Showing 75001 words to 78000 words out of 110329 words
Chapter 26 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
Mahaifanta kace baka son *yarsu, duk halaccin da suka yi maka, tun kana yaro har ka girma ka zama mutum sak. Suhaif ya ajiye kofin koko ya ce "Oh my God, Dad, Mum kun kasa gane abunda nake nufi. Akwai wacce na yiwa alkawarin aure bana so in zama mayaudari. Baba ya fusata ya ce "Kai dalla rufe mana baki Dad kake cemin da kuma Mum kake cewa Goggo? Wai kai dan boko ko? To badan Mahaifin Zubaidar ba ina zaka san sunan uwa da uba da turanci? Da ba kana kauye kana noma ba? Goggo ta ce "Wacece wacce kake so din, kasan yanzu duk wacce zata ce tana sonka badan Allah za ta so kaba saboda abun hannunka zata so ka. Ba gara ka auri *yar uwarka ba. Suhaif ya ce "Wallahi waccan ma don Allah take sona tun bani da komai. Goggo ta ce "Iman din dai har yanzu? Baba ya yi jan ido ya ce "To bari kaji maganar karshe ita ce ka auri Zubaida ka gama, ko bayan raina a daura musu aure. Kar ka kara kawo mana zancen banza, a garin neman Iman ka rasa aikinka. Idan ka sake kiran sunan Iman a gidan nan saina bata maka rai. Yanzu ka shirya ka kaini Kanon in je in yi magana da Usman.
Ran Suhaif ya yi mummunan baci, ya rasa abunda yake masa dadi, sai wata kwalla mai zafi ta cika masa ido ya gwammace bai zo ba ma kwata-kwata. Tun da suka shiga motar suna tafiya babu wanda ya sake magana shi da Mahaifinsa, har suka isa Kano. Suhaif ya wuce dakinsu ya kwanta babu abun da zuciyarsa take sai bugun uku-uku. Babu wacce yake tunowa a ransa sai Iman, baya fitar da ran zai ga Iman kuma ya aureta. Kamar daga sama ya sake jiyo muryar Mahaifinsa da Baban Zubaida. Bayan Baba na Doko ya gama fadawa Baba na Kano duk abunda yake faruwa tsakanin Zubaida da Suhaif da kuma hukuncin daya yanke. Yanzu kafin Suhaif ya tafi, dole ya bayar da sadaki koma ba'a daura auren ba, tuwona maina. Baba na Kano yana bude baki cewa yayi "Har yanzu banji kalma daya da Suhaif din ya ce ba. Naji na Zubaida, naji naka. Me shi Suhaif ya ce? Baba na Doko ya zabura ya rufeshi da fadan da ya saba ya ce "Kai! Kai dakata bana son kwakwa ni dai na gama magana, aure zan daura shi ko baya so yarinya dai tana so, ni da Mahaifiyarsa muna so.
Ya tashi ya fito yana kwallawa Suhaif kira. Suhaif ya fito da sauri, ya ce da Suhaif "Zo ka mayar da ni Doko suka tafi.
Maman Zubaida ma taji dadi sosai, haka Naja'at ba kamar ita Zubaida kamar zata zuba ruwa a kasa tasha. Amma banda Najib, yayi shiru bai ce musu komai ba, amma shi da Mahaifinsa sun san ra'ayin Suhaif har yau Iman yake so. Balle shi Najib da suke hira ta waya, kuma Najib ya je Lagos ya ga yadda Suhaif yake gudun *yan mata, shi har yau Iman yake so, yake kuma jira yaga ta ina zai bullo ya aureta. Suhaif ya kara kwana daya a Doko, sai ya dawo Kano. Zubaida da Naja'at wasan *yar buya suke da Suhaif, tunda ya zo bai gan su ba, sai dai ya tsinkaye su suna shigowa gida ko suna fita a motocinsu in zasu tafi makaranta ko suna dawowa. Daga nan kuma bai san ta ina suke tsallakowa cikin gida ba. Watakila ko zagayawa baya suke ta wundon dakinsu su haura. Fara'ar Mama da kirkin da take yiwa Suhaif ya karu, amma bata yi masa maganar ba. Baba ma bai ce masa komai ba, haka Najib ma bai ce masa komai ba, shima Suhaif bashi da abun da zai fada musu. Don haka duk gidan suna hira da Suhaif akan wani abu daban, ba'a hirar aure. Suhaif ya kara kwananki uku a Kano sannan ya shirya zai koma Lagos.
Suhai ya iske Baba a falonsa da sassafe misalin karfe bakawi. Bayan ya gaishe shi, ya shaida masa ya fito zai koma Lagos yanzu. Baba na Kano ya zaunar da Suhaif ya yi masa nasiha akan ya rike gaskiya akan aikinsa da al'amuransa na yau da kullum da abokan aikinsa. Musamman ma Manager da suke aiki tare, in har ya rike gaskiya duk kwangilar daya bashi yayi tsakani da Allah, to hakika zai sami alheri a wajen Manager nan sosai zai zama abun kwatance a kasar nan. Domin Manager mutumin kirki ne haka kuma wajen ana samun kudi sosai. Suhaif yayi godiya gami da yin alkawari zai yi amfani da shawarwarin daya bashi. Sai Suhaif ya zaiyana masa irin kyaututtukan da yayi a Doko da kuma alkawuran da ya yiwa Hajja, Iyayensa da kuma Iya Furera. Baba na Kano ya ji dadi ya kara karfafa masa gwiwa yana da kyau yayi kyauta, ya kuma ci gaba da taimako. Suhaif ya yi masa sallama ya mike zai fita daga falon. Baba ya kira sunansa "Suhaif, suhaif ya waiwayo, Baba ya ce "Kar ka damu da hukuncin da Mahaifinka ya yanke akan ka, zan lallasheshi ya janye. Kunya da nauyi ya rufe shi. Ya ce "Baba wannan ba matsala ba ce, hakan da yayi din yayi dai-dai ai kanwata ce. Suhaif ya juya ya fice. Baba yayi shiru yana tunani yasan Suhaif a kwai kunya da kara dole zai yiwa kansa ko zuciyarsa bata so. Suhaif ya shiga falon Mama ya isketa ita da me aikinta. Ya yi sallama ya shiga ya gaishesu, ya shaida mata ya fito zai tafi. Tayi masa fatan Allah Ya kiyaye. Ya dauko kudi mai yawa ya ajiye a gabanta. Ya ce ta kara jari ya kuma shaida mata ya bawa Mahaifiyarsa jari itama. Ya bawa mai aikin ma kudi mai tsoka, suka yi ta murna da godiya da fatan Allah Ya kiyaye. Suhaif ya fito ya nufi in da motarsa take, dauke da jakar kayansa. Sunyi sallama da Najib tunda asuba kasancewar aikin banki Najib yake yi ya fita tuntuni.
Kamar daga sama yaji ana jan jakar kayansa. Ya waiga da sauri yaga mai jan jakar, sai yaga Zubaida ce, Naja'at a bayanta. Wani kululun bakin ciki ya darsu a zuciyarsa da dacin takaici. Ba abinda ya dauki zancen Zubaida illa raini. Ta yaya zata dubi kwayar idonsa a matsayinsa na yayanta ta ce tana sonsa da aure? Shima son yayi garaje daya kama zuciyarta, yayi kuskure. Ya rike jakarsa tsan a hannunsa yaki sakar mata. Ya bata rai kai kace bai taba ko murmushi ba balle dariya a rayuwarsa. Ya tsaya cak yana galla mata uwar harara. Sai ta saki jakar ta ja da baya, gabanta ya hau faduwa. Ya waiwayo ya dubi Naja'at sai taji kamar ta rafsa ihu dan tsoro, tana rawar murya ta ce "Yaya Suhaif Allah Ya kiyaye hanya. Ya ja wani dogon tsaki, ya juya ya tafi ya shige mota, ya ja ya fice. Ya tsaya a bakin get suma masu gadi da direbobin gidan ya rarraba musu kudi masu tsoka sannan ya tafi.
Kuka wiwi Zubaida ta shigo gida dashi. Mahaifiyarta ce daman ta sa su raka shi. Baba yana daga falonsa yana jiyo duk hayaniyar da suke yi. Zubaida tana cewa "Uwar hararar nan tasa ya sakar mana gami da tsaki, ya juya ya tafi ya bar mu. Baba ya fito ya iske su a babban falo, Naja'at da Mama rike da Zubaida tana zabura tana faduwa share-share akan kafet. Ya tsaya cak yana dalla musu uwar harara fiye da wacce Suhaif yayi mata har take kuka. Tayi zunbur ta tashi ita da Naja'at suna shirin guduwa daki. Ya ce su zo su zauna a gabansa. Mama ta zauna itama. Bayan sun zazzauna ya fara zayyanowa Zubaida laifuffukanta ya ce "Akan abubuwa uku ki ka bata min rai, kallonki nake dama ina jiran Suhaif ya tafi tukunna.
Na farko baki taba fada mana cewar Suhaif kike so ba har kika kawo Muslim gidan nan, nan falon kuke hira rimi-rimi har ya taba zuwa muka gaisa, na ce za muyi magana da Mahaifinsa customer na ne a kasuwa. Mahaifinsa ya sameni munyi magana sosai akan auranku, amma dan kin iya gulma kika je Doko kika canja Muslim ki ka ce Suhaif kike so, ni nake son in miki auren dole. Abu na biyu kinsan sarai Suhaif yana da wacce yake so, yana jira har kuka yake, har addu'a yake cewa inyi masa Iman ta bayyana, zaki sa a cusgunawa yaro a ce sai ya aureki. Abu na uku kuma zaki raba mana zumunci, wato yaki yarda ya aureki mu ce mu ya yiwa rashin mutunci ba ke ba, mu kullace shi. Ko kuma mu ki yarda da auren Mahaifinsa ransa ya baci, a yi kaca-kaca a rabu, zumunci ya watse. To daga yau idan na kara jin zancen aurenki da Suhaif a gidan nan ran kowa zai baci. Kamar yadda daga makaranta kika saci hanya kika je Doko kikai gulma, yau ko gobe ki saci hanya kije Doko kice musu da kanki kin fasa auren Suhaif, Muslim zaki aura. Kada ki sake ki nuna saki aka yi dole, ki nuna ke kikayi tunani kika fasa. Daga karshe kuma ki bugawa Suhaif waya ki bashi hakuri domin ko ba komai kin daga masa hankali.
Mama ta bude baki zata yi magana, ya daga mata hannu ya dakatar da ita gami da cewa. "Duk wannan kisisinar ke kika koya mata kada ki sake ki cemin komai idan ma baki warware mata ba daga karshe ku zata kwabewa. Ya tashi ya koma falonsa ya rufe kofa. Zubaida ta rushe da kuka ta nufi daki, Naja'at ta bita tana lallashinta. Mama na zaune ta kasa motsawa abun duniya ya isheta. Najib na dawowa daga aiki karfe shida dai-dai na yamma ya iskesu su dukka a babban falo. Ya ce "Yauwa Zubaida dama so nake Suhaif ya tafi inci Ubanki. Yaushe Suhaif ya zama sa'anki da zaki ji yanzu shi kike so, dan kawai ki caza masa zuciya aga laifinsa bayan kinsan wacce yake so. Mama ta dakatar da shi ta ce "Ya isa haka dan Allah, yarinyar nan ta ce tayi kuskure a yafe mata. Da safe Babanku yayi mata fada zance ya wuce zata auri Muslim din wanda aka yiwa alkawari.
Daman matan nan haka suke....... Lolxxx
Reedwan Suraj Isma'il
:::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI
Duk abun nan da ake Suhaif bai sani ba, yana can yana ta lallashin zuciyarsa ya zaiyi dole ya hakura ya auri Zubaida. Amma yaji shiru babu wanda ya taba kiransa a waya yayi masa zancen auransa da Zubaida. Baba na Doko ma ya taba kiransa suka sha hira, har suka yi sallama bai yi masa zancen auren ba. Sai abun ya fara bawa Suhaif tsoro har ya damu, yana tsoron ko Baba na Kano yayi fushi ne yana ganin baya son *yarsa. Haka Suhaif yake ta wasi-wasi shi kadai a ransa. Ya kira Najib ta layin office suka gaisa suka sha hira Najib bai nuna masa alamar damuwa ba, babu alamar akwai wani laifi da yayi masa. Aka kwana biyu Suhaif ya kira Mama, ko daya bata canja masa ba. Sai ya kira number gidan makwabtansu, bayan sun gaisa da matar gidan Maman Faruk suke kiranta sai yace a kira masa Naja'at zai sake bugowa. Faruk ya zo kiran Naja'at bata nan sai Zubaida ce kawai a gidan. Ta tambayi Faruk "Waye yake kiran Naja'at? Ya ce "Yaya Suhaif ne ya ce ta zo ta dauki waya, mamaki ya rufe Zubaida ta fara tunanin ko dai wayar gidansu ta samu matsala ne ya kasa kamawa. Sai ta dauki kan wayar taji lafiya kalau tana yi. Ta ce da Faruk "Je ka ce gata nan zuwa.
Zubaida ta suri gyale ta nufi gidan makwabtansu. Tana shiga falon gidan ko gaisawa basu yi da Maman Faruk ba, waya ta hau ruri. Maman Faruk ta ce "Ina jin Suhaif din nema. Zubaida ta karasa wajen wayar a hankali, gabanta yana faduwa. Ta dauka ba tare da ta iya cewa komai ba. Da Maman Faruk ta ga Zubaida ta kasa magana sai tayi tunanin ko wani sirri za suyi sai ta ja hannun yaronta suka fita daga falon. Bata san fargaba, tsoro da tsananin son Suhaif ne ya hana Zubaida magana ba.
Lolllllxxxxx na 2 ya tafi kenan
YARENA ADDININA (III)-------> 3
PART 1
Suhaif yana ta magana shi kadai ya ce "Naja'at ce? Ta amsa da cewa "Eh" ya ce "Wai bakya magana ne? Ko baki iya gaisuwa ba ne? Ba'a ce miki Suhaif ba ne? Muryarta na karkarwa ta gaishe shi, sai ya gane muryar Zubaida ce. Yayi ajiyar zuciya ya ce "Naja'at ce ko Zubaida? Ta ce "Zubaida ce, Naja'at bata nan. Suhaif yayi shiru kamar ruwa ya cinye shi, ya rasa mai zai ce mata, kawai sai ya ajiye kan wayar. Bai so Zubaida tasan ya kira Naja'at ba, cikin sirri yake so ya tambayeta halin da ake ciki game da maganar auransa da Zubaida. Suhaif yayi dogon tunani yaga mafita ita ce ya kira Baba na Kano suyi maganar, hakika kamar yadda Mahaifansa suka fada gaskiya ne bai dace ya dubi idon Baba na Kano ba ya yi kirmisisi ya ki aurar *yarsa. Bayan ta fada shi take so. Ya ci sa'a kuwa ya sami Baba na Kano a layin wayarsa na office. Bayan sun gaisa sun taba *yar hira akan harkokin kwangila da kasuwanci, sai Suhaif yayi gyaran murya ya ce "Baba ina tunanin zan zo Kano karshen watan nan akan maganar da muka yi da kai. Baba ya tambayi Suhaif ya ce "Wacce maganar fa? Suhaif ya hau kame-kame can ya ce "Zancena da Zubaida. Baba yayi murmushi ya ce "Ai wannan zancan ya wuce tuntuni. Ba su fada maka bane? Karka damu kanka ka ci gaba da harkokinka, Zubaida ta yarda zata auri Muslim. Daman munyi maganar aurensa tuntuni da Babansa. Suhaif ya ce "Amma Baba ai.... Baba ya katseshi ya ce "Na ce ka kwantar da hankalinka, ka manta zancen ya wuce. Baba na Doko ma ya gamsu da hujjojin da na bashi. Ba komai Suhaif karka damu. Su kayi sallama suka ajiye kan waya. Suhaif ya shiga halin damuwa mai tsanani yana ganin anya Baba na Kano ko dai ya dauka baya son *yarsa ne? Sai Suhaif ya kira Najib ya tuntube shi da zancen aurensa da Zubaida. Irin kalaman da Baba ya fada masa haka Najib ya fada masa. Hankalin Suhaif a tashe ya hayo jirgi ya zo Kano babu shiri. Ya iske Mama ita kadai a gida, tayi matukar mammakin ganin Suhaif. Bayan sun gaisa sai ta ce "Amma baka ce min ba zaka zo kwanan nan ba. Suhaif ya ce "Wallahi nima ba shiri na taho. Bayan ya zauna tasa masu aiki suka kawo masa ruwa da abinci, ya tambayeta ina *yan gidan? Ta ce "Duk sun tafi harkokinsu sai ita kadai. Suhaif ya gyara zama ya zaiyana mata abunda ke tafe da shi, ya zo akan maganar aurensa da Zubaida. Ya fada mata yadda suka yi da Baba da Najib, sun ce ya kwantar da hankalinsa kar ya damu Zubaida zata auri Muslim. Sai yake ganin kamar fushi suka yi ko suna ganin shi ya ki aurenta. Shi kuma ba haka bane tabbas Iman yake so. Amma ina Iman din take yanzu? Kuma ko tana nan ai wata kusan tafi wata, gara ya auri kanwarsa Zubaida. Haka Suhaif ya karka ce yana yiwa Uwar *ya dadin baki, alhali har ga Allah Iman ya fi so ya aura.
Mama taji dadi sosai da kalaman Suhaif dan sauran kullatar da ta yi masa ta goge. Ta yi dariya ta ce "Haba haba Suhaif karma ka kawo wannan a ranka. Mun san ba zaka ki aurar kanwar ka ba, kai da idan ba ranmu kai zaka zabar mata miji na gari wanda zai rike ta amana. Ta zayyanowa Suhaif dalilan da suka sa Mahaifinta ya ce ta auri Muslim tunda har anyi magana da Mahaifinsa. Shima yaro ne mai hankali, mai sonta. Suhaif ya ji dadi tamkar an sauke masa wani kaya dingimeme mai nauyi a kansa. Yayi ta addu'a akan Allah Yasa haka shi yafi alheri kuma Allah Ya basu zaman lafiya. Mama tana amsawa da amin. Ya ce ta bashi mukullin motarta zai je Doko gobe zai dawo, jibi kuma zai koma Lagos.
Suhaif ya isa Doko ya ci sa'a ya iske Mahaifinsa da Mahaifiyarsa a gida. Ya zauna ya tambayesu dalilin da yasa aka fasa aurensa, shi dai ga yadda suka fada masa a Kano, ya Zaiyyana musu yadda suka yi da Iyayen Zubaida. Har ya nuna baiji dadi ba da aka ce an yiwa Zubaida miji don shi yanzu ya zo da shirin aurenta. Mahaifinsa ya ce "Ai daman Zubaida ta wuce ka, bayan har an kawo min kudin aurenta na karba sai dai ka nemi wata. In kuma har yanzu Iman kake jira sai ka yi ta jiran yarinyar da baka tabbatar bama ko tana raye ko ta mutu. Yanzu nan da watanni uku za'ayi auren Zubaida, Naja'at da Najib. Shima ya ce min ya sami mata zaiyi mana magana lokacin da zamu kai kudin auren. Ka zauna kana turo hula gaban goshi za ka tsufa baka yi aure ba kannanka zasu yi aure su haihu. Suhaif yayi dariya ya ce "Lokaci dai Baba. Goggo ta hau lallashin Suhaif akan yayi hakuri ya nemi wata ya hakura da jiran Iman shima nan da wata ukun a hada da na *yan uwansa.
Bayan komawar Suhaif Lagos da wata biyu Najib ya kira Suhaif a waya. A lokacin Suhaif ya tare a dankareran gidansa na Abuja. Yana zaune a bakin swimming pool din gidan a kishingide kan kujerar hutawa yana sanye da dan dajeren wando da yamma. Masu yi masa hidima duk maza ne suna ta kai kawo suna ta jera masa kayan makulashe akan teburin dake kusa dashi. Yana shafa gashin burgujejen Karen daya suyo daga England. Suhaif ya amsa wayar Najib cikin fara'a ya ce "Najib ka ki zuwa sabon gidana ko, balle ka kawo su Mama da Baba da Goggo, Hajja, *yar Hajja, Zubaida da Naja'at da sauran dangi suzo su sa albarka ko? Najib