Showing 36001 words to 39000 words out of 110329 words

Chapter 13 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt

22 Feb 2025

7478

tare, na kara miki zan baki dubu goma. Na zazzare ido don mamaki na fada a bayyane na ce "Dubu goma? Yasa hannu cikin wata *yar jakar hannunsa wato (brief case) ya zaro bandir din Naira dubu goma ya mikomin, na karbi kudin nan ina jujjuyawa don mamaki, murna ta kamani. Na ce a raina "Na sami kudin da zanje in biya Malamina su bani sakamakon Jarabawata sannan inyi kudin mota in koma gida. Nasa kudin a jakata. Ya jawo hannuna nazo na zauna a kusa dashi. Yasa hannu zai shafa wuyana sai naji maganar Hamma Huzaifa a karkashin zuciyata. "Kada kiyi zina, kiji tsoron Allah duk inda kike ko ina kika shiga kika buya Allah na ganinki. Saina zabura na mike tsaye na ce "Malam yi hakuri bude mun kofa tafiya zanyi bazan iya ba. Na bude jakata na dauko masa kudinsa na ajiye masa a gefensa. Ya bude baki yana kallona. Yace "Me yasa? Na ce "Kawai bazan iya ba, ina tsoron Ubangijina bazan iya zina ba. Ya kyalkyale da dariya ya ce "Ko ki karbi kudina ko karki karba babu yadda za'ayi in yadda ki subuce min gara ki tsaya in miki a hankali kafin inyi miki da karfi.
Na rataya jakata na nufi kofar fita, daman da mukullin a jikin kofar zan murda in bude, sai naji cimak an daukeni ta baya sai naji ni a tsakiyar gado yana shirin ya afkamin. Naji raina ya fara tafasa don tsananin bacin rai, nan da nan na rasa hayyacina, muyagun dake jikina suka tashi. Na lalubo wata katuwar kwalbar lemo dake ajiye a gefen gadon na rotsa masa akai. Ko sakon daya ba'a kara ba jini yayi masa hijabi a fuska. Ya rike kai sai ihu yake zanbadawa. Na yar da jakata da takalmi na bude kofa zan fita da gudu naci karo da jama'ar da suka jiyo ihunsa suka rugo suga meke faruwa. Caraf suka damkeni. Suna lekawa cikin dakin suka ganshi cikin jini. Suna kokarin yimin duka abinka da ba yin kaina ba naji na fara zubar da kartai a kasa suka sakeni ba shiri na arce waje na fita daga hotel din da gudu.
Harriet ma da nata saurayin dai-dai lokacin ya gaggalla mata mari ya kwace kudinsa ya tunkudota waje daga daki saboda ya tarad da ita da rusheshen ciki, itama ta lallabo ta fito waje. Janet itama dakyar tasha da nata yaga abunda nayi saiya korota ba tare daya bata ko kobo ba, da dabara da haure-haure ta fito daga hotel din ance sai an daketa tunda tare muke. A gida muka hadu wannan na shigowa sai kaga waccen itama ta shigo a guje a galabaice.
Ranar naga tashin hankali a wajen kawayena zagi da dungure kai nasha, wai duk ni nake jawo musu masifa. Har wayau basu daddara ba washegari suka sani dole na shirya muka fita amma muka canja hotel. Aka sake kwatawa duk yawan kudin da zasu bani bana iya yarda inyi zina domin tsoron Allah ya shigeni tun ina karama, Hamma Huzaifa ya cusa mun haka a raina. Allahu akbar Allah Yayi masa albarka ya sami ladana ta wannan bangaran. Ga tsananin bukatar kudi ina yi amma tsoron Allah ya hanani in aikata sabon Allah in sami kudi. Su kuma mazan idan naki yarda da su sai su kasa hakura dani su yi kokarin zasu yimin ta karfi daga nan san hankalina ya gushe raina ya baci in fita hayyacina in farfasa musu kai. Don barnar da nake musu ta yau tafi ta jiya, ta gata tafi ta citta kullum mune a guje an biyomu na fasawa maza kai, laifina yana shafar kawayena. Da kansu suka hanani binsu suka sha zagina suka ce sai in zauna a gida na dinga dafa musu abinci tunda haka nake so. Tafi nono fari daman haka nafi so.
Haka na kasance duk sanda zasu tafi su bani kudin cefane su zano mun abubuwan da suke so in suyo in dafa musu. Jikina yana rawa nake karbar kudin cefanen in hau achaba inje kasuwar Wunti ko Mudalawan da ke nan Bauchi in sissiyo in dawo. Da murhu da itace in dafa musu abinci idan da daddare suka fita to da sassafe nake dafa musu abinci kafin su karaso, idan kuma fitar yamma suka yi kafin dare na kare musu girkin dare. Duk da ba sabawa nayi da aiki ba, girkin ma ban iyaba balle hura wuta haka nake daddagulawa ina yi ina rugawa da gudu wani gida dake kusa damu ina tambayar matar gidan yadda zanyi kafin in kare girkin duk nayi wujiga-wujiga na fita hayyacina. Hawaye, majina, gumi, bakintukunya a rigata kaca-kaca. Amma duk da wahalar nan basa godewa, Janet ma saita yi fada da zage-zage kafin ta fara cin abincin. Ni dai hakuri nake basu don kar suyi fushi suce sun daina bani kudin cefane nima in fita in nemo.


Wata rana da yamma ina ta riki-riki da itace da tukunya sun hadani da babban aiki wai tuwan shinkafa miyar taushe suke so. Ina gudun bacin ransu sai ban fada musu cewar ban iya ba fargaba ta isheni bansan yadda zan hada miyar taushe ba, ga dai kayan taushe reras na cefano. Na dora ruwan zafi ya tafasa na wanke shinkafar tuwo na zuba tana ta dahuwa.


Daya daga cikin kawayenmu da muka saba a sanadiyar abokan Micheal wato Fadila dadiron Gibrel ce abokin Micheal a gidan Gibriel din take din-din-din ya tsare mata ci da sha da sutura. Ya saka mata takun-kumin fita wajen wasu mazan. Amma abunka da ba maganar Allah ba, zama ne na sabon Allah tana satar jiki ta fita ta hole da wasu mazan idan yayi tafiya. Ran da aka sami akasi ya dawo bai isketa a gida ba to fa ranar saiya fasa mata wani wajen ajikinta don duka. "Excuse. Sallamar arna tayi min. Na daga ido na dubi me shigowa duk da boy's quater a wangale take babu zaure ba tsakar gida don ba'a zagaye da katanga ba ko zana a fili muke wangal sai dakuna biyu a jejjere da dan karamin bandaki a tsurkukin kicin. A filin bakin kofar dakin nake girki. Ina zaune akan wani katan bulo na saka rigar aiki iya gwiwa. Hayaki ya cika mun ido sai hawaye nake shar-shar.
Na tashi da sauri na rungume Fadila don munyi wata guda bamu hadu ba tun muna gidan Micheal.


Wa'iyazu billah,,,, Allah dan girman Ka da tsarkin Mulkin Ka, Ka tsaremu daga rayuwar bariki. Allah Ka da Ka sanyamu a jerin ta6a66u duniya da lahira.


Uhmm gaskiya ni bana son Iman din ma,,,, cikin biyu za'ai daya ko Naja'at ko kuma Zubaida ehe......


@watsapp__ 08097365237




YARENA, ADDININA.....


CIGABAN LABARIN
Na tsashi da murna na rungume Fadila don munyi wata hudu bamu hadu ba tun muna gidan Micheal.
Amma tunda muka dawo nan bata zoba. Sai a
ranar tazo shima da tambaya ta samu gidan.
Nadauko mata tabarmar kwanciyata daga daki
nazo na shimfida mata a gefe yadda hayaki bazai
dameta ba nace ta zauna. Amma fadila ta kasa
zama, tayi tsaye kawai tana kalle-kalle gidan da muke zaune. Ta dubi ko ina harda daga labulen
kofar dakin da mukayi da zani ta leka dakin sai
girgiza kai take ta juyo tadubeni cike da tausayi
tace "cafdijam pretty haka kuka zama? Yanzu
kune acikin gidan nan haka harsu janet da harriet
agidan suke zaune haka?' Na sun kuyar dakaina kasa na kasa bata amsa. Taje tazauna a tabarmar
dana shimfida mata nan ma kafinta zauna saida ta
karkade tana wani yatsuna kamar wacce zata
zauna akan kashi. Kirjinta da kunnuwanta da
yatsun hannunta da hannuwanta da kafarta
tsadaddu. Kanta babu dankwali anyi gyaran gashi a saloon anyi karin gashi har baya an zubo
dashi, sai kamshi da kyallin mai. Nace "Gabrel
yana sakar maki kudi fadila.' Nafada mata haka
yayinda nake dubanta ina murmushi. Nanfa
tahau feleke tana wata kwalmada tana iyayi
daman gwanace awajen feleke. ita ta koyamun hausa na iya magana da hausa sosai domin ita
bahaushiya ce gaba da baya kuma musulma
bakatsiniya. Tace "wai dan kinga nasa gold aiba
komai kika ganiba pretty. Gibrel fa ya bude mun
account yana zuba mun kudi sannan duk sanda
yaje lagos zai suyo mun kayan tsukewa da leshina. Idan yayi tafiya infita inje wajen wasu
mazan duk haka muke dani da kawayena su
Ngozi. Wallahi pretty bakida wayo bakima san
abunda kikeyiba. Koda yake yarinta na damunki
gaki kuma 'yar fari. Micheal fayafi su Gibrel kudi
da kika kwantar da hankalinki da kinji dadin rayuwarki. Naji labarin abunda ya faru kinban
kunya ko tsoron harriet kike? Danshi fa ba sonta
yake ba ita take sonsa shike yake SO duk mun
san abunda yake faruwa. jiya ma har karfe dayan
dare yakai a gidan da nake yana baiyana mun
har yanzu yana sonki ki yarda dashi, zai canza miki rayuwarki. Harriet din banza inhar kin yadda
zai kaiki gidan dako get din gidan su harriet baza
su iya tabawa ba balle su shiga suyi miki wani
abu. Yace ashiye yake ya kashe miki duk abunda
ya mallaka don shi arayuwarsa bai taba jin
yarinya da yaji yana kauna ba kamarki." ta dafa kafadata tace "haba kawata dubeki yadda kika
zama duk kinyi duhu. Wannan gashi naki har
baya kamar na turawa duk ya cukurkude kodan
mai bakya shafawa. Da yar gayu dake, kala ce sai
an wanke hannu kafin a tabaki yanzu kin zama
kamar bola. Wai girki da murhun itace haba pretty kinci baya. Garaki shigo bariki kiji dadin rayuwa
hajiyata. "NA fisge kafadata natashi daga kusa da
ita ina girgiza kai, kallo daya tayi min tasan ta bani
haushi, raina ya baci sosai. Najuya na dubeta
nace" fadila ki kularmin da abincin nan zanje cikin
ginin can yanzu zan dawo.' Na nuna mata wani tsohon ginin benen da ba'a kareshi ba, babu
kowa a cikin. Ta harareni tace 'me zakiyi aciki? To
gaskiya kiyi sauri idan baki dawo da wuriba zaki
tarar bana nan, donni ban saba girki a gas cooker
bama balle murhu kece dai wahalalliya.' Nayi
murmushi nace "yanzu zan dawo bazan dadeba." nadauki buta natafi kamar tafiyata da minti goma
nadawo. Fadila takalleni awalakance tace 'oh
kashima bakuda wajenyi sai kun shiga kwango?
Gaskiya pretty kin shiga uku. To in fada miki
gaskiya kece abar tausayi don jannet har yanzu
tana tareda solomon abokin micheal kudi sosai take samu shiyasa bata cika kwana anan gidan
ba kawai tana ciyar dake don ki kulada kawarta
harriet wacce tadauko ciki ba zata iya fantamawa
ba. Amma da harriet garau take bazasu yarda su
zauna dake a gidan nan ba. Ke kuma wawuya kin
tauye rayuwarki kin kunshe anan ki taho kawai ki biyoni. Nida nice da kyau irin naki daba saina
buga tsiya agarin nanba.." Nakoma kan bulon
dana zamar dashi kujera na zauna na bude
tukunyar girkina naga har yanzu ruwan
shinkafar bata tsotseba na rufe na gyara itace.
Najuyo na kalli fadila wacce ta zuba min ido tana sauraron amsar da zan bata. Nayi ajiyar zuciya
nace "fadila hankalina yana tashi jikina yana
sanyi duk lokacin da muka hadu. Zaki ga kome
janet,Harriet dasu Ngozi kawayenki zasuyi na
bariki da tabewa da maza bana ko daga ido in
dubesu saboda nasan ba musulmai bane." fadila ta zazzaro ido tana kallona cike da mamaki tace
'pretty nadauka duk addininku daya dasu,
nikadaice musulma acikin ku? Meyasa jikinki yake
sanyi idan kika ganni? Nasake zubo da hawaye
daga idanuwana. Nasa gefen rigata na sharce.
Nace fadila a matsayinki na musulma gaba da baya musulmar ma bahaushiya, bahaushiyar ma
bakatsiniya hausawan asali masu al'adu irin ta
larabawa. Nayi mamaki da rayuwarki ta zama
haka fadila na zauna da masu irin addiniki kala-
kala na tantance addininku addinin musulunci
addini ne me tsafta. Har mamaki nake idan naga musulmi yana bin arna yana bata. Domin dani na
samu Allah yayini a musulma hausa fulani
tsantsan na sami tarbiyyar musulunci tun ina
yarinya banga dalilin dazaisa na sabawa
ubangijina ba....


YARENA ADDININA....CIGABAN LABARIN..., Jikin fadila ya fara sanyi ta dubeni cike da nadama
tace 'pretty ban fahimcekiba. "na nisa nace ina
mamakin yadda yar musulma zata iya buda jikinta
tayi zina nasan ko batada ilimin QUR'ANI sosai
duk inda take duk abunda take tasan Allah yana
kallonta. Ina sha'awar musulmai domin sun san darajar mata sai dai mace ta wulakanta kanta
domin addini yazo musu da cewar mace ta killace
kanta a gidan mijinta. Idan ya kama zata fita
unguwa ta suturce jikinta, hijab har kasa mace
musulma bata tsayawa da maza atiti kotaje gidan
wani suyi shakiyanci kota yarda wani da namiji ya taba jikinta ko su tafa hannu. Duk inda zata shiga
ita kadai ta saka tsoron Allah a zuciyarta Allah na
ganinta don Haka mijinta baya fargaba hartaje
inda zataje tadawo shiyasa nake sha'awar
addininku fadila. Amma ke kin zubar da duk
wannan gatan, don duk wanda Allah yayishi musulmi dan musulmai ba karamar kyauta Allah
yayi masa ba kuma Allah yaso shi da rahamarsa.
Bai kamata ki zubar da wannan baiwar ba fadila."
sainaga idonta ya cicciko da hawaye, ta zauna
tayi shiru tana tunani. Naci gaba da cewa "kina
musulma fadila ban taba ganinki kintashi kinyi sallah ba saboda karki batawa wani arne rai
Gibrel da kawayenki su Ngozi kin shiga cikin arna
gaba da baya kin bar addininki. Ga sabon Allah
da kike ciki tsantsa. Cinki da shanki da suturarki
duk haramun ne. Ga uwa-uba hakkin iyayenki,
kin fadamun aure za'ayi miki kikace bakya son mijin kika kai musun Gibrel suka ce czaki aureshi
ba kika hado kayanki kika biyo shi ku kazo kuke
holewarku? Iyayenki duk inda suke suna chan
suna tunaninki, kin dauki alhakinsu kin rusa duk
tarbiyar dasuka yimiki fadila. Kece mutum ta uku
da zan fada mata wani boyayyan sirri; daga hamma huzaifa sai mamarsa saikuma keda zan
fada miki yanzu. Fadila ni musulma ce, kuma
nakarbi musulunci a boye duk ranar da
mahaifiyata taji ina sallah zata yankani ne kawai."
fadila ta zazzaro ido tana mamaki. Naci gaba dayi
mata bayani, nace "butar nan da nake dauka in shiga ginin chan salla nake shiga in buya inyi.
Hijabina da abun sallata da carbina duk suna ciki
aboye banaso kowa yasan ni musulma ce shiyasa
nake mamakinki, karfi da yaji kinbar addininki
addinin tsafta da gaskiya. Kiji tsoron Allah fadila,
ki saka aranki duk inda kike Allah yana ganinki, akwai mutuwa, akwai hisabi, akwai wuta da
aljanna.
Kafin in rufe bakina fadila ta rushe da kuka ta
rungemeni tsam-tsam, nima kukan nakeyi. Cikin
kuka fadila tace mun "ban taba tunanin akwai
wa'azin da zaisa inyi nadama ba, inji na tsani abunda nake sai yau. Pretty kin fimu wayo ashe,
nake miki kallon wawuya?" dakyar na lallashi
fadila na mayar da ita wajen zamanta tazauna.
Nadauko muciya nafara tuka tuwona. Tambayoyi
fadila take mun wai yanzu yaya nake gani?
Inbata shawarar yadda zata canja rayuwarta. Shawarar dana bata nace ta tuba ga Allah shita
sabawa kuma Allah mai rahama ne, mai jinkai zai
karbi tuban wanda ya tuba. Sannan tabar zinar da
take, ta hada kayanta ta koma gidansu ta nemi
gafarar iyayenta, ta rike salla ta shiga islamiya
tanemi ilimin QUR'ANI da hadisi tayi addu'a Allah yafito mata da miji nagari musulmi tayi aure ta
hayayyafa ta bawa ya'yanta tarbiyar addinin
musulunci. Ta tambayeni toni kuma akan kaina
yazanyi da rayuwata tunda na fada mata
mahaifina musulmi ne amma mahaifiyata ba
musulma bace. Gashina musulunta a boye,? Nayi shiru ina tunani nikaina bansan yazanyi ba. Ina
fargabar komawa gida tunda karatu aka turoni
banyi karatun ba, kuma yadda zanje in zauna a
gidan da sabon addinina. Na faiyace fadila labarin
da bata saniba na game da rayuwata, na shaida
mata wani dan makwabcinmu shine ya cusawa zuciyata tsoron Allah. Shine ya musuluntar dani.
Abunda yafito daga bakinta shine ki auri hamma
huzaifa mana shine mai sonki zai kula dake ya
kuma kara koya miki addimin." najuyo da sauri
na dubeta can na tambayeta. "tayaya zan
aureshi? Kuma yaya akayi tasan inason huzaifa." tayi murmushi tace ai karshen so yana miki kema
kuma haka daman ginshinkin so shakuwa kin
shaku da huzaifa fiye da iyayenki. Huzaifa yana
burgeki saboda addininsa da halayensa shi yaja
ra'ayinki zuwa musulunci kawai ya daukeki kuyi
tafiyaku wani garin kuyi aurenku tunda mahaifiyarki ba zata yarda ba." zance fadila haka
yake babu namijin da naji ina so nake sha'awarsa
a matsayin mijina irin hamma huzaifa amma
nasawa raina bazai yuwu ba. Nayiwa fadila
bayani hamma huzaifa yanada tarbiya yana yiwa
iyayensa biyayya bazai yarda ya daukeni mu gudu wani gari muyi aureba. Na dai cewa fadila ta
tayani da addu'a amma rayuwata tana cikin wani
hali don haka nema nake sha'warta domin
uwarta da ubanta dukka musulmai ne kuma
musulmi zasu aura mata, bahaushe YARENSU DA
ADDINNISU daya. fadila ta tausayamin sosai kuka nake tamkar
idona zai fita naji na tsani rayuwata, naji haushin
mahaifina daya auro mahaifiyata wacce addinin
suba daya ba suka sakani a cikin rudani. Fadila
tayi nadama ta gamsu da shawarwarina ta shaida
min in Allah yaso ko..


Surayya Abubakar
Surayya Abubakar




________________ YARENA ADDININA.
___CI GABAN LABARI part 2


Nan da nan na nemi yawun bakina da makogarona na rasa sun bushe kamas don tashin hankali, sai zuciyata ta lalubo min addu'ar da Huzaifa yake karantawa a duk lokacin da bala'i ya tunkaroshi. Naji kafata ba zata iya daukar jikina ba da dan Jaririn dake hannuna sai nima na sulale na zauna kamar yadda tashin hankalin ganina yasa Mahaifiyata ta sulale ta zauna. Karkarwa suke suna nuna Jaririn dake hannuna, nima hannuna na karkarwa idanuna na zuba tamkar ruwa a famfo ina nuna gagarumin tashin hankali da nake hange a tare dasu.
Mahaifina yayi karfin hali yasa hannu ya tashi Mahaifiyata tsaye yana goge mata hawayen daya wanke mata fuska. Ya ja hannunta da kyar suke jefa kafafuwansu suka shiga gida suka barni a nan zaune cikin kasa turmus. Na kalli gabas na juya yamma, na kalli kudu na juya arewa, na kalli sama, na kalli kasa gaba daya duniyar tayi min zafi ji nake kamar ba a duniyar nake ba, dama a dau raina. Hankalina ya gushe, kaina ya dau zafi gumi ya keto min hade da hawaye mai radadi na rasa inda zan nufa inji sanyi a raina. Babu mai lallashina, babu wanda zanwa bayani ya gane halin da nake ciki bani da sauran gata sai Allah. Shi kadai nake ambato, kowa ya watse ya barni. Na kurawa Jaririn da ke hannuna ido ina kallonsa, sai tsala kuka yake har da hawaye kamar yadda nake hawaye, na fashe da kuka na rungumeshi tsam ina tausayin kaina amma na fi tausayin Jaririn, shi da baisan komai ba na rayuwa.
Tabita naji ta tabani na dago da sauri na kalleta itama hawaye take, ta rungumeni da dan Jaririn dake hannuna mu duka ukun kuka muke. Ta mika hannu ta karbeshi tasa hannu ta tasheni tsaye tana karkademin jikina, tace inzo mu shiga gida. Na girgiza kai, na sharbe hawaye nace "Mama Tabita ba zan iya shiga gidan nan ba da sunan in ci gaba da rayuwa. Tabita ta ce "Rufkatu me kike nufi da baza ki shiga gidanku kici gaba da rayuwa ciki ba? Ga Mahaifiyarki ga Mahaifinki su basu koreki ba, ke zaki kori

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login