Showing 27001 words to 30000 words out of 110329 words

Chapter 10 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt

22 Feb 2025

7486

da nake bautawa ba shi ya sa kike gudowa daga wajen bauta? Ke yarinya yaushe aka haife ki da har sai kin binciki me nake bautawa, sannan ki bauta masa? Ta yi ajiyar zuciya ta dafa kafadata ta fara cusa mun ra'ayinta a nutse yadda addininta yake. Da ta gama sai na mike tsaye na girgiza kai na ce "Allah guda daya ne shi ya halicci mutanen duniya gaba daya ya halicceki ya halicci Daddy. Ta amsa min da Eh na yarda da hakan. Sai na ce "To me yasa bakya sallah, shi kuma yake yi, me yasa ba za ku bautawa Allah Shi kadai ba? Ta daka min tsawa ta ce, tambayar ta ishe ta haka in tafi in kwanta. Har nakai bakin kofa zan fita sai na juyo na dube ta na ce "Allah guda daya ne, ba shi da uwa ko uba haka ba shi da da ko jika, ba ya bacci ko gyangyadi, yana kallonmu, mu ba ma iya ganin Sa. Na fice na bar Mahaifiyata, don mamaki saita dora hannu aka kamar me shirin kwala ihu.
Ta kwana bata rintsa ba ta shigo dakinmu ta rike hannuna tayi min addu'a ta fita taje suyi fada da Mahaifina wai shi yake cusa mun addininsa bazata yarda ba. Tun baya kulata har ta isheshi ya biye mata suka dinga fada kamar zasu daku. Saita sake dawowa dakinmu ta sake yimin addu'a haka ta kwana tana yi har bacci ya daukeni. Bayan ta sauke su Rabecca a makaranta ta wuce wajen aikinta ta dau izini zata je unguwa, sai ta wuce dani wajen bautarsu tana kuka tana shaidawa babbansu halin da *yarta take ciki. Sun juya suna magana yana fadin addu'a za'ayi min na sulale na arce ban tsaya a ko ina ba sai garin mumuyawa wajen kawayena muka ci gaba da wasanmu. Nake shaida musu su daina bautawa wanda suke kira Ubangiji, ubangiji Shine Allah wanda Ya halicci duniya da lahira. Sai karaf a kunnan Maho Mahaifiyar Mungai abokina ta taho da sauri ta jamu daki dukkanmu ta bubbugemin baki ta jajjawa sauran kunne tace karta kara jin nayi wannan maganar suma kuma kar su fadawa kowa, idan ba haka ba dodo zaisa a kashemu a kashe iyayenmu. Tace maza insa takalmina in tafi gida wasan ya isa haka.


A kofar gida naga Hamma Huzaifa a zaune akan mota ya dawo daga Yola a inda yake neman addimission zai shiga jami'a FUTY. Na karasa wajensa na gaishe shi cikin harshen Fulatanci kamar yadda muka saba da yaren fulatanci muka yin magana sai wani lokacin ne muke yi da turanci. Yayi murmushi ya ce "Pretty kin cika yawo wato dan bakya zuwa makaranta ko? Nan dai nima na dane kan mota kusa dashi na zauna ina ta jero masa tambayoyi game da addininsa kuma addinin da yafi shiga raina. Amma ban isa in bishi ba saboda tsoron Mahaifiyata. Musamman sallah ina sha'awar yadda mata suke saka hijab suna sallah. A lokacin Hamma Huzaifa ya dinga cusawa raina inji tsoron Allah kome zanyi. Ya ce kada in kuskura in yi zina, Allah baYa son mai zina. Allah Ya ce "Kada ku kusanci zina barema ku aika ta. A cikin kur'ani. Allah Yana kallon kowa, mutum ko ya kulle daki, ya kashe fitilarsa a duhun Allah na kallonsa. Kada kiyi sata, ko gulma, zaluntar wani duk ya hana bayinsa suyi, zai konani duk wanda yayi idan na mutu. Na yi shiru ina tunani can na ce "Yanzu ko karkashin motar nan na shige na kwanta nayi luf Allah Zai ganni? Hamma Huzaifa yayi dariya ya ce "Zai ganki mana. Na ce "Idan na zura da gudu na shige dakinmu na kulle na shige can cikin toilet dinmu zai ganni? Karshen kwatancen da yayi min shine ya ce ko cikin Mahaifiyata na buda na shiga aka mayar da cikin aka rufe ta daura zani ta saki rigarta ta dauko mayafi ko bargo ta lulluba Allah na ganina. Saina fara jinjina ikon Allah a zuciyata, lallai Allah Mai girma ne kuma Shi Ya cancanci a bautawa ba dodo ba da sassaken itace. A ranar Hamma Huzaifa ya fara fasalta min yadda ni'imomin aljanna suke, ya ce idan na bi Allah zan shiga aljanna. Sai kuma ya zano min azabobin wuta, ya ce idan naki jin tsoron Allah Zai konani bayan mutuwa.


Hmmm, ba sai na fada ba wallahi duk wanda bai bi Allah ba, maganar Huzaifa haka take. Allah Yasa mu dace. Ameen.


Hai jango........ Nasan su wa'e basu gane ba, sai gobe nake nufi.


Reedwan Suraj Isma'il




>>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA
____CI GABAN LABARIN


A nan kan mota Mahaifiyata ta zo ta sameni. Ta jawoni a fusace zata dakeni ashe tuntuni ta karada gari nemana ta rasani sama ko kasa ita da *yan wajen da take bauta. Hankalinta a tashe yake musamman yadda na nuna mata karfi da yaji naki addininta. Dakyar Hamma Huzaifa ya hanata dukana. Ya durkusa har kasa yana rokarta kasancewar tana ganin mutuncinsa saboda yana da hankali ga ladabi a unguwar, kunyarsa tasa ta hakura. Amma a lokacin tayi rantsuwa ko jarabawata ta fito naci inda nake so inje ni da kawayena ba zanje ba, wata makaranta zata nemarmin a kudu makarantar koyar da addininta. Kona ki kona so dole inso addininta. Ta dakamun tsawa ta ce in shiga mota mu koma can. Na shiga mota a tsorace yayin da hawayen takaici ya dinga surnanowa daga idanuwana. Hamma Huzaifa ya bini da kallo cike da tausayina saiya dagamun hannunsa sama da alama addu'a yake yimin, sai naga hawaye yana zuba daga idanuwansa, ta ja mota suka tafi.


Iman ta sharbe hawaye mai radadi, Malamai da mutanen da ke wajen suka dinga hawaye. Suhaif ma ya surnano da hawaye, ya dauko hankici daga aljihunsa ya mikawa Iman ta goge hawayen idonta. Sai Allahu Akbar suke kira. Wasu na girgiza kai don tausayin Iman. Ta dade tana sharbe hawayen idonta sannan ta ci daga da basu labari.


Tace "An kaini wajen bautarsu anyi min addu'o'i, cikin lallami shugabansu yayi min nasiha ya cusa mun ra'ayin son addininsu shine addinin gaskiya. Sai kaina ya sake cunkushewa na sake dabarbarcewa tunanina ya hautsine na kasa tantance addinin gaskiya.
Haka kuwa akayi mahaifiyata ta samo min makarantar da ake koyar da addininsu dake Enugu. Raina baya son kudu nasha kuka Mahaifina bai so ba amma Mahaifiyata ta ce saina je. Hamma Huzaifa ma yasha bacin rai, kawayena Mumuyawa sunsha kuka zamu rabu haka aka kaini garin Enugu.
Nasha bakar wuya a makarantar saboda yadda nake jayayya da Malamai a duk sanda aka zo darasi akan addininsu, ana fara wa'azi duk sanda suka fadi wani abu sabanin yadda Hamma Huzaifa ya fadamun saina tashi na karyata Malamin a aji. Ince Malam ba haka bane baka fada dai-dai ba, Allah baShi da uwa baShi da uba baShi da da ko jika. Sai suyi ta mamakina tun suna bani amsa a hankali suna kawomin hujjoji daga littafinsu amma bana dandara ko gobe Malami yazo aji ya fadi wani abu sabanin abunda Hamma Huzaifa ya fadamun zan tashi in karyata shi. To sai suka shiga dukana kamar Allah ne ya aikosu har da farfasamun jiki. Dalibai ma suka tsane ni. Seniors su kayi ta dukana suna zagina a hostel wai daman banyi kama da su ba watakila ni ba bafillatana bace dama balarabiya ce nazo in yada addinin Musulunci. Takai ta kawo duk an tsane ni duk da haka ban canja ra'ayina ba sai dai idan ba'a shiga ajinmu ba an fadi wata kalmar da bata yimin ba akan addini sai na musa. Malamai suka ga zasu kasheni saboda duka kuma baisa na daina ba, sai aka kaini kara wajen shugaban makaranta aka zauna meeting. Aka kirani ofishin suka zagayeni dukkansu tambayar da suka yi min shine "meye addinina? Na ce musu ban sani ba. Suka sake tambayata meye yarena? Nan ma bansan yarena ba, na dinga zano musu yare kala-kala da nake ji. Suka bugawa Mamana waya aka shaida mata tazo ta dauki *yarta don wannan makarantar koyar addininsu ce, *yar kuma ba irin addinin take ba Musulma ce. Mummyna ta fashe da kuka don takaici tace ba Musulma ba ce. Suka ce sun tambayeni yarena shima nace ban sani ba na zano musu yare iri-iri sufa sun kasa gane wannan wanne irin abu ne? Ta ba su hakuri ta ce kuma za ta zo karshen sati. Mummy ta zo makarantar ta ba wa Malamai da shugaban makarantar hakuri ta yi musu bayanin cewar Mahaifina ne Musulmi yake hure mun kunne da addininsa shi ne ma ta ga gara ta kawoni makarantar koyon addininta. Ta ce ni yarinya ce mai kaifin basira dukan da suke yi mini ba zai sa in canja ra'ayina ba, amma in har za su zaunar da ni cikin hikima da dabaru su karanto min addininsu a hankali, to tabbas zan rike a zuciyata sai in sawa zuciyata son abun. Ta zayyano musu yadda zasu bini har ta ce zata dinga biyan wani kudi na musamman ga Malamin da zai dinga ware lokaci yana yi min darasi na musamman ni kadai a kan yadda zan fahimci addinin sosai wato (extra Lesson). Ta kira ni gefe cikin dabara ta dinga lallaba ni tana yimini wa'azi har naji zuciyata ta fara karkata ga addininsu.
Na tsayar da hankalina a waje daya na sa karatu a gaba na yarda da abin da suka cusa min a zuciya. Ta kai ta kawo idan aka yi jarabawa akan addinin na fi duk *yan ajin cinyewa. Mahaifiyata tana jin dadi sosai, hankalinta ya kwanta. Idan na fara zayyano mata abin da yake kwakwalwata wanda aka koyamin a makaranta na game da addininta, mamaki yana rufeta tamkar na haddace littafin a kaina sai ta yi murna.
Mun gama shekarar farko har mun shiga shekara ta biyu a makarantar. Wata rana ranar Asabar da rana a makarantarmu na fito daga hostel zan tafi hall karbar abinci, na zo wucewa ta dakin seniors sai wata daliba *yar aji shida ta kirawo ni ta ba ni wata roba ta ce in karbo mata abinci daga hall. Na durkusa na karba don girmamawa don muna matukar tsoron *yan ajin gaba damu. Musamman ni da na yi kaurin suna a makarantar sun tsane ni ana min zargin ko ma ba addinin nake yi ba, na tafi hall sai na tarar teba aka yi da miyar danyar kubewa dama ni duk ranar da aka yi teba ba na ci, sai na karbi wacce aka aiko ni na fito, na kusa karasowa dakin sai na hango ta ta bude wata katuwar lokar da ke kusa da gadonta. Lokar cike take da kayan makulashe kai ka ce katafaren kanti ake shirin budewa. Biskit kala-kala, alewa, cingam, madara, milo, corn flakes, da dai sauransu.
Senior ta kalle ni ta yi murmushi da taga ina kallon kayan lokar, na mika mata robar teba na juya zan tafi sai ta kirani na dawo. Ta dauko leda ta dinga damko biskit da alewa kala-kala tana zubawa a ledar ta cika ta taf ta mika min, na kalle ta cike da mamaki na tambaya. "Wa zan kaiwa? Sai ta yi murmushi ta ce "Na ki ne, ki je ki ci ke yarinya ce mai hankali, ga shi ba ki da kiwa. Na yi murmushi, farin ciki ya rufeni, sai na duka na yi mata godiya na fito daga dakin. Ta fito har bakin kofar dakin tana dagamin hannu, ni ma ina daga mata. Duk waigowar da zan yi sai na ganta a tsaye a inda take tana dagamin hannu, har sai da na shiga dakinmu, ina ma da biskit kala-kala a akwatina, amma ba ni da irin wadannan tsadaddun, alewa kuwa ba ni da ita don *yar kadan mamana ta saya min, ta ce na cika shan zaki ida na ga alewa ko biskit ko abinci bana ci sai shan alewa.
Don haka tuni na shanye alawowin a kwana kadan. Na haye kan gadona na lankwashe kafa na bude ledata cike da farin ciki don yau na huta da cin abinci tunda na sami alewa da biskit. Na dauko wata katuwar alewa wacce aka yi ta da cakudadden bonbita da madara, daga gani zata yi dadi. Tun kafin in kai bakina har yawuna ya fara tsinkewa. Ledar alewar kadai abar kallo ce da sha'awa tun kafin ka bude. Nakai ledar bakina zan cisga in yaga sai na dakata cak ina tunani. Abunda ya fado mun a raina nasihohin da labarun da wasu Malamai da prefect suke bamu a Makarantar kasancewarmu kanana, sababbain suwa bamu san abunda yake faruwa a makarantar ba.


Ansha ja mana kunne akan mu guji cin abun wacce bamu sani ba, saboda akwai dalibai da suke kungiyar matsafa a makarantar, suna nan jifge guda har sun kafa kungiyarsu suna kuma jan *yan uwansu dalibai cikin kungiyoyinsu a boye. Wadannan daliban ba'asan ko su waye ba kuma babu wata shaida da zaka gani a jikinsu kace sune wadannan balle ka gujesu. Amma dai koda yaushe ana samun wadanda aka tsafe, wasu a sume, wasu kuma an kawar da hankalinsu sai dai a mayar dasu gida don basa iya tuna abunda ya faru.
Duk yadda suka boye kansu amma ansan wasu daga cikin daliban ana korarsu amma koda ankori iri-irinsu sai kaga sun sake yaduwa fiye da da. Kullum a tsorae muke musamman da daddare, anan ana tsoron fitar dare saboda aljanu, acan kuma haka ake tsoron fitar dare saboda matsafa. Idan kaga yarinya ta kwanta bacci anzo an tasheta bata tashi ba, a girgizata, a dauko ruwa a sharara mata bata farka ba. Daga karshe a dauko reza a tsattsaga jikinta ko motsi baza tayi ba. To *yar kungiyar ce kuma gangar jikinta ce anan ruhinta ya tafi wajensu. Sai sanda kurwarta ta dawo sai tayi firgigit ta tashi taji tsumu-tsumu cikin ruwa taji radadi wajen da aka tsaga mata. Duk a gabanmu muke ganin irin haka dan haka kusan kowa bai yarda da kowa ba, ko kawa ba'a cika yi ba kuma ba maicin abun wani. Sai dai in tuntuni kasan mutum. Wala gidanku daya ko *yan uwa ko gari guda, ko kun zauna kun saba ka karanci mutum ka yarda dashi.
Sai na mayar da alewar hannuna cikin leda na daure ledar na jefa ledar na jefa kan akwatina na fasa sha. Ga bakar yunwa ina ji amma wani barci mai nauyi na ba gaira ba dalili ya ruftomin ko idona bana iya budewa, tun ina jingine akan filo harna mike na kwanta akan gado nayi ta barci mai nauyi. Bazan iya fasalta yadda naji ba kamar a mafarki, kamar a ido biyu naga wasu irin mutane sun zagaye gadona mata da maza, manya magidanta ba dalibai bane, da kuma daliban har da uniform irin namu. Sannan *yan kananan yara *yan primary duk suna ta dariya da karfi mai tsoratarwa. Babbansu wani tsoho tukuf cikan harshen turanci ya ce mun "Rufkatu sannu da zuwa cikinmu, yanzu kin zama mu mun zama ke. Zamu yi miki arziki, farin jini, mu kara miki kyau da kwarjini da ilimi zaki ji dadin rayuwarki. Amma kada ki bi ko wanne addini domin bama son addu'a kowacce iri ce. Sai naji na ce "Bana sanku kuma bazan shiga cikinku ba. Ya jawo wata budurwar yarinya gabansa ya ce mata bude idonki ta ganki. Sai budurwar ta yaye wani gyale da ta rufe idonta sai naga wannan senior ce da ta bani biskit da alewa dazu. Sai ta ce "To meya sa kika ci alewa da biskit dina, ki biyani. Saina nuna mata kan akwati na ce gasu can ban ci ba, dauki kayanki. "Suka kwashe da dariyar mugunta suka ce "Rufkatu aikin gama ya gama ki bamu uwarki ko ubanki mu kashe. Na firgita amma na rasa addu'ar da zanyi a cikin addinina na kasa tuno addu'a daya da zanyi dan babu addini daya dana tsayar har in koyi addu'ar neman tsarin makiya da akeyi, sai na fara kwalla kara mai firgitarwa. Babbansu yasa hannuna ya kama gashina ya dinga cukurkudawa ina ihu kamar raina zai fita. Ni dai na bude ido naga *yan dakinmu gaba daya a kaina ana tambayata ihun me nake yi. Ban iya basu amsa ba naci gaba da ihu kamar zan tsaga kunnuwansu don a firgice nake ba zan iya tuna abunda ya faru ba ga tsananin ciwo da jujjuyawar da kaina yake mun. Dalibai suka dunga zazzagamun addu'a, ban daina ba sai aka je staff quarters aka kira malamai suma suka zo suka fara tasu. Saina daina ihun na fara wani bacci mai kama da mutuwa. Kwanana daya da yini daya a gadon asibiti ana karamun ruwa ban farka ba. Aka nemi wayar gidanmu ba'a samu ba a lokacin an rufe layin. Sai aka daukeni aka kaini wurin addu'a a garinmu ana ta cigiyar Iyayena. Nan da nan Mahaifiyata taji labari ta garzaya wurin taga ni din ce kuwa. Sai ta fashe da kuka, ganina cikin wannan hali . Ta tambayesu meya sameni suka bata labarin abunda ya faru. Sai tasan wannan ciwon nawa bana asibiti bane. Saita daukeni ta tafi dani wajen bautarsu. Nan fa suka dukufa da yi min addu'a ba kakkautawa ba dare ba raba ga karin ruwa ana yimin saboda bana ci bana sha a sume nake kawai a kwance kamar gawa numfashi kawai nake yi da an binneni, har tsawon kwananki biyar a haka a kwance. Mahaifina da yaga haka shima ya hado Malamai musulmai suka hadu har Hamma Huzaifa duk suka dauki Alkur'ani suka yi ta saukewa a kofar gidanmu. Ana yanka ana sadaka, addu'a bata faduwa kasa saina farka na bude idona.


Iman ta fashe da kuka haka *yan wajen sai hawaye ya dinga zubo musu. Sai girgiza kai suke dan tausayi. Ta jima tana kuka kafin taci gaba tace.


Nasha wuya, nasha wuya a wannan lokacin domin sai dai ban kwanta barci ba na dinga ganin wadannan mutane suna firgitani. Daga karshe Mamana ta hakura da makarantar aka dawo dani ta jeka-ka-dawo a nan jalingo ina zuwa ina dawowa gida a hankali-ahankali kuma ana yimin addu'a daga dukkan bangaran uwata da ubana, Hamma Huzaifa har rubutun kur'ani yake min yana kirana a boye yana bani ina sha yace kada in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login