Showing 42001 words to 45000 words out of 110329 words
Chapter 15 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
ciki. Yace aida asibiti nafara kaita kafin akirashi. Nace bazata iya hawa babur ba
dan a durkushe take kuma bamuda kudin zuwa
asibiti saiyazo. Ya figa ya kaini kofar katafare
guest house din micheal inda ina kyautata zaton
anan zan sameshi don fadila ta shaidamun yanzu
anan yafi zama. Nace hadi dan achaba yajirani in shiga inji yadda zata kaya. Nakwankwasa, mai
gadi yaki bude mun yace in tafi inbashi waje bazai
iya kirawo mai min micheal ba. Narokeshi nace
yace pretty ce. Ya tafi dakyar yafadawa
ubangidansa. Koda yaji sunana nanda nan
micheal yace yaje yashigo dani. Afalo na iskeshi 'yan mata biyu karuwai a zagaye dashi. Yana
ganina ya kuramin ido yana kallona, kallo irin na
'yan iska. Sai a lokacin ma na kula da cewar rigata
yar yaloluwace shara-shara 'yar karama iya
gwaiwa, ta barci, kaina ba dankwali. Takalmin
kafata wari da wari don gigicewa. Nasa hannayena nadinga kare jikina don kunya. Yayi
murmushi cikin harshen turanci yace "you are
well come pretty. I'm glad to see u my baby come
and hug me". Ya yiwa yan matan nan biyu nuni
da hannunsa alamar su matsa daga kusa dashi,
suka koma gefe. Na matso kusa dashi a tunaninsa zanzo in rungumeshi sai yaga na
durkusa a gabansa. Yayi murmushi yace
'common stand-up baby feel free, relax don't shy
i am your lover, i love you my baby yasa hannu
zai jawoni jikinsa na goce gefe muryata na
karkarwa nace "zance harriet ne ya kawoni." ya bata rai yaji an ambaci harriet yace fadi meye inji"
nace ka taimakemu kazo ka kaita asibiti zata
haihu..dan bazaka jeba kabamu kudi da direba. Bamuda
kowa agarinnan saikai kuma danka ne za'a
haifa." uwar tsawar daya daka mun bani ba 'yan
matansa ma sun razana sunja da baya. Na mike
da gudu nayi bakin kofa yace "fita daga gidan
nan kar in kara ganinki indai zancen harriet zaki dinga yimin. Ina ruwana da haihuwarta ta mutu
mana." ya kira 'yan matan sa ya rungumesu a
gabana suka dinga aikata masha'a. Ban daddara
ba na rushe da kuka naci gaba da rokarsa
yataimaka ko cikin banasa bane yataimaka ya
kaita asibiti. Yace ya tuna alkawarin daya yimana yace shi kadai muka sani agarin nan duk abunda
muke so zai taimaka mana. Maganar daya sake
yicewa yayi idan zan yarda in shiga dakinsa
inbashi minti uku mu kebe zai yarda yakai harriet
asibiti, idan kuwa bazan yarda ba na fice nabashi
waje. Na ishe shi da magiya akan basai nashiga dakiba yadaure yakaita asibiti tunda shi yayi mata
ciki. Yazaro belt ya biyoni aguje. Gudun da ban
tabayin irinsa ba, na bude get nayi waje ba shiri.
Na cewa hadi maza ya kunna babur mubar kofar
gidan nan. Tambayoyin da hadi yakemun "ku
arna inda ake kwararku kenan ba kamar mu musulmai ba kuje kuyi ta iskanci da mazan banza
suna muku ciki wai dan dakan kuka a haihu ba
aure. Ku acikin arnan ma karuwai ne ai munada
labarinku, makaranta iyayenku suka turoku
kuka falle kuka kiyin karatun. Kebakiyi kama
dasu ba kamar bafillatana kike ko balarabiya ko shuwa. Bai kamata ki shiga cikin arna ba kina
tacewa. "nasake rusa kuka naji na tsani kaina na
tsani rayuwata. Abakin dakin mu ya saukeni nace
ya tsaya in shiga in rikota ko zata iya hawa
achaba mu kaita asibiti. Nashiga natarar da harriet
wanwar a tsakar daki cikin jini kaca-kaca kan da yafara lekowa ta galabaita ko maganarta bata fita
sosai. Na kwalla kara na fito da gudu a gigice
nace da hadi dan achaba "taimaka min kazo mu
daukota jini ne yake zuba daga jikinta." ya
yatsuna fuska yace "to da jini zan dauketa, yaya
ma zatayi ta iya zama akan babur? Gaskiya mota yakamata ku samo, kuma da ace matar aure ce
zata haifi dan sunna da saimu bugawa wani kofa
yafito da mota yakaiku asibiti ace ya taimaka
amma duk an sanku a unguwar nan karuwai ne
babu me sauraronku. Yanzu ki biyani kudina
saiki bani wasu kudin inje intaso abokina me taxi yazo ya kaiku asibiti idan yaga an biyashi zaije."
namika masa naira ashirin din nan nace "ita
kenan garemu kataimaka." ya galla mun uwar
harara. Yace "akan naira ashirin kika katsemun
barcina dan ubanki? Ya kawo mun mari na kauce,
yayi wurgi da naira ashirin din ya buga babur dinsa ya tafi yana zagina. Na koma cikin daki da
gudu na tarar da kan da yana sake fitowa waje.
Ina kuka narike hannun harriet, tarikeni tace
pretty mutuwa zanyi idan na haihu dan yayi rai
kidauka kirike minshi amana nima yar uwarki ce
musulma ki taimaka ki rikemin dana ko 'yata. Kicewa iyayena su yafe mun. Pretty kici gaba da
kyamar zina, ki gujeta kikoma gida kiyi aure, irin
wannan rayuwar da muka jefa kanmu ba alkhairi
bace." harshenta yafarara hardewa sai gumi take
kamar ruwa sai wani nishi take da karfi kamar
akuya. Nahau salati da karfi itama saita kamayi sai tayi nishi mai karfi guda daya sai da ya sunbulo
ya fado ya cara kuka, yayin da ita kuma nishinta
na karshe a duniya ta cika.
Abun yafi karfin kuka saina koma na zauna ina
kallon bakin dan kankanin jariri yana tsala kuka
sai in juya in kalli uwarsa a kwance ta mutu. Jini face-face ajikin su bansan yadda zanyi ba, banida
sauran tunani. Harreit data zama gawa ta fini jin
dadin yadda nakejina a ranar. "dama nima
akamani a harbeni ace nina kasheta. Haka nake
addu'a. fakam naji an daga labule an shigo. Fadila
na gani sanye da rigar bacci irin tawa harma tafi tawa kankanta iya cinyarta. Ta dora hannu aka ta
kwalla ihu ganin harriet da dan ta face-face a
kwance a cikin jini. Tambaya take 'harriet ta
mutune?" na gyada kai don bana iya magana
alamar "eh ta mutu.
Saita jawo hannuna tace pretty tashi mubar dakin nan, taso mu tafi tun daga unguwarmu da kafa
na taho inzo in shaida miki abunda yake faruwa.
" na kalleta cike da fargaba nace "meke faruwa?
Jikita yanata karkarwa sosai a tsorace take. Tace
"janet ma ankasheta solomon saurayin janet an
kashe shi, ngozi da easter kawayena an kashesu. Ta rushe da kuka tace Gibrel saurayina shima
yana cikinsu ankashe shi. Yanzu motar yan sanda
ta zagaye gidan micheal za'a kamashi shima a
kashe shi? "Na zabura na mike tsaye na dafe
kirjina nace "me sukayi? Ta rushe da kuka tace
ashe duk kudin nan dasu micheal suke kashewa bana iyayen su bane, ba sana'a sukeyiba fashi
sukeyi. Micheal ne babbansu shi yake turasu suyo
fashi idan sukaje lagos ma fashi sukeyi. Dazu
suka tafi jos wai harda su janet suka rakasu
sukayo fashi yan sanda suka biyosu suna harbin
yan sanda 'yan sanda na harbinsu. 'yan sanda suka harbi tayoyin motarsu suka gangara motar
ta kife duk suka mutu. Wani abokinsu ne guda
daya emeka bai mutu ba amma ya jijji ciwo, ya fita
daga motar kafin yan sanda sukaraso yabi duhu,
ya tsere bakin titi ya dane motar daukar kaya. masu motar basu sani ba ya shigo Bauchi duk a cikin
daren nan. Ya dibi kudin Gibreal ya ce yanzu zai gudu
garinsu Lagos, nima na debo mana kudin mota, taho
mu gudu.
Zan karasa anjima insha Allah.
Surayya
Abubakar
Masu motar basu saniba ya shigo bauchi duk acikin daren nan. Yazo gidan da nake wujiga wujiga yace inyi ta kaina. Ya dibi kudin gibrel yace yanzu zai gudu garin su lagos nima na debo mana kudin mota, taho mu gudu.
Jikina na rawa na dauko zani na daura na yafa wani zanin gadon janet. Fadila ma tasaka wata doguwar rigata. Ta fisgo hanuna muka fito daga dakin. Dan jaririn harriet sa kwalla kuka yake nace mata "ban dauko dan jaririn ba. Ta daka mun tsawa "kidauko shi ki kashi ina? Zomu tafi muyi ta kanmu. Kinsan fa ansan tare muke dasu micheal zasu zo nan nemanmu fa. Harna juya na bita, naji yaron nan sai kuka yake. Nadawo da gudu cikin dakin, fadila ta biyoni tace "me kika dawoyi? Nace dan jaririn zan dauka. Ya zanyi in yanke cibiyar in rabashi da uwar? Tace "dauko reza. Sabuwar reza nabata acikin kayan kwalliyar mu. Fadila ta yanke cibiya, sake bani shawara take tana cewa in ajiye dan jaririn nan idan nadauke shi ina zan kaishi. Nima nayi tunanin haka amma tausayi ya hanani in tafi in barshi. Nadauko zanin mahaifiyarsa na lullubeshi na rungume shi a kafadata. Najawo mayafi na lullube fuskar harriet na tofa mata addu'a Allah yajikanta. Muka sakd juyawa zamu fita wani dan karamin hoton harriet ne a jingine a wajen kayanta tana dariya a hoton tayi kyau sosai. Nakoma nadauko shi. Fadila ta kwalla da karfi tace "pretty idan bazaki tafiba zan tafi ga karar jiniyar motocin 'yan sanda can watakila nan zasu zo neman mu mu yan matan yan fashi. Muka fito daga dakin muna ta gudu muna shiga gonakin mutane. Batare damun san inda muke nufaba. Akwai wani katon dutse a bangaren da za'aje wata makaranta jibrin aminu primary school a jikin dutsen muka labe. Idan muka hango motocin yan sanda saina toshewa dan jaririn baki yanata tsala kuka. Anan a gindin dutshen muka zauna muna rusa kuka tamka ranmu zai fita. Fadila tace mu "pretty kin fadamun gaskiya, rayuwar bariki ba rayuwar kirki bace. Mubi maganar iyayen mu domin muddin kaki bin iyaye bazakaga ci gaban rayuwarka ba, dubemu kiga irin rayuwar da muka jefa kanmu. Ta debo kudi mai yawa daga kudadenta tabani, tace inyi kudin mota intafi gida itama zata shiga mota ta koma gida. Dan jariri ya gaji da kuka sai yayi barci. Bamu fito daga bayan dutse nan ba saida gari yafa washewa muka farajin karar wucewar motoci da babura suna giftawa.
Allah ne yakiyaye mu ashe duk ramukan macizai ne a inda muka fake ga kunamai sunata gif-giftawa. Mukayi sauri muka bar wajen muka fito titi muka tari achaba gudu biyu muka ce tashar yankari. 'yan achaba ma hirar 'yan fashi da aka kashe jiya suke bamu, sai cikinmu yakara durar ruwa suna cewa "abun mamaki harda mata acikin yan fashin da aka harbe jiya. "naji kuka mai radadi ya zubo min bamu iyace musu komai ba. Suka kaimu tasha muka sauka muka basu kudinsu. Dan jaririn dai kuka yake tsalawa babu riga ko wando ajikinsa ko jinin haihuwar ma ba'a wanke masa ba ga uwa uba sanyi da yake surarsa da yunwa. Fadila shawarar da take bani itace inyar da yaron nan intafi gida. Natuna amanar da uwarsa ta bani, kuma tausayinsa nakeji idan nayar dashi bansan hannun wandazai fadaba watakila yatashi ba'a musulmi ba. Naji ajikina zai zama musulmi ya amfani musulunci duk da dai bansan inda zan tinkara da dayan jariri ba a yarda arikemu. Na shaidawa fadila bazan iya yarda shiba, zan tafi dashi. Na roketa nace ta rakani kantin dake cikin tashar in saya masa madara in bashi yasha kafin afara sayar da ticket din shiga motocin yankari expressg. Akantin na tambaya ko akwai madarar jarirai akace akwai. Nasaya sai muka je wajen wata mai koko da kosai na roketa Allah annabi ta bani ruwan dimi in damawa dan jinjirina madara. Tabani kadan a kofi da cokali nida fadila muka dinga tarfa masa yana hadiyewa harya koshi, muka yiwa matar godiya muka tafi wajen da ake yankar tiket din shiga motar. Nayanki tikitin jalingo, fadila ta yanki na katsina. Muka rungume juna muna kuka mukayi sallama kowacce tashiga motar garinsu muna dagawa juna hannu muka tafi. Na shiga garin mu, atasha nadauki shatar taxi wacce xata kaini har kofar gida. Na shiga unguwarmu na tarar unguwar shiru ba kowa. Nashi mummunar fargaba da mummunar damuwa yadd zanyi da dan jaririn nan. Ina cikin taxi ina waige-waige ina fargaba jinake kamar incewa dan taxi ya juya dani nafasa zuwa gidan. Akofar gidan su hamma huzaifa na kalla sai kuwa mukayi ido hudu dashi. Ya bude baki yana mamakin ganina. Saiya washe baki yayi min wannan dariyar tasa tanuna farin cikin ganina. Yasa hannu ya tsayar dame taxi gami da cewa "wait-wait." ya tunkaro motar ta tsaya da farin cikin sa. Mummunan faduwar gaba tadasu a zuciyata. Nazaro kudi nabawa dan taxi kafin bude kofar motar in fito hamma huzaifa da kannensa sun karaso wajen motar yasa hannu yana bude mun kofar cikin harshen fulatanci yake tsokanata. Yace inye pretty 'yan makaranta, yanzu angama level 1 an zama yan level 2 ko, point nawa kika buga mana? Nasan dai kin bugo samada 3 points ko mutuniya? Yana fada yana bude mun kofar mota....
Amin afuwa plz
YARENA ADDININA....CGBN LBRN
Nasa kafata daya awaje ina kokarn fitowa dakyar don jikina yayi sanyi. Huzaifa ya sake kallona cike da mamakin ganin yadda na zama kamar baniba. Bayan rashin fara'a gashi na yafa wani burgujejen zanin gado na lulluba, baki abushe, ido a kode sanadiyar kuka. Gashin kaina biyu-biyu a cukurkude. Alamar tambaya zaka iya gani a idanuwansa. Zai bude baki yayi min tambaya meke damuna yaga nazama haka? sai kukan jaririn dake hanuna ya mayar da hankalinsa ya kalli abunda na rungume, fuskar sabon jariri ya hango. Nanda nan ya canja zaka iya ganin fargaba da tashin hanakalin da suka rufto masa, yaja da baya da sauri jikinsa yayi sanyi sai kalmar innalillahi wa'ina ilaihi raji'un yake karantowa, kaji musulmin kwarai. Muka hau kalon-kallo, ya kalleni ya kalli jaririn hanuna. Abunda ya sake fadomin arai shine nasihar da yakemun tun ina yarinya. Yace "kada kiyi zina, Allah ya hana zina, yana kallon ki zai konaki, kiji tsoron Allah. Shima kuma daga dukka alamu abunda yake tunowa a zuciyarsa kenan. Wato na manta nasihar da yayi min? Ina tsoron Allah da yake ganin alamar yashigeni? Sai naga hawaye daga idonsa guda daya ya surnano. Ya girgiza kai ya juya ya tafi ya nufi gidansu yabarni anan a tsaye. Bakina yahau kaikarwa inaso inyi magana na kasayi domin nasan babu bayanin da zan iya yi masa awannan lokacin ya yarda dani me taxi yaja motarsa ya tafi. Kannena na hango sun taho da gudu zasu tareni sainaga sunyi kicibus sun tsaya ganin dan jinjiri a rungume a hannuna sukayi gefe suna kallona, nazama abar kallo. Mahaifina da mahaifiyata nahango awajen mota da alama motar zasu bude su shiga su fita, sai suka tsaya suna hange suna so su gaskata abunda suke hange gaskiyane ko kuwa gizau idanunsu suke musu. Jariri ne a rungume a hanuna ba gezau bane gaske ne. Na tunkaro inda suke a tsaye. Mukullin motane a hannun mahaifina saiya fado kasa don razana. Haka jakar dake rataye a kafadar mahaifiyata sai data sulmiyo fadi kasa. Mahaifiyata ta sulale ta zauna akasa tsabar tashin hankali. Muka hau kallon-kallo dasu yayinda nima idanuwana suka haskomin mummunan tashin hankali a tattare dasu wanda yafi tashin hankalin da suke hangowa a tattare dani. Naji tsananin bakin cikin da nake ciki tamkar shafar mai ne akan bakin cikin daya tunkaroni a yanzu yanzun nan. Shin gizau idanuwana sukayi min ko kuma gaskiya ne. Hakika gaskiya ne ba gizau bane. Turkashi, nanda nan na nami yawun bakina da makokarona na rasa sun bushe kamas don tashin hankali sai zuciyata ta lalibo addu'ar da Huzaifa yake karantawa a lokacin dabala'i ya tunkaro shi. Naji kafata bazata iya daukar jikina ba da dan jaririn dake hannuna sai nima na sulale na zauna kamar yadda tashin hankalin ganina yasa mahaifiyata ta sulale ta zauna. Karkarwa suke suna nuna jaririn dake hanuna, nima hannuna na karkarwa idanuwana na zuba tamkar ruwa a famfo ina nuna gagarumin tashin hankalin da nake hange a tare dasu.....
Toh littafi na dayan yakare da iznin Allah
YARENA ADDININA.
___CI GABAN LABARI
Mahaifiyata ta wuce tana fada, Tabita tana rawar jiki ta shigo ta dauki mayafinta ta fita. Har ta fita, na tashi da sauri na ce "Mama Tabita ki dauko min kayana set daya a durowata zan saka, ta amsa min da to ta tafi. Bayan tafiyar Tabita da minti biyar sai ga kanwata Rabecca ta shigo ta tsaya, ta kalleni ta kalli jaririn cikin harshen turanci ta ce min "Aunty Rufkatu kizo inji Daddy ki dauki kayan da kanki, Mama Tabita ba zata dauko miki ba. Na amsa mata da "To ina zuwa. Ta fita ta tafi, a zaune nake ina tunani wai me suke nufi da inzo da kaina? Shiguwar Mama Tabita ce ta katsemin tunanina, ta shigo da sauri ta ce "Pretty dauko yaron ki fito kizo muje gidan ki roki Mahaifanki gafara tun da sunyi fushi dake. Duk fadan da zasu yi miki suyi miki yanzu ki huta. Babu yadda za'ayi keda jaririn nan ku zauna cikin kunci da rashin gata. Na girgiza kai na ce "Ba zan shiga gidan ba "Tabita tayi ta lallashina dakyar na yadda na dauko mayafi na lulluba, ta mikamin Jariri na karba muka fito. A kicin Tabita ta labe ta ce in shiga cikin falon. Na kwankwasa kofar na shiga, gaba daya suka dago ido suna kallona na sunkuyar dakai kasa na wuce sum-sum cikin dakina, ina shiga na kwantar da Jaririn akan gado na bude durowa ta kayana na dauko wani leshi yellow riga da siket da dankwali na saka. Mahaifiyata ta shigo a fusace ta harari dan Jaririn dana kwantar akan gado, ta juyo ta harareni ta ce "Ki kwaso kayanki kakaf ki koma wancan dakin ki barwa Rabecca dakinta, kije can ki karata keda buhunhunan abinci. Na zubo da kayana kakaf akan gado na warware wani dan kwali na zuba na daure. Ta sake daka min tsawa "Kizo ki dauke wannan yaron kafin ya jikawa yarinya gado da fitsari. Na taho da sauri na dauke shi zuciyata cike da bakin ciki. Muryar Mahaifina naji ya kugamin kira cikin kakkausar murya, jikina na rawa na amsa na fito Mahaifiyata na biye da ni. Ya nuna min tsakiyar falo kan kafet ya ce inzo in zauna shi kuma yana zaune akan doguwar kujera. Mahaifiyata tazo ta zauna a kusa da shi. Ta juya ta kalli kannena ta ce "Su tashi su fita, ko su shiga dakinsu suyi kallo. Cikin fushi Mahaifina yake magana, cikin harshensa na fulatanci ya ce min "Fatima kin bani kunya, kin bani mamaki. Abunda kika yi kin kyautawa kanki kenan? A kwai wani yaro dan nan garin ne, dan abokina ne ya sanki, kece baki sanshi ba shima a ATBU yake tun wancan satin ya dawo gida sun gama jarabawa, na tambaye shi ko yana ganinki a makaranta? Ya shaidamin bakya makaranta, ya takaicemin yace sunanyenku na nan kafe an fitar da result an rubuta an koreku kwata-kwata, bakwa cikin makaranta kuna can kuna yawan iskanci. Baki taho min da result din jarabawa ba sai kika taho min da result din yawan iskanci kamar shi muka turaki. Kaina a sunkuye a kasa hawaye nake. Tun da nake da Mahaifina bai taba nuna min bacin ransa ba balle ya