Showing 12001 words to 15000 words out of 110329 words
Chapter 5 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
ce "Aikuwa *yar Hajja ta fiku kyau abu daya zaku nuna mata kunyi sakandire ita kuma bata yi ba. Naja'at ce tayi sauri ta fito daga wanka don ta mayar da martani tana jiyo hirarsu daga ban daki. Tana fitowa ta ce "Wallahi *yar Hajja bata fimu kyau ba fari kawai ta fimu. Yaya Suhaif ya ma za'a yi ka kallemu kace dogari ne zai taya? Suhaif ya tsuke fuska ya gallawa Naja'at harara ya ce "Ke wuce ki bani waje. Idan ana wasa daku sai ku wuce gona da iri. Gwaggo ta ce "Kai kuwa wallahi shegen son girmanka ne yake hadani da kai inda Najib ya fika kenan. Idan baka yi wasa da kannenka ba da wa zaka yi? Yaje ya wanke hannunsa ya zo ya zauna a gaban Gwaggo ya sa hannu suke cin dumaman tare. Naja'at da Zubaida suka kama bakinsu suka yi sim suka shige daki ba su kara cewa komai ba.
Bayan sun shirya tsaf suka fito suka yiwa Gwaggo sallama za su tafi makaranta. Suhaif ya tabe baki ya bisu da kallo ya ce "Kalli dalla har da goge kafa da sa sabon takalmi wai don za su ga Sarki. Gwaggo ta ce "A'a, wai ina ruwanka ne? Ka takurawa *ya*yan nana nawa shi yasa har yanzu sun kasa sakin jiki da kai suna ta dari-dari da kai. Har Iman ta zo ta tarar da yadda suke yi maka ita ma ta shiga wasan buya da kai, a ce kai da *yan kannenka babu maganar arziki sai gwasala da harara da tsawa da tsare gida, haba Babangida ka zamar musu dodo a gida kana tsorata su. Naja'at da Zubaida suka wuce suka nufi kofar fita ba tare da sun tsaya sunji abin da Gwaggo za ta fada musu ba, kafin Suhaif ya huce fadan da ake yi masa a kansu. Gwaggo ta yi ta yi masa fada bai iya ce maya komai ba tsananin yunwar da yake ji kasancewar bai ci abincin kirki ba jiya saboda fargaba da tashin hankalin rashin ganin amsar Iman. Yau kuwa ya ji dadi hankalinsa ya kwanta da ya ji amsar ta don haka fadan da Gwaggo take yi bai bata masa rai ba ko kadan don ba kasafai yake jin abin da take fada ba. Zuciyarsa na can na tuno masa da dadadan kalaman Iman da ta rubuto masa da kuma kyakkyawar fuskarta da lallausan murmushinta, sai ya tsinci kansa yana murmushi da annashuwa da annuri.
Gwaggo ta yi mamaki tana yi masa fada yana ta murmushi yana fara'a ta ce "Ka zamar da ni kakarka ko Babangida wato dariya nake ba ka? Ya nisa ya ce: "Gwaggo yi hakuri ki kwantar da hankalinki in sha Allah a gidan nan na daina bacin rai balle *ya*yanki su dinga ba ni haushi wallahi daga yau za ki ga ina ta farin ciki da fara'a. Ko ba haka kike so in dinga yi ba? Ai shi ne yanzu na fara fara'ar don ki san na ji fadanki. Su duka suka kyalkyale da dariya ta ce "Ka dai zamar da ni Kakarka kana min shakiyanci iri-iri. Suhaif ya mike yana sudar hannu ya ce "Da gaske nake zaku ga canji a gidan nan daga yau sai farin ciki da annashuwa za ki ga ina ta yi. Ya karasa wajen wanke-wanke ya wanke hannunsa ya juyo ya dubi Gwaggo wacce har yanzu take zaune da kwanan tuwo a gabanta ya ce "Bari in shiga dakina in dan yi baccin awa daya sannan in tashi in yi wanka in tafi makarantar su Iman wajen taro. Gwaggo ta ce "Wanne irin baccin ne na awa daya kuma, yaushe garin ya waye da za ka yi wani bacci kuma? Suhaif ya ce. Don dai ba ki san irin baccin da nake ji ba da kin ce in yi ta bacci har azahar. Ya nufi dakinsa. Ya sa hannu zai bude dan karamin kwadon da ya sakale kofar dakin sai ya ga wata takarda an soke a jikin kwadon kofar dakin, ya yi matukar mamakin ganin wannan wasika. Ya ce a ransa "A'a Iman ce ta dawo ta sake sakale masa wannan wasikar ko kuwa aikowa ta yi aka kawo masa? Ya bude takardar da sauri ya ga lallai wasika ce kuma tasa ce. Tashin farko ma abin da aka rubuta My Dear Yaya Suhaif. Ya yi murmushi yayin da farin ciki ya lullube shi marar misaltuwa. Ya girgiza kai ya ce a ransa. "Lallai Iman ta kamu da sona ba da wasa ba, Allah ya kara mata fiye da haka don na san ko kama kafar son da nake yi mata ba ta yi ba. Ya linke wasikar ya bude kofar dakin ya shiga ya tura kofar ya rufe ya haye shimfidar ya kwanta zuciyarsa cike da farin ciki. Yasan babu tantama wannan wasikar zata kara masa armashin dimbin baccin daya addabi idanuwansa. Zata sa masa kayatattun mafarkan so da kauna.
Ya gyara filon da yake kwance sai mamaki mai dimbin yawa ya sake hawa kansa ganin wasikar an rubuta da harshen hausa kuma Iman bata iya rubutun hausa ba. Yaushe ta iya hausar ma balle ta rubuta? To amma bai yi mamaki ba watakila ta iya ko bai sani ba, ko kuma tasa a rubuta mata ne saboda kawai tana sha'awar yarensa hausa, daman idan kana son mutum duk wani abu nasa kana sonsa. Wasikar kamar haka:-
[[f9.heart]] My Dear Yaya Suhaif.
_____ "Gaisuwa irin ta addinin Musulunci, hade da ta *yan uwantaka da tsananin so da kauna. Yau Allah Mai kowa Mai komai ya bani ikon in bayyana maka sirrin zuciyata. Wani boyayyen al'amari mai ban mamaki da firgitarwa daga karshe kuma mai farin ciki. A matsayina na *yar uwarka kanwarka na kasance na dade ina dauke da wani ciwo mai illar gaske ga lafiyata, wanda ya dade yana cutar dani yana damuna ina ta sake-saken ina zan samo maganin cutar nan sai naga babu likita ko malami ko bokan da zai iya warkar dani sai kai saboda ciwon a sanadiyyarka ne kuma kai ne kasan maganinsa. Yaya Suhaif na dade ina sonka tuntuni na rasa yadda zanyi in fada sai yanzu naga ya dace in fada maka don naga zaka tafi bautar kasa kusan shekara guda gara kasan kabar marar lafiya a gida. Mai sauraran ka kawo mata maganin da zata warke shine ka amsamin bukatata ka agajeni ka kaunaceni jini daya ba wasa bane.
Kanwarka a da, Masoyiyar ka a yanzu
Zubaida Usman {Mrs. Suhaif} [[f9.heart]]
Yai firgigit ya wurgar da wasikar ya tashi zaune ya fada a bayyane "Zubaida! Zubaida!! Zubaida kike sona? Kin cuce ni, kin cusgunawa rayuwarmu da Iman. Zubaida dan me zaki dauko hanyar sa za'a bata zumunci da Iyayenmu? Bana sonki Zubaida ba zaiyu ba. Ya ji kwalla mai radadi tana zubo masa ya mike tsaye a fusace yana kai kawo daga karshen bangon dakin zuwa kofar dakin yana zancen zuci wani lokaci a bayyane. Ya dunkule hannayensa biyuu yana dukan bango.
Ai mun afuwa sakamakon yanayin jikina ya sa ban yi da yawa ba.
Ina tare daku
Reedwan Suraj Isma'il
_____________________ YARENA ADDININA
CI GABAN LABARIN
Ya shafa keyarsa ya juyo ya leka wundo yana duban hanya yaga ta ina su Zubaida zasu bullo yanzu yayi wasan kura da ita har Naja'atun yasan bakinsu daya. Ya ce a ransa "Muddin Gwaggo da Baba suka ji wannan maganar to fa kashinsa ya bushe dan kamar anyi an gama kada ma iyayen Zubaida suji labari ai sai sunfi kowa murna saboda suna son Zubaida sosai. Da wanne ido zan kalli Najib dan uwana kuma abokina ince bana son kanwarsa uwa daya uba daya? Dubi irin kauna da mutuncin da Babansu, Baba Usman ya nuna mun kamar shi ya durkusa ya haifeni tun daga Nursiry har Jami'a shi yake biya min ya rikeni tsakani da Allah. Bani da kwabo, bansan yadda ake samowa ba duk daga aljihunsa nake samu, Duk sanda naji rashin kudi kawai sai in nufi wurinsa zai bani ko nawa nake so har wani lokacin ya hana dansa Najib ni ya bani. Da wanne ido zance bana son *yarsa Zubaida? Zubaida me yasa zaki mun haka? Danme sai ni kike so ba wani ba? Yaya zanyi da son Iman din daya ke kokarin ya lahantani gashi na furta mata itama ta kamu sai ta dauka yaudararta nake, bata da uwa ba uba ba dangi ni kadai zan aureta in rufa mata asiri in zama farin cikin rayuwarta. Na zame mata uwarta, ubanta, mijinta, danginta. Bazan so wani ya auri Iman ba in bani ba. Ba zai yuwu ba, bazan iya rayuwa ba Iman ba abar kaunata, bazan iya auran *yar uwata kuma in wahalar da ita ba. Don babu wannan soyayyar a tsakaninmu.
Haka Suhaif ya kasance a daki shi kadai kamar zautacce, ya kasa zama ya kasa tsayuwa ya kuma kasa kwanciya yana magana shi kadai. Idonsa yayi jajawur kamar tattasai ga rashin bacci ga tsabar tashin hankali. Zuciyarsa tafasa take kamar zata kone. Jiran isowar su Zubaida yake kawai ya dirar mata don zai iya kacaccalata yake ji kamar yadda take shirin kacaccala rayuwarsa yanzu nan.
Karfe biyu dai dai taro ya watse kowa ya kama gabansa. Yana tsaye a kofar gida bayan ya fito daga masallaci sunyi sallar azahar yana duban hanyar da zasu bullo. Sai ya hango Iman ita kadai ta nufo gida. Murmushin dole Suhaif ya kirkiro ya yiwa abar kaunarsa. Ta gaisheshi ya amsa mata, tayi kamar ta tambayeshi me yasa baije wajen taron ba don bata gan shi ba sai taji ta kasa yi masa magana ta wuce cikin gida kawai yaci gaba da tsayuwa yana dai ta sauraran isowar su Zubaida. Yaji shiru har biyu da rabi, ya juya zai shiga cikin gida zai tambayi Iman a ina tabar su Zubaida sai ya hango suna tafe. Suna karasowa inda yake tsaye ya kula da irin kallon da Zubaida take yi masa mai kunshe da kauna da tsananin kunya. Ya buga musu uwar harara lokaci guda suka dukar da kansu kasa. Naja'at ta ce "Sannu Yaya. Bai amsa mata ba suka wuce sum-sum zasu shiga cikin gida. Ya juyo a fusace ya ce "Ku shiga dakina ina son ganinku. Nanfa suka ji gabansu ya yanke ya fadi don yadda suka ga fuskarsa ba annuri lallai baiji dadin wasikar ba dole ne shima ya bata musu rai kamar yadda suka bata nasa. Gashi Gwaggo bata san sun dawo ba tana dakinta balle tazo ta taimake su. Me kwatarsu yau sai Allah. Cikin rawar jiki suka shiga dakin, ya biyo bayansu ya shiga ya mayar da kofa ya datse. Ya juyo a fusace ya kallesu yaji haushinsu ya kara kamashi musamman Zubaida. Ya daka musu tsawa mai firgitarwa ya ce "Duk kumin knell down ku daga hannu ku rufe ido. Ya dauko ashar ya narka musu. Sai suka hau rawar jiki suka yi abunda ya umarcesu. Ya koma kan kujera ya zauna yana fuskantarsu, yayi shiru ya rasa ta inda zai fara. Can yayi wani dogon tsaki ya girgiza kai ya gyara zama ya ce "Naja'atu da shawarar ki Zubaida ta rubutomin wannan wasikar? Kada ki kuskura kimin karya zan tattakaki idan baki fadamin gaskiya ba. Cikin rudani da fargaba Naja'at ta ce "Zubaida ta dade da fadamin tana sonka nayi mata nasiha na bata shawara karta kuskura ta shaida maka nasan ma ba zaka yarda ba kuma idan ka ji ba ita bama ko ni sai raina ya baci muka bar zancen. Kwannannan muka tace gaskiya ko zaka kasheta zata rubuta maka don ita tana sonka. Shine muka yi shawara ta rubuta ta soka a jikin kofarka.
Ya juya ya dubi Zubaida ya ce "Na miki kama da sa'anki da zaki ji kina tsananin sona a ranki? Ta yi shiru bata yi magana ba, sai hawaye da yake zubowa daga idanuwanta. Ya daka mata tsawa da karfi mai firgitarwa ya ce "Ki bani amsa ba kukan munafunci nace kiyi mun ba? Cikin shesshekar kuka ta ce "A'a Suhaif ya ce "To dan me zaki dubi kwayar idona ki ajiye mun wannnan wasikar ta soyayya. Kamar yadda ba za ki iya rubutawa Najib ki ce kina son sa da aure ba, haka kamar yadda aure ya haramta tsakanina da Naja'atu ina so ki sa wa ranki babu zancen aure a tsakaninmu ko soyayya. Idan na sake jin wata kalma ta so daga bakin ku sai na lahanta ku munafikai. Sai shesshekar kukan Zubaida ne yake tashi. Can bayan *yan mintoci babu wanda ya iya magana sai Suhaif ya ce "A cikin iyayen mu wa kuka sanarwa da wannan maganar? Naja'at ta yi caraf ta ce "Wallahi babu wanda ya sani ko Gwaggo ba mu fada mata ba. Iman ma ba ta sani ba ni da ita ne kawai muke maganar. Suhaif ya ce "Ko a Kano ba ku fadawa kowa ba? Naja'atu ta ce "Ba mu fada wa kowa ba. Suhaif ya yi ajiyar zuciya mai dauke da kwanciyar hankali, can ya nisa ya ce "Alhamdulillahi, babu wanda ya ji ko? To ba na son in kara jin wannan kalma ta so daga gare ki Zubaida balle wani ya ji, ka da ku kuskura ku fada a cikin gida a nan ko a Kano saboda abu ne marar yiwuwa ni ba sa'anki ba ne da za ki ce kina sona muddin kuka daga zancen wani yaji, hakika za ku ga bacin raina, kunga yanzu sakwa-sakwa na yi muku. Don haka ku tashi ku tafi zance ya wuce, kada a sake. Naja'at ta mike da sauri ta duka ta yi godiya ta fice. Zubaida ce take tafiya a hankali tana harare-harare tana bata rai, har ta fita. Suhaif yana harararta cike da tsantsar takaici, bayan ta fita ya rike baki yana girgiza kai ya ce a ransa "Lallai yarinyarnan daga dukkan alamu ba ta hakura da ni ba, ba ta ji fadanda na yi mata ba. Wai yaushe na sakar mata fuska har ta shaku da ni ta fara so na? Yarinyar nan za mu sa kafar wando daya da ita a gidan nan.
Suhaif da Iman sun ci gaba da son junansu amma babu wata alama da *yan gidan za su gani su ce akwai soyayya a tsakaninsu, sai dai a boye suke rubuta wa junansu wasiku. A rana daya sukan musayar wasiku kamar sau biyar. Kowanne na fayyace me yake ji a ransa. Kafin ka ce kwabo kwayoyin sinadaran so sun yi yado a zuciyoyinsu. Kowannensu yana jin ba zai iya rayuwa ba idan babu dayan. Yadda Iman take burge Suhaif haka Suhaif yake burge Iman. Duk da kalar fatarsa baki ne yana yi mata kyau sosai. Halayensa ma sun yi mata, yana da ilimi a dukkan bangarorin, ga shi da fara'a, ga rikon addini ga tausayi, ga bin iyaye, ga shi ya iya kalaman soyayya.
Kwanci tashi, lokacin tafiyar su Suhaif bautar kasa ya karato don haka, kafin ranar dole Suhaif zaije Kano ya je makaranta ya karbo takarda, sannan ya wuce. Kallo daya za ka yi wa Suhaif ka san hankalinsa a tashe yake, ba bacin ran tafiya kudu ne ya dame shi ba, rabuwa da gida da iyayensa da *yan uwansa da uwa uba wacce yake matukar kauna da bege a zuciyarsa wato Iman. Matukar damuwa ta tabbata a zuciyar Iman, amma sai ta danne ba ta fito da shi a fuskarta ba, gudun kada *yan gidan su gane. Tana kicin tana dumamen tuwo ta jiyo muryar Suhaif a tsakar gida yana yiwa su Gwaggo sallama. Zubaida da Naja'atu suka yi farat suka fito daga daki suka nufi wajen Suhaif bayan sun gaishe shi sai suka yi masa fatan Allah Ya kiyaye hanya. Iman ta ji wani mummunan faduwar gaba da bacin rai ya kuntso zuciyarta, ta gyara hijabinta ta fito a sanyaye, yayin da Suhaif ya zuba mata ido yana duban ta. Ta sunkuyar da kanta kasa ta duka ta gaishe shi ya amsa gami da cewa. "To Malama Iman mu dai zamu tafi sai a saka mu a cikin addu'a Gwaggo tayi murmushi ta ce "Ai kuwa kasan inda ya kamata ka roki addu'a domin Iman gwanar addu'a ce zata yi maka kuwa. Su duka suka yi dariya harda Iman din cikin sanyayyiyar murya Iman ta ce "Insha Allah addu'arka ita ce farko a cikin jerin Addu'o'in da nake yi. Suka sake yin dariya dukkansu. Suhaif ya ce kinyi alkawari? Iman ta ce "Insha Allah na dauki alkawari. Zubaida da Naja'at suka hada idon gulma, sunyi mamakin yadda Yaya Suhaif yake ta yiwa Iman fara'a haka da kuma yadda Iman duk wannan kunyar tata ta tsaya suke magana haka wasa da dariya. Yaushe suka saba? Alamar tambayar da suka ajiye a zuciyar su kenan sai sun kebe zasu tsarge amsar.
Iman ta durkusa ta karbi Jakar hannunsa ta ce "Kawo in tayaka. "Naja'at da Zubaida tace. Zo muma mu dauki hijab dinmu mu raka shi bakin titi. Suka shiga daki da sauri suka sako hijabansu kafin su fito Zubaida ta radawa Naja'at ta ce. "Wannan Iman din ta cika feleke da shisshigi da cusa kai. Kalli yadda ta shigewa Yaya Suhaif har suka saba itace ma zata rakashi ba mu ba. Naja'at tayi ajiyar zuciya ta ce "Zo muje rakiyar mu dawo mu tattauna. Suka fito daga daki suka iske Iman da Suhaif da Gwaggo a tsakar gida bayan sun fito sai suka dunguma suka fice "Soron kofar gida Gwaggo ta tsaya da rakiyar sai addu'a take yiwa Suhaif da fatan Allah Ya kiyaye hanya ya kareshi daga sharrin Mutum da aljan. Yana amsawa da amin, suka juya suka tafi ita kuma ta shigo gida tana sharbar kuka na bakin cikin rabuwa da danta.
Zubaida ta mikawa Iman hannu ta ce "Kawo muma mu dauka ko tunda rakiya muka fito yi muma "Iman tayi murmushi ta ce "Haka ne, to gashi. "Wata uwar harara Suhaif ya dakawa Zubaida ransa ya baci amma baiyi magana ba suka ci gaba da tafiya. Naja'atu ta zo gefensa Zubaida ma ta dawo daya gefen nasa suka sashi a tsakiya. Iman ta koma baya tana biye da su. Naja'atu ta ce "Yaya Suhaif awa nawa ne zuwa Ogun? Naga akwai nisa ko? Suhaif ya tsuke fuska ya ce "Oho.