Showing 99001 words to 102000 words out of 110329 words

Chapter 34 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt

22 Feb 2025

7470

suka rungume juna Iman ma ta cewa Zainab ta yafe mata. Mahaifin Suhaif yayi ajiyar zuciya ya ce "To mun godewa Allah, Huzaifa! Suhaif ya taho muku da gudunmawarsa zai bawa ango da amarya. Motoci ne guda biyu yake da niyyar idan zamu tafi ya baku, daya ta amarya daya ta ango. Huzaifa da Mahaifansa suka yi godiya, Iman da Iyayenta ma suka yi ta godewa Suhaif. Nan dai suka zauna suka yi ta magana ta farin ciki da godewa juna har zuwa lokaci mai tsawo, sannan suka fito dan za'aje aci gaba da gudanar da shagalin biki.
Huzaifa ya shiga gidansu kannensa su Bilkisu sun yi tatul sun cika da bakin ciki. Suna ganinsa suka hau yi masa korafi don me yasa zaiyi musu haka bayan sun shirya sun zo tun daga Abuja zai ce ya fasa ya barwa wani, ga anko har Lagos taje ta kai dinki, ga robobi da memo da kalandu duk sun bugo yanzu sun yi asara kenan. Suka bashi labari har Aljanu Amina ta tayar dan bakin ciki, dakyar ta sauka. Huzaifa yayi ta dariya yana tsokanar Amina yana cewa "Wato suma Aljanun sun yo sabon dinkuna zasu sha biki suka ji an fasa shine suka ji haushi kenan? Sai a lokacin suka bashi labarin tataburza da suka sha yi da matarsa Zainab tana kuka ta hada kayanta da *ya*yanta zata tafi suna riketa. Shi dai dariya yake tayi. Ya zauna ya wayar musu da kai ya fada musu dalilai masu karfi har saida suka gamsu suka saki ransu. Ya rokesu karsu fasa yin hidimar bikin da suka yi niyya, duk abunda suka yi niyya suyi, Fatima dama ai kawarsu ce. Kalandu ne kawai da memo mai hotonsu za'a kona robobi da kufuna kuwa sitika kawai za'a ciccire aje a sake bugo wata da sunan Fatima da Suhaif, zan baku kudin sitikar a lillika a raba. Suka amsa cikin fara'a suka ce babu damuwa sun huce.
Sai yanzu farin ciki ya cika zuciyar Iman, hankalinta ya kwanta saboda sanda taji da Suhaif aka daura bata yi bakin ciki ba amma abun ya daure mata kai ta rasa dalilin wannan sauyi, amma yanzu da taji haka daga bakin Huzaifa sai taji hankalinta ya kwanta farin ciki ya lullubeta. Bata da zargin kowa a kanta, don da tana damuwa saboda Suhaif yana ganin bata sonsa dama shine yake sonta. Ga matar Huzaifa ta damu tana kuka dan zata aure mata miji duk ta tsangwami kanta, tasan kuwa har abada damuwar tana ranta. Yanzu Huzaifa ya wanketa bata bata da kowa ba. Zumunci tsakaninsu yanzu ya kullu, haka tsakanin Iyayenta da nasa da Iyayen mijinta Suhaif Alhamdulillahi!
Aka sha biki! Budiri!! Birede!!! Babu kwabon Suhaif balle na Iyayensa duk Huzaifa ne yayi komai. Babu abinda Huzaifa bai tanada ba kuma bai fasa duk abunda yayi niyyar yi a bikinsa ba. Anyi liyafu kala-kala, haka duk abunda ake kaiwa gidan Iyayen Amarya na al'ada Huzaifa yasa an kai gidan su Iman a matsayin Suhaif ne ya bayar. Da aka kammala biki sai Suhaif da Iyayensa suka fara shirin komawa gida wato Kano. Yadda suka tsara tafiyar za'a kai su Baba, Goggo, Mama, Zubaida, *ya*yanta, mai aikinta da Naja'at Yola su hau jirgi su tafi. Sai Suhaif, amaryarsa Iman, Najib da Muslim su tafi a motar Suhaif. Huzaifa ya ce karsu damu su Suhaif su hau motarsu su tafi shi zai kai Iyayen nasu Yola su hau jirgi. Huzaifa da Iyayensa, kannansa, matarsa, Mamar Iman, Babanta, kannanta, Mama Tabita da kawayenta Mumuyawa duk sun rako ta bakin mota ana ta koke-koken rabuwa. Huzaifa da Suhaif suka yi musabaha suka gaisa Suhaif ya na masa godiya ba adadi. Huzaifa ya girgiza kai ya ce "Nasan dadin da kaji dan haka karka damu. Saboda Allah nayi, shi zai saka mun da alhairinsa. Huzaifa ya zaga wajen Iman yana mata nasiha ta bi mijinta sau da kafa suk da yasan ita me biyayya ce kuma ta sani amma tuni yake mata, cikin kuka take amsa masa yayin da kwalla ta cika masa ido shima. Iman ta rungume *ya*yansa Fatima da Huzaifa tana yi musu sallama tana kuka. Dakyar Iman ta shiga mota kannenta Abubakar da Hajara sai kuka suke suna rike mata hannu. Haka Mahaifiyar Iman ta damu dan rabuwa da *yarta, ba kamar Mama Tabita tayi kuka har idonta ya kunbura. Akwatinan lefenta guda takwas kadai aka saka mata a but.
Suhaif da Iman a bayan mota, Najib ne yake tukawa, Muslim a gaba suka ja suka tafi, suna daga musu hannu suma suna daga musu hannu. A sababbin dalla-dallan motocin da Suhaif ya bawa Huzaifa da Iman wacce ana bata ita kuma ta bawa Mahaifinta kyauta, a ciki za'a kai Iyayen Suhaif Yola inda za su hau jirgi, *yan rakiya suka dunguma wajen motocin. Matan ne kawai suka cika motar Huzaifa, su kuma su Baba suka shiga ta Mahaifin Iman. Mahaifin Iman ke tukawa suka dinguma filin jirgin Yola. Suna da kudin yankar tikiti amma Huzaifa ya hanasu su biya, ya biya musu gaba daya. Su Huzaifa ba su baro filin jirgin ba har saida suka tsaya suka ga tashinsu.
Suhaif da amaryarsa Iman suna zaune kawai suna kallon-kallo, farin ciki da kauna fal a zuciyarsu, sun bar Najib da Muslim a gaba suna ta zuba. Najib magana yake ba kakkautawa har saida Suhaif yasa baki ana hirar da shi daga nan Najib ya gangaro tsokanar Suhaif ya ce "Oh! Suhaif da tuni ka mutu, har ranka ya zo makogaro, ya aka yi ya koma? Dariya suke tayi har sai da cikinsu yayi ciwo ballema Iman. Muslim ya ce "Aini ban san farin ciki yana sawa a fasa mutuwa ba sai akan Suhaif. Suhaif dai dariya yake yana cewa "Kwaji da shi, ku ce duk abunda zaku ce ni dai na warke babu ciwo har abada.
Su Baba sun rigasu isowa Kano, kafin su Suhaif su karaso har an gyara musu wani bangare in da amarya zata sauka. Kwanan su uku a Kano amma Suhaif baya iya ko leka bangaran Iman saboda kunyar Iyaye sai dai su hadu a falo da safe su gaisa. Daga Kano ya dauketa suka tafi Doko nan ma a bangaren Suhaif aka sauketa. A bangaren akwai falo, daki, bandaki a ciki. Suhaif kacokan shi da kayansa ya kaura gidan Kakarsa Hajja acan yake kwana saboda kunyar Iyaye. *Yan garin Doko sun sha mamaki lokacin da aka fesa musu labarin Suhaif ya auri Iman gashi ya zo da ita. Suka dinga tururuwar bin layi waccan na fita waccan na shiga suna zuwa suna gaishe da Iman. Kawayenta na da duk sunyi aure da *ya*yansu suke zuwa su sha hira da Iman. Daman *yan garin Doko suna son Iman tana birgesu, abunda ya faru yasa suka kita da suka ji labarinta tun asali sai suka daina ganin laifinta. Suhaif da Iman satinsu guda a Doko, dangi sunga Iman, itama ya kaita taga dangi na cikin Doko da kauyuka. Da suke je Garki wajen Iya Furera sai Suhaif ya ce da Iman "Ko in kaiki Gumel ki shiga garin Gumel yadda kika ci burin zuwa Gumel Allah bai yi ba. Iman ta ce "Kaini in ga Gumel tunda gani a motata ma bata haya ba. Suhaif ya kai Iman Gumel daman su Suhaif suna da *yan Uwa dankam a Gumel, yini guda cur suna zagaya Gumel. Iman ta ce "Gaskiya naji dadin yadda Gumulawa suke karbar baki, sun karbeni hannu bibbiyu.
Bayan sun yiwa kowa da kowa sallama sai suka fito suka kama hanyan garin Abuja kai tsaye, suna tafe suna hira amma idan Suhaif ya dauko mata hirar soyayya sai ta rufe ido ta kasa bashi amsa, har yanzu kunyar nan tasa da take ji tana nan.
Sun isa Abuja lafiya, kai tsaye suka kutsa cikin katafaren gidansa. Masu gadi da ma'aikatansa sun fito taron Suhaif. Amma sai suyi turus su tsaya a lokacin da suka ganshi rike da hannun Iman. Kamar yadda Suhaif ya saba hira da su yana yi musu wasa sosai. Sai suke tambayarsa "Oga yaushe ka samu matar da zaka aura bamu sani ba? Suhaif yayi dariya ya ce "Ku biyoni falo zan baku labari. Gaba daya ma'aikatan gidan ya ce a kira su zo ya na da magana dasu. Suka hadu reras sunyi su ashirin, gaba daya maza ne. Ya sanar musu da cewa Iman matarsa ce yanzu haka daga Jalingo yake can aka yi bikin. Ya musu gargadi, ya ja kunne ya fada da kakkausar murya cewar su kiyayi bata mata rai, idan ta ce a yi to ayin, in ta ce a'a to a bari, saboda zai iya yanke kowanne irin hukunci akan wanda ya bata mata rai. Ya sanar musu da cewar zasu iya yi masa laifi sai dubu ya hakura amma idan suka yiwa Iman sau daya ba zai yi hakuri ba. Ko shakka babu sun ji ajikinsu da gaske yake yana son matar nan ko ba'a fada musu ba.
Akwatinan Iman direba daya kwaso daga but ya shigo da su falo sannan Suhaif ya sallamesu, kowa ya koma wajen aikinsa. Iman ta dubi Suhaif tayi murmushi ta ce "Yaya irin wannan fada da kake yi musu a kaina kamar ka auro *yar gwal? Suhaif ya ce "Ai kinfi *yar diamond ma Habitti (masoyiya). Tayi murmushi ta ce "Yanzu duk wadannan ma'aikatan gidan nan ne? Suhaif ya ce "Idan bakya sonsu sai in koresu a dauki wasu. Iman ta ce "A'a duk zamu zauna dasu ba kora, sai dai ina son a karo mata kamar guda biyar naga gaba daya maza ne. Suhaif ya ce "An gama Madam, za'a samo miki mata tunda gidan da mace yanzu, da ai gidan gaurone.
Suhaif da kansa yake kai kawo a cikin falon. Ya dauko juice a firij da kofi ya kawowa Iman. Ya koma ya dauko yagot ya kawo, yayi waya kicin ya ce a kawo mata kaza, aka kawo yasa anata kawo abubuwa ana jerewa gabanta har ta gaji ta ce ya isa haka. Suhaif ya zo ya dinga kinkimar akwatin kayanta yana hawa dasu sama, daya gama kaiwa ya dawo sai ya kama hannunta ya ce ta zo ya nuna mata dakinta. Suka dinga tafiya lungu da sakon a cikin gidan, dakuna barkatai da falo kala-kala. Ya kaita wani katafaren daki mai girman gaske ya ce mata "To ga dakinki kuma dakina, ni da ke babu raba daki har abada.
Suhaif ya dinga zagayawa da Iman ciki da wajen gidan, duk falon da suka shiga su kan dan zauna su kunna talabijin suyi kallo ko su bude computer. Daga karshe suka shiga shimfideden lambun da ke dauke da fulawoyi da bishiyoyin kayan marmari. Ba su fito ba saida magaruba. Suka yi sallar Magruba da Isha anan falon kasa. Kai tsaye suka wuce kan tafkeken teburin cin abinci da aka shake shi taf da abinci da abin sha kala-kala. Daman tun asalin Iman ba mai cin abinci ba ce da yawa, idan taci kadan sai tace ya isheta. Amma yau Suhaif ne yake bata a baki ko ta ce ya isheta sai yayi mata dubara ya sake saka mata a baki. Duk abubuwan dake teburin nan saida ya bata taci ta sha.
Da suka kammala sai Suhaif ya rufe kofar falon ya kama hannun Iman suka hau sama sun gama da kasa sai shirin bacci. Iman dai tayi tsuru a gefen gado, mutumin nata kuwa ya shiga ban daki ya hada mata ruwan wanka. Ya zo ya isheta da magiya sai ta tashi ta shiga wanka. Ta ce "Naga ikon Allah, dakuna sunyi guda goma a gida ina aka taba zuwa aka cusu a daki daya ance bazan zabi dakina ba. Suhaif yayi dariya ya ce "Nan ne dakinki, nima nan ne dakina mu biyu kenan. Amma tunda kina kunyata bari in tafi wani dakin inyi wanka, shiga kiyi. Suhaif ya fice san nan Iman ta shiga tayi wanka. Ya shigo ya iske Iman a zaune ta takure a gefen gado tana sanye da galleliyar rigar bacci *yar karama mai kyau mai laushi. Ya kalleta yayi murmushi ya ce "Daina takurewa, karki damu kwanta ki juya gabas ni kuma zan juya yamma muyi kai da kafa, kinga ba ruwan wani da wani. Ya kashe fitila suka kwanta.
Bayan wata guda cur da bikin su Iman, Huzaifa ya shirya shi da matarsa da yaransa zasu koma kasar su Bahrain. A jirgi suka zo Abuja ya sanarwa da Suhaif ta waya, shi da Iman suka daukosu a filin jirgi. Kwanansu daya a Abuja gidan su Iman sannan suka wuce Bahrain. Suhaif ya yiwa Huzaifa alkawari zasu zo Bahrain idan suka je Saudia a Umarar Azumi. A lokacin azumi saura wata biyu. Suhaif da Iman suna zaman jin dadi da kwanciyar hankali, haka ma'aikatan gidan suke cikin farin ciki. Saboda tun lokacin da Iman tazo gidan nan, kawai idan Suhaif ya bushi iska sai ya tarasu yayi ta raba musu kudi kyauta ba albashinsu ba kuma kudin masu yawa yake basu.
Suhaif ya kan je Lagos wajen hidimominsa amma kafarsa kafar Iman da ita yake tafiya. Duk in da zata je shine direbanta, baya bari kowa ya kaita. Iman tana mamakin irin wannan kulawa da Suhaif yake mata itama kenan balle jama'ar da suke ganinsu.
Watan azumi na kamawa Suhaif ya biyawa Iyayensa, Iyayen Najib, kannensa Naja'at da Zubaida, Iyayen Iman da kannenta, Mama Tabita da kuma Iyayen Huzaifa sannan shi da Iman kacokan suka dunguma suka tafi Umara har sai bayan salla za su dawo. Kafin su je Suhaif yasa an tanadar musu Hotel wanda ke daf da Harami, kowa bangarensa daban, ma'ana duk mata da mijinsu dakinsu daya. Haka zalika basu san sayan abinci ba. Bayan kudin tsaraba daya rabawa kowannensu.
Azumin shekarar gaba daya a Makka suka yi shi. Ranar salla suka wuce Bahrain sai su Huzaifa suka gansu reras kamar a mafarki. Satinsu guda a Bahrain suka shirya juyowa Nigeria, yayin da Suhaif da amaryarsa Iman suke rike da Visa tafiya kasashen biyar a hannunsu. Daga Bahrain London suka fara zuwa, yawon amarci sauran kuwa suka dawo Nigeria, *yan Kano suka sauka a Kano, *yan Jalingo suka runtuma garinsu.
Iman da Suhaif sun yi wata guda a London. Sannan suke wuce America, bayan sati uku suka wuce France. Bayan sati biyu suka je Dubai. Bayan wata guda suka taho Cairo suka yi sati guda suka iso Nigeria. Lallai sun huta, hutu kan hutu. Babu abinda Iman bata gani ba a kasashen nan. Babu abunda take so bata ci ba. Babu abinda tayi sha'awa bata suyo ba. Haka babu hamshakin Hotel din da basu shiga sun kwana ba. Iman bata da sauran matsala a duniya sai guda daya. Musamman idan taga yara kanana sai jaririn Harriet ya fado mata a rai. Tun tana boyewa Suhaif bata fada masa damuwarta har ya isheta da tambaya ta fada masa. Ya ce ta kwantar da hankalinta daman suna dawowa zasu je Kano, Doko da Jalingo sai su nemo Muhammad duk inda yake.
Haka kuwa aka yi bayan sun dawo daga tafiya da sati biyu suka taho Kano, suka kwana biyu a Kano. Sai a lokacin Iman tasan ashe Suhaif gini yake yi mata a Kano. Sun je sunga gidan har anyi nisa an kusa kammalawa. A unguwar su Najib ake ginin wato Badawa Layout. Gida har gida mai kyawun gaske ga ginin da ake yi mata. Dandatsetsan gida flat house da get dinsa shima an yi nisa da gini har an kusa kammalawa.


Nima ya gina min gida na mu ni da sweety Matawata.... Lolxx..


Reedwan Suraj Isma'il




YARENA ADDININA
CI GABAN LABARI


Sun isa Jalingo Iman ta sauka a gidansu shi kuwa Suhaif a Hotel ya sauka. Nan ma yasha alwashin wataran zai yi gini a garin saboda idan suka zo su dinga sauka. Bayan sun huta gajiyar hanya sai Iman ta shaidawa Iyayenta gaskiyar magana akan jaririn Harriet cewa bai mutu ba don haka yanzu zata bazama nemansa har sai ta samo shi. Suhaif ke tukata suka nufi gidan da aka ce mata marikan nasa nan suka koma. A bakin get din gidan Suhaif yayi parkin. Ya ce zai raka Iman ciki ta ce "A'a ya bari ta shiga ita kadai tunda gidan matan aure ne. Iman ta shiga cikin get bayan ta gaishe da mai gadin ta tambayeshi "Matar gidan tana ciki kuwa? Ya amsa mata "Eh tana ciki" ta tambaye shi "Yaran fa? Ya ce "Sun tafi Islamiyya. Iman ta ce "Su duka ukun? Ya ce "A'a su biyar dai. Iman ta ce a ranta "Su biyar? Anya kuwa gidan ne Abubakar da Aisha ne kawai ai sai Muhammad suka zama su uku, to ko Mamar tasu ta kara haihuwa tayi? Haka Iman take tunani har ta isa kofar falon gidan. Tayi sallama matar gidan mai suna Salma ta amsa gami da yin izini ga mai sallamar ta shigo. Iman ta shiga, tana shiga ta gane fuskar matar Mahaifiyar su Aisha ce domin taganta lokacin da ta haye kan bishiya, ita kuwa matar bata taba ganin Iman ba. Iman sai fara'a take yiwa Salma kamar ta santa, Salma cike da mamaki take kallon Iman tana tunanin anya ta san wannan matar kuwa? Ta gama tunanin duniyar nan taga bata taba ganin Iman ba. Ta nunawa Iman kujera ta zauna suka gaisa. Ta kwallawa mai aikinta kira ta ce ta kawowa bakuwa ruwa da lemo. Iman ta gyara zama tayi murmushi cikin yaren fulatanci ta ce "Baki sanni ba ko? Salma tayi murmushi ta ce "Gaskiya ban gane ki ba. Iman tayi gyaran murya ta ce "Ba zaki gane ni ba amma ni na gane ki. Shekarun baya nazo mai gadinku ya ce min kun tafi Umara ku duka gidan harda yaranki. Salma ta ce "Oh daman kece kika zo? Ya fada min wai nayi bakuwa ya ce wata fara tas. Ya ce ta tambayeni ta tambayi Muhammad . Ya ce har kina tambayarsa Muhammada ya girma, yana tafiya yanzu? Na dinga mamaki sai na zata ko ma Mahaifiyarsa ce ta zo, ta fada a hankali.
Iman tayi shiru can ta dago ta kalli Salma ta ce "Haka aka yi nice na zo. Da Aisha da Abubakar sun ganni me yiwuwa su gane ni amma ba lallai bane su gane ni saboda tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login