Showing 105001 words to 108000 words out of 110329 words
Chapter 36 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
tunani "Lallai gaskiya ne halin Pretty ya banbanta da namu tun a da, har muna tunanin bata da lafiya shi yasa bata zina. Yanzu ga makomar mu ita kuwa kalli yadda ta koma da alama tana cikin jin dadin rayuwarta. Iman ta ci gaba da yi masa wa'azi mai ratsa jiki yana sauraronta. Suhaif, Ibarahim, da Malam Shehu suma suka tsuguna a gaban Micheal suna taya Iman wayarwa masa da kai suna nuna masa karshen tayuwarsa bai zo ba, haka farin cikinsa a duniya bai kare ba. Ya yarda da Allah daya ne Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon ne. Can Micheal ya ce "Na yadda da Allah daya ne kuma Annabi Muhammd (S.A.W) Manzonsa ne. Sai gaba daya suka dau kabbara. Iman tana masa kalmar Shahada yana maimaitawa. Ta fashe da kukan dadi ta cewa Micheal "Ka zama Musulmi zaka ga alhairi a rayuwarka ta duniya da lahira. Daga yau ba sunanka Micheal ba zabi sunan da kake so a sunayen Musulmai. Ya ce "Sai yadda ku ka yi dani, ki zabar min kawai. Iman ta ce "Daga yau sunanka Ibrahim. Ta dubi Ibrahim marikin Muhammad ta ce "Saboda Muhammad tun a makaranta da sunanka ake kiransa ko? Su duka suka ce "Eh haka yayi.
Iman ta dubi Micheal ta ce "Ibarahim yanzu tunda ka dogara da Allah, ka yarda shi kadai ne mai iko, mai bayarwa, mai hanawa. Bari ka gani ma tun daga yanzu. Iman ta tashi ta fita ta je lungun data boye Muhammad ta kamo masa hannunsa suka zo wajen Micheal. Micheal ya kurawa yaro ido, yaro ya kurawa Micheal ido. Micheal ya ce a ransa "Ya aka yi wannan yaron yake kama dani? Cike da mamaki Micheal ya dubi Iman ta ce "Waye wannan yaron? Iman ta ce "Dan Harriet ne kuma danka ne bai mutu ba.
Micheal ya dora hannu aka ya fasa kuka share-share da hawaye. Jikinsa ya dau karkarwa yana yiwa Iman godiya ya ce "Yadda na zama dana ba zai iya taba ni ba dana rungume shi naji sanyi a raina. Ni kadai na rage a duniya yanzu Pretty bani da Uwa ba Uba, babu dangi. Ashe ina da da a raye? Na gode Pretty. Iman ta ce "Ka godewa Allah. Iman ta dubi Muhammad ta ce yaje ya gaishe da babansa, Muhammad ya yatsune fuska ya ce "Wannan ne Babana? A'a ga Babana nan. Ya nuna Ibrahim, dakyar suka kamashi suka kaishi wajen Micheal. Micheal ya shafa kansa yana kuka.
Micheal makale da sandarsa biyu ya rako su bakin mota suna ta bashi baki da shawarwarin yadda zai gudanar da rayuwarsa. Da yadda zai aiwatar da addininsa. Iman ta dubi Mansur wanda har yanzu yana shafa wuyansa inda yasha shaka. Ta ce "Mansur yi hakuri, ka taimakeni ka taimaki rayuwar Micheal, kaga kai Musulmi ne. Micheal ya Musulunta, ka shiryu shima ya shiryu ya daina fashi ka zama abokinsa don rayuwa baza tayi dadi ba mutum daya bashi da kowa babu mai zuwa wajensa. Ka koya masa wankan shiga Musulunci, sai ka koya masa alwala da sallah. Idan kaima baka iya ba ka kaishi a koya masa ko kuma zan baku kudi a dauki Malami ya dinga koya masa. Zan baku kudi ku gyara kanku da muhallinku. Ta juya ta kalli Micheal ta ce "Ka yi min alkawari baza ka kara shan giya ba, fashi, neman mata, balle ka datsewa mutane kafa ko kisa. Kamin alkawari baza ka bar Musulunci ba kuma zaka rike addininka duk abunda Musulmai suke yi kamar salla, azumi, da hakuri zaka yi. Sannan kamin alkawari kudin da zan baka zaka gyara gidanka da jikinka da kuma abinci mai kyau. Micheal yayi murmushi ya gyada kai ya ce "Nayi alkawari zan yi duk yadda kika ce, ko bayan idonki ne.
Iman da Suhaif suka shiga mota suka yi shawarar nawa ya dace a bashi. Kudi mai dumbin yawa suka bawa Micheal ya bude baki yana mamaki sai juya damin-damin kudin yake yana godiya. Iman ta ce "Ka sayi wayar hannu zan baka lambar mijina idan ka hada wayar sai ka kiramu. Ya amsa mata da "To zan saya. Mansir ma ya hau murza hannu don har kaikayi hannunsa ya fara yi tun kafin nasa kudin ya shiga hannunsa. Iman ta mika masa nasa duk da na Micheal yafi yawa amma yayi murna bai taba zata zai sami haka ba. Shima yayi mata alkawari zai tsaya tsayin daka ya ga ya taimaki Macheal akan komai ma ba addini kawai ba. Mansur ya shiga mota su Iman ma suka shiga suka tafi. Micheal yana daga musu hannu har suka tafi. Gidan Fadila Mansur zai nunawa Iman. Suka isa bakin get din gidan, lallai kuwa attajiri Fadila take aure. Iman ta ce su jira bari ta shiga ciki ta gani. Iman na shiga falon gidan ta tarar da Fadila a zaune a falo tana da tsohon ciki, ga karamin yaro zaune akan cinyarta da samari guda biyu suna zazzaune dukkansu suna kallon talabijin. Fadila ta amsa sallama gami da dago ido tana kallon mai shigowa. Fadila ta zabura ta sauke yaron dake cinyarta ta mike tsaye cike da mamaki ta tambaya "Wa nake gani kamar Pretty? Iman ta ce "Ni ce Fadila. Suka rungume juna saboda murna. Fadila ta kama hannun Iman ta ce "Zo ki zauna kawata Allah mai iko, ba dan ikon Allah ba da koda kudina ina zan nemeki? Iman ta ce "Kafin na zauna bari na shigo da baki a waje, mai gidana ne da wasu guda biyu. Fadila ta ce da samarin nan "Bishir jeka waje ka shigo da baki maza ka kaisu falon Babanku ka nuna musu bandaki. Iman ta ce "Sai ka shigo min da karamin yaron nan. Bishir ya amsa da "To Aunty, ya fita waje. Fadila ta ce "Kafin mu gaisa bari nasa masu aiki su harhado muku abinci. Bayan shigar Fadila kicin ba dadewa ta dawo wajen bakuwarta. Iman ta ce "Sallah nake so in fara yi. Fadila ta ce "To bari mu shiga daki. Suka dunguma zuwa katafaren dakin barcin Fadila, Fadila ta dubi Muhammad ta ce "Pretty danki ne wannan kuwa? Kai bayan rabuwarmu bai ci ki haifi wannan ba. Iman ta ce "Bari inyi salla zaki sha labaru. Kafin Iman ta idar da salla masu aikin Fadila sun jere musu abinci kala-kala da abun sha. Haka suma su Suhaif an kai musu nasu.
Wash! Idan ba na gaji da rubutun nan ba.
Lolxxx ashe ciwon S? ne ya kamani jiya ban sani ba...... uhmm
Daga gwauron ku.
Reedwan Suraj Isma'il
===============YARENA ADDININA
CI GABAN LABARI
Iman da Muhammad suna idar da salla sai suka fara cin abinci. Fadila ta sa Iman a gaba tana jiran labari. Abu na farko da Iman ta cewa Fadila shine "Dubi yaron nan Fadila da wa yayi miki kama? Fadila ta gama kallon Muhammad sai ta ce "Kinsan ban san Babansa ba, ke dai bai yi kama da ke ba. Iman ta ce "Baiyi kama da mai gidana ba, amma yayi kama da Mahaifinsa sai dai baki gane ba ne. Kin tuna dan gidan Harriet da suka haifa da Micheal? Fadila ta zabura ta sake dago kan Muhammad ta ce "Kwarai kuwa gaskiya kamar su daya da Micheal. Allahu Akbar. Pretty Allah Yayi miki albarka. Yanzu da dan nan kika je gidanku har ya girma? Wallahi kusan kullum sai Mahaifiyata tayi miki addu'a, da yake na bata labarin yadda kika yi min wa'azi har na koma gida na shiryu, na shiga Islamiyya. Babban abun al'ajabi bayan na shiryu ina gida samarina na da duk suka ki aurena wai ni karuwa ce, ko kuma Iyayensu su ki amincewa su aure ni. Tsohon da naki aura shine bai daina sona ba, kuma shi na aura yanzu. Kishiyoyina biyu suna Katsina har da *ya*yansu aurarru. Wadannan samarin da kika gani a falo suma *ya*yan sa ne, suna karatu a ATBU. Aiki ya kawo shi Bauchi ya taho dani, ashe da sauran shan ruwana a Bauchi. Ina matukar yin biyayya ga mijina, yana jin dadin zama da ni fiye da sauran matansa. Pretty zaman mace a dakin mijinta yafi komai dadi, yafi mutunci. Nayi rayuwar bariki na ji, ba rayuwar mutunci ba ce. Babu abinda ke cikin rayuwar bariki sai wulakanci da tashin hankalin duniya da lahira. Na godewa Allah na gode miki da kika yi sanadiyyar shiriyata. Na haifi dana na fari ga shi can Aliyu sunansa, sannan ga wani cikin, hankalina a kwance har na shiga ATBU nima yanzu ina Level 2 zan hada degree dina. Ke fa Pretty yaya rayuwarki ta kasance? Ina Hamma Huzaifa, shi kika aura? Waye ya kawo ki gidana? Iman ta fara zaiyanowa Fadila labarinta tun daga ranar da suka rabu har rana irin ta yau.
Suhaif ne yake wa Iman aike in ta gama su fito su tafi kada dare yayi musu a hanya, a yau zasu juya Jalingo. Iman ta bawa Fadila number ita ma Fadila ta bata tata. Iman ta karbi account number Fadila domin ta ringa aiko da kudi idan bukatar hakan ta taso a bawa Micheal. Fadila tayi alkawari zata hada dan mijinta da Mansur su je gidan Micheal saboda kai masa sako idan Iman ta turo din. Fadila sanye da hijabinta ta rakosu har bakin mota don ta gaisa da su Suhaif. Nan dai suka yi bankwana da Fadila da Mansur. Fadila tayi alkawarin duk sanda taje Abuja zata nemi Iman, don tana yawan zuwa Abuja.
Cikin dare sosai suka isa Jalingo suka fara zuwa suka sauke Ibrahim, Malam Shehu da Muhammad. Iman tayi alkawarin zata zo gobe su yini su sha hira da yara, yayin da ita da Suhaif suka nufi Hotel din daya sauka. Ranar da Iman suka yi sallama da Iyayenta wato sun fito zasu taho Kano daga nan su wuce Abuja. Sai da suka biya ta gidan su Muhammad suka yi musu sallama. Kudi na mamaki Suhaif ya bawa Ibrahim gami da bashi adireshinsa na Lagos da number waya ya je zaiyi masa hanyar samun saboda sunyi magana da Ibrahim ya nuna masa ya sami matsala wajen aikinsa. Haka Iman ta yiwa Salma kyautar kudi na mamaki, suna ta godiya tare da yiwa Iman alkawari zasu kawo mata Muhammad da kansu har Abuja idan anyi musu hutun makaranta. Muhammad ya fara sabawa da Iman shima, ta rungume shi tsam a jikinta yayin da kuka ya kece mata don kauna. Sannan Suhaif da amaryarsa Iman suka nufi garin Kano. KANO TA DABO TUMBIN GIWA, KODA ME KA ZO AN FIKA, in ji masu kirari.
Bayan shekara daya da bikin su Iman Allah Ya bata haihuwa ta haifi santalelen da namiji mai kama da Mahaifinsa, aka radawa yaro Huzaifa. Allahu akbar sun cure Huzaifa gam saboda taimako da abun alhairin da yayi musu a rayuwa. Mutane da yawa suka dinga cika zungura-zunguran motoci, wasu a jirgi suna zuwa taya Iman da Suhaif murna. Anyi kayatacciyar liyafar suna a katafaren gidan Suhaif na Abuja wanda ya kara kayata shi saboda suna. A cikin *yan suna harda Salma da yaranta dukka su Muhammad. Bayan suna kowa ya hau shirin komawa gida, Iman ta marairaice ta roke su su bar mata Muhammad ya dawo wajenta da zama zata dinga kawo musu shi hutu. Basu hanata ba tunda sun zama daya ga dinbin alherin da Ibrahim yake samowa daga Lagos a wajen Suhaif.
A shekarar Suhaif ya kantara gidaje uku iri daya a jere a wata sabuwar unguwar attajiran garin suka zamar da ita small London a cikin garin Jalingo. Gida daya na Iyayen Iman ne, daya na Iyayen Huzaifa, daya kuwa na Iman ne inda zata dinga sauka idan ta zo garin. Alhamdulillahi! Irin dadin da mutanen nan suka ji a lokacin da Suhaif ya danka musu mukullan gidan kamar su zuba ruwa a kasa su sha. Iman bata manta da Mama Tabita ba, gida sukutum ta saya mata ita da mijinta da basu jari mai tsoka yanzu sun daina aikin wahala an dauki wasu *yan aikin.
Iman da Suhaif sun gamsu da shiryuwar Micheal. Ya nutsu, ya rike addininsa, ya gyara jikinsa da gidansa, ya bar shaye-shaye. Koda yaushe Micheal suna gaisawa da Suhaif a waya, kuma yana fada masa abun da yake bukata idan matsala ta taso masa kamar yadda suka bashi izini ya dinga tambayarsu. Suhaif ya shirya ya tafi Italy ganin likitansa sai ya hada visar sa data Micheal sai a waya Suhaif ya ce da Micheal ya shirya ya taho Abuja ya same shi zai tafi Italy da shi ayi masa kafar roba, wacce zai dinga takawa kamar yadda kowa yake takawa. Hakika Micheal yaji dadi, farin ciki yayi masa yawa har ya rasa ta inda zai fara godiya, yau ya sake tabbatar da zancen Pretty data fada masa cewa farin cikin rayuwa bai kare masa ba in har ya yarda da Allah daya ne kuma ya rike addinin Musulunci. Iman ma taji dadi da Suhaif ya sanar mata abun alkairin da zai yiwa Micheal.
Suhaif a koda yaushe arzikinsa kara lunkuwa yake na yau tafi na gobe. Saboda kyakkyawar niyyarsa ta taimakon talakawa masu karamin karfi masu neman taimako, danginsa da kuma sauran al'ummar Musulmi gaba daya. Suhaif yana matukar kaunar Iman a zuciyarsa gaba daya, musamman dadin zaman da yake ji da ita. Babu abun da take dorashi akai sai hanya madaidaiciya tana matukar bashi shawara ya kyautatawa Iyayensa *yan uwansa, talakawa masu bukata, da kuma ma'aikatan da suke yin aiki a karkashinsa na gida dana wajen aiki. Kamar yadda Suhaif yayi kudi, Iman ma tayi kudi, domin kayan Suhaif na Iman ne. Bai yi mata Katanga ko iyaka da dukiyarsa ba. Ya bata izinin fitar da kudi duk yadda take bukata.
Iman bata da matsala bata da abunda zata yi da kudi komai an ajiye mata naci ko na sakawa, haka kafin tayi tunani siyawa Iyayenta wani abu tuni Suhaif ya saya musu dan haka bukatarta da kudi shine tayi amfani dasu wajen yada addininta. Tana shiga lungu-lungu, sako-sako, gari-gari. A jirgi ko a mota inda mota bata shiga ta hau keken shanu. Allah Ya dubi kyakkyawar zuciyarta da tsananin addu'ar da take yi yana cika mata burinta. Allah ne yasan dunbin jama'ar da suka Musulunta a hannun Iman saboda wa'azin da take musu a nutse cikin sassanyar muryarta har sai ya ratsa zuciyarsu ya shiga jijiyoyin jikinsu. Iman bata gajiya kuma bata fushi da masu zaginta tana ci gaba da basu hakuri, tana musu wa'azi har sai sun ji su da kansu ta fisu gaskiya. Bayan Musulunta sai ta bisu da dinbin dukiya wacce zasu dade basu ce babu ba. Allahu Akbar ita kuma haka Allah Ya halicceta tana tsananin son addininta ta kuma rike shi da karfinta. A zuciyarta da dukiyarta, a shirye take ta yada addininta ko za'a daketa ko a jefeta koma a rabata da rayuwarta. A shirye take da ta karar da duk abunda ta mallaka dan yada addininta, haka mijin ta yake taya ta son abunda take so, yana taimakonta da dukiyarsa da karfin jikinsa.
Katafaran kanfani Suhaif ya bude a Kano ana yin leda, man-gyada da kuma atamfofi. Kusa da nan Suhaif ya bude katon wajen sayar da manyan motoci (tifa) bayan hamshakan super market da a kowacce state ya bude branch. Najib tuni yabar aikin wahala wato aikin banki, dan uwansa Suhaif ya danka masa kacokan kula da kanfanoninsa na Kano da sauran harkokinsa. Zubaida da Naja'at suma Suhaif ya basu babban aiki a kamfaninsa. Haka Micheal bayan kafar roba mai kama da ta gaske da Suhaif ya kaishi aka yi masa a Ilaty suna dawowa Nigeria Suhaif ya bashi Upper ya dauke shi aiki a kamfaninsa akan albashi mai tsoka. Ya bashi zabi ya zabi duk garin da yake so kanfanin Lagos ko Kano. Micheal yana son Musulmi da addinin Musulunci nan take ya zabi Kano. Suhaif ya sa Najib ya samar masa gidan haya mai kyau zai biya masa hayar shekara biyu, kafin ya saya masa gida kyauta in har ya ji dadin Kano yana son ci gaba da zama a Kano. Micheal yayi farin ciki marar misaltuwa, godiya ba adadi.
Ya shiga Bauchi cike da murna ga kafa ras yana takawa kamar kowa ya zubar da sanduna. Babu mai cewa ba kafarsa ba ce, ga aikinsa a hannu. Micheal yana ta godiya ga Allah, godiyar da ya yiwa Ubangijinsa shine Allah Yake kara masa. A satin ya hadu da wata zankadediyar bazawara wacce mijinta ya mutu bayan sun haifi yara biyu mace da na miji a sanadiyyar natsarin mota. Sunanta Khadija Bahaushiya ce gaba da baya Musulma mai asali, sune Bauchi domin Mahaifinta na da sarauta a garin.
Khadija fara ce sal doguwa mai kyau ga Uwa Uba ilimi domin ta kammala karatun degree din ta a University of Maiduguri (Uni Med) ita ta fara nuna masa so da farko ya ki amincewa kasancewar yana da tabo a garin bai boye mata ba, ya bata labarinsa kakaf tun da har zuwa yanzu. Ta nuna masa duk babu damuwa tana sonsa haka tunda muna yiwa Allah laifi ya yafe mana. Tunda ya tuba ya gyara halinsa hakika Allah Mai karbar tuba ne. Khadija da Micheal sun shaku sosai soyayya ta hardesu, cikin dubara ta rurrufa ta tsara Iyayenta har suka yadda suka amince ta auri abin kaunarta Ibrahim (Micheal).
Bayan haduwar Micheal da Khadija da wata hudu suka yi aure, an kai amarya gidan angonta a nan Bauchi gidan Mahaifiyarsa da ya gada. Kayan daki na gani na fada aka shiryawa amarya. Dakuna uku ne duk an zuba gadaje, kujeru na alfarma a falon, kayan kicin na haduwa a kicin, sannan kayan bandaki na burgewa a bandaki.
Iman ta zo biki ta sauka a gidan Fadila, ta taho da Muhammad dan Micheal. Micheal ya ji dadi sosai ya nunawa amaryarsa dansa, ya kuma gabatar mata da Pretty daman ya dade ya na bata labarinta. Iman ta bawa amarya da ango gudunmawa mai ban mamali, kyautar dalleliyar mota ta basu kirar Camry. A bauchi Ibrahim (Micheal) ya bar matarsa Khadija shi yana Kano wajen aiki, sai dai duk karshen sati Bauchi yake zuwa. Itama amarya takan bishi Kano tayi *yan satittika. Zumunci mai karfi tsakanin Micheal da matarsa da su Naja'at, Zubaida da Najib a Kano.
Muhammad ya kaura Abuja kaco