Showing 69001 words to 72000 words out of 110329 words
Chapter 24 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
Mama dukkansu zuna zazzaune a babban falo. Bayan sun gaggaisa suka tambayi lafiyar mutanen Doko. Sannan Baba ya sanarwa da su Zubaida cewar sun sami admission kuma ya aika Gemany a shigo musu da motocinsu, suka yi ta murna suna godiya. Ya juya ya dubi Najib ya ce "Najib kai kuma wata mai zuwa za ka je Jos yin interview, Suhaif kuwa sati mai zuwa zaka je Lagos domin tantanceku. Alhamdulillahi abun alheri ya samu lokaci guda, ina rokon ku dan Allah masu karatu ku rike karatunku ku mayar da hankalinku ku ci jarabawa, ku gama karatunku akan lokaci. San nan ku kuma da Allah Yasa ku ka gama karatun lafiya, Allah yasa ku ka sami aiki kuyi kokari ku rike aikinku, har Allah Yasa kuyi iyali ku rikesu. Mama ma ta ce "Gaskiya ku godewa Allah Ya kara budawa Mahaifinku, ya sassaya muku motoci, ya yi kokari ya samar muku aiki, matan kuma ya taimaka kun sami admission a Jami'a duk lokaci daya.
Suhaif ya gyara zama ya ce "Haka ne, mun godewa Allah kuma mun gode muku, ku Iyayenmu da ku ka bamu ilimi. Kuma Insha Allah zamu rike aikinmu, ku kuma *yan makaranta ku san abin da ya kai ku jami'a, karatu ne ya kai ku ba zance da samari ba. Najib ya karba ya ce "Ku sani a jami'a zaku hadu da jama'a kala-kala kowa da dabi'ar gidansu, da al'adar yarensu don haka ku kiyaye ku san irin kawayen da zaku yi, ku guji mayaudaran samari, *yan matan suna amsawa da to. Bayan Suhaif ya koma dakinsa sai ya nemi bacci ya rasa ya shiga tunanin inda zaiga Iman shine matsalarsa, yayi tunani da kwakwalwarsa iya kokarinsa ya tankade ya bakace yaga kawai ba zai iya zuwa wajen aiki ba, domin rayuwarsa gaba daya ta sukurkuce saboda rashin Iman, babu aikin da zai iya a rayuwarsa. To amma ta ina zai kubce, ya ya zaiyi, wacce hujja zai bawa Baba akan ya rabu da shi ba aiki?
Ana gobe ranar da za'a tantance su Suhaif a Lagos, tun da daddare Baba ya bawa Suhaif kudin Jirgin da zai tafi Lagos ya ce ya shirya da sassafe a kaishi filin Jirgi ya tafi. Ran Suhaif bai so ba amma ya rasa ta inda zai fara yiwa Baba bayani. Ya kwana yana juyi yana tunani, yaji a ransa ba zai iya lulukawa ya tafi har Lagos ba, ba tare da yaje neman Iman ba don haka ya yanke hukuncin da yaga ya dace da rayuwarsa. Kudin Jirgin da Baba na Kano ya bashi na zuwa Lagos da sauran kudaden ya hada ya daure a cikin jakar kayansa daya shirya tafiya Jalingo neman Iman ba wajen aikin zai jeba. Ya rubuta wasika ya ajewa Najib a kan gadonsa yayin da yake ta shakar bacci da sassafe misalin karfe bakwai. Al'adar gidan ce bayan sallar asuba sai a koma bacci, sai dai idan akwai mai uziri ya tashi ya shirya ya yiwa masu aikin abinci magana suyi masa nasa kalacin ya ci ya tafi, sauran kuwa sai sanda yunwa ta addabesu za kaga suna fitowa daya bayan daya.
Daman Suhaif tun asuba yayi wanka ya shirya daya tabbatar kowa ya koma bacci haikan sai ya kinkimo jakar kayansa ya je ya saka a motarsa ya tashi mai gadi a hankali ya bude masa get in zai fita. Ya shiga mota ya na sanda ya kunna, ba tare da ya bata wuta ba, ya sulale ya fita don kar Baba yaji fitarsa. Misalin karfe goma sha daya Baba ya fito yana tambayar mai gadi "Ina Suhaif ya ce zai je ne tun karfe bakwai saura? Ashe ya ga fitarsa ta wundan dakinsa. Mai gadi ya ce "Bai fadamin inda zaije ba amma na ganshi da jakar kaya. "Jakar kaya, ina zaije da jakar kaya ba dai Lagos din zai tafi a mota ba, bayan na bashi kudin jirgi? Baba ya fada yayin da mamaki ya kamashi, Baba ya juya ya nufi gida da sauri ya shiga dakin su Najib shi ai zai san inda Suhaif din ya tafi, tunda bakinsu daya. Najib yayi dai-dai akan gadonsa yana shakar bacci bai san ma inda yake ba, sai da Baba yayi ta dukan hannunsa sanna ya farka. "Ina Suhaif? Baba ya tambayeshi. "Gashi can a gadonsa yana bacci. Najib ya fada cikin magagin bacci. Baba ya ce "Kai bude idonka. Ina Suhaif din yake? Ba ga gadon nasa babu kowa akai ba. Sai Najib ya tashi ya zauna yana murtsike ido yana soshe-soshe ya ce "To ban san inda ya tafi ba. Baba ya fusata ya fara fada yana cewa "Na fara gajiya da irin wannan rashin jin naku, kamar wasu kanana. To idan baku gyara halin nan naku ba zan cire hannuna akan ku kowannenku yaje ya nemo aikinsa. Yanzu yanzun nan daga Lagos aka yi min waya yau ake neman su Suhaif, tun jiya ya kamata yaje ya kwana acan yau litinin za'a tantancesu amma ya shiga mota ya tafi yawonsa kawai. Najib ya yunkura zai tashi sai yaji ya dafa wata takarda a gefensa, ya dauko ya bude yana karantawa sai mamaki ya kamashi gami da fargaba. Baba ya dube shi ya ce "Me aka rubuta? Najib yayi shiru can ya ce "Suhaif ne ya bar wasika ya ce ace maka ba zai iya aiki ba saboda tsananin damuwar da take damunsa ko ya fara aikin ma zasu gaji su kore shi. Don haka ya je nemo maganin damuwarsa shine ya tafi garin su Iman nemanta. Yadda ku kasan ruwan zafi ake watsa masa haka Baba yake jin labarin da Najib yake bashi. Sai ya hau balokoko yana fada, ya fito daga dakin ya nufi dakin matarsa itama ya hada da ita cewa yake laifin ta ne, ita ta sakarwa yaran suke abunda suka ga dama. Naja'at da Zubaida suma suka fito Mama ta kasa bawa mijinta hakuri saboda ransa yayi matukar baci. Suhaif dai ya kama hanya sai tafiya yake haikan ya tafi neman abar kaunarsa, ya bar *yan gida da shan fada ko ruwan shayi ya gagaresu kurba a safiyar yau, yau dai laifin wani ya shafi wani.
Suhaif ya isa Jalingo da magaruba, baiyi wata-wata ba ya zabi hotel din da yake so ya biya aka bashi daki, bayan anyi masa odar abinci yaci yasha, sanna yayi sallah yayi wanka ya kwanta amma tunani da murna sun hanashi bacci. Murnar ita ce yau gashi a garin su Iman dan haka yana da 50% din tabbacin ganinta. Tunanin kuwa shine ta ina zai fara nemanta? Gari kamar Jalingo ace an zo neman mutumin da ba'a san inda yake ba. Shi ba attajiri ba, ba dan siyasa ba wanda da zarar an fadi sunansa kowa ya sanshi. Allah gani gareKa. Suhaif ya fada lokacin da yake ta juyi akan gado.
Washe gari da sassafe Suhaif ya shirya ya fito neman abunda ya zo nema, da farko cewa yayi a nuna masa G.R.A. An kaishi G.R.A sunfi a kirga amma Allah baisa ya ci sa'ar ganin gidan su Iman ba. Ya yi kwatancenta, ya nuna hotonta, ya fadi sunayenta da ake kiranta dasu kakaf amma bai sami wanda ya santa ba. Har dare ya yi sanna ya koma dakinsa na Hotel ya kwanta, cike da bakin ciki. Haka washe gari ma da sassafe ya fita, amma yau wajen bauta ya nema ya dinga zazzagawa yana fadar sunan Mahaifiyarta da Mahaifinta basu sansu ba. Washe gari kuma ya nemi asibitoci yana tambayar Dr. Hani ko Allah zaisa yaga Dr. Hani ko a lokacin daya zukewa yaron Iman abu daga hancinsa ya rubuta adreshinta, bai samu inda Dr. Hani yake ba, anan ma har dare. Washe gari kuma kauyukan Mumuyawa ya yini, anan ne kuwa yafi shan wuyar banza. Ba sa jin yarensa, baya jin nasu, basu fahimci kalma daya ba daga cikin abubawan da yake tambayarsu. Sai suka zamar dashi a bin kallo, wasu kuwa ganin ya tunkaro su a mota sai su zura da gudu. Dole ya hakura ya dawo dakinsa na Hotel cike da takaici da dacin bakin ciki. Bai hakura ba sai ya shirya washegari ya nufi kasuwanni ko Allah zaisa yaga Iman, nan ma ya yini yana kallon masu saye da sayarwa babu Iman babu mai kamarta.
Ranar da ya cika sati guda a Jalingo ya saduda ya hakura ya hada kayansa a jakarsa ya biya masu Hotel ya fito ya nufi hanyar Kano. Hawaye sharaf-sharafa fuskarsa saboda bacin rai gashi a garin su Iman amma ya rasa inda take.
Ya iso Kano da misalin karfe shidda na yamma saboda irin gudun da yake zurawa don bacin rai, bai damu da ko motar zata fadi ba, ko yayi karo da wasu motocin, ya fitar da rai da son ci gaba da rayuwar duniya. Mai gadi yana bude masa get ya kutsa ya shigo cikin gida a fusace. Yaga *yan gida kakaf har da *yan Doko suna zazzaune a farfajiyar gidan, daga dukkan alamu tafiyarsa ta tayar musu da hankali, da rashin dawowarsa kwana da kwanaki. Ya je inda ake ajiye motoci yayi parkin ya dauko jakar kayansa ya rataya ya nufo inda suke ransa a bace yake kamar yadda yaga rayukan iyayensa a bace har da masu wurgo masa harara.
Ya karaso inda suke ya duka ya gaishesu, babu wanda ya amsa masa, sai Naja'at da Zubaida ne suka yi masa sannu da zuwa Najib ma dauke kai yayi baya ma kallon inda yake. Shima sai ya share, zai wuce cikin gida, Mahaifinsa Baba na Doko ya daka masa tsawa ya ce "Kai sha-sha-sha ina zaka je ne? Da wo nan kayi mana bayanin daga ina kake, suhaif ya dawo ya tsaya yayi shiru bai ce komai ba. Baba na Kano ya ce da Suhaif "Zo nan gabana, Suhaif ya zo ya durkusa, suka fara masa fada su duka hudun wato har da Goggo da Mama, har ma baya gane abun da suke fada domin carin yayi masa yawa. Naja'at da Zubaida suka tashi suka shiga gida suka labe, saboda kada a gama masa fada ya huce a kansu, gannin wata uwar harara da yake jeho musu. Najib ma yake tsoma baki a fadan. Suhaif ya zabura ya ce "Dalla Malam ka rufe mana baki ka bar wadanda suka isa suyi min fadan ba kai ba, Najib ya ce "Ai gaskiya ake fada maka, gashi nan akan Iman ka rasa aikinka, wata kilama baka ganta ba.
Baba na Kano ya ce "Ni dai ka kunyata ni, abokina ne manajan na rokeshi arziki ya daukeka aiki, ya kukuta ya soka ka amma shine ka gudu a ranar da ake nemanku. Baba na Doko ya ce da Suhaif "To kar ka shiga cikin gidan nan ka koma inda ka fito kaje can ta baka aikin tunda ka rasa wancan aikin da aka sha wuyar nemar maka, babu gidan wanda zaka je ka kwanta ana ciyar da kai. Suhaif ya ce "Kuyi hakuri dan Allah, nasan nayi laifi ku yafe min, Baba na Doko ya ce "Babu zancen hakuri wallahi sai kabar gidan nan yau, kuma kar ka je Doko, Suhaif ya mike ya saba jakarsa ya nufi wajen motarsa ya shiga.
Uhmmm to jama'a Angon Matawata ya gaji da daddanna hannunsa.
Sai na ce muku sai Allah Ya kaimu Monday, gobe da jibi kunsan "Weekend ne,,, ina tare da Matawata da Amaryata Zulaihatu... Lollxxxx.
Reedwan Suraj Isma'il
::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI
Da alama wannan hukunci da Baba na Doko ya yanke akan Suhaif bai yiwa kowa dadi ba musamman Mahaifiyar Suhaif, sai ta fashe da kuka tana cewa "Idan bai zauna a nan ba, bai je Doko ba ina zai je? Baba na Doko ya ce "Ina ruwana ya koma garinsu Iman. Baba na Kano ya yunkura zaije ya tsayar da Suhaif kada ya tafi Baba na Doko ya jawo shi ya ce ya koma ya zauna tunda ya rantse sai Suhaif ya tafi. Mama da Najib suka dinga rokar Baba na Doko yayi hakuri yabar Suhaif tunda yayi nadama ya ce yayi kuskure a hakura. Baba na Doko ya ce "Da gangan yayi, yayi tafiyarsa, dadi ne yayi masa yawa yana daga kwance ake ciyar da shi shiyasa bai san zafin nema ba, amma idan ya je yasha wuyar nema, gobe idan an samar masa aiki ba zai yi masa rikon sakainar kashi ba. Suhaif ya ja motarsa ya fice ba tare da yasan inda zai tafi ba. Bakin ciki goma da ashirin, yana ta yawo a gari daga wannan titi zuwa wancan, har karfe tara da rabi na dare sannan ya tuna da wani abokinsa Rabi'u wanda suka gama makaranta tare yanzu yana lecturing a B.U.K, yana zaune ne a staff qauters na B.U.K. Suhaif ya nufi gidan Rabi'u ta ci sa'a kuwa ya same shi daman bai yi aure ba, kai tsaye ya shiga gidan. Rabi'u ya yi murna da ganin Suhaif musamman da ya ce masa kwana ya zo taya shi. Sun dade suna hira sannan suka gangaro hirar dalilin daya kawo shi, Suhaif ya zaiyana masa labari kakaf. Rabi'u yayi masa fadan bai kyauta ba, dan me zai bar aikinsa ya tafi dole hankalinsa ya tashi. "Yanzu meye abun yi? Rabi'u ya tambaye shi. Suhaif ya ce "Bazan koma gidanmu ba saina sami aiki saboda haka gobe da sassafe zan bar garin nan duk inda aiki yake zanje in samu. Rabi'u ya bawa Suhaif shawara ya zo suje gidan gobe ya taya shi bawa Iyayensa hakuri tunda suna da hanya zasu iya samar masa wani aikin. Suhaif ya cewa Rabi'u ya manta da zancen bawa Iyayensa hakuri, domin ba zasu sauraresu ba, shi dai zai kara gaba neman aiki. Daga karshe Rabi'u ya bawa Suhaif shawarar yaje Lagos wajen abokin Baba wato M.D na port Authority ya duba yaga ko akwai yadda za'ayi a saka sunansa a cikin wadanda su kayi interview saboda akwai sanayya zai taimaka. Suhaif ya yarda da shawarar Rabi'u, ya yarda goben zai shirya ya tafi Lagos.
Washe gari da sassafe Suhaif ya shirya, bayan sun karya kumallo sai ya yiwa Rabi'u sallama, Rabi'u yayi masa fatan alheri da fatan Allah Ya kiyaye hanya. Suhaif ya kama hanyar Lagos tafiya yake ba ji ba gani, ya isa cikin dare sai ya wuce ma'aikatar N.P.A. A cikin motarsa ya kwana, da gari ya waye ya shiga Masallacin kusa da nan yayi sallah, da ma'aikata suka fara zuwa wajen aiki sannan yayi kokari aka yi masa iso wajen Manaja. Duk da sanin da Manaja ya yiwa Suhaif sai da ya sake tambayarsa "Daga ina? Suhaif ya gyara zama ya yi masa bayani. Manaja ya bata rai ya ce "Na gane ka ai, meke tafe da kai? Ai kasan mun gama tace wadanda zamu dauka ko? Infact na kira Babanka several times cewar ya ban ganka ba, tun yana boye mun har ya fada mun gaskiya cewar an rasa inda ka tafi baka son aiki.
Suhaif ya hau soshe-soshe ya ce "Ranka ya dade nasan nayi kuskure, and I realize my mistake, am sorry ran Iyayena ya baci har sun ce in bar musu gida. Sun ce in je in nemo aiki da kaina, dan Allah a taimaka min ranka ya dade. Manager ya yi sauri ya ce "Actually nayi iya kokarina in baka aiki kaine kaki, yanzu ba yadda zanyi maka kayi hakuri. Suhaif ya rike kai ya yi shiru. Manager ya ci gaba da cewa "Naga alama a gajiye kake bari in sa direbana ya kaika gidana ka huta. Suhaif ya ce "Na gode Baba kamar kasan a gajiye nake na yini na kusa kwana ina tafiya.
Bayan Suhaif da direba sun tafi gida, Manager ya kira Baba na Kano yake shaida masa ga Suhaif ya zo, ya zaiyana masa duk yadda su kayi aiki dai babu sun gama dauka. Baba na Kano ya roki Manager ya taimaka ya ajiye Suhaif a gidansa tun da akwai wajen ajiye baki ko Allah zai jeho wani aikin daga wani bangaren. Manager yana ganin mutuncin Baba na Kano ba zai iya kin yi masa duk abunda ya tambayeshi ba, ya amsa da "Ba damuwa za a binciko Insha-Allah ko a wani bangaren ne.
Suhaif yana zaune a gidan Manager har na tsawon wata biyu babu abinda yake yi sai kwanciya, babu aiki babu alamarsa. Sai dai Suhaif yana taimakawa Manager akan harkokinsa, yana aikensa wurare kuma yaje ya aiwatar masa da duk abunda yasa shi babu kuskure. Idan harkar kudi ne kuwa babu munafunci, ko kwabo ba zai dauka ba. Da gangan Manager yake hana Suhaif kudin kashewa kuma yasan bashi da kudi, yana son gwada hankalinsa ko zaice duk wannan wahalar da nake yi masa bai biyani ba, ko kuwa zai rinka rage kudin da yake aikensa. Sai yaga Suhaif ba haka yake ba kuma bai damu ba. Dan haka Manager ya cure Suhaif ya kudiri niyyar nemar masa aiki ko a wane waje ne. Amma a hirar da suke da Suhaif ya bugi cikinsa yaji ra'ayinsa game da aiki. Suhaif ya nuna baya son aiki kwata-kwata saboda a fadarsa yana da matsalar da ta dami zuciyarsa baya so ya fara aiki ya je ya zauna a office yana tunani ya kasa aikin yadda ya kamata. Da dai zai sami jari yayi business ko kwangila da yafi so. Duk da Manager bai gane damuwar da Suhaif yake ciki ba amma ya kudira a ransa zai yiwa Suhaif yadda yake so. Zai bashi kwangila da kuma kudin da zai yi kwangilar tunda bashi dasu.
Suhaif na zaune a bangaren da aka sauke shi a gidan Manager, shi kadai yana tunanin abar kaunarsa kamar yadda ya saba wato Iman. Ya ji wayar dake ajiye a gefen gadonsa tayi ruri ya dauka da sauri. Manager ne yake magana ya ce da Suhaif ya zo office ya same shi. Suhaif bai bata lokaci mai yawa ba ya je ya sameshi a office. Manager ya mika masa takardun wata kwangila mai tsoka ya ce "Ga wannan taka ce. Suhaif ya hau dogon tunani "Ni da bani da ko sisi ya zanyi in yi kwangilar miliyoyi? Manager ya bashi amsar tunaninsa "Mu zamu ranta maka kudi kayi, sannan mu biya ka akan lokaci "Tsarki ya tabbata ga Allah