Showing 6001 words to 9000 words out of 110329 words

Chapter 3 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt

22 Feb 2025

7459

da shi na aikin gida ta sanya wata yaloluwar riga fara (tea shirt) ta daura dankwali ta fito tsakar gida don fara aikin gida. Tsakar gida kaca-kaca saboda sunsha hirar dare anci gyada ansha rake duk an zubar a tsakar gida. Kwanukan da aka cicci tuwo ne a watse a tsakar gida. Wasu a kicin, wasu kuma an kaisu wajen wanke-wanke kusa da rijiya. Iman sarki tsafta, ta tsaya kawai tana kallon tsakar gidan saboda mamaki da takaicin daya dameta a zuciya tana fadin "Daman haka muka yi da tsakar gidan nan jiya da daddare a duhu ban share ba, yanzu a dattin nan muka kwana? Ga babban abun kunya a haka Baba ya fito yaga tsakar gidan nan, zaice bamu da amfani a gidan. Tama rasa ta ina zata fara, wanke-wanken zata fara ko shara? Sai ta tsayar da shawarar ta hada kayan wanke-wanke ta fara share tsakar gida da kicin. Haka kuwa tayi ta share gidan ral a binka da Siminti ya fita yayi tas ko tsinke bata bari ba ta tattara ta kwashe. Sannan ta dauko kujera da omo bayan ta jawo ruwa a rijiya ta zauna ta fara wanke kwanukan da suka bushe da tuwo miyar kuka.
Suhaif ne ya dawo daga rakiyar mahaifinsa, ya rakashi har bakin titi ya hau mota sannan ya dawo gida. Yana sako kai cikkin gidan saiya ga Iman a zaune tana wanke-wanke kanta a sunkuye a kasa bata ganshi ba, kuma karan kwanukan da take wankewa basu barta taji motsin shigowarsa ba. Ya tabbata Iman bata zaci zai shigo a dai-dai wannan lokacin ba kuma bata zaci yana kallonta ba data ruga daki ta saki hijabinta. Ba zata zauna da damammiyar rigar nan a gabansa ba, saboda bata bude ko wutsiyar gashinta a gaban wani namiji. Iman ta san addininta, tasan darajar ta *ya mace gata da kunya.
Daya tabbatar bata ganshi ba sai bai bari ta ganshi ba yaja da baya a hankali ya koma. Wani dan karamin wundo ya tsaya yana lekenta domin yana kokonto ko ba ita ba ce bama. Saboda shi har yanzu baima kare mata kallo ba balle ya santa sosai, tsakaninsa da ita ya ganta a lullube cikin hijabi ta durkusar da kai ta gaishe shi, wani lokaci ma fuskarta a rufe da nikaf kafarta da safa. Yasan fara ce amma bai dauka tas-tas kamar haka ba. Ya kurawa fuskarta ido yana kallon hancin dodar, ga wani lumshasshen ido mai dauke da far tas da bakar kwayar ido dara-dara. Gashin girarta mau taushi a kwance dodar bakinkirin. Bakinta karami dai dai ita ga lobawar kumatu ko magana take balle tayi murmushi ko dariya. Ga wata *yar siriritar wushirya a tsakiyar fararen hakoranta. Fatar jikinta abar kallo ce farinta mai kyau tas da ita kama daga fuskarta har tafin kafarta jawur da ita. Suhaif ya shiga tunani a zuciyarsa "Anya kuwa wannan ba *yar Larabawa ba ce? Kai dole ruwa biyu ce ko uwarta ko ubanta a sami balarabe. Tana da tsananin kyau wadda ko a mata sai sun tsaya sun kalleta sun kara kallonta balle namiji. Suhaif ya nisa ya ce a zuciyarsa "Lallai dole ki boye wannan kyawun naki saboda mu anan kasar bakake zaki zame mana tamkar wata zinariya abar kallo abar sha'awa wanda kowa yake fafutukar tara kudi ya mallaka domin zinare abun ado ne ga mata, kadara ce ga da namiji shiyasa kowa yake son ya mallakeshi. Allah Ka bani Iman, Allah Ka sani inason Iman tun ranar dana fara ganinta har cikin raina.
Dankwalin kanta ne ya sulmiye zai fadi duk da hannunta da bakin tukunya tayi kokarin sa bayan hannu ta dafe dankwalin don kada ya fadi abun ya ci tura, kasancewar yana da santsi sai ya sulale yayi kasa yayin da idanuwan Suhaif ya dira akan wani lallausan gashi dogo baki wulik. Ya sake murtsike idanuwansa yana kallo. Gashi ne dai Suhaif ba karya idanuwanka suke nuna maka ba. Ta lunkube gashin ta tufke bai san iyakar sa ba amma ko ba'a fada masa ba yasan zai tabo gadon bayanta. Gashin kanta bashi da alaka dana bakar fata daga gani wannan tsatson jajaye ce. Suhaif ya fada a ransa "Dolo Iman ta hada jini da farar fata ko Uwa ko Uba, amma bari mu saba zan binciketa a hankali.
Ko da ta mike tsaye ta dauki kayan data wanke tana mikawa kicin sai Suhaif ya bi kira da dirin jikinta da kallo. Wai!! Allah Yayi halittarsa ance mutum tara yake bai cika goma ba ko ta ina aka ragu wannan? Mai madaidaicin tsawo ce. Ta fi kiba daga kugu daga sama siririya. Kafarta abar kallo ce saboda anyi mata shape mai kyau wanda shi ya taimaka wajen kara dirar jikinta. Tea shirt din dake jikinta bata da kauri don haka ta sake fito da cikar kirjinta. Ya ja dogon numfashi ya shafa kirjinsa ya fada a bayyane "Allah Ka bani wacce nake gani yanzu, kasa ta soni kamar yadda nake sonta. Bayan ta gama kwashe kayan wanke-wanken sai ta zo ta wanke bakin dake hannunta da ruwan kyau da omo. Sannan ta dauki dankwalinta dake kasa a cikin ruwa ta kade ta daure kanta, ta dauko tsintsiya da ruwa da omo ta fara wanke wajen.
Yaji zuciyarsa ta hau dukan uku-uku saboda ya sake sarkewa da son abunda ba lallai bane ya samu sai ya shiga tausayin kansa kamar ya rushe da kuka. Yasa hannayensa biyu a aljihu ya jingina goshinsa a jikin bango ya runtse idanuwansa yana zulumi da takaicin ta yaya ma zai saba da Iman balle ya sami soyayyarta? Yarinyar da ko hada ido sau daya bata yarda su yi, zaman minti uku bata yarda suyi, magana jimla biyar basu taba yi ba. To yaya zaiyi? Yana tambayar zuciyarsa yana tambayar kansa. Motsi ya ji a bayansa ya juyo da sauri, sai yaga Iman ce dauke da tsintsiya a hannunta daya hannun kuma dauke da abun kwashe shara da kanzo a ciki tazo zata zuba a abun zuba sharar dake ajiye a zauren. Saboda tsananin firgita Iman ta zubar da abubuwan dake hannunta. Ya sake zare wadannan manyan idanuwansa ya kalleta sai taji wani abu yarr a cikin jikinta, taji kamar a tsirara take, hankalinta ya tashi yau wanda take tsananin kunya da jin nauyinsa ya ganta a haka. Ta fisgo dankwalin kan ta tana so ta rufe jikinta sai taji ta tuje gashinta ya zubo a fuskarta da bayanta yaraf, ta fara ja da baya. Yana kallonta ya durkusa a hankali ya dauki tsintsiyar da abun kwasar sharar ya fara tattara kanzon data zubar a gabansa. Sai gabanta ya fadi tana gudun ko tayi laifi ta zubar da kanzo yana kwashewa ta hau in ina ta ce "I'm sorry. Ya sakar mata wani lallausan murmushi ya girgiza kai ya ce "ba mishkila, tafi kawai. Abunda ya bashi mamaki sai yaga tayi masa murmushi ta duka ta ce "Thank you ta sunkuyar da kai kasa ta juya ta tafi. Ya ajiye tsintsiya da abun kwasar shara yazo ya jingina ajikin kofa yana kallon yalo-yalon gashin nan nata har sai da ta shige daki sannan ya dawo ya kwashe kanzon daya zube ya shiga dakinsa ya kwanta tamkar bashi da sauran laka a jikinsa. Babu abinda yake hangowa a idanuwansa da zuciyarsa sai Iman.
Tun daga wannan rana Iman ta sake kara jin kunyar Suhaif sai kara gudunsa take, haduwa tayi musu wuya sai wasan *yar buya in dai ba kure musu tayi ba bata yarda ta tsaya su gaisa. Abun yana damun Suhaif babu yadda zaiyi ya hanata wannan hali, kuma duk gidan shi kadai take yiwa haka duk sauran ta saki jiki dasu rai-rai yake jiyo hirarta amma a gabansa sai tayi shiru, a hankali sai ta zame ta gudu daki shi kuwa a zuciyarsa ya saba da ita don tunaninta da sonta ya zame masa abokinsa na yau da kullum, tana zuciyarsa koda yaushe yana tunaninta, son kuma karuwa yake yi.


A yau da yamma Najib ne ya dira a garin Doko daga Kano, ya iske Suhaif a dakinsa yana zaune kan katifarsa ya jingina a jikin filon daya jingina a jikin bango. Tunanin Iman ne yake damunsa ya saka wannan ya cire, ya saka wancan. Sallamar Najib ce ta katse masa tunani ya amsa a sanyaye yayin da hankalinsa gaba daya ya tattara ga kallon mai shigowa. Kasancewar yamma tayi ga babu wuta, dakin ya fara duhu. Suhaif bai gane fuskar mai shigowa ba duk da yaso ya dauki muryar amma yana kokonto anya kuwa Najib ne zai zo da yammar nan. Kuma a yadda suka yi da Najib ba zaizo yau ba, ya ce zai je Bauchi ya dawo tukunna. Najib ya karaso kan katifar da Suhaif ke zaune ya kama masa hannu suka gaisa sannan Suhaif ya gane ko wanene. Cikin mamaki Suhaif ya ce "Malam Najib kaine, kasan kuwa ban ganeka ba? Gaskiya mutumin nan kayi min zuwan bazata. Najib yayi dariya ya sami waje ya zauna a kusa da Suhaif ya ce "Haba dai, ba dai tun shigowata baka gane ni ba. Na dauka zaka gane muryar? Suhaif ya ce "Naso in dau muryar saina ce kai ba kai bane yaushe ka dawo daga Bauchi? Ko dai *yar Bauchin za'a samo mana ne? Ka cika yawan zuwa Bauchi. Su duka suka tuntsire da dariya. Naji ya ce "Kai wallahi ka cika rudu, bana gaya maka bikin Aliyu Bauchi course mate dina muke ba? Kasan ni ai sai Samira Tukur, bayan har yanzu yarinyar nan garani take ban samu shiga ba ina ni ina jijjibo wata kuma? Samira ta cika yanga da yawa. Suhaif ya fada yayin da yake tabe baki.. Najib ya kwashe da dariya ya ce "To meye kake tabe baki? Suhaif ya ce "Ai haka take idan zata yi magana a wani tabe baki a yatsune fuska kafin ta gaishe da mutum shi yasa ban cika rakaka ba wajenta.
Yanzu a label nawa take ne? Najib ya ce "Lebel two ta shiga tana Micro-biology anan B.U.K Old Side.
Najib ya gyara zama ya ce "Daman labari na kawo maka da dimi-dimi, da sai gobe zanzo naga kai gara in zo yau in fesa maka wannan abun farin cikin. Kasan kamar akan kaya nake Allah-Allah nake su turamu bautar kasa nan muje muyi mu dawo mu sami aiki mu ma a dama damu a gwamnati, Babana yana da abokai a kusoshin gwamnati. Last week ma ya kirani falonsa ya dubeni ya ce, "Wai kai da dan uwanka Suhaif yaushe zaku je bautar kasa ku fara aiki har na yiwa abokaina maganarku fa. Na ce "Mun kusa tafiya Baba. Suhaif ya harareshi ya ce "Kai mayen kudi ne wallahi baza ka iya aikin banki ba. Ni har yanzu baka fada mun labarin da ka kawo min da dimi-diminsa ba. Najib ya ce "Ina dawowa daga Bauchi na shiga School na tarar an kafe sunayenmu kowa da garin da zaije bautar kasa. Suhaif ya zabura ya dafe kirji ya ce "Kaga nawa? Najib ya ce "Ba dole ba ai kafin in tsaya in duba nawa naka na fara dubawa an turani Kaduna kai kuma Ogun.
Suhaif ya daka tsalle ya mike tsaye ya ce "Bazai yuwu ba, danme za'a turani kasar inyamurai? Ai nafadawa Baba, indai kudu ne ba inda zani don haka kayi shiru karma ka bari su Baba su sani dan ba zanje ba. Najib ya mike ya nufi kofar fita yana cewa "Kai wallahi dan yawa ne, bari in fadawa Baban da kaina dole ma kaje. Suhaif ya damko Najib ya rike shi, Najib kuma na kokarin fisgewa. Baba ya zo wucewa ya gansu suna kiciniya. Ya daka tsawa ya ce "Meye hakan, kamar wasu *yan yara kuke wasan kunce? Najib ya kyalkyale da dariya ya durkusa ya gaishe da Baba sannan ya gaya masa abunda yake faruwa. Suhaif kuwa sai bata rai yake yana tsaye yana hararar Najib. Baba ya fusata ya sharba masa Carbin dake hannunsa ya rufe shi da fada fafafafa "Sai kaje wallahi. Ko na mutu na bar wasiyya a tura ka. Yaro ka gama karatu bautar kasa ta gagareka wai kai sai arewa, kudun zaka je dole ne ai. Najib ya yiwa Baba sallama ya ce ba kwana zai yi ba.


Reedwan [[f9.heart]] Iman [[f9.heart]] Matawata ....... Mai mace daya aminin Gwauro.


Su wa'e a dage ai aure..


SAI GOBE IDAN ALLAH YA KAIMU


Reedwan Suraj Isma'il
08098715332 @watsapp




_____________________ YARENA ADDININA
CI GABAN LABARIN


Washe gari ranar Juma'a su Iman basu da makaranta don haka su Zubaida baccinsu kawai suke yi har karfe takwas na safe babu kowa a tsakar gidan. Iman a kwance take juyi kawai take ko itama ta samu ta danyi baccin safe yau taji yadda masu iya baccin safe suke ji don ita bata iya komawa bacci ba, bata san yaya suke ji masu yinsa ba. Ta duba agogo taga takwas ta dan gota sai ta mike ta cire *yar yaloluwar rigar baccin dake jikinta ta saka kayan da ta mayar da shi na aiki. Ta fito tsakar gida duk da ta share tsakar gidan da daddare tas yake babu datti amma ai ba za'a rasa kura ba. Sai ta shiga hado kayan wanke-wanke. Bayan ta wanke tas ta kawar da kayan saita share wajen ta kwashe kanzo da gayan tuwon da aka ci aka rage. Ta nufi zaure inda abun zuba shara yake. Akan wani dan dakali dake kofar gidan ta hango kafafuwan Suhaif bata hango gangar jikin ba amma ta jiyo dogon tsakin da yake ta ja da alama yana cikin damuwa, damuwar tasa ba zata rasa nasaba da zancen tafiyarsa bautar kasa ba, an tura shi garin da baya so kuma mahaifinsa ya ce dole yaje.
Ta taho a hankali ta leka inda yake zaune ta ganshi ya dukar da kansa kasa ya rike kai da hannu biyu yana girgiza kai saboda tsananin damuwar da yake ciki. Iman ta ji tausayinsa ya kamata, ba don tana kunyarsa ba data bashi hakuri ya daina damuwa da yawa amma baza ta iya tsayawa tayi magana ba. Ta juya a hankali ta shige cikin gida taje ta karasa wanke wajen da tayi wanke-wanke ta koma daki ta zauna sai taji ta kasa zaman, ta tashi ta fito tsakar gida ta tsaya taji ta rasa sukuni lallai wani abu yana damunta a zuciya. Ta rasa meke yi mata dadi a ranta kuma yanzun nan abin ya fara nukurkusar zuciyarta don kalau ta tashi a safiyar yau zuciyarta cike da farin ciki. Can ta tuna ashe halin da Suhaif yake ciki ne ya shafeta itama ta kasa sukuni. Sai ta shiga mamakin kanta da kanta. Yaya haka? Meye wannan? Yaya na shiga damuwa don Suhaif yana cikin damuwa? Inji zuciyarta. Sai wata zuciyar tace "Ai ya kamata ki taya Suhaif duk halin da yake ciki ko farin ciki ko bakin ciki. Ki tuna fa shine ya taimakeki a lokacin da kike neman taimako, kin shigo kasar da baki san kowa ba gaba da baya. Ya tsaya tsayin daka sai da ya ga kin sami wajen zama daram sannan hankalinsa ya kwanta. Ya kamata a ce kin taya shi bakin ciki, sai ta koma daki ta kwanta tayi shiru a kan *yar katifarta. Can a cikin zuciyarta taji ance "Gaba daya wannan ba mafita bace kinzo kin kwanta ranki ya baci shi wanda kike dominsa bai san me kike yi ba kuma ko da ya sani babu abinda zai kara masa kije ki tare shi ki bashi hakuri ki gaya masa kalaman kwantar da hankali ki bashi misali da hadisai in da Annabi ya fada mana mu bi maganar iyayen mu kuma yarda da kaddara. Sai Iman tayi zunbur ta tashi zaune tayi shiru tana tambayar kanta da kanta tayaya zata iya tarar Suhaif tayi masa magana har tayi masa kalaman da zai gamsu ya kwantar da hankalinsa bayan kunyarsa take matukar ji, kwarjini yake yi mata sosai. Sai taji ranta ba zai yiwu ta tare shi don baza ta iya ba, to amma tana tunanin me zai hana ta rubuta masa wasika ta kai masa. "Hakaa kuwa za'ayi. Ta fada a bayyane.
Ta tashi cak daga kan katifarta ta dauko jakar makarantar islamiyya dake rataye a jikin kusar dake manne a bangon dakin, ta dawo ta zauna akan katifarta ta bude jakar ta dauko littafi da biro, ta ciro takarda ta fara tsantsarawa Suhaif wasika cikin harshen turanci don shi tafi iyawa fiye da Hausa sai kuma fulatanci yarenta wanda shi tafi ji amma ai shi wanda zata yi dominsa baya ji. Da farko ta gaishe shi, gaisuwa irin ta addinin musulunci da kuma girmamawa. Sai ta nuna masa irin halin damuwar data shiga sanadiyyar ta ganshi yana cikin damuwa to amma ya bar damun kansa saboda abun bana damuwa ba ne in har zai barwa Allah zabinSa. Ta kara da cewa ya bi maganar mahaifinsa ya yi biyayya a gare shi hakika idan yayi haka zaiga budi a rayuwarsa. A ko ina yake ya sawa ransa Allah Yana tare dashi, kudu da arewa duk daya ne Allah yana ganin ko ina. Kada ya damu mutum yakan so abunda ba shine alheri a gare shi ba sai Allah Ya zabar masa abunda zai ji baya so kuma ya zama shine alheri a gareshi. Yayi hakuri yaje tayi alkawari zata zamanto mai yin addu'a a gare shi, insha Allah zaije lafiya ya dawo lafiya. Ta jawo wasu ayoyi a cikin littafi mai tsarki ta fassara taja hadisai tayi masa misali dasu. Ta kara yi masa nasiha daya kwantar da hankalinsa kada ya damu. Data gama rubutawa tsaf sai ta linke ta jawo zirmikeken hijabinta ta saka ta fito. Ta leka kofar gida ta hango Suhaif yana nan a zaune inda ta barshi sai ta tsaya tayi cak tana tunanin yaya za'ayi ta bashi wasikar. Mummunar faduwar gaba ce ta afko mata yayin da ta ga Suhaif a gabanta ba tare da ta ji motsin tafiyarsa ba. Shi ma yayi kicibus da ita, sai yayi kasake yana kallon ta bai zata zai ganta a nan ba, ya yi matukar mamaki da sassafen nan "Ina Iman za ta je, yau Juma'a kuma babu makaranta, bayan makaranta kuma babu inda Iman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login