Showing 30001 words to 33000 words out of 110329 words
Chapter 11 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
fadawa Mahaifiyata. Sannan nabar ganinsu a mafarki na dawo hayyacina kamar da. Naci gaba da harkokina kamar kowa kuma ina jin dadin sabuwar makarantar ta jeka ka dawo. Amma naci gaba da bincike akan addinai kuma ina zuwa wajen kawayena Mumuyawa kullum bayan na dawo daga makaranta, haka ban daina zuwa dakin bautar mai aikinmu ba Tabita ina ganin yadda ake bautarta ina yi mata tambayoyi. Kuma dolen-dolena in bi Mahaifiyata wajen bautarta duk ranar yin bauta. Musamman yadda Mahaifiyata ta sami karin girma ada aka bata mukami saboda saninta, da kwazo a bin addininta. Dukiyarta, jinin jikinta da duk lokacinta duk ta sadaukarwa addininta. Ta kai ta kawo duk ranar bauta bayan an tashi daga wajen bauta su Mahaifiyata suna shiga motoci su shiga kauyuka da burane suna wa'azi suna kira zuwa ga addininsu.
Na fara zama budurwa na kara wayo da hankali. Ina zama da Hamma Huzaifa a kofar gidansu lokaci-lokaci da yamma idan na dawo daga makaranta naga Mummy bata nan, kuma idan bana son zuwa wajen kawayena da abokaina Mumuyawa. Shi daman Hamma Huzaifa kullum da yamma idan yana gari bai koma makaranta ba a kofar gidansu yake shimfida darduma ya zauna yana karatun kur'ani, a lokacin yana karatu a FUTY jami'ar dake Yola. Sai inzo in zauna in yi ta sauraronsa domin karatun yana yimin dadi kuma ina sha'awa in koya. Idan ya shafa addu'a sai mu shiga hirar duniya a hankali sai mu gangaro hirar da muka saba ta addini. Na ce "Hamma Huzaifa ka bani addu'ar kariya idan abun tsoro ya tunkaroni. Sai ya koyamun ayatul kursiyyu, falaki da nasi, duk da nasha wuya kafin in koya amma na nace dakyar na koya da sudin goshi kuma na dauki lokaci mai tsawo kafin na iya sosai.
Watarana ina aji hudu na secondry ni da kawayena mun fito daga get din makaranta an tashi zamu gida saina ji dik mutum ya diro a gabana ina tafiya na tsaya cak sai naga wannan budurwar data bani alewa da biskit amma a suffar abun tsoro tazo mun, farata zaka-zaka da hakora. Ta mika hannu zata tabani na tsorata na fadi kasa ina karkarwa, sai Allah Yasa na tuno da addu'ar da Hamma Huzaifa ya koya mun saina fara karanto ayatul kursiyyu ta kasa tabani saita bace. Wadanda muke tafiya basu ganta ba ni kadai na ganta sunga kawai na fadi kasa ina karkarwa har sun wuce suka dawo suka tashe ni muka tafi. A lokacin na sake sakawa raina ina son Musulunci addinin gaskiya ne. Na ci gaba da bincike da koyon abubuwa a cikin addinin a wajen Hamma Huzaifa ko kannensa idan baya nan. Ko kuma kawayena Musulmai. Watarana in shiga library makaranta bangaren littattafan addinin musulunci in buya inyi ta karantawa. Ina da kokari a makaranta sosai don haka ina S.S 2 na zana jarabawar S.S.C.E tare da *yan S.S 3 kuma na cinye dukka. Mahaifana sunyi murna sosai, ba tare da bata lokaci ba Mahaifina ya samarmin addimission a ATBU yace can zanje idan naje Yola bazan yi karatun kirkiba saboda akwai *yan Jalingo da yawa kuma kusa da gida ne gara nesa. Da farko na damu sosai kawayena Harriet da Janet suka ce kar in damu dukkansu jami'ar ATBU zasu tafi saimu hadu kawai a can, sannan naji hankalina ya kwanta. An bani course din da Mahaifiyata ta karanta achetecture naji dadi Iyayena ma sunji dadi. Kafin inje registration saida Mahaifiyata da Mahaifina dani muka je London da China yawan shakatawa kamar yadda koda yaushe suke yimin alkawari idan na gama secondry naci jarabawata zasu kaini kasashen waje. Munyi sati hudu acan sannan muka dawo. Alokacin har naso in makara saboda an koma makaranta har an kusa rufe rigistration.
Cikin gaggawa Mahaifina ya hadamin kayan tafiya kamar sababbin dinkuna na zamani, privision. Takalman gayu akwatina masu tsada littafi biruka, Pencil da dai sauransu. Ya kaini har Bauchi
Da kansa ya tayani muka yi registration saida ya tabbatar ya kammala mun komai. Ya biyamun kudin daki a hostel dake cikin makarantar. Yayi min fada sosai in tsaya inyi karatu kamar yadda shi da Mahaifiyata suka yi suka fito da first calass degree. Har ya zazzagaya dani wasu wurare a makarantar yake nunnunamin inda suke zama da Mahaifiyata suyi karatu tare. Don haka kar in biyewa kawaye marasa son suyi jaratu. Abu daya Mahaifina ya bani mamaki da bai taba yimin fada akan in rike addinina ba, har yayi min fadan ya gama ya shiga mota zai tafi naga baiyi min zancen addini ba. Sai na ce "Daddy baka ce in rike addinina ba. "Ya tsaya yana kallona kwai ya kasa magana. Sai hawaye ya zubo daga idanuwana, na ce "Daddy ko dan ba addininmu daya ba? Jikinsa yayi sanyi hankalinsa ya tashi sosai. Cikin harshen fulatanci na yi magana na ce "Bakar saniya mai cin ciyawa koriya ta bada farin nono. Ya sake zare ido yana kallona, saina juya na tafi hostel ina daga masa hannu. Ya kifa kai akan sitiyarin motarsa, yafi minti goma sha biyar bai tafi ba yana tunani da hawaye. Ina lekensa ta daki, sannan ya share fuskarsa ya ja mota ya tafi. Daga Bauchi sai ya shiga Gombe garinsu don ya gaishe da Mahaifiyarsa da danginsa, duk da yana gani a fuskokinsu basu bukatar ganinsa sun ma cireshi a dangi haka kuma ko kyautar kudi ya yiwa Mahaifiyarsa bata karba kome ya sayo bata ci. Kuma duk sanda ta ganshi sai tayi kuka, dan haka hankalinsa yana tashi idan yaje Gombe sai ya rage zuwa sosai jifa-jifa.
Allah Ya tsaremu daga sa6awa Iyaye maganarsu. Ameen
Sai kuma Allah Ya kaimu gobe da yaddarSa.
Ina cigiya wanda yake da wannan littafin a hannu pls.
Reedwan Suraj Isma'il
"""""""""""""""""" YARENA ADDININA
____CI GABAN LABARIN
Na hadu da kawayena Harriet da Janet suma kuma duk cours dinmu daya. Ranar da muka fito daga lecture farko su Janet suka cemun ga wani abokinsu sunansa Micheal yazo daukarsu zasu je suga gidansa dake New G.R.A. Wai inzo in rakasu. Na ce meyasa zasu tafi bayan da yamma muna da lecture? "Suka ce "Ai yana da mota zai dawo damu kafin lokacin. Fadan da Mahaifina yayi min shiya fado min a rai, ya ce kada inyi kawance da wadanda basa son yin karatu. Sai nace su je ni ba zani ba. Suka takura mun, Micheal din ma ya zo yasa baki wai in daure inje yanzu zamu dawo a matsayinmu na baki a Bauchi shi kuma dan gari shine yake so ya nuna mana gari da gidansa. Ko ba komai dai mun san wani, koda muna bukatar wani abu, shi kuma zai rikemu a matsayin kannensa zai taimaka mana. Naji lafazinsa masu sanyi na shiga mota muka tafi. Ashe daga wannan tafiyar ba zamu sake dawowa mu shiga lecture ba. Gidansa mai kyawun gaske mai dauke da dakuna uku kowanne da bandakinsa. Falo babba, kicin cike da abinci kala-kala ga kuku mai dafawa ya jera a dining area. Ko'ina a gidan sai sanyin A.C, wannan gidan daya ne daga gidajen Micheal da babansa ya mutu ya bar masa ne, ga tulin dukiya. Sai yace mu zauna a gidan kawai ba sai mun koma zaman hostel ba, shi kuma zai tafi sauran gidajensa daman ba'anan ya fiya zama ba, ya ce mu zauna mu kadai kowacce da dakinta. Ina son gidan amma nayi tunani naga ba yadda za'ayi haka ta yuwu domin hostel Mahaifina ya kaini. Na ce musu ni tafiya zanyi bazan zauna ba. Harriet ta dinga mun masifa wai danme zance bazan zauna ba, bayan mu kadai ne a gidan ba iskanci za muyi ba, ga direba zai dinga kaimu lectures. Ni dai nayi shiru ina tsoron masifar Harriet amma ba dan raina ya so ba. A hankali su Harriet suka je suka kwaso mana akwatinan kayanmu daga makaranta kowacce tasa a dakinta. Sai mun shirya tsaf da litattafanmu zamu je lecture direba yazo ya daukemu sai inga anyi ZARANDA HOTEL. Sai in tambaya "A'a ba makaranta zamu je bane? Sai suce wai Micheal zasu gani a dakinsa na hotel yanzu zamu fito mu tafi. In zauna a mota ina ta jiransu su shiga ciki su dade sai ni sai direba a zaune a mota ina tsaki ina duban agogo. Can sai inga Micheal ko wasu abokansa su Debid, Solomon, Gibreal, Emeka da sauransu su zo suyi ta rokona wai in shigo ya zan zauna a mota, ga rana inzo mu shiga. Su dameni dole sai sun takura mun na shiga. A dakin hotel din nan ake zama ana hira ana ta ciye-ciye. Abin yana ba ni mamaki yadda na ga kawayena Harriet da Janet sun saki jiki ko fargaba ba sa yi, sun saba da mazan nan har tafawa suke yi, suna cin abinci tare suna kwantowa akan cinyarsu. Ashe daman ni suke yi wa dabara, samarinsu ne tun sanda suka fara zuwa. Ni dai ina makale da littattafaina na takure a lungu idan raina yayi dubu ya baci. Duk wanda ya matso kusa dani a cikin mazan sai inyi zumbur in mike ina shirin buda kofa in arce, sai Micheal ya yiwa abokansa tsawa ya ce, su kyale ni. Kome a ka kawo gabana na ci ko nasha sai in ki ci ko sha, suka yi ta roko na in ki. Idan suka gama ciny-ciye da shaye-shaye har da giya sai su ce za su shiga dakin disco su yi rawa inzo mu je, in ki zuwa. Micheal ya miko min jarida wai in kwanta in yi ta karantawa kafin su dawo, su fice su bar ni. Na fashe da kuka mai tsanani, na yi tunani bari kawai in tashi in fita in hau acaba, in yi tafiyata makaranta, sai in ji ashe sun datse ni ta baya, na dawo na zauna na sharbi kukana. Sai da yamma likis sannan direaba ya mayar damu gidan da muke. Ina shiga na hau hada kayana zan tafiyata makaranta su Janet suka hanani tun suna rokona da lallashi har ta kai ta kawo sun fadamun baro-baro ba zan je ba ni in je inyi karatu, idan na koma Jalingo in yada su a gari in ce ba karatu suke ba iskanci suke. Suka karanto min manufarsu shine in kwantar da hankali muci kudi kawai ba wahalar karatu. Idan muka sami kudin sai mu biya lecturers dinmu su ba mu marks. Akwai yarinta a tattare da ni ga rashin sani don a lokacin shekarata goma sha biyar kacal duk sun girmeni. Sai na yarda na saki jikina a gidan mukayi ta cin dadi. Kuku ya dafa mana abinci kala-kala. Micheal ya zo ya daukemu ya yawata gari damu, super markets kala-kala kowacce ta dauki abin da ranta ke so na ci ko kayan tsukewa jeans, t-shirt, takalma da dai sauransu.
Amma ko alama ban taba ganin wani daga cikin samarin nan ya neme ni da iskanci ba za su zo gidan mu zauna a falo mu yi ta hira. Dama ni ba na binsu Zarandah Hotel. Idan zasu je club su yi rawa. Su yi su yi da ni sai na ki, in shige dakina in kulle, ina kallon films. Su Harriet da Janet dai suna zuwa, kuma ko alama ba sa nuna min suna iskanci da mazan nan. Na san dai suna fita su dade su kai har sha biyun dare.
Kwanci tashi first semester ya kare *yan makaranta suka yi jarabawarsu suka gama mu kuma muna can muna hutawa. Micheal ya bamu mota da direba ya kaimu garinmu Jalingo. Sai dai kawai Mamana da Babana suka dawo daga wajen aiki suka tarar da ni a gida na dawo. Sun sha mamakin ganin yadda na yi kiba, na yi fari da kyau sosai. Abin da Babana ya fara cemini da ya dube ni sai ya ce min, Mamana kina karatun nan kuwa? Na yi murmushi na ce "Daddy ina yi. Mummy ta sake kallona ta ce "Ina sakamakon jarabawar? Nan fa na ji gabana ya fadi na zazzaro ido sai Daddy ya ce "Ai ba yanzu ba sai sun yi second semester exam za a kafe musu result. Na yi ajiyar zuciya don dadi, don ni ban san ma haka akeyi ba.
Hutunmu yana da tsawo don haka muna zama da Hamma Huzaifa sosai mu yi ta hira. Shi kuma a lokacin ya gama karatunsa na degree har yayi bautar kasa, don haka kullum yana gida ba inda yake zuwa. Saboda ni ya sayo wasu kujerun roba ya ajiye a bayan gidansu karkashin wata katuwar bishiyar mangoro, anan muke zama muyi ta hira. Kallo daya Huzaifa yayi min yaga na canja sai ya shiga jero min wasu tambayoyi masu wuyar amsawa ya ce da ni "Amma makarantar nan ta karbeki pretty. Nayi murmushi na ce "Meka gani? Ya ce "Kamar ba karatu kike je ba hutu kika je yi. "Nayi murmushi kawai, sai ya shiga baromin tambayoyi akan course din da nake karanta, nayi sauri na canja salon hirar. Ya sake dawowa da hirar karatu, yace in je in dauko masa litattafaina zai ga abunda ake koya mana. Nanma na amsa masa da "To sai gobe zan dauko maka. Hankalina ya tashi ainun na shiga fargaba. Abun mamaki Iyayena basu sani a gaba ba sun bincikeni haka sai Huzaifa saboda haka naga gara na rike shi mai sona ne na kuma nuna masa sha'awata ta Musulunta. Allah cikin ikonSa a cikin hutun ne na karbi kalmar Shahada, Hamma Huzaifa ya Musuluntar dani a boye ba wanda ya sani. Iman ta sharbe hawaye mai wuyar fita.
Taci gaba da cewa "Ya koyamin yadda zanyi wankan shiga Musulunci, wankan haila da janaba. Bayan na koyi duk wanna sai ya fara koyamin sallah da karatunta, bayan nayi wankan Musulunci sai na kulle kaina a daki nayi sallah. Kullum haka nake yi, amma duk ranar da Mahaifana suke gida sai naje gidan su Hamma Huzaifa in yi aboye don suma bana son kannensa su ganni balle zance ya fito aji a gidanmu. Mahaifiyarsa kawai muka sanarwa, sai ta boyeni a dakinta ta datse in shiga inyi sallah. Itama ta koya mun abubuwa da dama kuma tayi matukar farin ciki dana Musulunta. Haka danta Huzaifa har kukan dadi ya yi.
Inda gizo yake sakar kuma Mahaifiyata sai ta ce in shirya inzo muje wajen bauta inyi ta hanya-hanya har sai ranta ya baci ta zazzageni sannan in shirya in bita. Hankalinta ya kara tashi don da ta dauka na rungumi addininta ba wasa, yanzu taga na dawo da halina na da. Hamma Huzaifa yayi min wa'azi sosai ya bani tarihin Annabawa ba adadi, na karu sosai nasan abubuwa da yawa wadanda ada duk bincikena ban sansu ba. Daga karshen nasihar da yake min sai yace inji tsoron Allah. Allah Yana ganin duk abunda nake, kada inyi zina, in guji zina, kada in kusanci zina. Ko ina na shiga komai duhun daki Allah Yana kallona, sai in amsa masa da "To zan kiyaye. Hamma Huzaifa ya fito min da komai baro-baro baya kunya, baya boye mun abin addini. Idan na fara jin kunya kamar su wankan haila da janaba sai ya ce kada inji kunya ba'a kunya a wajen koyan ilimin addini.
Hutu ya kare zan koma makaranta, Hamma Huzaifa ya bani carbi da littafin addu'o'i saiya dauko kudi ya bani me yawa. Da farko naki karba ganin ba aiki yake ba, shima a jikin Mahaifinsa yake samu duk da Mahaifinsa mai hali ne. Sai ya ce kada inki alhairi, Musulmi dan uwan Musulmi ne. Kyauta tana kara dankon zumunci. Ya karamun da cewa in zama mai kyauta da son mutane duk da yasan halayena ne. Yayi min nasiha da in rike sallah kada inyi wasa da ita kuma inyi akan lokacinta. Mahaifana sun hadamun duk abunda zan bukata. Zasu sa direba ya kaini nace kawayena su Harriet zasu zo su daukeni a motar gidansu kamar yadda suka shirya min suka ce in fada, amma Micheal ne ya zo ya daukemu muka tafi. Ko makaranta bamu nufa ba gidansa kawai ya ajiyemu. Kowacce ta shigar da kayanta dakinta, muka ci gaba da zamanmu cikin jin dadi. Abunda yake bani mamaki shine yadda Micheal da abokansa suke kashe mana kudi kamar ruwa. A ina suke samun wannan uwar dukiya Oho? Nafi shakuwa da Micheal fiye da sauran, saboda kyautata min din da yake yi. Idan Harriet da Janet basa nan sai yazo ya kawo min kayayyaki kala-kala da damin kudi yace kyauta ya bani. Ban san me zan saya da kudin ba ko kuma wanda zan bawa ajiya. Hankalina ya tashi ince bazan karba ba. Ya ce dole in karba, ya fita ya barni da himilin kudi. Inyi sauri in sami lungu a dakina in boye. Dan ko zan hadiyi laya idan nace ina zamana ya dauko ya bani ba zasu yarda ba, naga shima a boye yake bani karsu sani. A hankali Micheal ya fara fito min da manufarsa, ashe shi sona yake yi yamin bayani ya ce babban makasudin da yasa ya bamu gida muka zauna saboda ni ya bayar kuma duk wannan hidimar da yake mana ya ciyar damu, ya shayar damu, ya saya mana saboda tsananin son da yake min ne. Amma baya so in fadawa su Harriet abunda ke tsakaninmu. Sai kawai naji na fara jin haushinsa saboda bani da ra'ayin soyayya, ban iya ta ba kuma, ban taba yi ba, kuma bana so nayi. Amma kunya dajin nauyin Micheal bai iya cewa bana sonsa ba sai dai kawai in dinga amsa masa sama-sama. Harriet da Janet basu cika yinin gida ba yanzu, da sassafe sai in ga sun shirya mota tazo ta daukesu basa dawowa sai dare. Ni kadaice a gidan sai wasu sababbin kawayenmu Fadila, Ngozi da Elizebeth suke zuwa mu yini muna hira da ciye-ciyen kayan dadi. Suma *yan matan abokan Micheal ne. Micheal koda yaushe yana zuwa ya taya ni hira haka kuma yake ajiyemin damin kudi duk sanda yazo. Na tambayeshi wai ina su Harriet suke tafiya yanzu basa zaman gida. Idan na tambayesu sai su ce in kyalesu tunda idan sun fadamun ba zuwa zanyi ba. Micheal ya ce min ai yanzu a wani sabon Guest house dinsa suke yini ko zanje ya kaini? Na ce "Ba