Showing 51001 words to 54000 words out of 110329 words

Chapter 18 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt

22 Feb 2025

7474

da binciken Jakata ina zulumin yau me zan cewa likitan nan, bani da kudin da zan biya shi wannan uban aikin da yayi min, sai na ji na lalubo sarkata ta gwal a cikin aljihun jakata na laluba kunnena na ji dankunnen sarkar a kunnena, zoben a yatsana da awarwaron gwal guda biyu a hannuna. Naga sarkar babbace sosai bazan iya bashi ba, awarwarayen ma sunyi girma sai nayi tunani in cire *yan kunnayen da zoben in bashi matsayin kudin aikinsa tunda bani da kudi. Shi dai yana tsaye yana kallona, na cire *yan kunnaye da zoben na dubeshi na dukar da kai kasa cikin ladabi da fargaba na ce "Likita na duba jakata ashe ban taho da kudi ba, ga dan kunnena da zobena na gwal ka karba a madadin kudin aikinka. Sai naji ya bushe da dariya ya ce "*Yan mata yaya sunanki? Na amsa masa cike da fargaba "Sunana Fatima. "Fatima, Fatima is a nice name, I like this name, Fatima is my Mother's name. Na ce "Na gode, ya ce "Fatima me yasa kikayi tunani bari ki bani gwal dinki a madadin kudin aikina, baki yi tunanin zan iya yi miki kyauta ba? Nayi murmushin karfin hali. Yaci gaba da cewa "Saka dan kunnanki da zobanki, karki damu nayi miki komai kyauta sai dai kamar yadda kika yi alkawarin zaki je ki kira wata babba ku zo tare ina jiranku kafin nan zuwa lokacin da zan tashi. Ina fatan zaku zo? Na amsa masa da "Eh yanzu zan je in kirata. Ya sake dubana cike da murmushi ya ce "Fatima zaki gaya min gaskiya game da jaririn nan, da inda kika samo shi? Domin kinyi kankanta ace danki ne wannan, baki yi kama da wacce ta haihu ba. Kiyi min alkawari zaki fada min komai harda sauran tarihin rayuwarki? Na amsa masa da "Eh nayi alkawari. Maganarsa ta karshe ita ce "Thank you very much my dear. Yayin daya ci gaba da kallona yana murmushi, na sunkuyar da kai kasa na fara tafiya, shi kuma ya fito bakin kofar dakin yana kallona ina tafiya.
Kamar daga sama naji an kira sunana na tsaya cak na waiga sai naga likitan ne yake kirana. Na juya na dawo inda yake a tsaye. Yayi min murmushi wanda ko bai min bayani ba nasan ma'anar murmushin. Wannan karon cikin harshen Fulatanci ba Hausa ba da Turancin da muke nagana tun dazu, ya ce "Baki tambayeni sunana ba. Nima cikin harshen na ce "To yaya sunanka? Ya ce "Dr. Hani. Nayi murmushi mai wuyar fita na ce "Dr. Hani na gode. Na juya naci gaba da tafiya bai bar wajen ba har sai da ya daina hango ni na fita daga get din asibitin. Ina fita na kalli gabas da yamma, kudu da arewa bansan ta ina zan fara ba, ina zan dosa? Meye abun yi? Ina mafita? Na farko bani da kudin achabar da zan koma gida, na biyu babu yadda za'ayi in je in kirawa Dr. Hani Mahaifiyata yayi mata bayani akan matsalar yarona, don ita kanta taki tsayawa taji gaskiyar al'amari akan yaron, haka daga ranar data gasgata bani nahaifi yaron nan ba to lallai dole in mayar da shi inda na dauko shi, ni kuma ina sonsa kamar raina. Don haka Dr. Hani zai tsufa yana jirana ba zai ganni ba. Sai babbar matsalata ta uku zancen aurena da Micheal da ya karato, ana zancan sati mai zuwa za'a zo da danginsa a zauna akan maganar auran. Sai naji zuciyata ta cushe na rasa me yake min dadi. Sai na rushe da kuka ina tafiya ina kuka. Na yanki hanyar cikin gari ba unguwar mu ba, bansan in da na nufa ba.


Nayi tafiya na gaji likis yaron dake bayana ya gaji da tsotsar hannun, ya gaji da mutsu-mutsu yunwar da ta fara masa illa. Sai ya fara rusa kuka tamkar an zuba masa ruwan zafi. Da sauri na karasa gindin wata bishiya mai inuwa mai sanyi, na kwanto goyon na zauna a karkashin bishiyar na fara jijjigashi. Baya jin lallashin da nake yi masa tamkar tunzura shi nake, shi dai kawai nono ko madara yake lalube. Dole yaji yunwa tun madarar sassafe da na bashi da karfe shida da rabi, har yanzu karfe sha biyun rana. Na rasa abinda yake damuna, na rasa yadda zanyi. Yara *yan makarantar Islamiyya ne suke wucewa an tasosu. Yara kanana guda biyu *yan gida daya mace da namiji, macence babba *yar kimanin shekaru shidda, kaninta dan kimanin shekaru hudu, masu kama daya suka tsaya suna kallon Jaririna yana tsala kuka. Cikin gigicewa da harshen Fulatansi na ce dasu "Kuzo ku yiwa kaninku wasa. Yaran dama haka suke so in ce, sai suka karaso inda nake suka fara yi masa wasa suna shafa kumatunsa. Cikin ikon Allah sai ya fara tsagaitawa da kukan yana kallon yara *yan uwansa. Macen ta ce "Ki bashi nono mana. Nayi murmushi na ce "Yasha nono yanzu. Sai karamin yaron ya ce "Ki bashi ruwa ya sha sai na ce "Bani da ruwa. Ya ce "Ga fanfo nan kusa dake. Ya nuna min gefena. Farin ciki ya kamani na tashi da sauri naje na bude fanfo ina debo ruwa a hannuna ina tarfa masa a baki, sai sha yake kamar wanda ya kai azumi. Yaron ya zo inda nake ya miko min kofin robar ruwansa dake rataye a kafadarsa ya ce "Ga shi ki bashi da kofina. Na karbe cike da murna na ce "Yauwa kana son kanin nan naka ko? Na tari ruwa, na tallafo kansa sosai don karya kware, kamar yadda likita ya kwatantamin na bashi ruwa yasha da yawa. Nima kishir ruwar nake ji, na sha ruwan yayi kofi uku sannan na bashi dan kofinsa. Muka dawo muka zauna a gindin bishiyar tare da yaran suna ta yiwa Jaririna wasa. Ya fara dariya da alama daman kishir ruwan yafi damunsa, da ya sha ruwan sai ya manta da yunwar. Iska mai sanyi tana kadamu.
Na dubi yaran na ce "Yaya sunanku? Babbar ta ce "Sunana Aisha, kanina kuma Abubakar sunansa. Na tambayesu ina gidan ku? Sai suka nuna min da hannu babu nisa da inda muke zaune. Gida ne lafiyayye na zamani, an zagaye gidan da kayatattun faulawowi da bishiyoyi, ba a zagaye da katanga ba ko waya. Farfajiyar gidan abude take har kofar da zata kaika falonsu. Naci gaba da tambayarsu ina babansu da Mamansu? Suka bani amsa, "Mamar su ta tafi Islamiyya itama, Babansu ya tafi aiki. Na tambayesu suna da yayye ko kanne? Suka ce su biyu ne kawai a gidansu. Na tambayesu ko suna makarantar boko? Suka ce eh suna zuwa, hutu suke yi yanzu. Daga nan nayi shiru, na shiga yiwa Jaririna sha'awar dama ace shine su Abubakar da uwarsu da ubansu, suje makarantar Islamiyya su je ta boko gata kan gata. Sai hawaye ya sirnano min ina fargaba ina tausayin yadda rayuwarmu zata kasance ni da shi.
Kamar daga sama Aisha ta katse tunanin da na ke ta ce "Aunty yaya sunan danki? Nayi duuum na ce "Sunansa Muhammad. Sai suka fara yi masa waka da fulatanci ta yabon Annabi Muhammad (S.A.W) wakar mai dadi, nayi shiru ina sauraransu. Kwatsam naji wani tunani ya fadomin a cikin zuciyata wanda ni kadai sai dana firgita. Zuciyata ta ce "Fatima mai zai hana ki kai yaron nan gidan su yaran nan ki ajiyeshi ki gudu ki barshi, ya girma ya tashi a Musulmai cikin gata. Idan baki kaishi inda zai tashi a Musulmi ba daga karshe dole Micheal zai dauki dansa ya tafi da shi ya tashi a tsakiyar arna cikin *yan fashi, kilama ya gaji ubansa ya tashi ya zama gawurtaccen dan fashi. Sai naji na hau karkarwa hankalina ya kara tashi yaya za'ayi in ajiye yaro in tafi, ai bazan iya rayuwa babu shi ba. Na sake yin tunani idan ban ajiyeshi ba rayuwata da rayuwar yaron tana cikin hatsari, don karshe dole mu koma hannun Micheal sai yadda Allah Ya yi damu. Kuma daman batun Musulunci kuwa babu shi. Na yi ta tunani, karshe na yanke shawarar dole mu rabu da jaririna in ajiyeshi a gidan Musulmai ya tashi a Musulmi. Tunda *yan gidanmu sun dauka ya mutu sai in barsau a ya mutun na bar gawar a asibiti za'a binne. Sannan ni kuma in yi ta kaina.
Na dubi Aisha wacce tana tayi wa Jaririna wasa na ce da ita "A kwai littafi da fensir a jakarki? Ta ce "Akwai. Na ce "Bani *yar takarda in yi rubutu. Ta miko min jakar gaba daya na bude na falli tsakiyar takardar na rubuta kamar haka "Sunana MOHAMMAD. Ni Musulmi ne, ku rike ni dan Allah. Na ciro *yan kunnayena da awarwarayena da sarkata na gwal na zuba a cikin takardar na nade. Na ce da su "Kunce gidanku babu kowa yanzu ko? Suka ce "Ba kowa sai mai aikinmu Barira. Na tambayesu yarinya ce ko babba ce? Suka ce yarinya ce. Na ce "To ku tashi kuje gida nima zan tafi gida. Abubakar ya bata rai ya ce "Da Mohammad zaki tafi? Na ce "Dashi zan tafi ko in bar muku? Suka hada baki "Aunty ki bar mana Muhammad kaninmu tun da bamu da kani. Na ji dadi a raina, har na hasko Mohammad ya girma a gidan, ya tashi cikin gata ai kuwa kowa zaice kaninsu ne na jini, domin yana kama dasu farare masu dogon hanci.
Na ce "To muje gidanku in ajiye muku shi kun ga kun sami dan kani. Idan Mamarku ta dawo kuce ta rikeshi, karku yadda akaishi wani wajen. Na nuna masu gwala-gwalan nan na ce "Wannan gwala-gwalan ku cewa Mamarku ta siyar ta dinga siyawa Mohammad madara yana sha tunda Mamarsa ta mutu, ni ba Mamarsa ba ce babu mai bashi nono. Suna tsalle suna murna suka amsamin to to. Muka dunguma muka tafi gidansu. Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, na dinga waige-waige kar wani ya ganni ina ta zare ido ina fargaba.
Muka isa kofar falonsu, zasu kwan kwasa na ce karsu kwan-kwasa mu zauna akan barandar mu huta kafin Mamarsu ta dawo daga Makaranta. Suka shaida mun mai aikinsu tana ciki ita kadai tana bacci, daman yawanci idan sun taso sai suyi ta bugun duniyar nan bata jiba har sai Mamarsu ta dawo ta iske su anan, sannan ta zagaya ta kwalla mata kira ta wundon dakinta. Na ce "Ba komai yanzu ma su bari idan Mamarsu ta dawo sai su shiga ciki. Na dan taya su zama cike da fargaba suna min hira bana fahimtar me suke cewa, na rungume jaririna tsam. Wani kuka mai radadi ya keto min babu yadda na iya na kwantar da shi a gabansu suna yi masa wasa, na dauko takardar da na rubuta sunansa na nade gwalagwalan nan nawa na ajiye a gefensa cikin zanin goyansa, ya tsaya yana kallona kamar yasan rabuwa zamu yi. Ni ma na dade ina kallansa, nayi karfin hali nayi masa wasa, sai kuwa yayi min dariya ni kuwa na fashe da kuka. Aisha da Abubakar suka hau murna suna cewa "Lah yana dariya, ba tare da sun kula da kukan da nake sharba ba.
Na juya zan tafi Abubakar ya ce "Kin bar mana shi da gaske? Na ce "Na bar mu ku shi. Ba kunce kuna son kani ba? Suka hau murna da tsalle. Na juya na tafi ba tare da na iya sake waiwayowa ba.
Na koma gindin bishiyar da muka zauna dazu, na kalli gabas da yamma naga babu kowa caraf na haye kan bishiyar nayi luf a cikin ganye ina hango abinda zai faru ga jaririna. Ba dadewa na hango Mahaifiyarsu Abubakar ta dawo daga Islamiyya a motarta. Shigarta ba dadewa naga ta fito ta kira wani saurayi tayi masa magana. Saurayin a gigice cikin sauri ya zo ya wuce ta gabana ya nufi makarantar Islamiyyar su Abubakar da Aisha da yake babu nisa. Ba jimawa sai ga saurayin da manyan dattijai da alama Malaman makarantar Islamiyyar ne da Limamin Masallacin unguwar da *yan unguwa masu salla a masallacin da yake jikin Islamiyyar ya kirasu ya shaida musu abun dana aikata na an tsinci Jariri. Suka zo suka wuce ta karkashin bishiyar dana labe ba tare da sun ganni ba, ina hangensu sun zagayeshi ana ta mamaki da shawarwari. Musamman ganin gwal din nan, sun tabbatar ba talauci bane, ko cikin shege yasa aka yasar da yaron. Uwa uba ga sunan yaron an rubuta har an kara da cewa Musulmi ne ku rikeni dan Allah. Sai suka kawar da zancen a kai shi gidan marayu ba a san baiwar da Allah Ya yi masa ba, gara a sami wani ya rike shi a cikin su, nan dai aka yi ta fafata shawarwari. Mahaifiyar Aisha aka tambaya ko tana so ta rike tunda a kofar gidanta aka tsinta? Ta ce "A'a baza ta rike ba, bata san ko wanne irin da ba ne. Jama'a da yawa suna so su dauka watakila kwadayin gwal ne, ko kuma da man suna son da ne ban sani ba.
Wani dattijan Malami shike rungume da Mohammad suka ce su tafi dashi Masallaci aci gaba da shawara. Sun juya zasu tafi sai Aisha da Abubakar suka ce basu san zance ba, kaninsu ne, su aka bawa kuma Mamar Jaririn ta ce ya zauna a gidansu ta basu shi. Haka suke ihu suna birgima ba za'a tafi dashi ba. Hankalin Mahaifiyarsu ya tashi sosai ta shiga kokwanto, ta yi lallashin duniyar nan yara suka ki sun tubure, daga karshe ta musu duka amma basu hakura ba, suka bi wadanda zasu tafi da Mohammad da gudu suna cewa a dawo musu da kaninsu. Dai-dai karkashin biyar da nake, nan suka sake tsayawa suna shawara, Mahaifiyar su Abubakar ta ce kar ayi saurin yanke hukunci inda za'a kai yaron ayi mata hakuri zuwa yamma mai gidanta ya dawo, ta tambayeshi idan ya yarda sai ta karbi dan ta rike, saboda Allah kadai Ya san dalilin da yasa aka wuce kowanne gida aka ajiye mata a kofar gidanta, ga yaranta suna sonsa. A haka aka tsayar da shawara, ta ja hannun yaranta suka nufi gida. Su kuma dattijai suka tafi da yaron Masallaci. Aisha da Abubakar suna rafsa kuka suna kiran Muhammad dinmu. Ina kan bishiya ina rafsa kuka ina "Nuhammad dina. Yanzu na rabu da kai har abada kenan? Na yi fiye da awa biyu a zaune ban sake jin motsin kowa ba. Na sauko daga kan bishiyar na nufi Masallaci don in ga halin da yake ciki, ina ta zagaye ina leke-leke, babu alamar yaro ko zancen yaro duk wadanda suke ciki ibadarsu suke. A kayi sallar la'asar, aka kira Magruba ina ta kai kawo a wajen. Na dawo kusa da gidan su Aisha inga ko Mahaifinsu ya dawo inji hukuncin da aka yanke, sai na iske ya dawo, ya dauro alwala ya zo ya wuce ni ya shiga Masallaci suka yi sallar magaruba ya fito ya nufi gidansa babu wanda ya tsayar dashi yayi masa zancen an tsinci Jariri a kofar gidanka, haka bai tambayi kowa ba ina Jaririn da aka tsinta dazu a gidana, ya shigewarsa gidansa ya mayar da kofa ya rufe. Gari yayi duhu kirin, kowa na gidansa sai mutane kadan a Masallaci, in takaice muku ina wajan akayi sallar Isha'i, aka gama karatu aka rufe Masallaci kowa ya kama gabansa, babu zancen dana. Nayi kuka har na gaji, hankalina ya tashi dan ban san halin da yake ciki ba, nayi dana sanin ajiye shi, haka na kama hanyar gidanmu da kafa, ga uban nisa ga kishir ruwa da yunwa da tashi hankali.


Allah Ya tsaremu daga shiga kuncin rayuwa, wadan da suke ciki Allah Ya fitar da su da girman zatinSa da ikonSa. Ameen.


Reedwan Suraj Isma'il




*************** YAREANA ADDININA
___CIGABAN LABARI


Na isa gidanmu da misalin karfe tara na dare, ina shiga na dora hannu aka na kurma kukan mutuwa a falonmu. Mama Tabita da Mahaifiyata suna kicin suka fito da gudu, Mahaifina da ya tafi nemana asibitoci kala-kala sai yanzu ya dawo a gajiye. Suka taru akaina suna tambayata lafiya? Cikin kuka na shaida musu Jaririna ya mutu an binne shi a asibiti. Daga dukkan alamu sun tausaya min su duka, suna bani baki inyi hakuri dama sun gaya min ya mutu na dauki gawa na kai asibiti. Ban daina kuka ba kamar zuga ni ma suke yi. Dole Mahaifiyata ta zaunar dani ta zuba min abinci da ruwa ta ce sai naci. Ci nake amma ban san dandanon abincin ba tamkar dusa nake cusawa ba abinci ba.
Ranar Mahaifiyata ta nutsu ta tsaya tayi min nasiha a tsanake yadda rayuwa take, ta ce kada in kuskura in sake bari rayuwa ta subuce min in shiga halin kakanikayi da nadama. Amma daga karshe ta fara cusa min addininta da aurena da Micheal. In da na dauke hankali daga sauraron abunda take cewa dan ba zai yuba. Sai a lokacin Mahaifina ya sa baki ya ce "Tunda danta ya mutu ai kuwa babu zancan auranta da Micheal, babu mai yiwa *yar sa aure tana da shekaru goma sha biyar. Sabon Adimission zai samar min in fara karatu. Ita kuwa Mahaifiyata bata yadda ba wai dole in auri Micheal sai inyi karatu a gidansa. Nan fa ta mike ta fara zuba masifa da yare kala-kala, duk hakurin Mahaifina bai cike biye mata ba idan tana fada irin wannan, amma yau ya biye mata har ma ya fita bugun kirji da jajircewa yana nan akan bakarsa babu mai yiwa *yarsa aure karatu zata yi. Kamar zasu tsagamin kunne saboda daga murya. Na tashi dakyar saboda tsananin ciwan kai da damuwar dake damuna, na shiga dakina na zube kan katifa sharaf. Tunda na kwanta ban sake farkawa ba haka ban sake jin ko kalma daya ba ta maganganun da suke don haka nake tunanin ba barci nayi ba sai dai idan suma nayi, domin yafi barci nauyi. Ban farka ba sai sanda agogon dakina ya buga karfe ukun dare daidai. Nayi karfin hali zan tashi zaune sai na koma yaraf na kwanta. A lokacin wani barci mai nauyi ya daukeni na dora da wani mafarki wanda ban taba yin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login