Showing 33001 words to 36000 words out of 110329 words

Chapter 12 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt

22 Feb 2025

7481

zani ba.
Watarana ina zaune a gida ni kadai da yamma tunani nake yi yayin da kuka ya rufto min saboda kawai bana jin dadin wannan rayuwar dana tsinci kaina a ciki. Micheal ya zo ya same ni hankalinsa ya tashi ganin ina kuka yayi ta bani hakuri gashi da iya lafazi masu dadi nan danan naji damuwar ta fara gushewa a zuciyata. Ya ce zaman kadaici ne yake sani damuwa inzo ya zazzaga gari dani. Muka fita ya kaini wajen shakatawa kala-kala. Daga karshe muka shiga Zaranda Hotel. Ya ce zai dauki wata takarda a dakinsa in raka shi ciki, ganin tunda nake dashi bai taba nunamin wata alama ta iskanci ba sai na yadda muka shiga daki. Naga mutum yasa mukulli ya datse kofa. Na ce "Ya haka, ba takardar zaka dauka ba mu tafi? Sai ya hau dogon turanci wai yadda muka gaji ya kamata mu huta wajen dare sai mu koma gida. Na ce bazai yiwu ba ni tafiyata zanyi. Kamar yadda na ce Micheal saurayine son kowacce budurwa saboda dan gayu ne na karshen zamani ga uwa uba kyau fari ne dogo sosai, hanci, ido ga iya magana mai dadi. Yayi ta lallashina yana roka na wai inzo in zauna a gefen gadon muyi hira, naki zama. Har durkusawa yayi akan gwiwarsa yana hawaye yana rokata. Hankalina ya tashi na kasa gane wannan al'amari "In zauna muyi hira. Kamar yaya? Ina ganin mutuncin Micheal ga hidimar da yake yi mana musamman ni sai nazo na zauna a gefan gado na takure. Ya zo ya zauna shima a gefe guda muna kallon talabijin din dake dakin. Yana ta yimin hira tun bana amsa masa har na fara kula shi da ke hirar duniya ce kawai, yana ba ni labarin kasashe daban-daban da al'adunsu da ke ya zauna a kasashen wajen.
A hankali Micheal ya matso kusa da ni, hirar kasashe ta fara komawa ta soyayya. Ya fara yabon halayena ina da hankali, ga nutsuwa ga ladabi da tausayi sai kuma ya koma yake yabon kyawuna yana suffanta ni wai irin macen da kowanne da namiji yake so na yi dan murmushi na ce masa "Na gode. Sai ya ji dadi ya sake matsowa kusa dani ya ce "Priety irinku ba su da yawa a Africa, kai a duk nahiyoyi. Na yi dariya na ce . "Kai haba ni din me? Ya ce, "Kin fi ma haka, kalli hannunki kamar na jarirai masu laushi ga kyau. Sai ya riko hannuna. Na ji wani yar a ranar namiji ya taba rike min hannu. Na janye hannuna da sauri. Ya sake rikewa ya fara marairaice mun yana rokona wai ban san yadda yake ji ba saboda so na. Na ce "To me zan yi maka? Ya yi murmushi ya gyara zama ya jawo ni jikinsa yana fadamin dadadan maganganu, na lumshe ido don maganganunsa suna sosa min zuciyata. Kalma daya ya fada ta zaburar da ni da yace in yarda ya nuna min irin kaunar da yake min, idan mun kwana tare babu wanda yasan muna nan ba wanda zai ganmu, ba wanda zai gane wani abu ya faru a tsakaninmu. Na mike tsaye zumbur na dauki jakata cimak na nufi kofar fita, na ce tafiya zan yi. Babu abin da ya fado min a raina sai kalaman Hamma Huzaifa ya ce "Kada kiyi zina ko kun rufe kun kashe fitila Allah Yana kallon ku. Ya taso ya biyo ni ya sa hannu zai rungume ni, yana min dadin baki, sai naja gefe na ce "Kar ka taba ni, bude min kofa in tafi gida. Ya zaro mukulli a aljihunsa ya ce "Kin ga mukullin ba zan ba ki ba ki balla kofar ki fita. Ya juya ya tafi kan gado ya kwanta ya boye mukullin a karkashin filo. Raina ya baci sosai nan da nan na kasa controlling kaina. Abin da da ke jikina wato matsafan nan da suke kokarin jana cikinsu suka motsa. Idona ya yi jawur, karfi ya zo min, hankalina ya gushe, tafiya nake akan yatsan kafata guda daya. Na tunkari inda yake. Ya firgita ganina a wannan hali, hannu daya nasa na fisgo shi na wugar gefe ya fadi ya buga goshi da bango goshin ya fashe. Na dauki mukullin kofar dakin na bude na fita, ni kaina sai da safe na ganni a kwance a falon gidan da muke ba zan iya cewa ga yadda na yi na zo gida ba.
Su Harriet sun ga goshin Micheal a fashe sun tambaye shi bai fada musu dalili ba, amma ya fada wa abokansa wadanda tun tuni sun san irin son da yake yi mini. Su kuwa abokan suka zagaye suka gulmata wa kawayena, wai ni na fasa masa kai don ya ce yana so na. Ni ban taba sanin ashe ni yake so a rashina yake kulata. Ashe sabon gidansa yake turasu su yini don ya sami damar zuwa wajena ba tare da sun sani ba. Ina kwance a dakina daya amma sai na ji Harriet ta shigo a fusace na tashi firgigit na zauna kafin in bude baki in gaisheta na ji wani wawan mari tas a kumatuna. Na rike kuncina na yi shiru, radadi ya hanani magna, balle in tambayi dalilin marin. Sai na fuskanci dalilinta a zage-zagen da take yi. Micheal nata ne, ita yake so shi ne daman nake sadan-sadan kamar ba ruwana, ashe gulama ce son sa nake yi, ina lallabawa in je wajensa. Na yi na yi ta bari in yi mata bayani ta ki saurarona, dakyar Janet ta janye ta suka fita daga dakina. Na kwanta na rushe da kukan da na sa ni, na sake ji an banko kofar dakina da karfi, na daga kaina da sauri na duba sai naga Micheal wannan karon ransa a bace yake sosai. Na dubi goshinsa naga ansa masa plaster ashe ba karamin buguwa yayi ba goshin yayi loto tamkar dan jinjirin Jaki.


Hmmm Allah Yasa mu dace, Amin


Sai kuma gobe da yardar Allah.


Reedwan Suraj Isma'il




YARENA ADDININA
____CI GABAN LABARIN


Nayi zumbur na tashi a tsorace na shige lungu ina makerketa. Cikin rawar murya cikin harshen Turanci na ce "Micheal yi hakuri bada gangan nayi maka ba, ban zata zaka ji ciwo ba. Ya daka min wata tsawa wai in rufe masa baki. Ya karaso inda nake yasa hannu ya damko gashin kaina ya fisgoni daga lungun. Na durkusa kasa na rike gashin don karya fisge. Cikin tsawa ya ce "Ina kudina, bani kudaden da nake baki. Na nuna masa inda suke da hannu. Ya sakeni, na tashi jikina yana bari naje na bude lokar da nake ajiya na dinga zaro dami-damin kudi. Harriet da Janet suka shigo sai kawai suka bude baki suna mamaki, ashe daman kudi Micheal yake cusa mun haka? Ko su da suke fita suna bariki haikan don su sami kudi basu kama kafar wannan kudin ba, gani ni da nake kunshe a gida kullum na tara wannan makudan kudi.
Ya fisgo hannuna ya fegeni farfajiyar gidan. Yace kar in kara shigo masa gida in kama gabana. Harriet da Janet suka zo wajen da nake durkushe ina kuka. Saina hau rokarsu su tayani bashi hakuri idan ya koreni ba inda zanje, idan na koma gida ansan ba'a yiwa *yan makaranta hutu ba sannan makaranta ma bansan kowa ba, dakin da muka kama da nasan wasu sun shiga babu yadda zanje ince bed space dina ne. Abun kunya ne yanzu in shiga makaranta, ince nazo yin me? Ko kuma ina nasan inda *yan ajin namu suke lecture nida ko I.D card bamu dashi. Su Harriet suka yi shewa suka tafa suka fara zazzaga mun wulakanci wai ba cin amana nayi niyyar yi musu ba, ni me wayo nazo na tara kudi na barsu to ai gashi nan don haka babu ruwansu. In san nayi karma in gansu a hanya ince na sansu. Micheal daman saurayin Harriet ne nake so in kwace shi. Na fara rantsuwa na ce ban sanma saurayinta bane don ban taba ganin wani abu ya faru tsakaninsu ba. Nasan dai duk ana zama ayi hira kuma ni ba soyayya muke yi dashi ba ranar ne kawai ya nuna yana sona ban yarda ba kuma. Ban rufe baki ba naji jiff Micheal ya watsomin akwatinana kakaf waje, kayana suka zubo daga cikin akwatinan suka watse a kasa. Ya ce "Good bye pretty, I don't want to see you near my house again. Ya juya ya shige gidan. Su Harriet suka sake yin shewa suka juya suka ce "Muma kinga shigarmu babu ruwanmu da inda zaki tafi. Sun saka kafarsu daya a cikin gidan zasu shiga sai Micheal ya turosu waje ya fito ya tsare kofar shiga yasa hannu a bakin kofa ya kare. Suka dubeshi cike da mamaki "Ya haka, me yasa ya hanasu shiga gida? Sai yayi murmushi yace "Kuna nufin ku zaku ci gaba da zama anan gidan bayan na kori pretty? Suka tambaya "Bamu gane ba? Ya ce "To don ita na baku gida, ci da sha da sutura don tun farko ma ita nake so, tunda bata sona bata yarda dani ba ku ma sai kun bar gidana kamar yadda ta bari "Harrie ta fusata ta kai masa mari ya rike hannunta ya sharara mata wani sharbeben mari.
Ni dai ina gefe ina linke kayana ina kuka ina kallonsu Janet ta fusata ta fara fada masa bakar magana sai ya zaro belt din jikinsa ya dinga dukan duk wanda ya samu. Da naga haka sai nima na zubar da kayana nayi ta kaina. Ya bimu da gudu muka nufi get kafin me gadi ya wangale get ni da Janet mun kama get mun dirga. Harriet ce ta kasa haura get din da yazo ya sameta ya dinga tafka mata belt din dakyar me gadi ya bude mata get Micheal ya angazota waje ta fadi kasa, muka rirriketa dukkanmu kuka muke tamkar Iyayenmu ne suka mutu. Me gadi da Micheal suka dinga jido kayan mu suna watso mana kofar gida bakin titi.
Harriet tace "Micheal to albishirinka har yanzu wannan cikin daka yimin yana nan ban zubar ba don haka kasani idan ba haka ba kaji kara a kotu. Yace "Cikin banza kije kisan yadda zaki yi dashi. Kinzo kin takura min kin makalemun, bana sonki kinsa na miki ciki. To sai inga uban da zai kawo da ko *ya yace kin haifar mun saina fasa dan. Ya jawo get din gidan sa ya rufe me gadi yasa kwado ya bame. Sai gaba dayan mu muka sulale muka zauna, sai kuka muke rusawa. Na nanata a raina ciki, ciki, Harriet ciki tayi? Mun shiga uku mun lalace, cikin kuka Janet ta ce "Ku hada mana kayanmu gefe guda bari in je in nemo mana wajen zama zama ko Boy's quarter da Segun yake zama ya bamu daki daya mu zauna. Na ce "Waye Segun? Ta ce "Wani mutum ne me sayar da giya, mun saba da shi. Bashi da mata shi kadai ne kuma tsoho ne, ina masa kyautar kudi sosai idan ya kawowa su Micheal giya. Nasan Boy's quarter da yake zama don mun taba zuwa da su Micheal rannan da daddare muka taso shi ya sayar mana da giya shima a nan cikin G R A yake wajan Bauchi Club ku jirani yanzu zan dawo, na amsa mata da "To sai kin dawo. Ta tafi da sauri ni kuma na hau harhada mana kayanmu da suka watse a titi. Harriet kuwa bata iya komai ta takure a jikin get sai kuka take kamar ranta zai fita. Na gama hada kayan kenan sai ga Janet ta dawo akan achaba tace mu kwaso kayan mu tsayar da wasu achaba mu tafi ta shaida mana ta samu Mr. Segun din ya amince muzo mu zauna a daki daya, muka tare wasu achaba muka hau mu da kayan mu, muka tafi.
Hankalinmu ya yi mummunan ta shi ganin wannan banbararriyar Boy's quarter. Sumintin kasa duk ya ciccire, ba finti ba filastar kirki. Muka shigar da kayan mu dakin daya ko gilashin wundo babu, wasu daga cikin silin sun ciccire. Kura da yana sun cika dakin. Da sauran kudi a jakar Janet ita ta biya *yan acaba suka tafi. Sai muka fara tunanin yadda zamu fara gyaran dakin, Mr. Segun ya zo ya tsaya a bakin kofar dakin ya fara zano mana dokokin da dole mubi idan muna so muci gaba da zama a gidansa. Ba kawo maza, ba kazanta, kada muyi masa sata, kuma ba ruwa a fanfo mu zamu dinga dibo masa. Muka amsa masa da mun yarda zamu kiyaye. Muka roke shi aron tsintsiya ma yace bazai bayar ba muje mu siya ya kara da cewa na manta ban fada muku ba babu aro a tsakanin ku da ni komai ku nemi naku. Ya dauki kayan giyar sa ya tafi talla bayan ya kulle dakin sa da kicin. Nan dai muka tambayi wajan da ake saida tsintsiya muka siyo muka hau shara da cire yana da goge-gogen kura, wundunan dakin dai a wangame suke ba gilas muka dinga tsinto guntun katakwaye da langa-langa muna karewa mukayi labule da zannuwan mu san nan muka shiga tunanin akan me zamu dinga kwana. Ko waccan su ta zazzage dan kudin da yake jakarta ashe ba masu yawa bane, sun baro masu yawan a dakunan su a gidan Micheal wannan kuwa kwalelen su. Ba yadda za ayi su shiga wannan gida su dauko kudin su, sun sha takaicin kudadan su domin suna da yawa tun farkon zuwan su suke tara kudin nan wanda suke samowa a harkar barikin su. Domin sun yarda da wannan kalmar ta ayiwa maza wayo a karbi kudi, in sun fita daga daki a sata haka zakaji suna fada a hirarsu. Janet ta dube ni ta ce ke baki da ko sisi ma ko? Na ce "Eh. Ta ce "To badan halinki ba zamu suyo tabarma guda uku kwannen mu dai-dai. Amma cinki, shanki ke zaki nemo dan yanzu kowa yayi ta kansa. Ko sabulun wanka babu me baki ba wai kina wani kam-kam da jikinki ba, ke ba *yar iska ba mune *yan iska ko? To dole ki fito ki nemo maza ku sami kudi idan kinki yunwa ta kasheki ba ruwanmu. Na fashe da kuka na ce "Yanzu ina zan fita in sami mazan da zasu bani kudi? Janet ta harareni ta ce "Kullum da daddare dole mu fita mu tsaya a titina wato Good evining ko muje hotels mu sami me daukarmu mu kwana dasu su biyamu. Amma fa duk inda kika san zaki hadu da Micheal ki gudu bashi da hankali har bindiga gare shi, zai iya harbe ki. Nayi ajiyar zuciya nace "Yaushe za'ayi hutu ne mu tafi gidajenmu mu huta? Su duka suka harareni suka ce "Au ke yanzu gida zaki koma, kicewa iyayenki me idan suka ce ki kawo result? Na rushe da kuka nace "Ba cewa kuka yi ba zamu sami kudi mu bawa Malamai su bamu marks ba? Janet ta mike tana tsaki ta ce "Ke ta boko ma kike. Wanne lecture ne zai karbi kudinki ya baki marks? Ni kinga tafiyata acahaba zan hau inje kasuwa wunti in suyo mana tabarmi, tukunya da plates na cin abinci. Ta fice ta barmu. Na dora hannu aka ina rusa kuka ina fadin yaya zanyi? Me zan fadawa iyayena?
Harriet wacce kamar duk ta fimu damuwa ta rasa yadda zata sa rayuwarta, cikin dake jikinta shi ya dameta gashi yayi girma da akwai hatsari cire shi. Ita daman ta barshine don Micheal ya aureta, wato ai dai sun haihu tare ba yadda zaiyi saiya aureta taci kudi tana daga kwance. Yanzu ga irin wulakancin daya yi mata. Ta dafa kafadata itama kukan take tace "Pretty, yi hakuri duk wannan tunanin result bazai gagara ba idan da kudi, ki yarda mu fita mu nemo maza masu kudi zasu bamu kudin da zamu biya lectures su bamu marks. Idan baki yarda mun fita mun nemo ba ko kudin motar Jalingo babu mai bamu. Na dakata da kukan na dubeta na ce "Kema a haka da cikin zaki je wajen wani? Ta sunkuyar da kai kasa sai ta rushe da kuka. Tace "Pretty yaya zanyi? Wa zai bani idan na zauna? Muka rungume juna muna ta kukan dana sani.
Washe gari da daddare suka shirya suka sani na shirya muka tsuke da dan karamin siket din jeans da *yar riga ba dankwali da takalmi me tsini sai jaka kowacce ta rataya, muka fita. Janet ta ce da masu achaba su kaimu Hotel. Nayi mamakin yadda aka yi suka san in da zamu sami *yan iskan maza suma himili guda manyan masu kudi. Suna ganinmu suka yo kanmu kowannensu yana cewa ni yake so daga karshe dai wani mutum ne ya daukeni, bana jin dai Musulmi ne kuma a kalla ya bawa shekaru hamsin baya. Suma kawayena duk suka sami nasu costomers dakunan da muka shiga dukka ukun ajere suke. Su Janet sun fahimci a tsorace nake ko hannuna ya rike sai in fisge kafin mu shiga dakin Janet ta kirani gefe ta zazzageni tace saura kuma idan na shiga in ki yarda dashi, dole in saki jiki in faranta masa. Kafin ayi wani abu in tabbata ya bani kudina nasa a jaka. Na amsa mata jikina yana karkarwa sannan na dawo wajensa itama ta koma wajen nata kowacce da nata, mu ka shiga dakuna. Ya mayar da kofa ya datse sai gumi ya keto min na hau karkarwa. Ya zauna akan gado ya jawo hannuna na zauna a kusa dashi kamar ace kule ince cas in zura da gudu dan tsoro. Ya dubeni yayi murmushi ya ce "Wai ke wannan ya haka, ko dai sabon shiga ce? Ya miko hannu zai tabani nayi zumbur na mike tsaye na goce. Ya sake kallona cike da mamaki ya ce "Lafiya kike guduna, to nawa zan biya kwana daya? Nayi shiru can na ce dubu biyu. A ganina na ballo wasu makudan kudi masu yawa. Ya kwashe da dariya harda buga kafa. Ya ce "Haba baby ai kinfi dubu biyu ko kallon fuskarki da nayi ai na biyaki dubu biyu balle mu kwana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login