Showing 96001 words to 99000 words out of 110329 words
Chapter 33 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
ce "Dan Uwana Najib mutuwa zan yi, ciwon da yake kokarin kama ni sana diyyar rashin Iman shine zai zama ajalina. Na dauka zan iya daure rabuwa da Iman ashe bazan iya ba. Kar kuji haushina, kada kuga laifina, kar ku dauka ni na dorawa kaina. Allah ne Ya dora min Shi zai cire min kuma bai cire min ba. Nayi addu'a da kaina Allah Ya yaye min tun ba yau ba sai gashi sai kara son ta nake. Na rasa Iman na rasa ta har abada, haka kuma zan rasa rayuwata. Mutuwata ita ce hutu, Najib kumun addu'a gara na mutu da in zauna na dauwama a cikin wahala da kunar rai. Na rasa farin cikin rayuwata har abada, gara na bar duniyar. Dan Allah kada ku bari Iman tasan sonta ne yayi sanadiyyar mutuwata. Kada ku bari Huzaifa ya san halinda na shiga har yayi sanadin ajalina. Huzaifa ya na da kirki, yana son Iman zai riketa. Na godewa Allah da Iman ta samu miji irin Huzaifa, ina son Iman ta huta a rayuwarta saboda tasha wahalar rayuwa. Najib na gode da kokarin da kayi min da taimakona da kasha yi dan na samu Iman Allah ne Bai yi ba, na gode. Najib ya rushe da kuka ya rungume Suhaif suka kankame juna suna kuka su duka. Muslim yayi tagumi ya sa su a gaba yayin da idanuwansa suka cika taf da hawaye dan tausayi, yanzu ya gane makasudin damuwar Suhaif.
Sai kawai Suhaif ya mutu.
Labarin ya kare daga nan......... Lolx
Daga wannan Tuzurun na ku mai suna
Reedwan Suraj Isma'il
[[[[[[[]]]]]]]-----------YARENA ADDININA
***CIGABAN LABARI
Ana ta magana da fulatanci, a fassara da Hausa haka dai ake ta bayani a wajen daurin auren. Liman mai daura aure da waliyan ango da amarya duk sun hallara. Aka sanar cewa ga sadaki nan waliyan ango za su mikawa waliyan amarya, za'a daura auren akan sadaki naira dubu ashirin.
A lokacin da mai sanarwa a lasafika yayi sanarwa karshe sai da kowa ya gigice. Iman da kawayenta suka fito waje da gudu. Goggo da Mama da suke zazzaune a dakin Maman Iman da Maman Iman din da sauran mata suka kado da gudu falo. Maman Huzaifa da kannensa da danginsu mata a cikin gida sun yi wuf sun fito kofar gida. Najib da Suhaif da suka kankame juna suna kuka suka yi firgigit suka rabu. Shin meye ya gigitasu ne haka? Me aka ce da kowa ya firgice ya fito? Maza kawai aka sani a wajen daurin aure. Amma wannan daurin auren ya zama na maza da mata a cakude. Suna zaton wanda yake sanarwar ne bai jiyo dai-dai ba, ya yi kuskure sai suka ji ana mai-maitawa, wani ma ya karbi lasifikar yana sake mai-maitawa da Hausa, da fulatanci ba kuskure bane gaske ne an daura auren Fatima Lamin Gombe da Suhaif Hayatu Doko ga sadaki nan lakadan an mika, har aka kara salati goma da kulhuwallahu da sauran addu'oi aka shafa. Kowa ya kasa tafiya gida sai ya ji kwakwaf. Waye Suhaif? Kowa Huzaifa ya sani, kuma saboda shi aka zo daurin auren.
Huzaifa yana ta yiwa jama'a bayani cewa kada su damu haka Allah Ya rubuto, ya barwa Suhaif ya aureta. Saboda Suhaif ya zama dan uwansa duk daya ne shi da Suhaif din. Haka jama'a suke watsewa suna tafe suna sake jinjina wannan abun al'ajabi. Wasu kuma suna ta rububin zuwa kallon Suhaif mai tsananin rabo tsuntsu daga sama gashasshe. Masu daukar hoto da bidiyo suna ta bin Huzaifa da maroka, Huzaifa yayi dariya ya nuna musu Suhaif ya ce "Ga ango can ku bishi. Huzaifa ya mikawa Suhaif hannu suka gaisa ya ce masa, "Congratulation. Haka Suhaif yake kallon Huzaifa tamkar gunki ya rasa kalma guda daya da zai fara yiwa Huzaifa ta godiya. Mamaki marar misaltuwa a fuskar Suhaif da Najib. Suhaif a cukurkudansa yake, babbar riga a hannunsa takalminsa a hannun Muslim, hularsa a hannun Najib haka suka yi wuf suka fito daga dan sakon da suka labe. Sai Huzaifa ne ya ankarar da su ya ce "A'a yaya ango a haka ku saka masa rigar da takalmin mana.
Huzaifa da jama'ar da suka baibayeshi ya na ta musu bayani suka dunguma suka yi can bakin titi inda suka ajiye abubuwan hawansu. Baba na Doko, Baba na Kano, Baban Iman da Baban Huzaifa ne suka fito daga falon su Iman. Najib ya tare su ya ce "Baba ya aka yi haka ta faru? Sai Baba na Kano ya ce "Yauwa, ina Suhaif din? Ku taho gaba dayanku. Ku aika akira Iman, Mamarta, Mamanku Goggo duk ku zo mu hadu a falon Baban Huzaifa za muyi magana. Suhaif ya kalli Najib, Najib ya kalleshi. Suhaif ya ce "Tabani ko mafarki nake yi. Najib ya mintsine shi a keya ya ce "Ka ji zafi? Suhaif ya shafa wajen ya ce "Eh naji zafi da gaske ne kuwa ashe, Najib kaganni na warke na daina jin ciwon komai. Najib da Muslim suka kwashe da dariya.
Yadda mamaki ya hana Suhaif sakat haka ya yiwa Iman wanna illar ta kasa sukuni, ta shiga ta fita ta tambayi kawayenta anya kuwa kunnuwanta sun jiye mata dai-dai, Suhaif aka ce? Kowa yana shaida mata abunda taji gaskiya ne, Suhaif ne angonta. Sai take tambayar su Naja'at wadanda murna ta cika musu ciki wai ya akayi haka ta faru? Suka amsa mata suma da suke a nan cikin gida tare da ita basu sani ba. Hajara kanwar Iman ce ta zo tayi kiranta ta ce ta zo za'a shiga meeting da Iyayensu, Naja'at da Zubaida ma suka bita. Gaba daya sun hallara a falon, Huzaifa kadai ake jira. Duk wanda ka kalli fuskarsa a wajen yana cike da tsananin mamaki da jinjina ga Allah bisa ikonSa daya nuna yanzu-yanzu nan. Ikon Allah ya wuce haka. A jima Goggo ta ce "Allah mai iko. Mama ta ce "Ikon Allah. Baba na Doko ya ce "Allah mai girma, Baba na Kano ya ce "Allah Ya wuce haka. Suhaif ya girgiza kai ya ce "Cafdijam, Allah kenan, Najib ya ce "Ka godewa Allah ka sake gode masa. Mamar Huzaifa tayi ajiyar zuciya ta ce "Haka ne komai da yadda Allah yake tsara shi. Iman ta sunkuyar da kai kasa, a jima tayi ajiyar zuciya ta ce "Uhm.
Huzaifa ya shigo da fara'arsa ya ce "Don Allah kuyi hakuri na barku kuna jirana, mutane nake ta sallama. Ya tafi kusa da Suhaif ya zauna, yayi shiru yana sauraron abunda Mahaifinsa ke cewa. Bayan Mahaifin Huzaifa ya bude taro da addu'a cikin harshen Hausa yake magana ya ce "Ba mu kadai ba yau duk wanda ya halacci daurin auren na ya tafi da dimbin mamaki, har wanda za'a bawa labari a wani waje zasu yi mamakin abinda ya faru yanzu-yanzun nan. Amma duk abunda aka ce Allah ya wuce mamaki. Gaba daya suka dauka "Haka ne, gaskiya ne.
Baban Huzaifa ya ci gaba da cewa "Kamar yadda ku kaji haka, nima haka naji. Cikin daren jiya misalin sha biyu, har dakina Huzaifa ya je ya tasheni ya shaida mun yana ganin zai hakura da Fatima ya barwa Suhaif. Na rasa meye Suhaif? Ya ce suna ne Baba, Suhaif bakin da suka zo daga Kano. Na tambayeshi kamar yaya zaka bar masa Fatima? Kamar wata shadda ko yadi ko atamfa da ya gani a jikinka ya ce yana so. Yayi min bayani mai tsawo har sai da na gamsu. Na shi masa albarka akan tausayawar da yayi, ya sani a gaba cikin dare muka taso Mahaifin Fatima, shima da kyar ya gane abunda muke fada masa. Ga bacci a idonsa ga wani cukurkudaddan labari. Bayan ya gamsu da hujjojin Huzaifa sai yayi addu'ar Allah Ya zaba abunda yafi alheri. Dashi muka dunguma a mota zuwa Hotel din da Mahaifan Suhaif suke, suma da kyar muka tashe su suka bude mana kofa muka shiga muka zauna. Mun kayi musu bayanin abin dake tafe damu sai suka ki amincewa da farko. Suka ce baza'ayi haka ba, su da suka zo daurin aure sai a buge da daura musu. Huzaifa yayi musu bayani cewar babu damuwa, karsu damu Allah Ya sani tsakani da Allah ya yiwa Suhaif wannan kyauta daga yanzu sun zama madauri daya. Suma suka yi ta godiya dashi albarka. Huzaifa ya rokemu kada mu bari wani ya sani musamman mata, idan aka daura zasu ji don haka har ita Fatima da Suhaif din basu sani ba.
Najib ya yi gyaran murya ya ce "Baba wanne bayani Huzaifa yayi muku haka har ku ka gamsu ku ka yarda? Baban Huzaifa ya yi dariya ya ce "Waka a bakin me ita tafi dadi, gaka ga Huzaifa a kusa da kai. Huzaifa yayi dariya yayi gyaran murya ya gyara zama ya ce "Na kasance tare da Fatima tun da aka haifeta, ina daukarta har ta fara girma a wajena take yini. Idan tana kukan makaranta ni nake mayar da ita in bata alewa sannan ta zauna. Haka bayan ta fara girma ta fara sanin meye duniya, meye matsalolin duniya, ni take tara tana tambaya. Da kanta ta tambayeni addinai daban-daban, na wayar mata da kai, na dinga cusa mata addinina da yadda zata yi da kuma yadda zata yi taka tsantsan da rayuwar duniya. Har ta girma tasan ciwon kanta, tasan abu mai kyau da marar kyau.
Na tafi Madina makaranta na tafi da son Fatima amma na tafi da tsananin bakin cikinta, a tunanina Jaririn dana gani nata ne. Haka baisa na daina sonta ba, ko na tsaneta, ko nayi tunanin fasa aurenta. Ina karatu, har bayan shekara guda cur da tafiya ban samu nayi magana da mutanen gidanmu ba, a lokacin gidanmu babu waya sai dai idan na hadu da wanda na sani a can in rubuto wasika. Na hadu da matata Zainab *yar kasar Bahrain sun zo aikin Hajji ita da Mahaifinta, ta nuna tana sona har ta shaidawa Mahaifinta. Abu kamar wasa, da farko naki yadda saboda ina ganin da wacce na ajiye anan ina tunanin ita zan aura, domin ina ganin nine kadai zan iya aurenta da da, in kuma tsaya tsayin daka in ga ta kula ko taci gaba da addininta tun da Uwa da Uba duk ba Musulmai bane. Mahaifin Zainab ma ya ki yadda ya ce ba zata aureni ba, amma ita ta dage har sun koma kasarsu sai naga sun dawo. Ni da Mahaifinta muka zauna muka yi magana sosai ba yadda na iya, da ya amince sai nima na amince.
Mahaifina da *yan uwansa suka je can Madina muka hadu muka tafi Bahrain zancen auren. Daga Bahrain muka dungumu da ita da Mahaifinta mu ka zo Nigeria suka ga gidanmu da asalina. Anan aka daura mana aure, amma kafin aurenmu na shaida mata akawai wacce nake so kuma munyi alkawarin aure da ita sunanta Fatima, rayuwata kankat ita nake da burin aura kuma ko yau idan Allah Yayi zan iya auranta. Zainab tana sona tace duk ba matsala. A lokacin da na zo ban samu Fatima ba ance ta tafi an rasa inda take. Mahaifiyata tayi min bayani tas akan jaririn Fatima cewar ba danta ba ne. Nayi takaicin, nayi kukan batan Fatima har bayan na koma na dauwama a cikin yi mata addu'ar Allah Ya kareta duk inda take, duk da nasan neman ilimi take da kuma inda zata zauna tayi addininta.
Na haifi *yata ta fari na saka mata suna Fatima saboda son da nake mata. Kamar yadda dukkaninku ta baku labari na mata hanya ta je Saudiya karatu muka sake haduwa acan, duk da ni a lokacin na kaura Bahrain amma koda yaushe muna waya kuma muna zuwa Hajji da Umara mu hadu. Na fada mata ina son in aureta sai taji banbarakwai domin ta daukeni tamkar Yayanta, ta nuna min ba zata iya aurena ba, badan bata sona ba sai dan wani girma da matsayi da take jina a zuciyarta. Ga kuma matata kawarta. Na nuna mata duk abubuwan data zano bai haramta aure tsakaninmu ba. Ta amince daga baya, tun a waya muka shaidawa Iyayenmu, babu wanda bai yarda ba a cikinsu
Mun hadu da Suhaif da Najib a satin da zamu taho daurin aurenmu. Bani da masaniya akwai tsohuwar soyayya a tsakaninsu, na dai kula Najib ya fi Suhaif fara'a da son hira. Sai na zata halittarsa ce haka, sai ban damu ba. Muka dunguma muka taho Abuja, to a ranar na fara sanin halin da ake ciki. Zan shigo kenan cikin falon da Najib da Fatima suke zaune sai na ji suna hira Najib yana shaida mata damuwar da Suhaif ya ke ciki a sanadiyyar sonta. Itama tana kuka tana fadar halaccin da Suhaif yayi mata. Abunda ya fi dagamun hankali shine da aka ce yaki aure saboda jiranta, kuma ba zai yi aure ba har abada idan ya rasata. Ban nuna musu naji hirarsu ba, a mota hanyarmu ta zuwa Kano nake tambayarta yadda suke da Suhaif ta bani labari tas zamanta a garin Doko, da taimakon da Suhaif yayi mata har da yadda suka yi da matsafan da suke cutarta. Amma bata ambaci kalmar soyayya da take tsakaninsu ba saboda kada in sani raina ya baci.
Na ci gaba da kula da Suhaif da halin damuwa da yake ciki, tun daga Kano har zuwasu daurin auran nan. Tuntuni nake tunani ko na bar masa ita tunda yana tsananin sonta? Sai na shiga kokonto ina zulumi domin ina sonta nima, idan na bar masa ita kuma zan cutu. Naci gaba da addu'ar Allah Ya zaba mana abunda yafi alkhairi kuma duk sanda zan kwanta barci sai nayi istahara Allah Yasa inji zabi mafi alheri da yafi kwantamin a zuciyata. Jiya da daddare ana hira sai Suhaif ya tashi ya fito, Fatima ta biyo shi, ni ma sai na biyosu. Na ji duk abunda suka fada, yana kuka tana kuka har Suhaif ya ce tayi masa addu'a idan ya mutu. Ya roketa kada ta bari in san ciwon son ta ne ya kashe shi.
Dukkanmu nan Musulmai ne, duk Musulmu ya san Hadisin Annabi da ya ce "Imanin dayanku ba zai cika ba har sai ya sowa dan Uwansa abunda ya sowa kansa. Ina son Fatima, Suhaif ya na son Iman fiye da ni, har yana kokarin haramtawa kansa aure gaba daya a rayuwarsa, yana kokarin rasa ransa saboda sonta. Itama tana sona amma kuma tana kukan rabuwa da shi tana tausayinsa, zata dauwama cikin tausayinsa musamman idan ya rasa rayuwarsa a kanta.
Nayi koyi da hali, dabi'a, kirki da karamci irin na mutanen Madina. Yadda suka yiwa Manzon Allah (S.A.W) a lokacin da yayi Hijira daga Makka zuwa Madina shi da Sahabbansa. Mutanen Madina da murna suka tare shi, su raba gidajensu suka basu rabi, wasu su saki matansu suka aura musu. Don haka ko da ace na auri Fatima zan iya sakinta in bawa Suhaif ya aura. Idan na auri Fatima na so kaina da yawa saboda ina da mata guda daya, shi kuma Suhaif ba shi da ko guda daya, yana cikin ukuba da tashin hankali ya rasata, ni kuma ina cikin walwala da jin dadi zan aureta. Sai naga bazan iya yiwa dan uwana Musulmi haka ba. Na yanke hukuncin na barwa Suhaif Fatima ya aura ni na hakura. Alla Ya dubi zuciyata Ya san dan shi nayi, sai Ya yaye mun damuwa da bakin ciki. Yanzu haka ni da Ubangiji ne kadai nasan dadin da farin cikin daya rufe min zuciya. Gaba daya suka dauki kabbara, Iyayen Suhaif, Mahaifansa Huzaifa, Mahaifan Iman suka dinga shi masa albarka. Hawaye ke zuba a idanuwansu su dukka harda Huzaifa. Suhaif ya rungume Huzaifa ya kasa magana sai hawaye kawai ke zuba. Iman ta rungume Mahaifiyarta su dukka kuka suke.
Mahaifiyayar Iman ta share hawaye ta ce "Lallai sai yanzu na sake gaskatawa, na sake rungumar addinin Musulunci da karfina, zuciyata, da dukiyata gaba daya. Hakika Musulunci addini ne mai salama, addini ne mai girma, addinine mai karamci. Ya koyawa Musulmai son junan su, su hana kansu su bawa dan uwansu, a taba Musulmi daya suji kaman su duka aka taba. Suna da kishin addininsu, na kara gane gaskiya, gaskiya ce, na kuma gane addinin gaskiya. Allah Ya sanar dani hakan ta hanyar *yata ta cikina. Tun da cikinta kafin na haifeta ina mafarkan da suke min nuni da hakan zata faru nan gaba, sai na ki ganewa. Bayan na haifeta sai naga fassarar mafarkaina Musulma na Haifa, mai kira zuwa ga addinin Musulunci, duk naki yarda da gangan na danne sai daga baya naga da gaske Malama na haifa a cikina kuma tana kira zuwa ga gaskiya sai na yarda na bita. Na godewa Allah, Huzaifa na gode, Allah Zai saka maka sakayya da gidan Aljanna dalilin wannan abunda kayi. Huzaifa ya amsa da "Amin na gode Mummy. Mahaifiyar Huzaifa sai yanzu tayi magana ta ce "Huzaifa dana, na yarda da kai dari bisa dari. Nasan tausayinka, kana kaunar *yan uwanka da ma sauran Musulmi gaba daya. Nasan zaka iya haka, zaka iya abunda yafi haka. Mutane suna ta mamaki amma ni dana haifeka banyi mamaki ba. Tunda na sanka fiye da kowa, nasan halinka Allah Yayi maka albarka, Allah Ya saka maka da Aljannah. Hawaye a idon Huzaifa ya amsa da "Amin Fetal" yadda suke kiranta kenan.
Wayyo Allah! Ruwan kaina zai kare nima mutuwa zan kawai kowa ya huta tunda na rasa Iman ....... Lolxxx..
Amma dai bari na sa dangana in taimaki Hajara (Rabecca) in aureta.... Lolxxx
Reedwan Suraj Isma'il
_____________________ YARENA ADDININA
___CI GABAN LABARI
Huzaifa ya dubi matarsa Zainab cikin harshen Larabci ya ce mata "Zainab kinga rayuwa ko? Kinga muhimmancin hakuri ko? Kawayenki a can suna zuga ki wai danme zaki yarda ayi miki kishiya bayan ku a kasarku ba'a cika yin haka ba. Kika dauki zuga kina cewa saidai in sake ki, dakyar na shawo kanki to kin gani komai sai Allah Yayi. Idan ba wata kaddara ba mai tsanani bani ba kara aure har abada, daman ita ce kadai wacce nake tunanin zan aura. Zainab tayi murmushi ta gyada kai ta ce "Hakika na ga muhimmancin hakuri, kuma na sake gane zaman duniya. Na yi nadama ku yafe min. Ta dubi Iman ta ce "Ki yafe min. Iman na kuka