Showing 48001 words to 51000 words out of 110329 words
Chapter 17 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
Micheal ya hau zare guru-gurun idanuwansa tamkar bai gane abunda nake nufi ba sharri nake masa. Mahaifina cike da mamaki ya ce "Wai meke faruwa ne, me yake damun Fatima ne take magana kamar tababbiya? Micheal fada mana gaskiya me take nufi? Mamaki marar misaltuwa zaka iya gani a idon Micheal ya ce shima bai san me Pretty take nufi ba, shi dai abinda ya sani shi ne yayi mata ciki, ciki yayi wata tara, da hannunsa ya kaita asibiti ta haihu yana shirin ya siyo musu kayan haihuwa ya kawota gida, ta gudo tazo tana nunawa kamar bata sanshi ba yanzu. Mahaifiyata ta fusata ta mike ta nufi inda muke tana fada tana cewa "Na zamar dasu kamar wasu yara kanana yaushe aka haifeni da zan musu wayo in nuna ma bani na haifi yaron ba, don haka duk ranar da na kara duban kwayar idanuwansu na ce ba nice Mahaifiyar yaron nan ba saita fasa min baki. Ta tunkaro inda nake tsaye a fusace, a zatona ma dukana zata yi saina rufe fuskata da hannuna Tabita ma jikinta ya dau rawa ta taso tana bata hakuri sai na ji ta fisge goyon daga bayana ta tafi da yaron wajen Micheal. Na sulale na zauna a kasa don takaici da radadin da zuciyata take yi. Tabita na bani baki akan kar in damu kar in sake yin musu akan bani na haifeshe ba in barsu haka. Na ce "Mama Tabita zancen aure fa suke yi, wai tunda ga da a tsakani zai aureni mu rike danmu. Tabita ta ce "To ai babu komai ki aure shi Rufkatu, yaro ne mai hankali mai kyau kuma, kin fada mun yadda yake matukar sonki tun farko ma ke yake so ba Harrier ba zai rikeki sosai tunda yana sonki. Na girgiza kai hawaye bai daina zuba ba nace "Ba zan iya auran Micheal ba Mama Tabita Micheal dan iska ne, macuci ne, bashi da tausayi ko kadan, dan fashi ne, duniya yasa a gaba babu addinin da yake yi. Haka Tabita ta tsaya a kaina tana kallona tamkar sassakakken gunkin da take bautawa, daga dukkan alamu ta fara zargina da yiwa Micheal kazafi saboda kiyayyar da nake yi masa.
A can falo suka yiwa jaririn adddu'a irin tasu, suka sakawa yaron suna Citibin. Micheal ya dauko Camara ya daddauki yaron a hotuna kala-kala, ya dauki Mahaifiyata da Mahaifina da Jaririn a hoto, sannan abokinsa ya dauki Micheal da dansa sannan ya dauki Micheal da dansa da Mahaifana a hoto. Daga karshe suka yi addu'a, Micheal yayi musu sallama akan da zarar yaje gida zai sanar da Mahaifiyarsa ya gano inda Pretty take da Jaririnta dan hankalinta ya tashi daya sanar mata Pretty ta gudu kuma baisan garinsu ba. Ya ci gaba da zuba musu karya ya ce itace tace lallai-lallai yaje ya nemo Pretty duk inda take. Yanzu kuwa zata fi kowa jin dadi idan taji labarin ya ganta ita da Jaririn suna cikin koshin lafiya. Kuma zai daukota su zo taga yaron sai ayi zancen aure. Mahaifiyata taji dadi kwarai saboda zata hada zuriya ko kuma ma in ce ta hada zuriya da babbar Malamarta a wajan bauta, mai tsananin yiwa addininsu hidima da dukiyarta da jikinta wato Mahaifiyar Micheal. Dari bisa dari taji aurena da Micheal ya kwanta mata a zuciya. Mahaifina kuwa ba yabo ba fallasa, ba haka yaso ba wai kanin miji yafi mijin kyau. Bashi da zabi tunda matarsa sai yadda tayi dashi, jikinsa yayi sanyi kalau dan yasan ba'a yin haka a addininsa na da, mace ta haihu a titi ba tare da anyi mata aure ba. Mahaifiyata ta kwallawa Tabita kira tazo ta dauki dan Jaririn da lubgin kayan da Mahaifinsa ya sayo mana kala-kala ta ce a kawo min. Nayi farin ciki da kayan Jarirai *yan waje dan daman yana fama da rashin kaya, bayansu kuwa duk sauran basu burgeni ba. Leshinan da atanfofin basu isheni kallo ba, saidai madarar Jarirai suma ya burgeni da yayi tunani ya siyo, dan kuwa yasan yaron ba uwa gareshi ba balle yasha nono.
Haka na kasance kukan dare daban, na rana daban, na yamma daban. Ko gidanmu bana son shiga ina nan nane da Mama Tabita, ita kadai ta rage mun mai kwantar mun da hankali ta bani hakuri idan ina kuka, ta tausaya mun halinda nake ciki. Na kanyi kuka na musamman idan na tuna babban rashin da nayi na Hamma Huzaifa, ina tsananin jin takaicin ya tafi da bakin cikina a ransa, na ganina da jariri ba tare da na wayar masa da kai ba cewar ba dana bane, kuma fadan da yake mun, naji fadan ban taba aikata zina ba. Huzaifa ne abokin hirata mai kokarin amsa min tambayoyi, mai kaifin basirar yanke mun kyakkyawan hukuncin duk wata matsala data dameni. Allah baya barin wani dan wani. Ya daukemun Huzaifa.
Iman tayi shiru tsabar yin kuka tayi magana ta gaji, gashi babu koshi a tare da ita. Suhaif ya aika wani gida kusa da inda suke ya ce a debo mata ruwa ta sha. Idanuwanta sunyi luhu-luhu tasha kuka ta godewa Allah. Abun tausayi, da aka kawo mata ruwa kurba daya tayi da kyar ta hadiye saboda tsananin rayuwar da ta shiga. Suhaif yayi-yayi ta sake shan ruwan ta ce ba zata iya shaba, ta dauki lokaci mai dan tsawo kafin ta sake cewa wani abu.
Ta ci gaba da cewa "A tunanina iya sanina bana zaton akwai yarinya mai irin shekaruna, da ta taba shiga irin kuncin rayuwar dana shisshiga. Amma na sa a raina Allah Ya na sane dani kuma baya bacci. Kowanne bawa akwai yadda Allah Ya ke jarrabarsa, ni kuma ta haka Allah Ya ke jarrabata. Nasha wuya a wannan lokacin saboda kula da jaririn bana samun bacci da daddare kuma dole in bar dakin Mama Tabita saboda mijinta ranar zai kwana a gida domin wani yana canjarsa. Ni kadai a dakin da aka ware mun, tun bansan yadda zan lallashi yaro ba nar na fara sabawa, shima kuma ya saba da jagwalgwalon da nake masa har yayi shiru ya koma bacci. Yana rungume a hannuna, ni kuma ina zaune ina gyangyadi har sai na tabbatar barcin nasa yayi nisa sannan nake kwantar dashi in kwanta. Ana jimawa zai farka in sake katse baccina in bashi madara, idan yaki komawa bacci saina goya shi ina jijjigashi. Ni kadai a zaune cikin dare yayin da duk bil'adama suna bacci. Idan na gaji sai in ta kuka ni da jaririn a rasa mai lallashin wani. Kar kuce da safe zai barni inyi bacci, a'a garin Allah na wayewa zan shiga kacaniyar hada ruwan wanka Mama Tabita tayi masa, ana jimawa in dama masa madara in bashi, a jima yayi kashi, ajima yayi tunbudi, ajima inyi wankin kayansa. Haka dai muka kasance babu hutu ni da Tabita kuma ga aikin gidanmu.
A lokacin na sawa raina Mahaifana basa sona ko kadan don ina bukatar taimakonsu da kulawarsu basa mun, ina takaicin wannan al'amarin musamman idan naga kallon da Mahifina yake min, hankalina yana tashi kamar ba shine mai sona ba, yayi hira da ni, yayi wasa dani, yau gashi idan na gaishe shi dakyar zai amsa min a cicciki. Mahaifiyata kuwa daman can ta saba yimin haka tun ina yarinya, kullum muna rigima da ita saboda bana zuwa wajan bautarsu, ta fuskanci bana yin addininta, tayi dukan tayi zagin ta gaji. Ina tsananin jin takaici idan naga Mahaifina tare da Mahaifiyata da kannena sun dunguma za su tafi wajan bauta duk ranar bauta. Nakan gigice inyi kuka saboda takaicin Mahaifina ya bar addininsa na Musulunci. Babu wanda yake cemin in shirya in biyo su wajen bauta. Kamar yadda suka san Tabita da addininta nima sunsan dole da addinina daban ba nasu ba.
Jaririn ya fara warwarewa yana girma watanninsa uku a duniya. Mahaifiyata tasa kanwata Rabecca ta kira ni a gidan Mama Tabita, ina yi masa wanka. Mama Tabita ta karbe shi ta ce in je kiran da ake min, ina zuwa na duka na gaishe da Mahaifiyata cikin harshen Igbo. Ta amsa a shelake ta nuna min wata katuwar jaka a makare da kaya ta ce "Ki dauki jakar nan sako ne daga Micheal ya aiko jiya da daddare hade da wasika, wasikar kuma gata na karanta, ya ce ranar asabar mai zuwa yana nan tafe da Mahaifiyarsa da *yan uwansa akan zancen aurenku. Kada ki sake bamu kunya, kada ki kuskura ki bude baki ki fadi wannan bayanin naki na rashin hankali cewar bake ce kika haifi yaron ba, daga karshe kuma kada ki sake ki fito min da wata tsirfar wani addini idan ba irin namu ba. Ni da Micheal da Mahaifinki addininmu daya don haka dole addinin da muke shi zaki bi, haka danki ma. Ranar lahadi zamu dunguma dasu Micheal dukka aje wajan bauta, saura ki ki zuwa ko kuma kije ki faki idanuwanmu ki gudo kamar yadda kika saba tun kina yarinya. Idan ki ka kunyatamu, ki ka ki auransa to fa ke da danki zamanku ya kare a gidan nan, don babu wanda ya ce ki je kiyi ciki ki haihu dole ki aure shi ku tarkata ku tafi. Baza ki jawo mana abun kunya ba, abun fada, ana ganin girmanmu ana mana biyayya kisa girmanmu da mutucinmu ya zube a idon jama'a. Yanzu ma Allah ne Ya dubi zuciyata ya rufa mana asiri Micheal ya zo da kansa yayi zancen aure da bansan me zan fadawa mutane ba *yata ta haifi da marar uba.
Jinta kawai nake amma tuntuni tasan bana cikin haiyacina nayi sharkaf da hawaye. Wata uwar tsawa da ta daka min ina tsugune sai da ni mike tsaye ta ce "Kukan me kike yi? Rufe min baki ko in tashi in tattakaki. Mama Tabita ce ta katsemu ta shigo da gudu a gigice dauke da Jaririn a hannunta, zanin jikinta ya fadi a hanya bata sani ba, daga ita sai dan siket da riga. Karkarwa take ta nufo wajen da Mahaifiyata ke zaune tana cewa "Madam ki taimakamin ina sawa yaro riga idanuwansa sun kakkafe sama, babu numfashi, babu motsi. Subhanallahi! Irin bugun da zuciyata tayi a lokacin inda yazo da karar kwana, zuciyata ta fashe na fadi na mutu. Na karaso da gudu na karbe shi ina jijjigashi hakika ko ba'a fadamin ba nasan yaron ya rasu. Mahaifiyata ta gigice gaba dayanmu ihu muke. Mahaifina na kwance a dakinsa yayi wuf ya fito, ya karbi yaron ya jujjuya, sai ya girgiza kai alamar babu. Nayi kuka nayi kururuwa, babu lallashin da basu yimin ba naki yin shiru. Na rike yaron tsam a hannuna, suka yi juyin duniyar nan su karbe shi naki basu. Abun mamaki sai suka ga na sabashi a baya. Suka tambayeni ina zanje cikin kuka na ce "Asibiti Mama Tabita ta rikeni tana cewa ya mutu me za'ayi miki a asibiti, na fisge na shiga dakina da gudu na dauko jakata na fito, kuka nake, tana rokona in hakura in sauke dan, idan mutum ya mutu babu abin da *yan asibiti zasu iya yi. Na ki fur nace ni dai asibiti zan kai shi. Mahaifiyata ta ce da Tabita ta barni inje asibitin in na je ma zan dawo, likitoci suna farfado da matacce ne? Haukar banza da yarinta, manya sun fadamin ya mutu ni na san mutuwa ne da zance asibiti zani. Mahaifina yana ta kwallamin kira na fice da gudu na nufi titi ina kururuwar kuka tamkar tababbiya. *Yan unguwarmu suka firfito suna tambaya "Meya sami Pretty? Aka sanar musu dana ne ya mutu na goya shi na ce asibiti zan kai shi. Sai suyi dariya suce "Yarinta ke damuna ban san mutuwa ba ne, lallai da ban je asibiti ba. Na hau dan achaba ina karkarwa na ce ya kaini asibiti.
Daidai get din shiga asibiti naji yaron yana tamin mutsu-mutsu a baya, wani dadi marar misaltuwa ya lullubeni, nan da nan na cewa dan acaba ya sauke ni a nan. Yana tsayawa na diro da sauri daga kan babur na kwance goyon da sauri yayin da nayi ajiyar zuciya gami da ambaton alhamdulillahi a lokacin da nayi ido hudu da dan jaririna. Saboda tsabar gigicewa gami da jin dadi, mantawa nayi ban biya mai achaba kudin babur dinsa ba, na ruga cikin asibitin da gudu. Ina shiga ba tare da na yanki kati ba, haka ba tare da na tuna ana bin layin ganin likita ba, haka na tsallake dandazon matan dana iske a zaune akan bencina suna bin layin ganin likita, sai kawai na tsallakesu na rufta dakin likita, kowa ya bude baki yana kallona cike da mamaki. Ma'aikaciyar jinya (nurse) din dake aiki tare da likitan ta biyoni cikin dakin da sauri tana tambayata "Ke baiwar Allah lafiya kika zo kika iske mutane a layi, wasu a ciki suna ganin likita kika shigo? Nayi guru-guru da ido in kalleta in kalli likita in kalli matan dana iske a gaban teburin likita yana dubasu. Haka shima likita ya zura min ido gaba dayansu suna sauraran bayanin da zai fito daga bakina.
Nurs din ta sake tambayata "Ina katinki na ganin likita ko shima baki je kin yanka ba? Na gyada kai alamar eh ban yanka ba. Sai haushina ya rufeta ta hau fada tana cewa in fito kar in bata musu lokaci in likita zan gani inje in yanki kati in bi layi irin na kowa, akwai mutane a gabana saman da talatin. Na rushe da kuka ina rokarsa ya taimakeni yarona suma yake yi yanzu ya farfado. Cike da tausayi likitan ya dubeni sai ya cewa nurse din ta rabu da ni bari ya dubani bata ganin ni yarinya ce watakila bansan yadda ake yi ba. Nurse ta fita ta jawo mana kofar ta rufe. Ya juya ya dubi matan guda biyu da suke zazzaune a kujerun dake gaban teburinsa suma rungume da yaransu ya ce suyi hakuri bari ya duba min yaron. Ya mika hannu ya karbeshi ya fara duba shi yana bude bakinsa, hancinsa, cikinsa da kirjinsa, ya zabura ya mike da sauri ya nufi kan wani gado dake ofishin na kwantar da mara lafiya domin dubawa. Na ji gabana ya fadi na dafa kirji cike da fargaba nake tambayar likita "Meke damunsa? Bai bani amsa ba yaci gaba da aikinsa. Ya dauko wani abun gwaje-gwaje yana auna numfashin yaron, ya sake daukar yaron da sauri ya nufi kofar fita, yayin da kuka ya kece min ina binsu a baya, na tabbatar akwai matsala mai yawa ganin likitan hankalinsa a tashe. Muka fito muka nufi wani daki. "Malama me kike nufi ne kin ruga da gudu baki biyani kudin achabana ba? Dan achabar da ya kawo ni ne yake tambayata a cikin kakkausar murya. Na juya inda sautin maganar ke fitowa naga dan achaban ne ransa a bace. Hannuna yana rawa na bude jakata na dauko naira ashirin na mika masa gami da bashi hakuri na ce mantawa nayi. Na sake runtumawa da gudu na bi bayan likita a lokacin harya shiga dakin. Muna shiga likitan ya cirewa yaron kayansa, ya daga kafafuwansa sama kansa a kasa yana jijjiga shi, yayin da yaron ya shide yana kuka, amai ya fara diddikowa ta hanci ta baki, ya mayar da yaron ya kwanta ya kafa masa wani inji mai doguwar roba ya sakala masa ta hanci da baki. Kukan da nake ina tambayar likita meya same shi? Ya tunzura likitan yayi fushi ya ce in fita waje in jira na barshi yayi aikinsa.
Me zaku ce game da Member 2 da suke son zama Admin a wannan page?
Na daya zai dinga rubuta littafin SHAFI'U DAUDA GIWA
Na biyu shi kuwa WA'AZANTARWA zai dinga yi
Ya kuka gani? Kuma me zaku ce?
________________ YARENA ADDININA.
___CI GABAN LABARI
Na fito bakin kofar dakin na tsaya ko ban fada ba kowa yasan ina cikin tashin hankali. Ina son Jaririn Harriet tamkar dan da na haifa a cikina. Ina tsoron halin da zan shiga idan aka ce min ya mutu. Fitowar likitan ya katse kukan da nake. Ya ce in shigo dakin, ya fara min bayanin abun da yake damun yaron ya ce "Yaron baya samun kulawa, ma'ana ana bashi madara ko nono ba tare da ana tallafo kansa ba, a kwance ake bashi yadda zai zuraro ta hancinsa ya kware. Haka kuma bayan ya sha ba'a dagashi akan kafada har sai yayi gatsa, sai a barshi a kwance har nonon ya gargara yabi ta wajan da yake shakar iska. Sannan ana bari yana shakar sabulu idan an zo yi masa wanka. Sune suka taru suka hana shi numfashi badan anyi saurin kawo shi asibiti ba an zuke masa, gaskiya daya rasa ransa. Na sulale na zauna kan wata kujera ina rusa kuka, ya dube ni sosai sai ya ce "Danki ne? Na gyada kai alamar eh. Ya girgiza kai ya ce "Fada min gaskiya ba ke kika haifi dan nan ba, ina Mahaifiyarsa? Dole ki fada min gaskiya don kar a sake samun irin wannan matsalar. Saboda rayuwar yaron tana cikin hatsari dole in yi magana da Mahaifiyarsa idan ma yara irinki take barwa danta to ta daina. Cikin sheshekar kuka na ce "Mahaifiyarsa ta mutu. Ya ce "To wacece take rike da shi? Nayi shiru can na ce "Ni ce cike da mamaki ya tambayeni "Ke ce? Ina Mahaifiyarki? Na ce tana gida. Ya ce "Lallai-lallai ina son in yi magana da ita ko wani babba ba ke ba. Na goge hawaye na ce "To bari inje in kirasu. Ya ce "Yauwa gara kije ki kirasu in yi magana da wani babba. Na ce "Zan iya tafiya da shi? Ya ce "Ki dauke shi ai nagama yi masa abunda zanyi masa ya samu sauki Insha Allah. Na saka masa rigarsa da wandonsa, sai tsotsar hannu yake da alama yunwa yake ji, na goya shi.
Na bude jakata zan dauko kudi in biya likita, sai naga wayam babu ashe ashirin din dana bawa mai babur din nan ita kenan. A zatona da kudi a cikin jakar sai nayi kasake ina dogon tunani, san nan na tuna ashe na kashe kudin shekaran jiya tsabar rudewa tasa na manta. Na ci gaba