Showing 57001 words to 60000 words out of 110329 words
Chapter 20 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
can. Tana bani labarin yadda suka saba da balarabiyar, Baban Maman Amina ne ya taba yi musu aikin gadi, waccan shekarar baban ya rasu. Dan haka *yan gidansu kakaf sun saba, kuma har yau har gobe kusan su suke ciyar da gidansu Maman Amina. Kayan abinci buhu-buhu suke kaiwa gidansu, kudin cefane, kwancen kayansu na sawa da zakka. Shi yasa itama duk sanda tazo garin alkawari ne tazo ta gaishesu, duk sanda taje sai taji Balarabiyar tana jajen *yar aiki bata jin dadin yadda basa iya kula da danta. Danta guda daya, ga kuma yadda take ji dashi, shekaru goma da aure sai yanzu suka samu haihuwa.
Na tambayi Maman Amina sun kauro Nigeria kenan baza su koma kasarsu ba? Ta ce mun zaiyi wuya su koma gaba daya suna dadewa ma basu je ganin gida ba. Duk harkar samun kudinsu da kasuwancin su suna nan Kano. Mijin dan kasuwa ne, matar ma ta bubbude super market da Nursiry ana karatu. Dai-dai lokacin Maman Amina ta cewa mai tasi "Nan zamu sauka. Na bude baki ina kallon kerarren gidan da ban taba arangama da irinsa ba a ido biyu. Ta biya shi kudinsa muka dunguma kofar gidan, kafin mai gadi ya bude get sai da ya liko ta windo ransa a bace zaiyi mana wulakanci ko da yaga Maman Amina ya ganeta sai ya washe baki ya ce "Sannunku da zuwa" da sauri ya wangale get muka shiga riki-riki da jakunkuna a hannuna. Muka tsaya suka gaisa da buzun mai gadin sannan muka wuce cikin gidan bayan mun keto ta lambuna da swimming pool ga ruwa yana bulbulowa ta cikin wasu duwatsu suna bawa grass carper ruwa da fulawowi. Abun tamkar a film ba a ido biyu ba. A Nigeria dai ban taba ganin irin ginin nan ba, sai dai a waje lokacin da muka je da Iyayena.
Mun iske balarabiyar matar a katafaren falonta na alfarma tana kallon talabijin tashar Makka ce ana sallar azahar, ta burgeni matuka ganinta sanye da hijabi tana jan carbi a hannunta. Ta amsa sallamarmu, sai ta taso da fara'a da sauri ta tari Maman Amina gami da rungumeta ta sunbaci kumatunta, ina gefe ina kallon sabon salon gaisuwar da ban taba gani ba ina kuma sauraron yaren da ban taba jiba a sarari wato da larabci suke magana. Ban san me suke cewa ba naga Maman Amina tana magana tana nuna ni da alama dai gabatar dani take. Sai naga sun tuntsire da dariya dukkansu, Maman Amina ta juyo inda nake tsugunne ta ce mun "Na mata bayani ta ce kamar kuwa nasan tana tsakiyar neman mai raino. Ta ce kinyi mata dari bisa dari, kinga ko bata nan danta zai ganki kamar ita saboda kema kinyi kama dasu Larabawa, wai kamarku daya anya ke ba balarabiya ba ce? Sai nima nayi dariya, suna Magana Maman Amina tana fassara mun. Matar ta zano dokokin gidan, da abun da zanyi da wanda zan kiyaye. Tana ta maimaita mun in kular mata danta sosai shine burinta. Sannan nawa zata dinga biyana a wata? Nayi caraf na ce "Bana bukatar ko kwabo fata na su rikeni amana kuma su sani a makarantar Islamiyya har in sauke alkur'ani shine burina.
Da Maman Amina ta fada mata abinda nace sai ta bude baki tana mamaki. Tace in matso kusa da ita ta mikamin hannu muka gaisa tana larabci tana shafamun kai, Maman Amina na fassara mun abunda take cewa, bata taba ganin yarinya mai hankali wacce ta rike maraicinta ba irina, nayi tunani mai kyau kudi bai kai ilimi muhimmanci ba. Tayi alkawari zata kaini Makarantar Islamiyyar da take yi, ta *yan kasar su ce larabawa ne ziryan a makarantar. Da yamma ake zuwa Makarantar kullum banda alhamis da juma'a ranar asabar da lahadi ayi da safe. Akwai ajujuwan yara, manya tsofaffi, maza da mata, ana biyan kudi da yawa saboda kwararrun Malamai, tayi alkawari zata biya mun har in sauke kur'ani. Naji dadi sosai nayi ta godiya sai ta fada min sunanta Naila, sunan mijinta Abdul-Samad danta kuwa Abdul-Malik. Ta tambayeni sunana na ce mata sunana Fatima, sai ta rike kai ta ce babban suna ne a wajenta ba zata iya kiran sunan ba. Sunan Mahaifiyarta ne kuma sunan uwar mijinta ne zata dinga kirana da IMAN to daga nan na samo asalin suna Iman.
Anan gidan na zauna tare da Mummy Naila zaman jin dadi da kwanciyar hankali. Idan kuka ga dakina a gidan tamkar dakin *yar shugaban kasa da ban dakina a ciki. Na saba da danta Abdul-Malik shima ya saba dani har yakan ki zuwa wajen Mahaifiyarsa da Mahaifinsa sai ni kawai. Aikina shi ne kula da Abdul-Malik kawai dan haka na zage ba rana ba dare ina kula da shi matuka ko Mahaifiyarsa sai haka. Shekarunsa biyu kacal a lokacin amma dakinsa daban shima an zuba masa kayan wasan yara kala-kala ba ya iya rabuwa dani, ko Mahaifiyarsa ta ce in kai shi dakinsa ya kwanta to fa da tsakar dare zan tashi in je in dauko shi dakina mu kwana tare ko ni in kwanta a dakinsa. Na kan rungumeshi inyi kuka idan na tuna da dan Jaririna. Haka idan ina masa wanka ko shirya shi, ko ina masa wasa sai dan Harriet ya fado min ina tunanin halin da yake ciki yanzu, inji dama ace shine Abdul-Malik muke tare haka cikin jin dadi, wadata da kulawa mai yawa.
Kamar yadda na cika mata alkawari da na dauka na kula da danta, itama ta cika min alkawari ta saka ni a makaranta mai dunbin kwararrun Malamai. A kaimu a mota a dauko mu a mota duk ranar da baza ta samu damar zuwa ba ni da Abdul-Malik ake kaiwa direba ya jira har a tashe mu. An bude ajin kananan yara kamar *yan shekara biyu zuwa hudu anan ajin aka saka Abdul-Malik shima, tun yana kuka ina lallashinsa har ya saba. Ina jin dadin rayuwata sosai amma Mummy Naila ta fini jin dadi, bata da fargabar bar mun danta ko ina zata je. Tana matukar sona da kula dani, babu abunda na rasa, babu wani abu ko wani daki da tayimun katangar shigarsa, komai nake so zanci, ko ina zan shiga a gidan. Ta yarda da gaskiyata. A kwai kuku mai dafa abinci akwai Liliyan me share-share da goge-goge, a kawai Lantana mai wanke-wanke. Isa mai yanke fulawa. Isyaku da Kasim masu wanki da guga, ga masu gadi da masu sharar farfajiyar gidan ba adadi. Dukkansu girma suke bani, rissina mun suke suna kirana da Madam nima, dan su a tinaninsu jinin masu gidance banyi musu kama da *yar aiki ba. Na kara yin fari kal, nayi kiba, nayi fes na samu gyara ga sutura kala-kala, duk da ma nayi kwalliyar zurmikeken hijab nake sawa.
Mummy Naila tana dan jin Turanci amma mijinta yana magana da turanci sosai ta haka muke magana. Amma na dage saina koyi Larabci dan haka nake kin yin magana da turanci, nake kwaba larabci. Ita kuma tana rokona in dinga yiwa danta turanci tana so ya koya kafin ya shiga makarantar boko. Na samu shekara guda a gidan larabawan nan cikin ikon Allah larabci ya zauna a bakina saboda a gida larabci, makaranta daman kakaf larabawa ne komai da larabci ake yi don haka siffata, shigata da maganata duk ta larabawa ce. Haka a shekarar na sauke Alkur'ani mai girma, na haddace Hadisai masu yawa, nasan Tauhid da Fikihu. To kunji inda naji yaren Larabci na kuma iya karatun Alkur'ani.
Iman tayi hawaye tasa gefen hijabinta ta goge. Su Suhaif sun zuba mata ido suna jin wannan labari mai dinbin al'ajabi kamar almara. Iman taci gaba da cewa "Sai kuma yanzu za kuji dalilin barina gidan. Gidan da ake min gata, ake kaunata tamkar jinin jikinsu.
Ta ce "Babu wani mugun hali da suka yimin har nabar gidan, haka nima har muka rabu babu ha'inci ko zamba ko cin amana dana yi musu, illa mugayen matsafan da suke jikina suka rabamu. Tun sanda na kama addinina haikan ba dare ba rana bautar Allah karatun Alkur'ani ya shiga bakina sai kuma na shiga tashin hankali, rayuwata ta shiga barazana. Kullum na kwanta barci sai in ga wadancan matsafan a mafarki kuma kamar ido biyu. Suna kirana kuma suna lallabata, suna bani shawara in fita daga addinnin da nake. Sabida addinin akwai addu'a mai zafi da nake damunsu da ita suna nisanta daga gareni, su kuwa a kullum suna tare dani dan suna sona, zasu bani arzikin da zanfi kowa. Inyi farat in tashi a firgice amma da addu'ata fal baki. Da naga haka sai na shiga bin Malaman makarantarmu daban-daban suna bani addu'o'in tsari daga sharrin mugaye. Na kuma bazama neman litattafan addu'oi iri-iri sune abokan hirata.
Haka kuma nake ganina a mafarki inata kona su da Ayar Allah, don haka na fara fin karfinsu. Matsafan ma suka bazama neman abun tsafin da zasu tsafeni suci galaba a kaina, suna kai kukansu kasa-kasa, gari-gari wajen manyansu suce wai yarinya karama ta gagaresu shakara da shekaru.
Da Allah Ya kaddara za suci galaba a kaina daga baya sai na zama yin addu'ar yana min wuya. Musamman da daddare sai in kasa addu'a in zan kwanta bacci. Wata rana cikin mafarki sai naga matsafan sun daukoni suna murna, suna tsalle suna waka. Suna magana da duk yaren da nake ji, suka daure ni a jikin wata bishiya, suna waka suna zagayeni. Ina ta zullo ina so in kwace daurin da suka yimin na kasa kwacewa, sun kuma dauremin bakina na kasa ihu balle addu'a. Babu abin da zan iya hanga a wajen sai dokar daji da *yan bukkoki, sai itatuwa waje-waje an kunna wuta, suna rike da wasu itatuwan a hannayensu suma a kunne da wuta. Matansu da Mazansu, yara kanana da manyan dukkansu babu sutura ajikinsu. Gajerun wanduna mazan suka saka sai jajayen kyallaye a daure a kansu da dukkannin gabobin hannayensu da kafafuwansu. Haka suma matan banbancinsu da mazan karamin siket ne maimakon gajeran wando sai dan siririn jan kyalle da suka daura suka rufe kirjinsu. Sunyi zane-zane da farin fanti a goshinsu da cikinsu, kayan tsafi kuwa gasu nan birjik ko ina jifgi guda a gabansu, kamar su kan dabbobin gida daban-daban da na daji, kan kunkuru, kan macizai da kokon kan mutane. Abun mamaki naga wasu mutanen da na sani a cikinsu, naga wannan senior data fara sakani cikin ukuba naga da yawa daga cikin *yan makarantarmu na sakandire harda wani babban mutum makocinmu ne mai suna Mr Izera.. Babban abin tausayi harda yara *yan furamari.
Babbansu ya fito suka matsa masa suka bashi hanya yazo gabana, da sauri suka dauko masa abun zaman ya zauna, ya dube ni ya tuntsire da dariya mai karfi da firgitarwa ya ce "Rufkatu! Rufkatu!! Rufkatu!!! Yau gaki a hannunmu amma duk da haka kinfi karfinmu ko yanzu muka bude miki baki zaki karanto addu'ar da zata kona mu. Kinyi nisa mun kasa rinjayarki cikinmu, kuma mun so mu halakar da ke mun kasa saboda karfin addu'arki, da wacce dan Makwabtanku yake yi miki da Mahaifinki. Amma yanzu ladan wahalar da kika bamu zamu zamar dake abar tsana, abar gudu, abar cutarwa a cikin *yan uwanki Musulmai. Yanzu ma zamu gwada miki abunda muke nufi. Sai naga sun dauko wani yaro. Ina duban fuskar yaron sai naga Abdul-Malik dan rainona. Hankalina ya tashi ina ta fisge-fisge ina so na balle na kasa. Suna dariya irin ta mugunta suka bankare yaron sun shake shi zasu kashe shi yana ta tsala kuka. Cikin ikon Allah na daka tsalle da karfi sai na kwance daurin da suka yi min na fusge kyallan da suka rufe min bakina, na dinga karanto addu'o'i, suka fara ja da baya naje da gudu na dauke Abdul-Malik na zura da gudu cikin daji. Sai suka biyoni da gudu. Muna ta gudu ba tsagaitawa, dai-dai nan nayi firgigit na farka daga barci ina ta shesheka kamar da gaske nayi gudun. Jikina gaba daya ya min nauyi yana ciwo zuciyata tana ta bugun uku-uku. Hankalina a tashe, na firgita kwarai da gaske, don ban taba mafarki irin wannan ba. Na gyara fulo na jingina ina mai matukar damuwa da tashin hankali, na fara hawaye ina tunanin yadda rayuwata zata kasance nan gaba. Gashi yadda nake jin yanayin jikina duk sanda zanyi addu'a sai na kasa, nasan dole sun fara samun galaba a kaina. Na tuna irin wahalar da nasha a lokacin da nake Bauchi duk da dai wadanda na farfasawa kai *yan iskane masu san aikata masha'a dani. Nayi sauri na jawo Abdul-Malik da yake kwance a gefena na dube shi, na firgita na mike da gudu yayin dana ga numfashinsa na harbawa sama-sama, jini yana zuba ta hancin sa. "Ina zaki je ne? Kije ki dauke shi a kai shi asibiti, waye yasan abunda kika gani a mafarki? Zuciyata ta fadamin haka.
ALLAH YA KAREMU DAGA SHARRIN MAKIYANMU AMEEN
INA MUKU FATAN ALKHAIRI
Reedwan Suraj Isma'il
*************** YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI
Karkarwa nake tamkar a lokacin hunturu, har hakorana na sama da kasa suna hadewa. Numfashina yana sama yana kasa, kai kace hakar rijiya nake yi. Ina sanda na zo inda Abdul-Malik yake kwance. Na dauke shi da kyar na fito na nufi dakin Mahaifiyarsa ina kuka ina kwankwasa musu kofa. Ta tashi da sauri ta bude kofar gabanta na faduwa, tana ganina tasan ba lafiya. Karar sautin da take tambayata ya firgita mijinta ya fito da sauri shima. Na kasa bayani saina mika mata yaron ko da suka ga jini sai suka rude tana kuka mijinta kuwa ya hau karkarwa, suna sake tambayata meya same shi? Na daure na bude baki nayi musu bayani cewar nima naji yana ta nishi sama-sama dana kunna fitila sai na ganshi cikin wannan hali. Aka tashi direba muka shiga motar har dani muka dunguma asibiti, duk da tsakar dare ne misalin karfe uku na dare likitoci suka dukufa aikinsu na ceto ran yaron da kuma gano mahassadin ciwon. Hankalin Mahaifansa ya fara kwanciya ganin likitoci suna aikinsu, kuma sun yarda da aikin likitocin saboda kwarewarsu, amma ni kuwa hankalina yaki kwanciya, kuka nake naki tsagaitawa. Mummy Naila ta dawo ita take lallashina inyi hakuri in daina kuka zai sami sauki da ikon Allah.
Abu kamar wasa Abdul-Malik ya kwana biyu bai farfado ba ana ta kara masa ruwa. Hankalin kowa ya tashi har likitocin don sunyi iya kokarinsu sun kasa gano irin wannan cutar, kuma da wuya ace sun yiwa mara lafiya irin wannan taimakon bai sami sauki ba. Mahaifinsa ya fara shawarar su fita da shi asibitin kasar waje. Na san duk abunda yake faruwa na kasa fada, duk sanda na kwanta bacci zanga matsafan sun bishi asibiti suna jagula aikin da likitocin suke yi suna sake shake shi yadda jikin zai rikice. Suka shaida mun cewar bayan sun gama wahalar da shi sannan su kashe shi ba kuma mutuwa salin alin ba yana kwance, a'a a hannuna zai mutu yadda za'a kamani ace ni na kashe shi. Suna nan suna biye da ni zasu min sharrin da kowa zai tsaneni karshen rayuwata ta kare a gidan yari. Da naji haka hankalina ya tashi sosai nayi kuka har na gaji daga karshe na yanke shawarar gara na bar gidan nan saboda in ceto rayuwar Abdul-Malik. Ina son Abdul-Malik yana sona, haka Mahaifansa ma suke sona. Sun nuna min gata, sun rikeni tsakani da Allah dole ce tasa na bar gidan duk da nasan jin dadi da gata ya kare kuma ban san inda zan dosa ba. Na rubuta wasika cikin harshen Larabci na ajiyewa Mummy Naila akan gadonta lokacin tana asibiti wajan danta, ni kuma na dawo gida zan kai abinci. Da farko nayi mata godiya bisa taimakon da tayi min da kauna da take min tsakani da Allah, na mata addu'a Allah Ya kara mata budi da arziki da wadata Ya kuma karbi addu'arsu ta samun haihuwar *ya*ya da yawa masu albarka, kuma kyawawan halayansu da son taimakawa marayu da talakawa ya bisu har kabarinsu, san nan nace ina mai matukar damuwa dare da rana safe da yamma akan halinda da Abdul-Malik yake ciki, ina yi masa fatan Allah Ya bashi lafiya. Shawarar da nake baku shine ku dauke Abdul-Malik daga asibiti kuma kar kuyi wahalar kaishi kasar waje ciwon Abdul-Malik bana asibiti bane. Ku komo gida ku dukufa ku dinga yi masa addu'a ba dare ba rana, kuma ku hado manyan Malamai ayi ta sauke muku Alkur'ani a tofe kowacce kusurwa a gidanku kada kuyi sakaci, kada kuki daukar shawarata, ina son Abdul-Malik bana son ya hallaka. Nayi alkawari zan zamo mai yi masa addu'a a duk inda nake, kuma ba zan ci gaba da zama a nan gidan ina ganin halin wuya da Abdul-Malik yake ciki ba. Na yi kuka na gaji sannan naje na ajiye wasikar a tsakiyar gadonta a bude yadda zata gani da zarar ta shigo dakin. Ina da suturu na gani na fada kala-kala akwati akwati, riguna da siket kala-kala, riga da wandunan jeans, jallabiyoyi bakake na Larabawa tsala-tsala ba adadi, leshina da atamfofi manya-manya babu kanana mai arha. Takalma da jakunkuna, kayan kwalliya kamar su jan baki da hoda a cike a gaban madubi, wasu kuma jifge a akwati. Babu abinda na dauka sai dogayen riguna guda uku da atamfofi kala biyu. Kudin da ke jakata basu da yawa, na fito na bar gidan. Tafiya nake da sauri fatana na bar unguwar don kar in hadu da idon sani. Kutsawa nake cikin unguwanni ba tare da nasan inda zan nufa ba. Motoci na alfarma suke tsayawa suna rokata wai na shigo su kaini inda zanje, sai naki shiga. Pure water kawai nake tsayawa in saya in sha sai in kara gaba. Dana gaji da tafiya sai na hau bus da naga kowa ya shiga ana cewa "Bata-Bata. Muka isa Bata kowa ya fito daga mota ya nufi inda zaije, ni kuwa na fito, na sake ganin bus ana lodin Dawanau sai na shiga muka isa Dawanau can ma banga wajen zama ba ga dare yayi. In takaice muku a rumfar kasuwa na kwana. *yan iskan maza kala-kala suka yi ta lallabani za su cuce ni, naki yarda dasu ina ta addu'a