Showing 93001 words to 96000 words out of 110329 words
Chapter 32 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
sai dai Zainab matarka ita ce mai tsoro. Najib ya ce "Je ka rakata. Huzaifa yayi dariya ya ce "Tsokanarta nake yi ai bata da tsoro ko kadan, wannan sai dai ta dinga rakanu ma ni da Zainab din gaba daya. Duk kansu suka yi dariya. Goggo ta dora musu labarin rashin tsoro irin na Iman a zamanta na Doko. Iman tana dariya ta fita.
Tana fita ta mance da sakon Zubaida sai ta shiga wurwurga ido ko zata ga Suhaif, amma bata ganshi ba, har motocinsu ta lelleka baya ciki. Ta zagaya bayan gidan kamar da wasa, bata yi tunanin zai shiga cikin ciyayi da duhun nan ba sai kuwa ga Suhaif ya rike kai a tsugune. Ta tunkaro shi da sauri tana kiran sunansa gami da tambayarsa "Lafiya? Me ya faru? Me ke damunka? Ya zabura ya daga hannu biyu ya dakatar da ita kada ta karso in da yake. Ya kara da cewa ta yiwa Ubangijinta ta tafi ta kyaleshi babu abin da aka yi masa shi.
Iman ta rushe da wani kuka mai turiri tun daga kahon zuciyarta zuwa idanuwanta, ma'ana kana jin kukan kasan yana dauke da bakin ciki mai tsanani ba irin wanda ake kirkirowa bane wato kukan dadi ko na kissa. Tsananin damuwar da Suhaif yake ciki, zazzafan kukan da ya labe yana sharba sai ya lafa, hankalinsa gaba daya ya tashi ya dira akan halin da yaga Iman ta shiga yanzu-yanzu. Iman me ya saki kuka? Me aka yi miki? Suhaif ya fada a lokacin daya je ya tsaya a gabanta. Ta kasa magana kuka take tayi abinta. Ya gigice gaba daya, ya hau lalube-laluben aljihu ya lalubo mata wani farin hankicin ya mika mata yana mai tsananin bata hakuri, har sai da kukan ya lafa. Ta dago ta dubeshi cikin sanyayyiyar murya ta ce "Na yi zaman mutunci da amana ni da *yan uwanka, iyayenka, da jama'ar garinku. Mun yi zama ni da kai zaman amana, ka taimake ni, ka tsaya tsayin daka har sai da na yi rayuwar jin dadi da kwanciyar. Mun rabu kana kuka ina kuka, na tafi na barka da sona da tunanina, na tafi da tunaninka da sonka. Ko da yaushe kana addu'ar ka ganni, nima ina addu'ar in ganka. Kamar yadda Najib ya fada min kazo garin nan nemana, nima na taba zuwa Doko nemanka da daddare na aika Yaro gidanku aka ce ka kaura Lagos, takanas don kai naje Doko tun daga filin jirgin Kano lokacin da zan tafi Makka karatu. Tunaninka ne yayi min yawa dole na je ganinka koda jirgi zai tafi ya barni. Ina gani na a Kano naji bazan iya barin kasar nan ba tare da naje na ganka munyi sallama ba kafin in wuce. Duk sanda naga mai sunanka, ko mai kamarka sai naji gabana ya fadi in zata kai ne. Mun hadu ni ina murna kai kana bacin rai, duk da dai mun hadu a cikin wani yanayi na babu zancen soyayya tsakaninmu. Suhaif ina sonka ne kawai a raina amma nasan bazan aureka ba saboda har tsinuwa Mahaifanka suka ambata idan baka rabu dani ba. Amma ina son muyi rabuwar arziki yadda idan mun hayayyafa *ya*yanmu zasu yi zumunci ko kuma ma suyi aure tunda mu bamu yi ba. Suhaif bani da niyyar in yaudareka, ba yaudararka nayi ba. Kaji dalilin da yasa zan auri Hamma Huzaifa ba kai ba. Mun rabu a zatona ma kayi aure ka manta dani. Sai kuka ya kece mata.
Sai nima kuka ya kece min domin na tuna tsumammen tsumin so da kauna wanda na sha nai tatul daga karshe........... Gwalo... Bazan karasa ba ehe.
Reedwan Suraj Isma'il
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI
Suhaif ya matse idanuwansa ya ce "Daina kuka, kar kiyi kuka. Kukan nan naki zai iya dasuwa a raina ya zamarmin damuwa. Iman nasan baki yaudareni ba, nasan ba mu isa mu gocewa kaddarar Ubangiji ba. Damuwata ita ce yadda rayuwata zata kasance nan gaba. Sai ya yi shiru ya kasa magana. Iman ta ce "Kamar yaya? Suhaif yayi shiru ya girgiza kai ya ce "Kimin addu'a duk lokacin da aka ce miki na mutu kada ki sake ki bari Huzaifa yasan ina sonki. Ya juya ya tafi, ya dafe kirjinsa da alama zuciyarsa ce ta matsa masa da ciwo. Da kyar yake iya jefa kafarsa ya nufi cikin mota ya zauna ya kifa kansa akan sitiyari.
Iman ta kalli gabas yamma, kudu da arewa ta rasa mai taimakonta, ta ji kamar ta zauna tayi ta kwala ihu sai ta kamo kalmar Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Ta taho ta nufi hanyar gidansu kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki, dakyar take tafiya. Ta zo dai-dai motar da Suhaif ya shiga ya kulle kansa ta kwankwasa masa glas, ya dago ya dubeta, ta ce ya sauke gilas. Ya girgiza kai alamar a'a, yayi mata nuni da hannu alamar ta tafi. Hawaye mai radadi yake zubowa daga idanuwansu. Sai ta daga masa hannu ta ce "Good bye Suhaif I miss you. Shima ya daga mata hannu ya ce "Bye-bye Iman I miss you too. Ta tafi tana waiwayansa tana daga masa hannu, shima yana daga mata hannu su duka kuka suke har ta kure ya daina ganinta, ta daina ganinsa.
Iman tasha mamaki da taga Hamma Huzaifa a zaune a cikin get din gidansu akan wani benci kusa da dakin mai gadi, shi da ta bari a gida tare da su Najib. Yaushe ya fito? Ta ina ya biyo basu ganshi ba? Mai ya zo nema? Sai tayi sauri ta goge hawaye ta hau murmushin karfin hali. Taje wajensa tana tambayarsa ita ya zo nema? Yayi dariya ya ce "Na zo in ganki kafin inje in kwanta, yau kwana zan yi a zaune, ba zan iya barci ba saboda farin cikin daurin aurenmu gobe. Zan auri macen da na taba so a rayuwata, wacce nake so a rayuwata, wacce na fi so a rayuwata, wacce zan ci gaba da so har karshen rayuwata. Sai Iman ta fashe da kuka ta zauna a gefensa a sanyaye. Huzaifa ya rikice ya tambayeta kukan me take? Sai ta ce masa kukan me zata yi wanda ya wuce kukan dadi. Ita kuwa ji tayi hankalinta yayi mummunan tashi, ta taho da tausayin Suhaif ga kuma Huzaifa. Duk sun yi mata halacci a rayuwa, kuma ta saba dasu su duka.
Najib da Muslim sun zo sun iske Suhaif zaune a cikin mota. Sun nemi Huzaifa basu ganshi ba, sai suka shiga mota suka tafi, daman sallama zasu yi masa. Sun shiga katafaren Hotel din da aka sauke su, dakinsu yana kusa da dakin Babansu. Sauran dakunan ma duk bakin su Huzaifa ne daga garuruwa daban-daban, wasu kuwa abokansa ne daga Saudiya da Bahrain har da abokin nan nasa El-Sadik shima ya zo. Najib ya taba kofar dakin Babansu yaji a kulle daga ciki, munsharinsu na tashi, shi ya tabbatar masa sun dade da yin bacci.
Su Najib sun shiga sun kwanta yayin da gajiya ta dannesu kan kace kwabo Najib da Muslim sun yi bacci amma ban da Suhaif. Idonsa biyu ya kurawa fitila ido yana tunani. Tambayar anan shine shi bai gaji bane kamar yadda sauran suka gaji? Amsar ita ce Suhaif ya gaji shima yadda sauran suka gaji, amma wani yakin yafi wani, damuwar da yake ciki tafi gajiyar damunsa. Idan ya gaji da kwanciya sai ya tashi ya zauna. Ya sauko kasa ya kwanta kan kafet. Ya gaji ya hau gado duk juyi yana ambaton La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntum minal zalimin, da dukkan addu'ar data shigo bakinsa.
<3 ______RANAR DAURIN AURE______ <3
Da misalin karfe goma sha daya na safe za'a daura auren Hamma Huzaifa da Iman. Misalin karfe tara Huzaifa ya shigo dakin su Suhaif cike da fara'a kai ka ce an masa albishir da Aljannah ne, hannunsa dauke da wata katuwar leda. Bayan yayi sallama ya shigo Najib ya je da fara'arsa ya mika masa hannu suka gaisa ya yi masa kirari ya ce "Ango kasha kamshi. Ango na Fatima da Zainab. Baban Fatima, kai ne Huzaifa Baban Huzaifa. Angon Fatima kuma Baban Fatima. Huzaifa ya kyalkyale da dariya ya ce "Najib a ina ka iya kirari haka kamar wani maroki? To na nadaka sarkin maroka a wajen daurin auren nan. Suka kwashe da dariya su duka dakin har da Suhaif. Huzaifa ya mikawa Muslim hannu suka gaisa, sannan ya mikawa Suhaif hannu. Gaban Suhaif sai da ya yanke ya fadi da yaga Huzaifa. Babu abinda Suhaif ya keji yau sai faduwar gaba da tashin hankali. Yasa hannu ya rike bangaren kirjinsa na hagu inda zuciya take. Shi kadai sai Ubangijinsa yasan halin da yake ciki a safiyar yau.
Hamma Huzaifa ya zazzage kayan cikin ledar akan gado. Sai ga wasu dandatsa-dandatsan shaddoji farare sol a dinke set uku iri daya. Riga da wando da babbar riga sunsha dinkin surfani da brown din zare. Hade da hular data shigo da kayan itama guda uku. Najib yana dagawa yana gwadasu yana yaba kyawun da suka yi. Hamma Huzaifa ya ce "Kaifa Suhaif sun yi maka kyau? Suhaif ya matso ya daga yayi murmushi ya ce "Kyau kai! Ai dole ma a kalle ka Ango. Amma yaya har guda uku iri daya? Huzaifa ya ce "Ni da kai da Najib na dinkowa saboda kuma abokan ango mu fito fes iri daya. Sai su duka suka ce "A'a bai kamata suyi anko dashi ba ai an fi so ango yafi kowa caba ado saboda ya bambanta, kowa ya ganshi yasan shine. Muslim ya na taya Huzaifa rokar su Suhaif akan su yadda suyi ankon babu komai shi daman haka yafi so. Daga karshe Suhaif suka yarda zasu saka. Huzaifa ya dauki nasa kayan ya saka a leda yayi musu sallama yace zai tafi gida sai sun hadu a wajen daurin auren kar suyi African time.
Najib ya lura da Suhai baya cikin hayyacinsa sosai, da alama akwai ciwon da yake damunsa asafiyar yau. Baya jin dadin jikinsa da asuba ma ya lura da kyar yayi salla yana yawan cije baki ya dafe kirjinsa. Abinci ma da aka kawo bai ko dandana shi ba. Najib ya dube shi ya ce "Suhaif ta shi ka fara wanka muyi mu shirya kar mu makara. Yayi minti biyar a zaune sannan ya yunkura zai tashi sai ya koma ya zauna ya kasa mikewa, da sauri Najib ya tare shi. Ya ce "Lafiya Suhaif, ko in kaika bandakin? Suhaif ya girgiza kai alamar a'a, ya tashi yana tafiya a hankali ya shiga ban daki hannunsa dai a dafe da kirjinsa. Yana shiga suka ji ya ce "Subhanallah" Najib ya shiga a guje yaga Suhaif daure da tawul yana tsugune yana rike da hannunsa. Najib ya tambaye shi "Lafiya? Suhaif ya ce famfon ruwan zafi ya bude ya manta ya tara hannunsa shine ya kone. Najib ya ce "Wai tunanin me kake yi haka har ka budewa kan ka ruwan zafi, ga hannunka nan ya sale? Haba Suhaif kayi hakuri mana ka barwa mai duka komai. Najib ya surka masa ruwan wanka, ya ce ya shiga yayi wankan. Najib ya fito daga ban dakin hankalinsa a tashe. Muslim wanda bai san abunda yake faruwa ba sai ya hau tambayar Najib "Wai me yake damun Suhaif ne? Najib ya ce "Baya jin dadin jikinsa ne.
Bayan Suhaif ya fito Muslim ya shiga wankan. Kayan ma Suhaif ya kasa sawa a dai-dai sai karkarwa hannunsa yake Najib ne yake gyara masa. Najib yana ta bawa Suhaif baki ya kwantar da hankalinsa kada ciwo ya kama shi. Budar bakin Suhaif sai ya ce "Dan Uwana Najib kayi min addu'a, yau za'a daurawa Iman aure nima kuma yau zaku yi taron jana'izata. Najib ya ji gabansa ya fadi ya zabura ya dafe kirji. Ya ce "Suhaif, haba Suhaif meye duniya? Daman nasan abunda yake damunka kenan. Ko kuma ka hakura da zuwa wajen daurin auren ka kwanta. Suhaif ya girgiza kai ya ce "Zanje, zan iya zuwa karka damu. Najib ya zauna kan kujera yayi shiru ya zurawa Suhaif ido ya rasa yadda zai taimake shi. Dame zan taimaka masa ya rage damuwa? Babu! Iman ce kawai maganin, babu Iman kuma.
Muslim ya fito daga wanka ya ce da Najib "Yayana shiga, na fito. Najib ya tashi dakyar yake tafiya saboda damuwa. Yana shiga shima ya kwalla kara. Muslim ya shiga da sauri sai ga Najib a tsugunne ya rike hannu, tunani yasa shima ya budewa hannunsa famfon ruwan zafi ya kona hannnu. Muslim ya ce "Yau lafiyarku kalau kuwa? Ya yi masa sannu ya fito ya jawo kofar ban daki ya rufe cike da tunani ya kasa gane kan Suhaif ga Najib shima yana kokarin rikicewa.
WAJEN DAURIN AURE ---- <3
Karfe goma sha daya dai-dai sai ga Suhaif a wajen daurin auren, daman su Babansu sun dade da tahowa goma ma anan tayi musu, suna tare da Baban Huzaifa a falon su Iman. Wajen daurin aure ya cika dankam da jama'a duk lungun da ka waiga mazane. Yare iri-iri ke tashi a wajen daurin auren, dangin Huzaifa da dangin Mahaifin Iman daga Gombe yaren fulatanci suke. Wasu jama'ar yaren Hausa suke, abokan Huzaifa daga Saudia da Baharain larabawa ne dan haka yaren Larabci suke. Abokan Iman Mumuyawa suma sun hallara suna yaren Mumuyanci, wasu daga cikin dangin Mahaifiyar Iman sun zo suma suna nasu yaren Igbo.
Huzaifa ya fadawa masu daurin auren cewa su daura auren da Hausa saboda ba kowa ne yake jin Fulatanci ba amma yawancin Fulanin suna jin Hausa. Ango Huzaifa, Suhaif, Najib suka jero suka taho kayansu iri daya, hula iri daya, tsayinsu daya, dogon hanci dukkansu, dara-daran idanuwa dukkansu, fararen hakora cas idan suka yi dariya dukkansu, farar fata dukkansu. Duk da Huzaifa ya fisu fari, shi fari ne sosai. Jama'a sun yi mamaki da suka ga ango da wasu sun yi anko, har wasu suka shiga tunani ko daurin auren mutane uku ne. Maroka sai kirari suke musu, makada sai buga ganga suke suna wakesu su duka ukun, bayan sun tambayi sunayen su Suhaif.
Suhaif tsaf da shi, ga mutum har mutum amma a zuci dai ba mutum bane, domin zuciyarsa ta nutsa ta tafi tunani mai tsanani. Dai-dai lokacin da aka hallara ana daf da fara daurin aure Suhaif ya ji numfashinsa yana kokarin kakarewa saboda tsananin damuwa. Ba ya so Suhaif ya gane halin da yake ciki, sai ya faki idon Huzaifa da Najib yayi wuf ya bar wajen ya tafi can bayan wani gida da yake gefen gidansu Iman ya jingina a jikin katangar ya runtse ido. Yana bude ido Iman ya gani da dandazon mata kawayenta da *yan Uwanta. Amarya ta cancada ado kamar wata India suna take mata baya kamar wata sarauniya. Za su shiga gidan da Suhaif yake jikin katangar, a nan zata zauna ita da kawayenta saboda duk gidajen sun cika da mutane. Haka aka hau kallon-kallo shi da Iman har suka wuce. A cikin kawayen har da Zubaida da Naja'at suna shiga get din gidan sai Iman ta fashe da kuka, Naja'at da Zubaida ma kuka suke kamar ransu zai fita. Sauran suka yi ta basu hakuri amma suna ta mamaki, kansu ya daure meke faruwa ne haka suke kuka? Can gidan su Huzaifa kuma Mahaifiyar Huzaifa da kannensa suke fama da matar Huzaifa Zainab, ta dauki *ya*yanta da kayanta wai ita kasar zata bari kasarsu zata tafi ta fasa auren tunda yayi mata kishiya. Da tana ganin wasa ne yau ta tabbatar da gaske ne da ta leko kofar gida ta wundo ta ga taron *yan daurin aure da gaske kuma daurawa za suyi baza su fasa ba. Maman Huzaifa da sauran mata dukkansu babu larabci, ita kuma babu Fulatanci babu wanda yake gane abunda take cewa. Aka aika wajen daurin aure a kira Huzaifa ba a samu ganinsa ba saboda taro. Sai aka aika aka kira Iman don ta fassara musu larabci abunda Zainab take cewa. Kafin Iman ta fassara musu abinda Zainab take fada, sai suka ga Iman ta fashe da kuka itama. Hankalinsu ya sake tashi dakyar aka lallashi Iman ta tsagaita da kukan, sannan ta shaida musu abun da Zainab take fada. Shine fitowar Imar da Iman tayi da kawayenta a cikin tashin hankali kuma ta hadu da Suhaif a irin halin da take ciki koma fiye da nata. Abu ya hadu duk yayi mata yawa, tana shiga ciikin gidan sai ta shiga daki tayi ta fusge kwalliyar da aka cancara mata tana rusa kuka ana bata hakuri.
Najib da Huzaifa suna ta waige-waige ko za su ga Suhaif basu ganshi ba. Najib ya cewa Huzaifa "Bari in je in kira shi. Huzaifa ya ce "To" Najib ya tafi ya kutsa cikin jama'a yana ta neman Suhaif, sai Muslim ya gani. Ya tambaye shi ko yaga Suhaif? Muslim yake shaida masa yaga Suhaif ya wuce ta gabansa, ya nuna masa in da ya nufa. Suka nufi wajen da ya nufa, sai suka hango shi a zaune cikin ciyawa ya hada kai da gwiwa. Suna karasawa wajensa ya zabura ya tashi yana cewa "Kar ku karaso wajena, ku rabu da ni. Idanuwansa sun kumbura, kallo daya zaka yi masa kasan yana cikin tashin hankali kamar mai shirin zautuwa. Najib ya durkusa a gabansa yana lallashinsa yana bashi baki, dakyar Suhaif ya yarda ya zauna. Muslim ya ce da Najib "Ko in ke in kira su Baba ne? Ni na kasa gane abunda yake faruwa. Najib ya ce "A'a ba zaka iya ganinsu Baba ba, suna can cikin falon su Iman wajen masu daurin auren.
Dai-dai lokacin suka ji lasafika ana sanarwa ana cewa "A saurara za'a daura auren yanzu. Suhaif ya zabura zai tashi a gigice. Ko ina zai je? Najib da Muslim suka rike shi suka mayar da shi ya zauna. Haka zuciyarsa take ta bugawa fuf-fuf-fuf yayin da numfashinsa yake sama yana kasa, ya dafe kirjinsa saboda tsananin ciwon da zuciyarsa take yi masa da tsananin ciwon kai. Yana rungume da hannun Najib da kirjinsa, Najib ya tsuguna a gefensa, Muslim ma a daya gefen suna tofa masa addu'a suna masa firfita da babbar rigarsa da suka cire masa ganin gumin da yake hadawa.
Suhaif ya daga ido ya dubi Najib ya