Showing 9001 words to 12000 words out of 110329 words
Chapter 4 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
take zuwa? Wasu lokutan ne ma takan raka su Naja'at su je su gaishe da Hajja Kakarsu.
Ta durkusa ta gaishe shi ya amsa ya ci gaba da kallon ta a zuciyarsa cike da alamomin tambaya. Ya ga Iman dai a tsaye ba ta shige gida ba, ba ta kuma fita waje ba, kanta a sunkuye a kasa. Ya ce "Iman unguwa za ki ne? Ta girgiza kai ta ce "A'a. Ya ce "Kawai kin leko kofar gida ne? Sai ta yi murmushi ta dora takardar da ke hannunta a kan wundon da ke kusa da inda suke tsaye ta juya ta shige cikin gida. Suhaif ya bita da kallo yana cewa:
"Wasikar tawa ce ko kuma wani zan kai wa? Ba ta iya juyowa ta bashi amsa ba saboda kunya. Ya yi ta mamakin irin wannan kunya ta Iman, amma babu mamaki kunyar Fulani ta wuce haka. Sai ya sa hannu ya dauki wasikar da mamaki da kuma zumudi, wani bangaren cike da fargaba, Allah Ya sa ya ga abin da yake fita a cikin wasikar, ma'ana, Allah Ya sa ita ma ta fahimci son da yake yi mata, ita ma a ce tana yi masa. Ya shiga dakinsa ya sa makulli ya rufe ya zauna a kan wata tsohuwar kujerar da ke dakin. Ya yi bismillah sannan ya bude wasikar ya fara karantawa Suhaif ya tsinci kansa da tsananin farin cikin abin da ta fada kana kallon fuskarsa za ka iya ganin farin cikin da ya lullube masa zuciya, daman Hausawa sun ce. Labarin zuciya a tambayi fuska. Nan da nan ya ji mugun bakin cikin da tsananin damuwar da ke addabar zuciyarsa sun ware. Ya gamsu kwarai da bayanan Iman. Ya ji ya sake son ta fiye da son da yake yi mata a da. Ya maimaita karanta wasikar nan fiye da sau goma saboda ta yi masa dadi. Murna yau ba za ta misaltu ba a zuciyarsa. Can ya dau biro da takarda ya fara rubuta amsar wasikar.
Bayan ya yi mata sallama irin ta addinin Musulunci sai ya nuna mata jin dadinsa da ta kula da halin da yake ciki har ta damu ta dauki biro da takarda ta rubuta wasika ta yi masa nasiha. Ya yi godiya sannan daga karshe ya yi mata alkawari zai yi amfani da shawarwarin da ta ba shi zai kuma bi abin da mahaifinsa yake so sannan shi ma ya yi mata alkawarin zai zamo mai yi mata addu'a a ko yaushe Allah Ya ba ta miji na gari mai tsananin son ta, saboda haka shi ma kuma yana rokarta a cikin addu'ar da ta yi alkawari za ta dinga yi masa ta ce Ubangiji ya ba shi wata yarinya da yake tsananin so da bege. Ya sa yarinyar ta san halin da yake ciki ita ma ta so shi, saboda wacce yake so din ba ta san yana yi ba. Ya bayyana mata cewar wannan dalili yana daya daga cikin dalilan da ya sa ba ya son tafiyar. Da ya gama rubutawa sai ya nade wasikar ya ajiye biron, ya dade a zaune yana tunanin a inda zai gan ta ita kadai ya bata wannan wasika. Ya dubi agogo ya ga karfe tara daidai, sai ya ji a jikinsa ai *yan gidan ma ba su tashi daga barci ba, tunda sukan kai karfe goma suna barci. Yayi zumbur ya fito tsakar gida ya tarar babu kowa, sai yaji motsin kwanuka a kicin, ya nufi kicin sai ya tarar da Iman ce take damun koko. Tana dagowa ta ga Suhaif suka hada ido sai dukkansu suka sakarwa junansu wani sanyayyen murmushi. Ta yi sauri ta sunkuyar da kanta kasa bata yarda sun kara hada ido ba. Ta ajiye ludayin da take juya kokon tayi sauri ta saka hijabin data cire ta dora akan cinyarta. Suhaif yayi murmushi ya jefa mata wasikar kan cinyarta ya ce "Ina daki ina jiran amsa nasan baza ki iya kwankwasa min kofa in fito in karba ba to sai ki dora akan wundon da kika ajiye mun dazu. "Bata ce masa komai ba kanta a durkushe a kasa tana ta murmushi. Ya dakko kofi a kwando ya mika mata. Ya ce "Zuba min kokon. Ta karba ta zuba masa ya karba ya tafi. Zumudin karanta me Suhaif ya rubuta bai barta ta gama juye kokon a kwanukan sha ba sai kawai ta rufe da faifai ta mike ta shiga daki. Ta tabbatar su Naja'at har yanzu barci suke haikan sannan ta zauna kan katifarta ta bude wasikar ta fara karantawa. Fuskarta kawai zaka kalla kasan tana farin ciki. Ta karanta ta sake maimaitawa, sai tayi doguwar ajiyar zuciya ta lumshe ido. Ta dade tana tunanin me zata rubuta masa.
Bayan ta gama tunano meya kamata ta rubuta, sai ta jawo jakarta ta dauko biro da takarda ta fara tsantsara masa wasika. Ta fara da yi masa godiya game da alkawarin da yayi mata addu'a Allah Ya bata miji na gari mai sonta. Sannan tayi masa addu'a Allah yasa wacce yake so ta soshi sai dai ta bashi shawara ya kamata ya sanarwa wacce yake so kafin ya tafi kada yaje tunaninta ya dameshi. Ya kuma cire tsoro da fargaba da gudun ko ba zata soshi ba, ta tabbatar masa da cewa shi saurayi ne irin wanda kowacce *ya mace take addu'a Allah Ya bata kamarsa don haka tana tabbatar masa yaje ya tareta zata soshi kowacece yarinyar. Daga karshe ta bashi shawara ya guji zurfin ciki da yawa musamman a fagen so, domin a bari ya huce shi ke kawo rabon wani. Ta linke wasikar ta fito zaure, taga takalmansa abakin kofar dakinsa da alama yana ciki. Sai ta je ta dora wasikar akan takalminsa ta kwankwasa kofar sannan ta shige cikin gida. Suhaif na bude kofa sai yaga babu kowa yayi sauri zaisa takalminsa ya leka waje ko mai kwankwasa kofar ya fita sai yaga wasika. Ya durkusa ya dauka ya koma daki ya zauna ya bude ya fara karantawa.
Wanan karon farin cikin daya lullube shi ya wuce yayi murmushi sai dai dariya. Ya kyalkyale da dariya shi kadai, ya mike tsaye yana kai kawo a tsakar dakinsa yana sake karanta wasikar. A zuciyarsa yana tambayar anya kuwa Iman ce ta rubito masa wannan wasikar ko kuwa shine bai karanta daidaiba. Ya sake murtsike idonsa yana karantawa yaga da gaske ne abun da yake gani. Sai ya koma ya zauna ya dauko biro da takarda ya fara rubuta mata wasika. Fargabar da yake a zuciyarsa ta kau, kai tsaye ya fayyace mata abunda yake ransa na game da soyayyarta data damki zuciyarsa. Sai dai yana rokarta don Allah taji tsoron Allah, Allah Yana kallonta kada ta boye masa ta fada masa gaskiya menene ra'ayinta game da soyayyarsa. Idan bata amince ba ta fada masa wannan ba zaisa ya damu ba kuma zumuncinsu na nan a matsayin kanwarsa ya dauketa. Daya gama rubutawa sai ya nade wasikar ya fito. Kafin ya fito tsakar gida sai ya hango Zubaida da Naja'at a bakin rijiya suna brush. Don haka sai yaji duk ransa ya baci bai so suka tashi daga barci yanzu ba. Ya koma daki ya dauko kofin daya sha koko ya fito. Maimakon ya kai wajen wanke-wanke da ya hango Iman a kicin sai ya nufi kicin din ya mika mata kofi, ta karba sai taga wasika ce a cikin kofin. Ya juya ya fita, Naja'at da Zubaida suka yi sauri suka duka suka gaishe shi. Ba tare da sakin fuska ba ya amsa musu, ya wuce ya fita kofar gida Iman ta zare wasikar ta soke a cikin zaninta sannan ta fito takai kofin wajen wanke-wanke. Ta shaidawa su Naja'at ga kokonsu nan a kwanan sha, suka amsa mata da "To mun gode. Iman ta shiga daki cikin sauri ta dauko wasikar ta bude ta karanta. Sai ta tsinci kanta da tsananin farin ciki, sannan ta sake tabbatarwa da kanta ashe wannan tsananin kunyarsa da take yawan ji ashe so ne, sai dai kash yanzu su Naja'at sun tashi sai dai wani lokaci. Ta bude can kasar jakar kayanta ta boye wasikun.
Hankalin Suhaif ya tashi yaga har azahar Iman bata rubuto masa amsar wasikarsa ba. Duk motsin da yaji a jikin kofarsa sai ya leko yaga ko Iman ce ta ajiye wasika amma sai yaga wayam babu komai. Ya sake duba kan wundon dake zaure inda ta ajiye masa wasikar farko nan ma babu komai bata ajiye ba. Sai ya sake shiga damuwa da zulumi. Ya shiga cikin gidan baya ganin Iman tana daki a zaune. Da yamma ne ya hangota a kicin tana dora tukunyar tuwo. Naja'at tana daka daddawa, Zubaida na wanke-wanke. Gwaggo kuma na zaune a tsakar gida. Yazo ya zauna yaji duk hankalinsa baya jikinsa, Gwaggo na magana bai cika fahimtar me take ce masa ba. Ta dala masa duka a kafada ta ce, Wai kai yau meke damunka ne tun zancen tafiyar jiya ka bi ka susuce, kayi hakuri mana kasan fa halin mahaifinka sarai idan yace sai anyi to fa sai anyi gara ka kwantar da hankalinka kawai. Suhaif yayi murmushi ya mike tsaye ya ce "Ke ta tafiya kike Gwaggo ni abunda yake damuna yafi karfin damuwar tafiya. Ta ce "Meke damunka ka fada mun mana. Bai iya ce mata komai ba ya fice. Har dare bai ga amsar Iman ba sai ya tabbatarwa kansa Iman bata amince ba kuma tana kunyar rubuto masa a'a sai ya zauna ya bude sabon tunani mai dauke da tsananin bakin ciki. Bai iya cin abincin dare ba ko loma daya da yaga barcin ya gagara sai ya daura alwala ya dinga nafilfili yana addu'a yana kai kukansa wajen Ubangiji Ya taimake shi yayi masa agaji ya sami soyayyar wacce yake so. Hawaye ne ke kwaranya daga idanuwansa yayin da yake ganawa da Ubangijinsa. Shi kansa yana tsoron halin da zai shiga muddin Iman ta kishi har asuba yana zaune yana addu'a. Da yaji ana kiran assalatu sai yaji motsin mahaifinsa yana bude kofar gida zai je masallaci, yayi wuf ya fito suka dunguma suka tafi tare. Bayan an idar da salla wasu na zama suyi zikiri a masallacin har sai gari ya waye. Suhaif da mahaifinsa suka zauna suma aka yi zikirin dasu har sai da gari yayi tangaran sannan suka fito daga masallacin. A hanyarsu ta tahowa gida ne Suhaif yake bawa mahaifinsa hakuri akan zancen tafiyarsa bautar kasa da ya nuna baya so amma yanzu yayi tunani yaga yayi kuskure yanzu ya sawa zuciyarsa ba komai zaije din. Mahaifinsa yayi farin ciki ya dora masa da nasihohi masu ratsa jiki na kwantar da hankali. Suhaif ya wuce dakinsa, mahaifinsa ya shiga cikin gida.
Suhaif na shiga daki sai ya kwanta ya runtse ido zatonsa zai iya barci saboda kansa yayi masa nauyi, idanuwansa suna masa tsaki-tsaki da alama dai barcin daya kwana bai yi ba ne yake tambayarsa. Amma ina! Barci ya gagara yazo, mummunar faduwar gaba data addabe shi idan ya tuna Iman bata amince masa ba. Bakwai da rabi dai-dai ya jiyo muryar Iman tana yiwa Gwaggo Sallama akan zata tafi makaranta saboda taron da za'ayi yau a makarantarsu har ana sa ran Mai Martaba Sarkin Gumel Alh. Ahmad Mohd Sani zai halacci taron bude wasu sababbin ajujuwa da masallaci da za'ayi a makarantar. Kasancewar Iman itace aka nada shugabar dalibai saboda kwazonta da kulawa da makarantar da take yi shine yasa, aka ce tazo da sassafe tasa yara su share filin makarantar a kamo bencina su fito dasu su shirya wajen da manyan baki zasu zazzauna.
INA MUKU BARKA DA SALLA !!!
Am sick, pls i need Ur prayers
Reedwan Suraj Isma'il
_____________________ YARENA ADDININA
CI GABAN LABARIN
Iman na fitowa zaure saita debi tsintsiyoyin dake wajen zuba shara ta kara gaba ta fita. Suhaif yayi firgigit ya tashi ya bude labulan Wundon dakinsa yana lekawa. Ya hangota sanye da hijabinta tasa nikaf ta rufe fuskarta da tsintsiyoyinta a hannu tana tafiya a nutse. Ya ce a ransa "Duk wanda yaci sa'a Allah Ya bashi mace mai addini irin Iman hakika yaji dadin duniya da lahira don ko yaki Allah Iman zata tuna masa hanyar bin Allah. Ya sake murtsike ido yana kallonta. Can a cikin zuciyarsa yaji ance "Ka bita ka tareta kuyi magana gar da gar mana karka cuci kanka. Ka tuna fa ita da kanta tace ka rage zurfin ciki musamman a fagen soyayya. A bari ya huce shike kawo rabon wani. Sai yayi wuf ya fito da sauri zaisa takalminsa ya bita. Abun daya bashi mamaki sai ga wasika a ajiye akan takalmansa. Yaji ajiyar zuciya sannan ya tsuguna ya dauka ya bude ai kuwa rubutunta ne. Sai ya koma daki ya zauna ya fara karantawa.
Layin farko na wasikar gaisuwa tayi irin ta so da kauna. Suhaif ya lumshe ido yayin da lumfashin kauna ya fara dira a hunhunsa. Ya ci gaba da karantawa, yakan tsaya yayi dogon tunani harya tattaba jikinsa ya tabbata shine kuwa da gaske ko kuwa a mafarki yake jinsa. Sai yaga shi din ne ba mafarki ba ne. Iman ta fayyace masa sirrin zuciyarta cewar ta amince masa tana kuma sonsa fiye da tunaninsa. Ta bashi labari cewa ashe wannan kunyar data ke ji bata komai bace illa so da kauna, amma bata tantance ba sai bayan daya shaida mata yana sonta, sannan tasan ashe itama ciwo daya ne yake damunsu. Farin ciki da yayiwa Suhaif yawa sai ya kalli gabas ya yiwa Allah sujjada ya gode masa. Yayi masa kirari ya ce "Allah Mai jin kan bayinSa. Allah Kaine mai badawa a duk lokacin da kaso. Allah mai amsa addu'ar bayinsa, Allah kaine abin godiya, Allah na gode maka daka amsa addu'ata ka bani Iman.
Sai yaji a ransa ya tsaya yana rubuta wasika ma ai bata lokaci ne yanzu sai dai yaje ya tari Iman gar dagar suyi magana. Amma a ina zai iya tsayawa da ita ba tare da *yan sa 'ido sun gansu ba? Sai ya tuna ai yanzu ba aji zata shiga ba share-share zasu je suyi me zai hana ya bita makarantar yaje suyi magana tunda kannensa suna gida ita kadai ta tafi. Sai ya fito yasa takalminsa ya nufi makarantar su Iman. Kananan yara ya tarar suna ta share farfajiyar makaranta. Ya waiga ko ina bai ganta ba sai ya tambayi wata rayinya ko ina Iman. Yarinyar ta ce "Yanzun nan muke yin shara sai tari ya turnike ta ta shiga ajinsu ta zauna. Suhaif ya ce "Ina ne ajin nasu? Ta nuna masa da hannu, ya nufi cikin ajin da sauri gabansa na faduwa yana tunanin meye sameta take tari? A can a karshen aji ya hangota ta kifa kai akan Tebur. Ta karasa gareta, yayi mata sallama ta dago da sauri gami da yaye nikaf din data rufe fuskarta ta mike tsaye ta gaishe shi taci gaba da sauraronsa a zatonta ko kiranta ake a gida. Yayi murmushi ya ce "Koma kiyi zamanki zuwa nayi in duba ki ance kina shara tari ya turnikeki kin shigo aji kin zauna. Lafiya kike tari? Ko kura ce ta yi miki yawa ta saki tari? Ko daman kina da asma? Iman tayi murmushi ta koma ta zauna. Suhaif ma ya zauna akan kujerar da ke gaban teburinta yana fuskantarta. Ta nisa ta ce "Kura ce ta sani tari bani da asma amma ina da ciwon kirji. Suhaif ya ce "Ai da baki tarki shara ba da kinbar yaran sunyi kina zaune kina kallonsu, ko da yake neman lada kike yi kema, nasan baza ki bar ladan nan mai tsoka ya wuce kiba ko? Tayi murmushi ta sunkuyar da kai kasa.
Ya kara ce wa "Naga wasilarki wacce ta sani farin ciki naga ya dace in rubuto godiya sai naga biro da takarda baza su iya zana mun irin godiyar da nake miki ba gara inzo da kaina in gode miki. Domin ba karamin ceto raina kika yi ba da kika amince mun. Iman tayi shiru sai murmushi kawai take yi. Ya ce "Nasan a yanzu baza ki iya bani amsa ba amma nagode da kika iya zama kike fuskantata kika bude fuskarki nake kallon kyakkyawar fuskarki har kike min murmushi. Sai su duka suka kyalkyale da dariya. Sai tai sauri ta saki nikaf din ta rufe fuskarta. Suhaif ya mike tsaye ya ce "To nabar ki lafiya sai anjima idan mun zo ganin Sarkin Gumel. Naji ance kece za kiyi wa manyan baki tafsiri ko? To zamu zo muji. Kin ga dana iya karatu da sai in dinga ja miki baki kina fassarawa. Ba tace komai ba kuma ta rufe fuskarta balle yaga yanayin fuskarta amma daga dukkan alamu murmushi take yi, ya juya ya fara tafiya har ya kai bakin kofa sai ya juyo ya ce "na tafi fa. Sai yaga ta daga masa farin hannunta. Shima ya daga mata hannu sannan ya fita daga ajin ya nufo gida cike da farin ciki.
Ya wuce cikin gidansu ya tarar da Gwaggo a zaune a tsakar gida tana cin dumamen tuwo. Naja'at na wanka, Zubaida kuma tana goge hijabinsu da abun gugar gawayi. Zubaida ta duka ta gaishe shi. Da yake yau yana jin farin ciki ya amsa mata da fara'a harda tsokanarta ya ce, "Lallai yau dole a fesa wanka a goge hijabi tunda za'aga Mai Martaba Sarkin Gumel ko Allah Zaisa dogari daya ya taya. Gwaggo ta harareshi ta ce "Dogari fa kace? Amma ka cika wulakanci ina laifin hakimai amma a Dogari zasu tsaya wadannan kyawawan *yan matan nawa danma Iman tana sa abu ta lullube fuskarta ai da duk bakin sai sun taya. Suhaif ya ji wani kaikayin kishi ance duk bakin zasu ce suna son Iman yayi sauri ya ce "Ai banda Iman da Naja'atu da Zubaida ne naga ana fesa wanka da guga. Gwaggo ta ce "Ko suma sunfi karfin dogarai karma kayi musu baki. Zubaida tayi dariya tace "Yaya Suhaif kasan Dogarai baza su tare mu ba sun san mu ba kalar su bane, kai ko *yar Hajja tafi karfin Dogarai. Suka kwashe da dariya. Gwaggo ta ce "*Yar tawa *yar Hajja kika raina? Suhaif ya