Showing 60001 words to 63000 words out of 110329 words
Chapter 21 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
basu matso kusa da ni ba. Gari ya waye na roki ruwa na yi salla, na kara gaba, haka na yini ina yawo daga wannan unguwa zuwa waccan, duk macen dana gani sai in bita ina rokarta ko zata dauke ni aiki, Allah Baisa an sami wacce ta amince in bita ba. Kudin motata ya raunana, canjin kawai ya rage a jakata a lokacin ina tsakiyar tashar *yan kaba. Abunda ya fado kunnena shine naji wani kwandasta ya ware murya yana ce wa "Gumel! Gume!! Gumel!!!
Naje na tambayeshi menene Gumel? Saboda sunan ne kawai yayi min dadi, yayi kama da albarka. Sai yayi dariya ya ce "Malama yanzu duk zamanki a kasar nan bakisan garin Gumel ba? Gumel gari ne mai mata da maza, yara da manya, attajirai da masu Sarauta, masu Mulki da manyan Malamai bayin Allah. Garin da suke da faffadar Masarauta. Sune suke bikin Sallar Mauludi (sallar gani) ake tururuwar zuwa daga gari-gari da kasashe-kasashe daban-daban. Garin da suka taba yin ministan sufuri General I.D Gumel. Sai na tsaya kawai ina kallon bakinsa har ya kai aya. Sai nayi murmushi na ce masa "Zanje Gumel. Ya ce "To shiga zungureriyar bus din nan *yan mata, yanzu kuwa zamu kai ki garin Sarki Amadu.
Mota ta cika makil direba da kwandastansa suka shiga aka rufe kofar mota, muka fara tafiya. Yayin da iska mai sanyi take busowa cikin motar na lumshe ido dadi ya lullube zuciyata naji a raina daga lokacin dana shiga garin Gumel bakika damuwata zata gushe da Izinin Allah.
"Ku hado kudin motarku. Inji kwandasta. Na laluba canjin daya rage a jakata sai naga basu da yawa, nan fa gabana ya hau faduwa na shiga mota babu cikakken kudin mota, yana fadar yawan kudin motar nasan bani da su. Jikina yana rawa na mika masa abun da Allah Ya hore min. Nan fa tarwatu ya tashi da tonar asiri.
Ya kirga kudin dana mika masa sai ya harareni ya ce "Malama ciko kudinki bai cika ba. Na narairaice na ce "Bani da wasu su kenan. Ya ce "A'a wannan zance kike da ganganne haihuwa da damuna inji masu iya magana, falleliyar budurwa kamarki ace baki da kudin mota? Idan ma wasa kike to ya isa wasan ki ciko mana kudinmu. Nayi murmushi na ce "Da gaske nake kudina kenan, ku taimakamin. Ya sake cewa "Ai ba laifin mu bane, mu ma balance muke hadawa mai ainihin motar, da zarar kwabo bai cika ba, za'a daga mana hankali koma akwace motar a bawa wadansu, shi yasa bama wasa da karbar kudin mota. Ko kuma idan Allah Ya sa akwai wanda a cikin motar nan zai yi kudunbala ya biya miki cikon kudin motar ai babu matsala. *Yan cikin motar suna jin mu babu wanda yake da niyyar taimakamin, sai ma tura kai suke cikin wundo suna kallon daji kamar basa sauraran abunda muke fada. Bai daina magana ba, bai kuma hakura ba, shi dai a dole sai na ciko kudin motar nan.
Ya ce "Yarinya baki fito da sa'a ba, sa'ar kuwa ita ce, yau da kin shiga motar nan da Haj. Yalwa Gumel da kinga yadda ake taimako, ba cikon kudin mota ba ma kawai da mota zata saya miki kyauta. Ace kin yi sa'a kin hadu da Yusuf Gumael wato Barman Gumel kuma (special adviser) da kinga taimako. Haka kuma yau da kin hadu da Malam Abdul-Salam Mohd (M.D NPA) da bakin cikinki ya warke. Ko kuma Alh. Adam I.D Gumel (Sarkin yakin Gumel) ko kaninsa Alh. Nasir I.D Gumel. Ko kiyi kicibus da Alh. Muhammad Alkali (Sardaunan Gumel) ko matemakin gwamnan Jigawa wato Alh. Ahmad da kin warke. Wannan ina zano miki mazan fa kenan, a mata kuwa da kika hadu da Haj. Fatima da Haj. Rafi'atu matan Alh. Ahmad (depety Govern Jigawa State) ko Haj. Sadiya da Haj. Ummi matan Yusif Gumel wallahi ba tantama zasu biya miki kudin motar nan. Ko Allah Yasa ki hadu da Haj. Maryama I.D Gumel yau da kinji dadi. Da kin fito a sa'a yau a ce a motar nan akwai Haj. Hajara Adam I.D Gumel ko kanwarta Haj. Aisha Nasir I.D ko Haj. Mariya Nasir I.D Gumel da kin huta da takaicin kudin mota. Ke bari inyi miki dungurungun ki hadu da Haj. Binta da Binta matan Malam Abdul-Salam Mohd ko Haj. A'i uwar gidan Alh. Muntari dan Muloniya (darwaton Gumel) ke da kin zama abar kwatance da nunawa a tashar Gumel. Ni dai ina sauraronsa ina kuma kallon bakinsa yadda yake zaro magana baya gajiya, bai yi shiru ko na sakon daya ba tunda ya shiga motar magana yake kowa na sauraransa.
Na katse shi na ce "To tunda banyi katarin haduwa da wadannan bayin Allah ba, inci albarkacinsu mana ka yafe mun kudin motar. Ya zabura ya ce "A'a niba dan Gumel bane ni nan da kika ganni Bahadeje ne, baki kula da tsagun ba, ko baki ganni baki wulik ba? A samu Bagumule daya ya biya miki cikon kudin nan mana. Ko babu Bagumule a motar nan? Ya tambayi *yan motar, shiru babu wanda ya amsa masa. Ya ce "Kwarai da gaske ni fa nasan babu dan Gumel a motar nan kirarin da na yiwa Gamulawa da an samu wani ya tofa, to ke *yan mata yau kin fado motar *yan cirani, *yan kwadago, fatake ne daga kasuwa zuwa kasuwa. Ashe fa yau Laraba yau ne Kasuwar Gumel ta ke ci. Sai a lokacin wani daga cikin *yan motan ya tanka masa ya ce "Malam ka ishe mu da bara, har kana kiranmu fatake, ba muyi niyyar cika kudin motar ba, idan ba zaka yafe mata ba ka sauketa a inda kudinta ya kare. Direban ma ya tsoma baki ya ce da kwandantan "Abba dan Allah ka ishemu da magana, tun da a Doko kudinta zai kare sai mu sauketa kawai. Ni dai ina sauraransu, nayi mamakin irin wanan rashin tausayi da tsananin son kudi irin na direba, kwandasta da dukkan jama'ar da suke cikin motar.
Ana zuwa Doko, direban ya tsaya kwandasta ya bude mota ya ce "An zo Doko *yan mata anan kudin motarki ya kare, ba rabon ki je Gumel. Ki ga garin Sarki Amadu. Sai naji hawaye ya surnano min, takaici marar misaltuwa ya lullube zuciyata saboda ban je Gumel ba, amma nayi tawakkali na bawa zuciyata hakuri nayi addu'a Allah Ya sa nan ne yafi Alkhairi a gareni. Na sauko daga motar jikina sanyi kalau, suka ja motarsu suka tafi. Na sake saba jakar kayana a lokacin ana kwada rana mai zafi, ga yunwa da kishirwa ina ji. Na hango wasu Fulani masu siyar da fura da nono da *yan mata guda biyu suna sayar da abinci. Na karasa wajansu na gaishesu, saina zauna a kusa dasu. Naji dadin yadda suka kula ina jin yunwa, da kansu suka dama mun fura da nono suka miko min ruwan sha. *Yan matan ma suka zubomin wake da shinkafa na ci na koshi na musu addu'a Allah Ya biya musu bukatunsu, Allah Ya taimakesu kamar yadda suka taimake ni. Ina zaune a tsakiyarsu ina ta hira da su, daga baya ma muka juye Fulatanci da Fulanin har kusan magaruba, sannan suka tashi kowa zai kama hanyar gidansu. Nauyi da fargaba na kasa ce musu zan bisu rigarsu, ina kallonsu suka tafi suka barni. Masu wake da shinkafa ma suka tafi. Da gari yayi duhu shine na kutsa cikin garin Doko, ina tafiya na hangi fitilar *yar Hajja tana sayar da gyada, kwai da goro, ita da kwayenta samari da *yan mata suna wasanni shine na nufi wajansu na zauna a gefensu ina kallansu. Har Allah Ya kawo Suhaif yana rabon kwai ya hango ni. Ya zo ya tambayeni daga ina nake? Ba tare da na shirya karyar da zan yi ba, na bude bakina naji na ce masa daga Saudia aka kamoni kuma ban san kowa a Nigeria ba.
Dalilina kuwa don aji tausayina a taimakamin a rikeni. Saboda bana son a mayar dani garinmu. Ina son Musulmai, ina son addininsu, ina so kuma in sami ilimin addini sosai kafin in koma ga Iyayena, in basu hujja mai karfi yadda zasu yarda da ni su bar addininsu, su shigo nawa. Amma ina yi ina tsoron cutar da muyagun Matsafa nan za su yiwa al'ummar Musulmai a sanadiyyata. Da Suhaif yaji bayanina ya tausaya min ya kuma taimakeni ya kaini ga Iyayensa, suma mutanan arziki sun rike ni amana. Na sami ilimin addini mai yawa a garin nan, na karu da abubuwan da a da ban sansu ba. Na sake haddace Alkur'ani mai girma, na sake sanin Sunnonin Annabi Muhammad (S.A.W) da Hadisansa masu yawa. Hamma Huzaifa ne wanda muka shaku sosai, ya taimakeni akan addinina wanda daga baya shakuwarmu ta zama soyayya. Nayi takaicin rashin Huzaifa, na shiga kunci sosai dan ina kaunarsa, na kaddara cewa haka Allah Ya rubutomin na bawa zuciyata hakuri da dangana. Sai Allah Ya mayarmin da madadinsa Ya hadani da Suhaif. Tun sanda na hadu da Suhaif na ji raina na sonsa, da muka zauna da shi muka saba naga yana da kirki matuka kuma yana tsananin sona tsakani da Allah sai nima nake son sa. Babu abin da zan ce sai dai Allah Ya saka masa da alheri tunda tawa ta kare, Allah Ya bashi mata ta gari mai sonsa.
Dalilin da yasa jama'arku suka yi ta mutuwa aka ce nice nake kashesu kuma shine, idan baku manta ba na fada muku abinda Matsafan nan suka fada min cewar zan zamo abar tsana, abar gudu a cikin Musulmai har sai na gaji na bar addinin. Yadda suka yimin shine idan wani abu ya hada ni da mutum na rashin jituwa misali da farko Malam Nayaya ya ce yana sona kowa ma a makarantar yasan yana sona, ban tsane shi ba, saboda ina son duk wani Musulmi musamman Musulmi irin Malami wanda yasan ilimin addini, amma kuma gudun kada Matsafan nan su cuce shi shine yasa na guje shi. Da ya takura min da zancen yana sona, sai na fada masa yayi hakuri bana soyayya. A zatonsa da tunaninsa sai ya dauka wulakanci nayi masa irin na *yan mata, sai ya tsaneni kullum zagi da duka. Ban damu ba, a inda ya duke ni a wurin zanyi kuka na share hawayena, na kaddara a raina duk jarabawa ce daga Allah. A daran da zasu kasheshi wani ciwan kai mai tsanani ya kamani tun daga magaruba, na kasa sallar isha'i balle nayi addu'a idan zan kwanta, dan haka na kwanta da wuri saboda barcin da yake wartata mai nauyi ban san meyasa ba.
Mafarki abune daga Allah Ya ke saukowa bayinSa don Ya nuna musu wani abun da basu sani ba, ko wani albishir, ko gargadi akan wani mugun hali da suke aikatawa a doron kasa. A lokacin Annabawa kuwa ana saukowa Annabawa wahayi a cikin mafarki. Wani mafarkin kuwa daga shaidan yake, ko *yan tsubbu, Matsafa ko Aljanu. Yayin da wasu bayin Allah suke mafarki da Annabawa ko karatun Alkur'ani da massalatai wasu har aljanna Allah Yake nuna musu, su tashi daga barci suna masu godiya ga Allah da sadaka suna murna suna fadawa masoyansu, ana taya su murna.
Ni nawa mafarkin bala'i ne, abun bakin ciki ne da tashin hankali. Ina cikin wannan barci marar kan gado, sai naga Malam Nayaya a mafarki matsafa sun kamo shi sun daudaureshi kuma na ganni sanye da kaya irin nasu suna sanar dani cewa ga wuka da hannuna zan kashe shi. Amsar da na basu itace bazan kashe Malamaina ba. Ban ankara ba naga sun fadar dani kasa sun daure min hannaye suna gana min azaba. Babbansu ya fito dauke da wuka baiyi wata-wata ba ya sokawa Malam Nayaya wuka ya mutu. Na kwalla kara mai tsanani a lokacin na farka daga barci jikina na rawa, zuciyata cike da bakin ciki. Kwatsam sai da safe aka cemin ya mutu. Nayi kuka mai yawa, nayi takaici, amma babu wanda zan iya fadawa gaskiyar abun da ya faru, na dukufa da addu'a ba dare ba rana akan Allah Ya kare mu daga sharrinsu ni da *yan uwa Musulmai, amma duk ranar da Allah Ya yi wani zai mutu ta sanadiyyata gaba daya a wunin nakan kasa addu'a ko da na fara bakina yana yimin nauyi, idan na takura hakorana suna datse harshena. Bacci mai nauyin gaske ya hanani sukuni, dole na kwanta ba shiri, sai naga wanda zasu kashe a mafarki sun dauko shi sun zo sun kashe shi. Don haka a zaman makoki na fi kowa kuka da damuwa.
..... Tofa Matawata ta ce tana gaida Masoyanta da fatan suna cikin koshin lafiya, sai dai bata ji dadin abun da yake faruwa akan Iman ba..... Lolxx.
Ehem na fara tara *ya*ya, Junior ta ta haihu, zanso addu'arku akan su.. Nagode.
Reedwan Suraj Isma'il
*************** YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI
Dole in damu saboda nasan meye sanadin mutuwar tasu. Shi yasa nake kaffa-kaffa ko da Malamina ko a kawayena *yan ajinmu nake gudun hatsaniya ta hadamu, da zarar sun harzuka sai inyi ta basu hakuri, amma suki hakura lallai sai sun daga murya asan muna fada, rashin sani sai su zazzageni. Zasu kwanta da daddare lafiya zanyi mafarki an kashesu da safe za ace min sun mutu. Da naga anyi haka sau daya, sau biyu, kafin ayi na uku sai na hada kayana cikin dare zan gudu in bar garin. Niyyata kuwa inkaura dokar daji inyi rayuwa da namun daji in sun gaji dani su cinyeni. In shirya kayana in fito inyi ta tafiya, sai naji hankalina ya dauke in fadi in yi ta barci, sai in yi mafarkin matsafan sun daukoni aka sun dawo dani har dakina kan shinfidata. Ina farkawa daga barcin a shinfidata zan ganni, inyi ta mamaki. Mun yi haka dasu yafi a kirga. Da ga karshe dole na hakura na zauna. Amma basu dai na hadani fada da jama'a ba suna kashesu cikin dare. Allah cikin ikonSa jama'a basu gane ba har sai da Maimuna *yar garinmu tazo ta tona min asiri. Ta fadi gaskiya bata yi karya ba, ta sanni sosai duk da ba kawarta ba ce kawar kannen Hamma Huzaifa ce su Bilkisu Islamiyyarsu daya.
Bayan na sha kuka da takaicin tona asirin data yi min, sai bacci da ciwon kai ya kamani. Hakika gangar jikina ce a kwance ruhina ya tafi wajansu, ranar raina a bace ina ta zaginsu akan su rabu dani, su rabu da jama'ata. Nayi-nayi inyi addu'a Allah bai bani ikon yi ba, ina ji ina gani suka kashe Maimuna. Su Baba, su Goggo a kaina suna tashina ban farka ba sai da kurwata ta dawo, na farka daman ba bacci bane. Ina tashi kuwa na samu labarin Maimuna ta mutu, daman ko basu koreni ba dole in kori kaina.
Bayan na tafi samari suka bini zasu dake ni, to tun daga nan na rasa hankalina, suka turani tsohon ginin gidan Mahaukacin nan na shiga. Sun sami yadda suke so, Musulmai sun koreni, na zama ta su kenan. Na zamo a zaune kawai nake sun zagayeni babu ci babu sha, babu alwala bare salla, bana magana balle inyi addu'a. Gagarumar liyafa suka hada cikin dare a cikin gidan don murna, yau na zama tasu, yau sunci galaba kaina. Mutanen da nake so wato Musulmi sun kore ni daga cikinsu kwata-kwata. Ta kai ta kawo na ma daina ganinsu a mafarki ido biyu nake ganinsu. Suhaif ya ga jini an diddiga tun daga kofar gidan har cikin dakin dana ke, su suka disa akan takalmana, suka daura takalmi daya a akan saman rufin dakin yana diga, daya kuma yashe a tsakar gida da jini a jikinsa. Sunyi haka ne don Suhaif ya gani ya shaida ni mayya ce, suka daura min jajayen kyalle a jikina, sai daga baya na ciccire.
Suna fakon Suhaif sosai, sun kudiri niyyar sai sun kashe shi, saboda shine kadai ya rage mai takura musu da addu'a, shine bai tsane ni ba, bai rabu da zuwa inda nake ba. Babu makawa sun gama shirye-shiryen kashe shi tsaf a cikin daren dana ce masa ya kwana yana sallah yana addu'a kada yayi bacci. Da suka je zasu kashe shi suka kasa shiga inda yake balle su ganshi su kashe shi, sai suka kufula a daren kwana suka yi suna gana min azaba. Ban damu ba tun da mutuwa nake nema.
Babu wadanda suka jawo min wannan matsananciyar rayuwa sai Mahaifana, tun farko da na hadu da Matsafan da sun hadu sun taru sun rabani dasu da karfin addu'a da haka bata faru ba, duk da nasan kaddara ce. Amma kowannensu addininshi daban, wannan yana jin haushin wannan, idan ya kawo mai addu'arsa yana ganin kara min ciwo ake, kawai sai rigima ta harde su, daga karshe suka kyaleni da ciwo yana bibiyata har girmana. Duk lokacin da waninku ya hadu da dangina ku shaida musu abubuwan da suka faru dani har izuwa mutuwata. Nasihata zuwa ga Mahaifana itace su dawo su rungumi addinin Musulunci, suma su mutu a cikinsa kamar yadda nima zan mutu Musulma.
Iman ta rushe da kuka mai tsanani sai jama'a da dama a wajen tausayinta yasa su kuka suma. Cikin kuka ta dukar da kai kasa ta ce "Na gama labarina ku kasheni kamar yadda ku kayi alkawari, na gaji da rayuwar wulakanci da kyama da tsangwama a cikin *yan uwana. Kafin wani ya bude baki yayi magana, ganin Iman akayi ta daka tsalle ta fadi can gefe kamar wani ne yayi ball da ita. Sai ta tashi a gigice tana kallon wani gefe tana magana kamar a kwai wadanda take gani mutane basa gani. Cikin harshen Turanci take magana take cewa "Ku rabu dani, karku matso kusa dani, baku zaku kashe ni ba, ku bar *yan uwana Musulmai su kashe ni. Suhaif yana jin haka ya tashi da gudu ya fisgota ya kawota tsakiyar Malaman yana fassara musu abunda yaji tana fada da Hausa. Sai suka gane cewar matsafan sun zo su kasheta saboda ta tona musu asiri. Yanayin halin da suka lura Iman na ciki shine matsafan suna rike da ita suna shirin su kasheta.
A gigice Suhai yake janta yana so ya kwace ta daga hannun matsafan duk da baya ganinsu yasan