ya yi sallama ya shiga gidansu ya iske Mahaifiyarsu a tsaye a tsakar gida ta yafa gyale. Mahaifinsa kuwa a zaune akan kujera.
Suhaif ya tambaya "Goggo unguwa zaki je ne? Ta harareshi ta ce "Unguwa wacce iri? Ance mun ka zo tun dazu ka aiko da jakarka ban ganka ba, na leka kofar gida aka ce mun ka sake shiga mota ka tafi, shine zan fita in tambaya ina aka ga ka nufa. Babangida meyasa kake yin haka ne? Ka shekara cur ban ganka ba, sannan ka zo garin amma ka sake tafiyarka. Suhaif ya ce "Malam Dauda bai fada muku ba? Na ce ya ce muku na tafi gaishe da Hajja. Mahaifin Suhaif ya ce "Kin gani ai, na fada miki yaran yanzu basu damu da Iyayensu ba. Iyayen ne suka fi damuwa da su. Goggo ta ce "A'a Babangida ba haka yake ba, bacin rai ne yasa shi yin hakan amma da haka kawai ne ba zai shekara bai zo gida ba. Suhaif ya karkade kujera ya zauna yana sauraronsu. Bayan Goggo ta sami waje ta zauna Suhaif ya durkusa ya gaishesu. Suma abu na farko da suka fara masa fadan shine danme ya shekara bai zo gida ba. Suhaif ya basu hakuri, yasan ya yi kuskure su yafe masa.


To fa! Cafdi!! Rigiji gabji!!! Budar bakin Mahaifinsa keda wuya sai ya ballowa Suhaif wani danyen aiki. Da ya fesa masa labarin da yake tafe da Zubaida. Baba ya ce "Da kuka Zubaida ta shigo mana wiwi a zaton mu ma wani ne ya mutu a Kano. Mahaifiyarka kuwa tuni ta zata kaine kayi hatsari tunda an ce mana gaka nan zuwa. A gigice muka tare ta muna tambayarta "Waye ya mutu? Ta ce "Ba mutuwa aka yi ba, bayan mun lallasheta, ta daina kukan muka takura mata da tambaya meya faru sai take shaida mana cewar Babanta ya ce zai musu aure. Naja'at tana da saurayin da take so itama Zubaidar tana da saurayi amma bata sonshi kai take so.
Suhaif ya yi shiru ya sunkuyar da kai kasa tamkar ruwa ya cinye shi, ya kasa magana. Goggo ta ce "Ban da abun Zubaida wannan ai ba abun daga hankali ba ne, tuwo na maina. Na san kai ma zaka fi son hakan *yar uwarka, jininka. Mun ce mata ta kwantar da hanakalinta insha-Allah ba zaka koma Lagos ba sai da daurin aurenku. Suhaif ya zabura ya mike tsaye kamar cinnaka ne ya cijeshi. "A'a kai! Lafiya kake zubure-zabure kamar kayi gamo? Baba ya tambayeshi "Allah Ya kyauta "Suhaif ya fada yayin da ya dauki jakarsa ya nufi dakinsa dake zauren kofar gida ya bar Mahaifansa suna kallon-kallo.
Suhaif kwance yake akan yaloluwar katifarsa yana tunanin mafita "Kai babu mafita Zubaida tayi min da baibaiyi da sakar karfe mai wuyar tsinkawa. Wanda hakori ko wuka ba zasu iya cizgewa ba, da dai na tsumma ne, inji zuciyar Suhaif. Ba na son in auri Zubaida, ina sonta a matsayin na kanwa, bana so ta tsinci kanta a matsayin matata saboda zata wulakanta, zata sha wuya ba zata samu soyayyata ba. Tamkar GANGAR JIKINA ZA TA AURA, zuciyata da ruhina yana wajen Iman har abada. Kamar na Ramla da Haisam, Suhaif ya fada a baiyane.


Nima dai na ce GANGAR JIKINSA zata aura zuciyarsa da ruhinsa yana ga Iman.


Ehem anya ba zamu sasanta da Suhaif ya ce a aura min Zubaida a MADADInsa ba?


Reedwan Suraj Isma'il
08097365237 @watsapp




:::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI


Da daddare a tsakar gida Suhaif da Iyayensa suna cin tuwo suna hira. Baba ya sake tuntubar Suhaif da zancen Zubaida sai Suhaif yaji ya kasa kai lomar dake hannunsa bakinsa, yayi shiru bai ce komai ba. Goggo ma tasa baki suna ta yi masa nasiha, suna nuna masa alhairin hakan. Yana jin nauyi, yana jin tsoron bacin ran da zai afku a zuciyar Iyayensa idan suka ji amsar da zai fada. Amsar ita ce "A'a bana so. Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce "Ka fadi alhairi ko kayi shiru. Dan haka Suhaif ya yi shiru bai ce musu komai ba.
Yaran unguwa ake ta aikowa daga kofar gida "Wai Suhaif ya zo inji abokansa. Ya san mutanen da ya yiwa alkawari ne, suka taru a kofar gida. Ya ce da *yan aike su ce musu yana zuwa. Hajja da jikarta suka shigo da kuka, hankalin Mahaifan Suhaif ya tashi Goggo ta tare su da gudu tana tambaya "Waye ya mutu? Suhaif bai damu da yasan dalilin kukan ba, ba zai wuce godiya suka zo yi ba. Ya je ya wanke hannunsa a wajen rijiya. Hajja ta ce "Ba mutuwa aka yi ba godiya muka zo muyi, dadi ne yayi mana yawa har muka yini muna kuka. Suhaif ya tuntsire da dariya ya ce "Shegiya *yar Hajja kema har dake kukan? Bari in haskaki da fitila, na san kukan karya kike yi. Hajja ta ce "Ni na ce tayi kuka ko ba hawaye saboda wannan abun arzikin yafi karfin mu shigo ba kuka. Suhaif ya kwashe da dariya yayi ta dariya har cikinsa yayi ciwo, ya fice kofar gida wajen abokansa, bayan ya shiga dakinsa ya ciko aljihunsa da kudin da zai raba musu. Hajja ta mike kafa ta zaiyana musu abun arzikin da Suhaif yayi musu alkawari. Iyayensa su ka ce su basu ma sani ba, bai fada musu ba. Sun ji dadi sosai har fiye da Hajja da jikarta, yau ga dansu ya zama mutum yana abun alkhairi da dukiyarsa. Suka hadu suna ta shi masa albarka.
Suhaif bai dawo gida ba sai da misalin sha daya na dare. Shi da abokansa sun nutsa cikin gari gaishe-gaishen *yan uwa da abokan arziki da aka dade ba'a haduba. Har Garki suka je wajen Babbar yayar Mahaifinsa Iya Furera. Itama ta yi masa kukan danta zai yi aure kuma bashi da kudin hada lefe. Suhaif ya yi alkawari zai hado masa lefen. Ya dauko kudi mai tsoka ya bata, tayi murna sosai. Lokacin da Suhaif ya dawo gida Iyayensa har sun kwanta, su Hajja sun tafi gida tuni, ya rufe kofar gida ya shiga dakinsa ya kwanta. Bacci ya gagari idanuwansa yana ta kwatanto Zubaida a matsayin matarsa, ya ga ko zai hakura, ya danne zuciyarsa ya aureta, sai ya ga ina! Bazai iya ba, Iman ce har yau a cikin lissafinsa. Gashi babu Iman amma ya kasa hakura ya auri wata, ba Zubaida kawai ba *yan mata da yawa suna sonsa amma ya kasa sonsu.
Manyan dalilan shine duk wadanda yake haduwa dasu basu da nutsuwa da halaye irin na Iman, ko kusa bai taba samun mace mai hankali da biyayya irin na Iman ba. Ya sha daurewa zuciyarsa ya fara zuwa zance gidajen *yan matan da suke rokarsa ya je amma idan yaje sau daya, sau biyu baya komawa na ukun. Saboda *yan boko ne, yanzu wayewa ce ba'ajin kunyar saurayi sai su saki jiki da saurayi kamar mijinsu. Daga zuwa zance wata budurwa ta tubure masa wai sai ta bashi abinci a baki. Tun daga ranar ya rabu da ita. Wata kuwa daya gwada zuwa gidansu, da gyale a jikinta da ta ganshi sai ta cire tasa matsattsan kaya. Wannan rashin kamun kan ne yasa ya barta, don ba haka Iman dinsa take ba. Daga karshe ya hadu da mai saka hijabi har kasa kamar Iman, har ya fara murna ya samu mai hali irin na Iman. Ashe hijabin ne iri daya ba zuciyarsu daya ba. Sun yi watanni tare har yana saka ran zai yi maganar aure da manya a rashin Iman. Wata rana yayi mata zuwan bazata gidan da ake rikonta, gidan yayarta. Ya isketa da kananan kaya (english wares) matsattsu. Tana zance da wani dan caburos har yana kai hannu yana taba ta. Tana ganin Suhaif kafin ta iya motsi ya shiga mota yayi tafiyarsa. Tasha kuka tasan ta rasa Suhaif, daman hijabin yaudara ne, ta lura yana zon mace mai hijab shine take yaudararsa da hijab. A zamanin nan ina zan samu mace kamila mai tsoron Allah irin Iman? Suhaif ya fada yayin da hawaye yayi masa kawanya yana kwance.
Washe gari misalin karfe goma na safe, bayan Suhaif yayi wanka ya fito tsakar gida ya gaishe da Iyayansa. Bayan Goggo ta bashi koko yana sha sai ta dube shi sosai taga idanuwansa a kunbure suke. Ta tambaye shi, "Babangida kuka kayi, ko kuwa rashin bacci ne idanuwanka suka kunbura? Suhaif yayi murmushi bai ce komai ba. Goggo ta dauko masa zancen abun arziki da ya yiwa Hajja Mahaifiyarta. Tayi ta shi masa albarka, ta ce ya ci gaba da taimako irin wannan. Amma ya kamata ya dinga samunta ko Mahaifinsa yana fada musu abun alherin da ya yiwa wani ko neman shawararsu akan abunda yake so ya bawa wani domin ya kamata su sani kar a zo yi musu godiya su hau zare idanu basu san akan me ake yi musu godiya ba. Suhaif ya amsa mata da "To daman gani nayi saboda Allah na yi, shiyasa ban fadawa kowaba' Mahaifinsa ya ce "Haka ne, amma mu dai ya kamata ka fada mana.
Suhaif ya shaida musu yana so ya biya musu Makka amma yaga Baba na Kano ya biya musu waccan shekarar sai yayi tunanin ya rushe gidan nan ya sake gina musu na siminti, na zamani. Amma yaya suka gani? Suka ce haka yayi tunda sunje Hajji wancan shekarar ya musu gyaran. Baba ya ce "Kafin ka fara yi mana gini na fi son ka bani kudin da zanyi noma sosai wannan shekarar in dauki ma'aikata, in sayi takin zamani da magungunan kwari. Goggo ma ta ce jari take so ya bata tana so ta dinga saro atamfofi daga Kano tana rabawa ma'aikata. Suhaif ya ce "Duk mai sauki ne zan baku kafin in tafi.
Baba ya gyara zama ya sake dauko zancensa da Zubaida, ya ce "Muna magana tun jiya ka ki cewa komai ka barmu muna bolokoko mu kadai. Ni yanzu da ka ganni Kano zan je ko in aikeka Kanon ka kiramin Usman Mahaifin Zubaida, mu zo a hadu da Mahaifiyarka da Yaya Furera ta Garki a yi magana. Suhaif ya yi caraf ya ce "Baba ya kamata ku gane abun da nake nufi, tunda amsar da zan baku ta yi min nauyi a bakina, na kasa ce muku a'a bana so. Dan Allah Baba ku yi hakuri ku bar zancena da Zubaida. "Sai wa kake so ka aura tunda baka son *yar uwarka? Baba ya tambayi Suhaif a shelake. Suhaif ya ce "Babu wacce nake so takamaimai, amma ina gudun a bani *yar uwata in zo in wulakantata. Goggo ta ce "Kai Babangida kaji tsoron Allah, har ka iya kallon idanuwanmu ka ce baka son Zubaida. To kar ka sake ka dubi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login