Showing 45001 words to 48000 words out of 110329 words

Chapter 16 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt

22 Feb 2025

7473

fada min bakar magana, tsakani na da shi sai wasa da dariya da nasiha. Ya dakamin tsawa gami da kawo min duka da gefen hannunsa na goce ya ce "Ba tambayarki nake yi ba kika yi shiru kina min kukan munafunci? Na ce sakamakon jarabawar kenan kika kamo hanya ki shigo min gida da goyan shege? Na sake rusa kuka, na kasa magana.
Mahaifiyata ta tambayeni ta ce min "Waye uban dan? Nayi shiru ban amsa ba. Ta sake daka mun tsawa "Waye yayi miki ciki? Na share hawaye na ce "Ina so inyi bayani. Mahaifina ya daka min tsawa ya ce basa son bayani na, in amsa musu tambayar da ake min. Waye uban dan? Cikin rawar murya na ce "Wani ne mai suna Micheal a Bauchi yake. "Micheal suka hada baki suka maimaita. Na gyada kai na ce "Eh. Mahaifina bai kara magana ba ya koma ya jingina da kujera. Mahaifiyata sai ta hau murmushi. Abun ya bani mamaki. Ta gyara zama ta ce "Meye addininsa? Nayi shiru can na ce "Addinin ku daya. Ta harareni ta ce "Addininmu daya banda ke? Taci gaba da cewa "Naji dadi da Allah Ya sa addininmu daya, kina da labarin Mahaifinki da kannanki mun zama addini daya muke bi, kin ci sa'a kuma ga uban danki addininmu ne. Na daga ido na kalli Mahaifina sai ya kawar da kai gefe. Hawaye mai radadi ya zubomin. Dukkansu sun gane banyi farin ciki ba da wannan sabon labari dana ji, sunsan yadda nake kin addinin tun ina karama, su kan rasa to ni me nake bautawa. Na dora Jaririn akan kafadata ina jijjigashi don ya tsula min fitsari ya jikani ya hika zanin da aka nade shi. Nayi gyaran murya cikin marainiyar murya na ce "Nayi kuskure, nayi laifi, ku yafemin. Nima ba da son raina ba na bar makaranta inda ku ka turani karatu. Wannan yaron da kuke gani ba dana bane tsintarsa nayi. Su duka suka yo kaina kamar zasu cinyeni danya tun ban dahu ba don masifa, kowannensu na zagina da yarensa. Wai in rufe musu baki basa son karyar banza, su zan mayar yara. In tashi in basu waje kafin suyi ball dani da Jaririn. Na tashi cimak ina rusa kuka na nufi dakina da aka nuna min aka ce in koma in bar dakina na da. Tabita ta biyoni dakin ta fara lallashina ta ce inje kicin in zauna bari ta share mana dakin ta kade kura, ta shimfida mana wankakken zanin gado a tsohuwar katifar dake jingina a dakin. Haka kuwa akayi, ni da kayana kakaf na dawo dakin nan.
Tabita kullum na shigowa ta yiwa yaron wanka ta bashi madara nima ta kawomin nawa abincin. Sabida tashin hankali bana iya ci sosai. Allah Ya dubi zuciyata Yasa yaron ba mai rigima bane sosai. Baya min kukan dare duk da wataran a dakin Mama Tabita yake kwana idan mijinta yana aikin dare, me gadin gidan mu ne watarana ya kwana wata rana wani ke canjarsa. Tana kula da ni sosai da jaririn. Tana gasa masa cibiyarsa dare da rana da safe don haka a kwana uku cibiyar ta fadi. Mama Tabita tana kula dani, ko kadan bata ga alamar jego a tare dani ba audugar matan data siyo min tana nan ko budeta ban yi ba. Ga fama da take dani saina bashi nono, ni kuma naki sai dai madara.
A tsanake take tambayata gaskiyar al'amarin nan. Na zauna na bata labarin abunda ya faru tsaf. Ta gamsu dani ta kuma kara tausayamin da dan Jaririna. Ta ce min ba dan Mahaifana zasu ga laifinta ba, daman yanzu ma harararta suke idan suka ganta da yaron, da taje ta basu labarin abunda ya faru, amma ba zasu saurareta ba, na ce kawai ta kyalesu. Ranar da muka yi sati biyu da dawowa, da misalin karfe daya da rabi na rana, na fito daga gidansu Hamma Huzaifa da goyon dan Jaririna a baya. Na je sallar azahar kasancewar Mahaifiyata tana gida yau asabar bata je aiki ba. Sai naga wata mota katuwa baka kirar CRB tana biye da ni ana min hoon. Na juya na dubi motar sosai sai naga babu abinda nake gani kasancewar gilasan an fentesu sunyi duhu, kuma ban taba sanin me irin wannan motar ba, sai na sawa raina ba dani suke ba. Na juya naci gaba da tafiya na nufi hanyar gidanmu. Dai-dai get din shiga naji an sake matsa hoon an ja burki an tsaya dab da bakin get dinmu. Har na bude karamin get zan shige sai dai na sake juyowa na dubi motar. Sai naga an sauke gilashin. Yanzu ina iya ganin samari guda biyu a cikin motar gabadayansu sanye suke da kwabta-kwabtan bakaken gilasai a idanuwansu. Ina yiwa dayan kallon sani amma na kasa gane ko waye. Suka bude kofofin motar suka fito suka tunkaro ni suna min murmushi gami da kiran sunana "Pretty. Nayi kasake ina kallonsu naga da gaske ni suke tinkarowa sai na tsorata naja da baya, dogon sosai ya zare gilashin dake fuskarsa ya ce "Pretty baki gane ni bane?
Kallo daya na yi masa ba gilashin na gane shi Micheal ne. Wata uwar tsana da takaici da tuna baya suka ruftawa zuciyata. Sakon daya yayi yawa annurin fuskata kakaf suka gushe, na bata rai, na murtike fuska tamkar naga kashi mai tsutsa naja dogon tsaki gami da wata uwar harara na kada kai na fada get din gidanmu, suka yi wuf suka biyoni ciki. Micheal na rawar murya yana magiya in saurare shi inji sakon da ya zo min dashi, bai isheni kallo ba balle in saurari maganarsa. Ficik naji an fincikoni inda nake tafiya a arewa naga an juyo dani kudu. Micheal ne ya fisgoni ta baya. Cikin fushi na fara zaiyano masa kalaman batanci, da zagin da ban taba yiwa kannena ba balle kawayena ko balle uwa uba na gaba dani. Ransa ya baci ya dakamin tsawa ya ce "Ya isa haka, kanki ya zare ne, don me zaki ce in bar kofar gidanku bayan ga dana kina goye dashi. Na fusata na ce "Danka? Ya aka yi ya zama danka, daman kana da da? Ya sake fada cikin fushi "Ki bani dana sai kiga nabar zuwa gidanku. Na sake fusata na ce masa "Ban gane abunda kake nufi ba. Ya aka yi wannan yaron da nake goyo ya zama danka? Dan makwabtanmu ne na daukko raino. Yayi murmushi ya ce "Pretty kin dauka bani da labarin Harriet ta haifar min cikin da nayi mata? Ko bani da labarin ke kika dauki yaron? Wannan abokin nawa dan garin nan ne, bayan haka munyi waya da Fadila ta fadamin kakaf abunda ya faru, na nemo wannan abokin nawa a waya na sanar masa na masa kwatancen gidanku na ce ya zo ya bincika mun kin zo da jariri? Ya ganki da idonsa goye da Jariri da yayi kama da ubansa. Ko kin manta nasan gidanku, mun taba zuwa daukarki? Dan haka na shiryo nazo takanas dan inga dana.
Nayi shiru tamkar ruwa ya cinyeni na rasa abun cewa, na tsani Micheal bana kaunar ganinsa, amma kuma ina son dansa bana son rabuwa dashi kuma na saba da shi sosai a cikin sati biyun nan. Kamar daga sama naji Micheal ya ce "Pretty me zai hana muyi aure mu rike yaron nan. Kina da labari har yanzu son da nake yi miki yana nan? Na fusata bansan sanda na fisge zanin goyon da nayi ba, na kunto yaron daga bayana na dungura masa dan gami da cewa "Idan danka ne gashi nan, ko bayan raina bana son ka matso kusa da gawata balle ni da kaina in aureka. Na fashe da kuka na juya naci gaba da tafiya. Kukan da yaron yake tsalawa ne naji tamkar mashi ake caka mun a zuciyata. Babu abinda ya fadomin a rai sai idan na barshi ya tafi da yaron nan ko shakka babu sunansa ba Musulmi ba, idan ma ba a ci sa'a ba ya tashi cikinsu *yan fashi ya koyi fashi da iskanci da shaye-shaye irin na ubansa. Sai na ji na tsaya cak, na juyo na dubesu suna nan a tsaye suna kallona. Na juyo na dawo na mikawa Micheal ya miko min dan na rungumeshi ina kuka, har cikin raina bana son rabuwa da dan nan duk rintsi. Aka rasa mai yin magana har tsawon wasu *yan mintuna. Sai Micheal ya ce in zo bakin mota in ga wani abu. Naki tafiya saida yayi ta min magiya sannan na bishi a baya, abokinsa ma na biye damu. Fargaba nake karfa su danke ni da jaririn su wurga a cikin mota, sai baya-baya na keyi. Ya bude mun but din motarsa na kalla babu abinda nake gani sai hadaddun akwatina guda biyu manya-manya. Koda ya budemun ciki sai naga tsala-tsalan rugunan Jarirai ne masu kyau da laushin gaske *yan waje masu tsada, ga pampers katan guda. Daya akwatin kuma leshina ne da atamfofi da shadda har da takalma da jakarsu da turaruka masu tsada. Cikin fushi na ce "Mungode amma ka juya da abunka bama bukata. Na yi gyaran murya na ce "Micheal ka yiwa Allah ka dubi girman iyayenka ka rabu damu ka daina zuwa gidanmu balle iyayena su ganka, ka kuma cirewa ranka zaka aureni har abada, na riga na shaidawa iyayena duk yadda aka yi Harriet ce ta haihu na taho da dan kuma ita kanta bata san wanda yayi mata cikin ba. Kana da kunya yanzu zaka dubi idona kace dan gidan Harriet danka ne? Ka manta lokacin da take sanar maka cewar har yanzu cikin da kayi mata bai zube ba? Kace mata duk ranar da ta kawo maka da ko *ya ta ce naka ne sai ka fasa dan? Ka manta ranar da zata haihu bamu da kudin zuwa asibitim nayi maka magiya ka zo ka kaita asibiti ka ce kai ba danka bane su mutu mana. Ka manta ne Micheal? Hawaye yaci gaba da kwaranyo min yayin da Micheal ya sunkuyar da kansa kasa yayi shiru. Abokinsa na cikin mota a zaune yana saurarenmu, sai gyada kai yake yana sauraron wannan abun al'ajabi.
Ma sharbe hawaye na sake rungume yaron na ce "Kamar yadda kace Harriet ta mutu idan har kai zaka kaita asibiti, to baka kaita asibitin ba kuma ta mutu. Amma kafin ta mutu cemun tayi in rike danta amana bata cemun in kaishi wajen Mahaifinsa ba. Micheal ina rike yaron nan ne saboda kawata marigayiya Harriet badan kaiba. Ka cuceni ka hanani karatu amma duk nawa mai saukine tunda baka batamun rayuwa ba ka yaudareni. Wa danda ka yaudara ka rabasu da makaranta, ka yiwa Harriet ciki, Janet ka hadata da abokanka ta zama *yar fashi daga karshe kai musu sanadiyyar barinsu duniya dungurungun. Ka tafi ka bani waje bana son ganinka zan rike dan Harriet amana, kuma in Allah Yaso bazai zama mai irin halinka ba. Na juya na nufi gida ina sharbar kuka nabar Micheal anan tsaye abakin but tamkar an gina shi.
Ina shiga ban tsaya ko ina ba sai na nufi dakina da sauri ina shesshekar kuka. Mahaifiyata na wuce a falo tana karatun jarida ita da Mama Tabita tana gogo-goge suka bar abunda suke yi cak suka bini da kallo. Ina shiga daki na datse, na haye kan katifa na bude sabon shafin kuka, yaron ya bude idansa yana ta tsotsar hannu alama ma yunwa yake ji. Nayi kuka ya ishe ni nayi addu'a Allah Yasa Micheal ya tafi ya rabu dani kar Allah Ya sake bashi ikon dawowa. Na tashi na tsiyayo ruwan zafi a flaks na dama masa madara ina bashi. Hirar da Tabita take yi da Mahaifiyata ita ta tsayar dani daga abunda nake, nayi tsai ina sauraronsu. Labarin dana bata na game da Micheal da Harriet take bata. Abun mamaki kafin Tabita takai aya Mahaifiyata harta rufeta da fada wai karyar banza wannan labarin bana kamawa bane. Wai karya nake dana ne.
Muryar Mahaifina naji ya shigo sai kuma naji muryar maza da yawa da alama bashi kadai bane da baki yake tafe. Nayi sauri na karasa bashi madarar, na sake daukar zani na sabashi a baya na lallabo na bude mukullin dana datse kofa na bude kofar kadan na leko cikin falon. Gabana yayi mummunan faduwa a lokacin dana hango Micheal da abokinsa a zaune tare da iyayena suna gaisawa. Mahaifina ya ce "Nazo zan shigo na gansu a tsaye a jikin get da motarsu sunyi jigun-jigun, bayan mun gaisa suka ce mun wajan Fatima suka zo taki sauraronsu, ta shige gida ta barsu. Suna cemin daga Bauchi suke saina ce to su shigo. Mahaifiyata ta kalle su ta ce "Cikinku a kwai Micheal? Micheal yayi murmushi ya sunkuyar da kai kasa ya ce "Mama nine. Sai Mahaifina ya ce "Oh kai ne ka hana *yata karatu kayi mata ciki? Micheal ya yi shiru ya sunkuyar da kai kasa. Mahaifina ya rikice da fada inda ya shiga bata nan yake fita ba fada yake tun karfinsa tsakani da Allah. Har fadi yake sai dai kotu ta raba su. Mahaifiyata tana lallashinsa tana bashi baki da kyar ya fara saukowa. Micheal da abokinsa suka durkusa gwiwoyunsu a kasa suna rokon a gafarta masa yayi kuskure.


A tunanina da Micheal yaji zancen kotu zai fadi gaskiyar abunda ya faru, cewar bani ya yiwa ciki ba kawata ce kuma ta mutu a garin haihuwa na dauki yaron. Sai naji Micheal ya kaikaice ya narkar da murya yana bada hakuri wai haka Allah Yayi, ya san bai kyauta ba da yayi sanadiyyar hanani karatu. Amma son da yake min ne ya ja haka, yanzu ya zo ne ya ga dansa ya kuma kawo masa kayan haihuwa kuma a radawa dan suna kuma in da za'a yadda a bari ya aure ni don mu rungumi dan mu. Kuma ya dau alkawarin zai rike ni da dana amana cikin wadata da kulawa kuma zai dau nauyin karatuna tun daga degree har sama da haka idan ina so kuma a kowacce kasa kuma ko nawa za'a kashe. Tashi daya kalaman mayaudari Micheal ya sanyaya zuciyoyin Mahaifana, suka ji lallai Micheal ya dace abi shawararsa. Shine kadai mafita tunda ga da waye kuma zai aure ni da dan wani, gara ubansa. Daman babban takaicin shine karatuna dana rasa amma yanzu gashi na samu mai nemomin makarantar fiye da ta da, ai shikenan. Mahaifiyata ta gyara zama ta ce masa "Micheal meye addininka? Ko da ya fada mata, taji addininsu daya sai suka hau dogon kwatance. Daga karshe sai ta gane Mahaifiyar Micheal mai bi ce sosai itama, shugabar wani babban wajan bauta ne a Bauchi. Tun Mahaifiyata tana ATBU nan take zuwa bauta duk ranar bauta. Zata iya tuna Micheal lokacin yana yaro karami. Lallai Micheal ya fito daga gidan manyan mutane, ga arziki ga addini. Farin ciki ya rufe Mahaifiyata daman ita babban burinta taga na auri miji wanda ba Musulmi ba domin ta kula dani bana son addininta. Huldata da Hamma Huzaifa ma bata so, saboda ta fuskanci akwai ranar da zata ji wani labari na game da aure a tsakaninmu domin shakuwar da kaunar junanmu tayi yawa. Ashe ita wannan Jaririn gaba ta kaita wai gobarar Titi a Jos.


Hmmm ku huta da karatu anan
Wanda ba su ga farkon na biyu ba su shiga wajen "Show More" yayi kasa zai gani


Reedwan Suraj Isma'il


________________ YARENA ADDININA.
___CI GABAN LABARI


Mahaifina baiyi magana ba daga dukkan alamu wannan labarin auren baiyi masa dadi ba. Baiyi niyyar aurar da ni yanzu ba nayi kankanta a lokacin shekaruna goma sha biyar. Amma yaya zaiyi na dauko goyo? Gara in tafi can da dan mu karata. Mahaifiyata na cikin farin ciki ta kwallawa Tabita kira ta ce "Ta kawo musu ruwa da lemo. Micheal ya cewa abokinsa ya je mota ya dauko akwatina da kwalayen da yayi mana shopping.
Matukar bacin rai ya darsu a raina bansan sanda zuciya ta fito dani falon ba na tsaya a tsakiyar falon gaban Micheal da Mahaifana na ce "Micheal karya yake yi bani ya yiwa ciki ba kawata ce. Don haka bazan aure shi ba. Mamaki marar misaltuwa zaka iya gani a fuskokinsu su duka. Mahaifiyata ta daka min tsawa ta ce in tafi in basu waje kar in yiwa mutane rashin kunya. Wana dauka kananan yara? Ai ana ganin Jaririn anga ubansa. Ita kawar tawa bata da hannun rike dan sai ni zan rike mata? Mahaifina ya ce to ai wannan maganar bata sauraro ba ce ya akayi na bar makaranta na shiga gari? Har kuma ina musu ina cewa ban haihu ba. Babu yadda za'ayi in dauko dan wata in tinkaro gidanmu da shi da sunan dan kawa. Micheal ya hau rantse-rantse har da sa hannu a aljihu ya dauko wasu hotunanmu daya ni da shi, daya kuma ni da shi da abokinsa, don ya iya munafunci bai dauko na ni da shi da su Harriet ba. Takaici yasa na nufi gidan Mama Tabita da gudu ina rusa kuka. Babu yadda zata yi da ni sai lallashi ta ce min inyi hakuri. Bubby kanina ya shigo ya iskemu cikin wannan hali ya dube ni duban tausayi ya ce "Aunty Rufkatu ki daina kuka kiyi hakuri, Mummy ta ce ki kawo Jaririn babansa zai ganshi. Tabita ta miko hannu zata kwance shi daga bayana na fisge na ce "Bazan bayar ba, Mama Tabita Micheal mugu ne baya tsoron Allah, shi yayi sanadiyyar mutuwar Mahaifiyar yaron nan yanzu kuma dan zai kashe, daman ya fada sai ya kashe dan duk ranar da aka ce dan sa ne. Bubby ya bude baki yana kallona cike da mamaki. "Kamar yaya Micheal yayi sanadiyyar mutuwar Mahaifiyar dan, ba kece mahaifiyarsa ba? Ya tambaye ni. Na sake rusa kuka na ce "Bani ba ce Bubby yayi wuf ya fice ya nufi gida yana zuwa ya tarar da Micheal da Mahaifanmu a falo a inda ya barsu, ya dubi Micheal ya dubi Mahaifiyarmu da ta aika shi ya ce "Ta ce ba zata bada yaron ba Micheal mugu ne shi ya kashe Mahaifiyar yaron ya ce sai ya kashe yaron shima. Nan fa aka hau kallon-kallo,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login