Showing 66001 words to 69000 words out of 110329 words
Chapter 23 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
ita ta kankame bishiyar da karfi tana yare wanda babu wanda yake jin yaren. Haka kuma bai hanasu daina ragargazarsu da ayar Allah ba. "Mu muna sonta tun kafin ta rungumi addininku. Ta fada cikin wata kakkausar murya wacce ko kusa bata yi kama da muryar mace ba, cikin harshen Hausa take magana yanzu. Wani Malami ya ce "Karya kuke makiya Allah yau sai munga bayanku azzalumai. Kamar yadda kuka kashe sai an kasheku. Ana ta karatu an zagaye bishiyar da ta rike ta rasa inda zata sa kanta, idonta yayi jajawur sai zufa take keto mata tamkar ana ruwan sama ta jike hagaf. Ta sake cewa "Kuna kona mu kuna kashe mana *ya*yanmu da jama'armu fa. Sai su kuwa masu karatun suka sake daga murya suna karatun da karfi. Ukuba tayi ukuba, zafin kuna yayi zafi, sai Iman ta fadi kasa numfashi sama-sama. Baisa sun daina karatu ba, ana ta jan ayoyi masu karfi. Matsafan ji suke kamar ana musu ruwan wuta. Yau sunga ta kansu sun gamu da gamunsu, a yau suka yi nadamar haduwa da Iman, sun yi dana sanin nacin da suka yi shekara dashekaru. Tuba suke, hakuri suke bayarwa daga yau zasu rabu da ita. Ko hanyar da tabi ma sun daina bi, amma tuba da nadamarsu yau baza tayi amfani ba. Babu mai sauraronsu, babu mai tausayinsu, babu mai shirin sassauta musu. Tun ana jin abinda Iman take fada har ta fara magana a hankali yadda ba'a fahimtar ta har tayi shiru bata ce wa komai ta rufe ido kamar mai bacci. Ba'a tsagaita da karatun ba yi ake tayi. Can Iman tayi magana wannan karon muryarta ce. Ta ce "Gaba dayansu gasu nan sun mutu, sun kone kurmus da wuta. Suhaif yayi ajiyar zuciya ya fada a baiyane "Alhamdulillahi. Ana ta karatun ba a daina ba har saida Iman ta tashi zaune daram tana kallon kowannensu daya bayan daya cike da mamaki. Sai ta tambayesu "Me yake faruwa? Suka tsaya da karatun itama suka tambayeta meya faru tsakaninta da matsafan? Ta yi shiru tana tunowa can ta ce "Na gansu suna ihu suna kamawa da wuta daga karshe suka fadi suka mutu, sun kone kurmus gaba daya garinsu ya kone kayan tsafinsu ma ya kone. Sai gaba daya *yan wajen suka yi kabbara. Malami daya daga cikin Malaman ya ce "Muna miki albishir kuma muna taya ki murna daga yau kin sami lafiya, kin rabu dasu har abada da izinin Ubangiji. Wannan wutar da kika gani tana konasu karatun da muka taru muka yi miki ne don haka mun konesu kurmus da ayar Allah.
Iman taji dadin da tunda uwarta ta haifeta bata taba ji ba. Sai ta rushe da kuka tana godiya ga Allah. Wani Malami ya ce "To ai shikenan sai ta dauki kayanta ta koma gidan su Suhaif ta ci gaba da rayuwarta, ku kuma jama'ar gari kunji da kunnuwanku ba laifinta bane don haka banda tsangwama da kananan maganganu. Samun mutum irin Iman sai an tona a wannan zamanin. Ta sadaukar da rayuwarta, ta sallama rayuwar jin dadin duniya saboda ta shiga Musulunci. Sai kowa yayi kabbara.
*Yan garin Doko gaba daya suka ji suna son Iman, saboda karfin Imaninta. Da gaske Iman take tana son Musulunci da *yan uwanta Musulmai. Yarinya mai kunya da ladabi, ko a hanya taga mutane zata yi musu sallama ta duka har kasa ta gaishesu. Haka jama'a suka gauraye wajen da yabonta. Suhaif yaji dadi sosai har kamar zaiyi tsalle don murna. Ya dauko jakar kayanta ya dauko mata takalmanta ya ce "Iman saka takalmanki ki zo mu tafi gida kiyi wanka, kici abinci ki huta kinji. Ta sharbe hawaye ta yi murmushin karfin hali ta ce "Na gode Suhaif Allah Ya saka muku da alheri kai da Iyayenka, *yan uwanka da mutanen Doko gaba daya. Ba zan kara ko kwana daya a garin nan ba, yanzu lokaci ne da zan koma gida wajen Iyayena in ga halin da suke ciki. Alhamdulillah abunda na zo nema na samu, na samu ilimin addinina. Zan iya kare addinina in kuma bada hujjoji masu karfi da za'a yarda abunda nake bautawa shine gaskiya. Hakika zan sami Iyayena in musu wa'azin da zai ratsa su, su karkato zuwa ga addinina musamman Mahaifiyata nafi ji, ta Mahaifina mai sauki ne domin yasan gaskiya karfinsa aka fi kawai. Ga Mama Tabita mai kaunata zan so ta kasance Musulma ba mushirika ba. Zuwana Kano da Doko na karu sosai, kuma a sanadiyyar haka na samu lafiyar ciwon da ya dade yana addabata.
Malamai su ka ce "Ai haka ya yi gara ki koma garinku ko hankalin Iyayenki zai kwanta, kin bar gida shekaru biyu kenan. Wannan hukuncin bai yiwa Suhaif dadi ba ransa ya baci, jikinsa yayi sanyi, ya shiga damuwa. Baya son Iman ta tafi ta barshi. *Yan sanda suka ce to ta shiga motarsu, su kaita Kano sai su sakata a motar garinsu. Suhaif ya yi caraf ya ce "A'a ku barta gobe zan kaita Kano in sakata a motar garinsu. Babansa yayi wuf ya katse shi ya ce "A'a ka bari tunda ga masu tafiya ka bari a kaita yau mana. Kafin Suhaif ya sake magana Iman har ta shiga mota, dan sanda daya ya karbi kayan Iman a hannun Suhaif ya saka a mota. Malamai suka shiga motocinsu, *yan sanda ma suka shiga, kafin aja motar *yan garin suka baibaye jikin wundon da Iman take zaune suna tayi mata sallama da fatan alheri. Iman tana hawaye tana mika musu hannu suna musabaha da bankwana ko rai kanga rai. Zubaida da Naja'atu suka zo wajen Iman, sai kuka ya kece musu su duka ukun. Zubaida tayi karfin hali ta ce "Iman ki yafe mana abubuwan da muka yi miki, baki taba yin fushi ba, baki taba kai kararmu wajen wani ba, bakya gaba damu. Cikin kuka Iman ta ce "Na yafe muku tuntuni Zubaida ku yafe mun nima.
Suhaif da Najib suka karaso jikin wundon Iman, sai kuka ya sake barkewa Iman ganin hawaye daga idanuwan Suhaif. Suhaif yayi karfin hali ya ce "Iman tafiyarki zata iya haddasamun abubuwa guda biyu, na daya zan iya rasa jin dadi a rayuwata har abada, na biyu zan iya kamuwa da ciwon rashinki har ya ja in iya rasa raina saboda damuwa. Iman karki tafi ki barni. Ta ce "Suhaif karka damu, kada rashina ya haddasa maka ciwo, Allah ne ya hada mu, kuma shine zai raba mu a yau. Shine kuma idan Ya so da izinin Sa zamu sake haduwa. Zai yi wuya in manta da kauna da halaccin da kayi mun a rayuwata, babu wani mahalukin daya taba sadaukar da rayuwarsa a kaina irinka. Ka soni a lokacin dana zama abar tsana, abar tsoro, abar gudu. Ina sonka nima bazan daina ba ko zai zamanto bazan sake ganinka ba har karshen rayuwata...... Ba ta karasa maganarta ba aka ja motar suka tafi. Tana hangen Suhaif yana ta bin motar da gudu yana ce wa "A tsaya! A tsaya!! Kuka mai zafi ya rufto musu ita dashi. *Yan gari suna ta dagawa Iman hannu har saida suka daina hango motar. Gwaggo da *yan matanta kuka suke tukuru na rabuwa da Iman. Haka jama'a da yawa basu shirya yin kuka ba, amma sai suka ji hawaye ya kece musu saboda bakin cikin tafiyar Iman. Sabo turken wawa, Iman ta shiga ransu sun saba da ita, ta saba dasu.
Zaku tausayawa Suhaif idan ku kaga halin da yake ciki, a cikin kasa ya zauna turmus yana damkar sawun tayar motar da Iman take ciki. Najib ya dade yana bashi baki amma kamar zugashi yake. Kowa ya watse ya barsu shi da Najib a wajen. Suhaif yaki tashi su tafi shi kuma ya kasa tafiya ya barshi, Suhaif sai rokon Najib yake Allah Annabi yake, ya tafi ya kyale shi anan shi ba zai koma gida ba, Najib yaki tafiya. Baba ya fito sallah Masallaci ya hangosu a zaune sunyi jugum-jugum ya zo ya same su, ya tambayesu me suke yi. Najib ya fada masa abunda yake faruwa. Ya shiga bawa Suhaif baki akan yayi hakuri ya manta da Iman Allah zai iya bashi wacce tafi ta. Suhaif yana dagewa shi fa Iman yake so gashi bai karbi adireshinta na garinsu ba, babu inda zai ganta. Haka Baba da Najib su kayi ta lallashin Suhaif da kyar Suhaif ya tashi suka nufi gida.
Iman ta tafi tabar Suhaif da tunaninta, begenta da tsantsar kaunarta. Baya walwala, baya son shiga mutane balle yayi hira dasu daga Masallaci sai dakinsa. Abincinsa kuwa idan yayi cokali daya, biyu, baya iya yin na uku sai yaji ya kasa ci. Babu abinda yake yi sai tunaninta wani lokaci ya debo wasikunta da hotunanta yana kallo. Sai ka ga hawaye ya surnano masa saboda tsananin damuwa. Abunda yafi tsaya masa a rai, shine irin wahalhalun da tasha a rayuwaarta shima yasa yaji ya kara sonta yana kuma tausaya mata yadda rayuwarta zata ci gaba da kasancewa bayan rabuwarsu. Yana ganin abu daya zai sa hankalin Iman ya kwanta a rayuwarta shine idan Allan Ya bata miji na gari mai tsoron Allah, mai sonta tsakani da Allah. Wannan mijin kuwa ba kowa bane illa Suhaif. Ina son Iman tamkar yadda nake son rayuwata, yadda bazan iya wulakanta rayuwata ba haka bazan wulakanta rayuwar Iman ba. Allah ka bani Iman. Ina zan sake ganinki Iman? Na rasa Iman na rasa mace ta gari, mai kirki, mai addini, mai kunya da tsananin tsoron Allah. Suhaif yana fada yana kuka.
Najib bai daina yiwa Suhaif nasiha ba har lokacin da ya shirya ya koma Kano. Mahaifan Suhaif basa jin dadin yanayin damuwar da Suhaif yake ciki. Suna ta bashi baki da nasiha kala-kala. Daga karshe Mahaifin Suhaif ya bashi shawara ya shirya ya koma Kano ko hankalinsa zai fi kwanciya, har Allah Yasa aikin da ake nemar musu ya fito. Suhaif bashi da zabi yasan Kano da Doko duk daya ne tunda ba Iman zai gani ba. Bai ki yarda da shawarar Mahaifinsa ba, ya shirya kayansa kakaf ya tafi Kano. Can ma bata sauya zani ba cikin damuwa yake, amma yana samun dan sanyi a ransa tunda koda yaushe Najib yana tare da shi dakinsu daya, su kwana su tashi tare. Ko zasu yi fada Najib bazai fasa fada masa gaskiya ba, yana cewa wannan damuwar daya saka a ransa babu abinda zata kara masa illa ciwo. Iman dai ta tafi zai yi wuya ta dawo dan haka gara ya barwa Allah komai, idan Allah Yaso zai sake hadasu kamar yadda itama Iman din ta fada sai su hadu. Tamkar dalmar wuta kalaman Najib suke yiwa Suhaif a zuciya, su Suhaif da Najib suyi ta fada wai dan me zai ce ya daina damuwa Iman ta tafi kenan. Daga baya Suhaif ya fara yadda da zancen Najib gaskiya ne babu alamar dawowar Iman, gashi wata da watanni. Sai ya fara bawa zuciyarsa hakuri yana daddaurewa yana fita wasu harkokin.
Baba Usman Mahaifin Najib ya shigo da wasu motoci guda biyu iri daya kalace kawai suka banbanta, daya kalar ja, daya kuma shudiya ce, motocin sababbi dal-dal a ledarsu, irin na zamani da kowanne matashi mai ji da kudi ko Mahaifinsa mai ji da Naira yake mafarkin samunta. Aka yiwa Najib da Suhaif albishir cewa ta su ce. Wai!! Wayyo Allah Najib yaji dadi har da ihu. Suhaif ma ya ji dadi sosai, suka je wajen Baba suka yi godiya suna baiyyana farin cikinsu. Baba yafi su jin dadi ganin yayi musu gwaninta kuma wadanda yayi dominsu sun gode.
Wai meya sanya wasu suke cewa ba'a tashi inda aka tsaya ne? Wa ya fada musu ana tsallake?
Gimbiya Zarah Matawata kenan ta ce ta ji dadi da ba'a mance da ita ba a wannan dandali..... lolxxx
:::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI
A falon Baba suka hadu ana ta hira, wasa da dariya ga Mahaifiyar Najib itama tana taya su godiya. Ta ce "Baban Najib sauran *yan matan Naja'at da Zubaida gashi suma kwanan nan zasu fara zuwa B.U.K kamata yayi suma a saya musu *yar karamar mota irin ta *yan mata koda guda daya ce su biyu a daukar musu direba ya koya musu. Bai musa mata ba sai ya ce "Suma na aika Germany a cikin motocin da za'a auno min za'a taho dasu Civic kowacce tata daban saboda idan ma aure suka yi su tafi da kayansu gidan mijinsu. Gaba daya falon ya hargitse da murna.
Suhaif ya sake dukawa yayi godiya ya tashi ya nufi dakinsa, yana murmushi a baiyane kada a gane labarin da yake zuciyarsa. Hakika Suhaif yaji dadi sosai da wannan abun arzikin da Baba na Kano ya birgesu shi da *yan uwansa, amma babu wacce ta fado masa sai Iman dama da ita zasu ci arzikin nan tare, yaji a ransa dama Iman tana nan su shiga motar tare, a zahirin gaskiya yaji baya son motar nan tun da ba Iman. Sai ya ji kuka ya kamashi ya kulle kansa a daki ya sha kukansa shi kadai yayi ya gaji. Bayan Doko daya tuka yaje ya nuna musu ya dawo babu inda yake hawa motar yaje kullum yana gida a kwance a daki. Ba kamar Najib ba ai shi tun ranar da aka danka masa mukullin motar idan ya fita da safe sai da yamma zai dawo ya ci abinci, yayi wanka, ya canja kaya ya sake fita sai karfe goma na dare kuma. Har yawon Najib ya fara damun Mamarsa tana masa fada tana masa misali da dan uwansa Suhaif baya fita ko ina kullum yana gida. Don an saya maka mota cewa akayi ka fita yawo da abokai? Sannan Najib ya fara dan zama a gida. Shi dai Suhaif ya zama tamkar mutum-mutumi a gidan bashi da tunani, bashi da abun yi sai ina zaiga Iman? Dama ya ganta, ko a wanne hali take ciki yanzu, yaya za ta kasance da Iyayenta? Aikinsa kenan tunaninta.
Suhaif na kwance kan gadonsa, daya daga cikin masu aikin gidan ta kwankwasa masa kofa ta ce da shi ya zo Baba na kiransa. Ya tashi ya nufi falon Baba ya iske shi shi kadai bayan sun gaisa ya tambaya "Ina Najib? Suhaif ya ce "Baya nan, Baba ya gyara zama ya shaidawa Suhaif cewar Naja'at da Zubaida sun sami admission a B.U.K. Zubaida ta sami Geography, Naja'at kuma Biochemistry. Suhaif ya yi murmushi gami da yi musu addu'ar fatan alkhairi da sa'ar farawa da gamawa lafiya. Sai Iman ta fado masa arai saboda su uku suke tare, gashi su biyu zasu fara Jami'a ya yiwa Iman sha'awar dama da ita. Jikinsa yayi sanyi idonsa ya ciko da kwalla amma bai bari Baba ya gane ba. Baba ya ci gaba da cewa "Don haka ka shirya kaje Doko ka dauko su Naja'at domin an ce min har an fara bayar da admission letter. Suhaif ya amsa da "To Allah Ya kaimu goben, sai Baba ya sake cewa "Ga wani sabon albishir din, na so ace kai da Najib kuna tare ku bani goran albishir. Suhaif ya tattara hankalinsa gaba daya yana sauraran abinda Baba zai fada cike da zumudi, babu abinda yake fata irin dama ya ce masa Iman ta dawo Doko. Amma sai ya tuna ashe Baba na Kano bai san Iman ba, sai dai Mama ta bashi labarin abubuwam da suka faru, da yake bashi da son labari a nan ya watsar bai sake tayar da maganar ba. Baba ya katse masa tunani ya ce "Kun sami aiki kai da Najib. Kai a Nigerian Port Authority Lagus, Najib kuma a Union Bank Kano Branch. Suhaif ya kurawa Baba ido yana kallonsa tamkar hoto. Wani tunani ne ya fado masa, yana tuna ranar da Iman ta hada masa takardunsa na neman aikin a wani file. Da hannunta ta rubuta masa takardar neman aiki da Baba ya ce su rubuta, ita kuma da kanta ta zaba masa inda zai zaba. Har Iman tana tsokanarsa tana cewa "Idan suka daukeka aiki a NPA kafin shekara ka zama mai kudin gaske, zaka yi mana wahalar gani sai mun cike form. Yau ga aikin ya fito amma Iman bata nan. "Kai lafiya, meke faruwa? Ka zama kamar gunki, tunanin me kake? Baba ya tambaya. Suhaif ya sunkuyar da kai kasa yayi shiru ya kasa magana, "Suhaif wai me yake damun ka ne, kwana biyu naga alamar akwai abinda yake damunka har ya shafi walwalarka baka son shiga mutane kullum kana kwance a daki shiru? Baba yake tambayar shi. Suhaif ya boye masa ya ce "Babu komai Baba, Baba ya ce "Akwai wani abu Suhaif, karka boye min ka fada min ko maye. Ko sai Baba na Doko kake fadawa matsalarka? Suhaif yaji zancen Baba banbarakwai yana nufin dai ko dan bashi ya haife shi ba. Suhaif da yaji haka sai yaga bari ya fada masa kada ya dauki wani abu daban. Sai ya gyara zama ya bawa Baba labarin Iman tun daga farko har karshe ya kuma shaidawa Baba son Iman ne kadai matsalarsa da damuwarsa. Baba yayi murmushi ya ce "Ai duk wannan ba matsala ba ce zamu je garinsu mu nemo maka auren Iman. Suhaif ya ce "A kwai matsala Baba saboda ban san adireshinta ba Baba. Baba ya gyada kai ya ce "Lallai tunda babu adireshi babu zuwa amma duk wannan ba zai sa ka ci gaba da damun kanka ba ka barwa Allah komai. Ya yiwa Suhaif nasiha kala-kala, ya bashi hakuri. Hakika Suhaif yaji dan sanyi-sanyi a ransa, yayi godiya ya tashi ya nufi dakinsa. Sun bar maganar aikin akan gobe za'a ci gaba da maganar idan Najib yana nan.
Washe gari da sassafe Suhaif ya shirya ya fadawa Najib idan *yan gida sun tashi ya ce musu ya tafi Doko dauko su Zubaida. Najib ya tambayeshi "Lafiya? Suhaif ya amsa masa "Lafiya kalau munyi magana da Baba ne ya ce a daukosu sun sami admission a BUK. Najib yayi murna ya ce "Lallai yaran nan sun faso gari. Wai wa yaga idanuwansu a Jami'a? Suka yi sallama Suhaif ya fita, a motarsa ya tafi Doko. Da la'asar likis suka shigo Kano sun kuwa ci sa'a Baba da Najib suna gida, da