Showing 1 words to 3000 words out of 178828 words

Chapter 1 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt

18 Dec 2025

1428

[10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=ems_copy_t



*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)


NA


MAMAN AFRAH


. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 1️⃣

*JAN HANKALI GA MASU BIBIYAR LABARIN NAN*

*Labari ne da yake ɗauke da ɓangare uku, kowane ɓangare akwai muhimmiyar rawar da zai *taka. Labarin manyan taurarin cikin littafin guda uku wacce kowacce ɓangaren ta akwai tarin abubuwan da za mu yi nutso a ciki, muna da labarin ZALIKA, akwai labarin SADIYA, sannan akwai labarin JIDDA sai dai in ce ku biyo ni sannu a hakali domin jin da mai labaran nasu zai zo NGD* .

Da sallama Malam Bala ya shigo gidan nasa, wanda yake sallamar kamar zai tsaga gidan, Mama Habiba da take kwalfar ruwa ta ɗago tana amsa masa a inda ya mata kallo ɗaya ya doka uban tsaki tare da ɗauke kai.

Ƴan matan gidan ya shiga kwaɗawa kira ɗaya bayan ɗaya, kowacce tana ɗakin nasu da aka warr musu a gidan, jin kiran Aisha ta yatsina fuska ta ce


"To fa! Watan cin ubanmu ya kama mun shiga uku yanzu Baba zai fara faɗan nashi bari mu je mu ji da mai ya zo"

Malika ta taɓe baki tare da ci gaba da danna waya, haka suka fito sumi-sumi kowacce ta zo a ɗarare ta zauna a kan tabarmar gabansa ganin ya koma kan kujerar plastic ya zauna.

Wani ƙullin magani ya fito daga cikin babbar rigarsa ƙullin ƙato ne ya ce

"Kai ni dai na shiga uku! Allah ka bani ɗa namiji ko kangararre ne!" Mama Habiba da ta ji sautin maganrsa ya sosa ranta duk da ba yau ne ta fara jin wannan furucin nasa ba, amma dai kullum furucin yana zama tamkar sabo ne a kunnuwan ta. Gabaɗaya ƴan mata sai kowacce ta sunkuyar da kai kasancewar daga su har iyayansu suna matuƙar tsoron Baba, saboda ba ya ragawa kowa. Cikin sanyin murya Mama Habiba ta ce

"Haba Malam ka daina wannan maganar wallahi babu daɗin sauraro, haba kowane jinsi ma ai kyauta ce ta ...

Wata tsawa da ya doka mata ya sanya sauran maganar da ta guntso za ta amaryar masa ta haɗiye, a fusace ya ce

"Habiba ina miki kashedi koyaushe a kan shiga sabgata da ƴaƴana bakya ji ko? Mai ya sa kike saka baki a abin da babu ruwanki? Ko namijin da na ce a bani ke na tambaya ki ban?" Kai ta shiga girgizawa ya ci gaba da faɗin

"To ahir ɗinki, Allah na ce ya bani ɗa namiji ko kangararre ne ba ke ba, ai ko maganar ce ki bari masu haihuwa su faɗa amma ke da baki da ko ƙuda a gidan ina ruwanki" Kai ta sunkuyar idanunta suna kawo ƙwalla tana jin zafi da ɗacin gorin Malam duk da ta san Allah ne yake bada haihuwa kuma shi yake hanawa ta yi imani da hakan amma gorin mijinta yana ci mata tuwo a ƙwarya, saboda tana ganin da a ce shi ne ba ya haihuwa ko a haka za su dawwama to ba za ta taɓa masa gori ba kuma za ta rungumi ƙaddara ta zauna da shi har ƙarshen bugun numfashin ta, amma shi ban da kishiyoyi uku da ya mata har sai yana mata bita da ƙulli dulan kabarin kishiya.

Mama Talatuwa da ta firo daga ɗakinta jin abin da yake faruwa duk da ba wannan ne karon farko ba, amma koyaushe idan yana yi wa Habiba cin kashin nan tana jin babu daɗi a ranta, haka ta fito tana nufar wajen da Habibar take don ta bata baki, sai dai tana dab da zuwa ta tsumayi maganar Malam yana cewa

"To uwar ƴan tausayi me raunatacciyar zuciya, ke irin kishin nan ma na mata bakya yi, bakya jin daɗi mijin ki ya duzga kishiyarki, sai ki yi kamar wanda aka taɓa wata ƴar uwarki ta jini" Juyowa ta yi cikin sanyin murya ta ce

"Haba Malam ai duk mace mai hankali ba za ta so ta ji daɗin don mijin ta yana tozarta kishiyarta ba, domin rayuwar duniya yau gare ka ne gobe ga waninka, kenan ni ma jifa zai iya zuwa kaina ko in ce... Hannun da ya ɗaga mata ya sa ta yi shiru ya ce

"Ki ciko bokiti da ruwa ki kawo min" Da to ta amsa tana kallon Habiba da tausayawa ta nufi wajen ruwan za ta ɗakko, Mama Habiba kuwa sai ta kama hanyar ɗakin ta tana jin tamkar an ajiye mata dutsi a ƙirjinta na gorin haihuwar nan kasancewar ta mace mai son yara sai kuma ƙaddararta ta kasance ta rashin haihuwa, sannan mijin ta ba ya tausaya mata a kan rashin haihuwar sai dai ya yi ta yada mata baƙar magana tamkar ita ta hana kanta haihuwar.

Mama Talatuwa bokitin ta ɗakko me cike da ruwa ta kawo gabansa ta ajiye tana kallon ƴan matan yadda kowacce fuskarta cike da damuwa. Ledar ya since ya zazzage maganin kofuna guda biyu ya sa Hafsa ta ɗakko ya gauraya ya cika kofin ya miƙawa Hafsa ya ce

"Karɓi ki kafa kai ki shanye ki miƙo min, ai ni zama bai ganni ba wallahi tun da na ajiye ƴanmata kamarku a gida babu mashinshini, dole na nemi maganin farin jini ko a samu masu kwasa in kawar da ku in huta da raina, amma yara sai shagen baƙin jini, ni dai ba ni kuka biyo ba sai dai iyayenku mata tun da ni dai gashi nan sai dai na rufe ƙofa wato na auri mata huɗu, da ina da baƙin jini wa zai aureni"? Ya faɗa yana musu wani kallo ba yabo ba fallasa kowacce kai ta sunkuyar suna jin babu daɗi a ransu tun da cikin su babu wacce ta haura shekara ashin wasu ma sha takwas suke amma saboda ya ƙwallfa rai a kan su ko kaɗan ya hana kansa sukuni.

Hafsa da kurɓa ɗaya ta yi wa maganin ta ji wani uban ɗaci har tsakar kanta, da hanzari ta cire kofin daga bakinta tana mayar da kallon ta kan mahaifin ta cike da tsoro, a fusace ya ce

"Kin shanye kin miƙo kofin ko kuwa" Cike da tsoro ta ce

"Baba wallahi maganin nan ɗaci ne da shi, na jiya ma da na sha gudawa ya sakani" Ta faɗa tana kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka.

Kafin Baba ya furta wani abu Malika ta yi karaf ta ce

"Wallahi Baba ko ni jiya wanda ka bamu da daddare cikina ya yi ta ciwo, kuma ma fa Baba shan magani ba bisa ƙa,ida ba yana da haɗari ga lafiyar jiki, sannan magungunan nan masu ɗaci idan ba likita ko wani masani ne ya bayar ba yawan shan masu ɗacin nan ba bisa ƙa,ida ba yana iya sakawa mutum ciwon hanta, idan akwai sinadarai masu illa lalata hanta ko ƙoda yake, duk da wasu magungunan masu inganci suna da tasiri in an yi amfani da su bisa ƙa,ida... Hannun da Baba ya ɗaga mata ne ya dakatar da ita daga ƙarasa maganar yana nuna su da yatsa ya ce

"Ba ɗaci ba ko maɗaci ne kan ɗaci sai kun sha maganin farin jinin samarin nan, ina zan iya duka mata kun cika min gida, shiga goma zan yi gidan nan sai gabama ya faɗi in na ganku, kowacce ya ci a ce tana gidan mijin ta amma ƴaƴa shida duka mata kuma ɗaya na aurar haba kamar dai wanda aka mini baki, ai ina roƙon Allah ya bani ɗa namiji duk lalacewar namiji ka amfane shi, duk kangararsa wataran zai maka magani amma mace fa?" Ya faɗa yana bin su da kallo, Mama Talatu da take gefe tsaye kamar mai jiran tsammani don tana tsoron ta bar wajen ya ce ta raina shi, cikin sanyin hali da na muryarta ta ce

"Haba Malam don girman Allah ka daina wannan maganar, kowane ɗa yana da ranarsa, kawai mutum ya yi addu'ar Allah bashi na gari sannan ya nema musu shiriya da kuma saka musu albarka, wani sa'in mace ma ta fi wani namijin jin ƙai da taimakon, amma kana maganar kangararran ɗa to ta ina zai tallafa maka ɗin tun da a kangare yake? Mace ma tana da tata ranar kuma wasu ma suna nan suna neman haihuwa ido rufe amma bai kamta kai da Allah ya azurtaka da su kake wannan furu... Tsaye ya miƙe a zafafe ya nuna Mama Talatu da yatsa ya ce

"Keee! Kin san dai babu abin da za ki nuna mini na sanin abin da ya dace ko wanda ya kamata saboda haka kar na ƙara jin bakin ki" Yana kaiwa nan ya koma ya zauna.

Kallo ɗaya ya yi wa Hafsa da ta kafa kofin sai da ta shanye tasss ta miƙa masa ya kwalfo ya ba Malika sai da ta runtse ido ta shanye ta miƙa masa kofin, kowa ya sha saura Arfat da ya miƙa mata tana yin kurɓa ɗaya amai ya yunƙuro ta da sauri ta cire kofin a bakinta tana saka hannu ya toshe bakin, jin aman yan barazanar zubowa ta ajiye kofin a wajen ta miƙe a hanzarce ta bar wajen sai da ta gama aman ta dawo Baba yana sababi ya ce

"Wato ke kece shafaffiya da mai, kullum in zan bayar da magani ke ce mai yi wa mutane amai, uwarki ta ɗaure miki tsantsa a kan cewa wai tu tana goyonki kike amayar da magani ko da na asibiti ne ko ɗura miki aka yi sai ya dawo, ɗauke wannan maganin ki shanye kuma wallahi kika sake kika amayar sai na lahira ya fiki jin daɗi"

Haka ta shanye maganin tana dantse bakin ta ganin bata yi aman ba.

Baki ya buɗe zai yi magana amma jin kuka daga zauren ƙofar gida ya sa ya dakata, sai kuma suka fara jin wasu muryoyi ana faɗin

"Ta ɓata jikin ta" Shigowar Aisha gidan tana kuka, kowa ya bi ta da kallo, Mama Talatu ce ta kalle ta da alhini ta ce

"Aisha kukan me kike mai aka miki?" Aisha wacce ta ja ƙasan hijabin ta ta rufe fuskarta hannun ta riƙe da jakar buhu irin wacce ake ɗinkawa da buhu, sanye take da farar riga da wandon uniform sai farin hijbi wanda aka masa tattara da koren yadi a ƙasan ƙafar wandon ma akwai koren, bata ba Mama Talatu amsa ba, cike da tsawa Baba ya ce


"Kee! Kukan uban me kike?" Da sauri ta cire hijabin fuskarta saboda ta cikin yadin hijabin nata wanda bashi da kauri kasancewar yadin ba mai tsada ba ne, ta haka ta shigo gidan sai dai bata kalli saitin inda su Baban suke ba shi ya sa bata san yana nan ba, ita kuma Mama Talatu da yake daga nan gefen da take tsaye kusa da hanyar zauren ne shi ya sa Aishar ta ganta.

Mama Bilki wacce take ɗaki tana jin kaf abin da yake wakana a gidan, tun da in da sabo sun saba da wannn halayyar ta gidan duk da kasancewar kowa a gidan shi yake nemawa kansa abincin rana damkarin kumallon safe idan tuwo bai kwana ba, domin iya tuwon dare ne kawai Malam ɗin yake bayarwa a gidan shi ma wataran idan ya hana kuɗin kayan miya sai dai wacce girkin ta ne ta siya ta yi haka za a yi miyar babu maggi sai dai kowa in an zuba masa ya nemi maggi dunƙule ya barbaɗa, abincin rana kuma sai ranar da ya ga dama jifa-jifa yake bayarwa.

Ba wai don bashi da halin wadata su ba, sai don sarewa irin tasa shi a tashi fatawar ƴaƴa mata kawai da ɗakin miji suka dace domin mijin ne ya dace ya ɗauki ɗawainiyar mace, shi ya sa yake ta fafutukar ya ga ya aurar da su sun bar gabansa, babu tunanin samun nagartaccen miji. Komai sai dai uwa ta ciru ta ƙullu ta nemawa ƴarta ko su ƴaƴan su nema shi abu ɗaya yake da buri kuma yake fata shi ne ya haifi ɗa namiji, a ganinsa idan namiji ne zai taya shi ɗaukan ɗawainiya amma mace yana ganin ita sai dai ya nemo ya basu ba ya tunanin haƙƙi ne Allah ya ɗora masa.

Aisha cike da jin nauyin mahaifinta kuma tana jin kunya sai ta kasa faɗa masa dalilin kukan nata, ƙara zaburowa ya yi yana kumfar baki sai ga Mama Bilki ta fito daga ɗaki ta ce

"Wai mene ne kike neman mayarwa da mutane gidan makoki, ke ga mai arahar hawaye?" Jin tsawar da Mama Bilki ta mata da kuma wacce Baban ya yi sai ta sunkuyar da kai hawayen yana zuba ta ce

"Wai don na ɓaci shi ne ƴan ajinmu suke min dariya" Ta faɗa tana jin ɗacin abin a ranta, sai lokacin ƴanmatan kowacce ta mayar da kallonta jikin Aisha, domin sun fahimci matsalar shi kuma Baba bai ma gane inda maganar ta dosa ba hakan ya sa ya ce

"Ba dole suke miki dariya ba tun da sun ga sakarya, ke da girmanki amma kuka ba ya miki wahala" Mama Talatu cike da tausayin Aishar ta ce

"Haba Aisha ai da kin saka ƙunzugu a jikin ki, amma kya tafi cikin mutane a haka kuma kin san dai ƙawaye da sheƙiyanci" Wani kallo Mama Bilki ta jefawa Mama Talatu ta ce

"Sai aka ce miki bata saka tsumma ba, to ta saka, zo ki wuce ki je ki gyara jikin ki" Mama Bilki ta faɗa rai a ɓace saboda gabaɗaya haushi ta ji an tsinka ƴarta, Aisha tana fara tafiya kowa ya juya ya bi bayanta fa kallo, ashe ta saka wani ɗankwalin atamfa ta ɗaura a ƙugunta hakan ya sa ba a ganin ɓacin da jikin nata ya yi.

Mama Bilki cike da takaici ta ce

"Ai wallahi sha'anin gidan nan sai a hankali wallahi, a ce wai sunan yara suna da uba amma kamar marayu, a ce ubansu yana da hali amma ba zai ɗauki ɗawainiyarsu ba sai dai ya ce kowacce ta ɗauki ɗawainiyar kanta, to ko namiji ne aka ce ya ɗauki ɗawainiyar kansa ai an buɗe masa hanyar yin abin da ya ga dama varw kuma ƴa mace da ake son killace ta a yi takatsantsan da rayuwar ...

Kafin ta kai aya Baba ya tari nunfashin ta da faɗin

"Sannu uwar kinibibi, yanzu saboda rashin godiyar Allah sai aka ce komai sai uba ya yi wa yara? Ita uwarsu mene ne amfaninta? Kun mata kun ɗauki namiji kamar bawa komai shi zai yi a gida ba za ku taimaka ba, in banda son kai yanzu audugar wata-wata ma ni zan saya musu?" Mama Talatu ta ce

"Malam ai ba a ce wai lallai sai ka saya auduga ba amma akwai wasu ɗawainiyoyin da dan har ka ɗauke musu to zai zamana kuɗin da za su yi ɗawainiyar sai su sayi audugar da ƙananun abubuwan, amma a ce mace budurwa ita za ta yi wa kanta komai, hatta omon wanki da sabulu mai na shafawa ita za ta yi kai hatta ciyar da kanta ita za ta yi haba malam Allah ne fa ya ɗora maka nauyin iyalinka daga kan ƴaƴa da mata...

Wata harara da yakr jifanta da ita ya sa ta yi shiru ya ce

"Wato in mutu da ɗawainiya ni kullum in ƙare a tsaye? Ai shi ya sa da a ce maza na haifa da tuni ina ɗaki ina bacci da munshari su kuma suna can suna nema, in za ku kama sana,a kowa tashi ta fishshe shi.

Mama Sa'ade ce ta fito daga ɗaki tana hamma ta ce

"Ai lamarin gidan nan sai addu'a amma dai kam ana fama"

Baba kallon ƴanmatan da suke gabansa ya yi ya ce

"Kai ku tashi ku bani waje kowacce ta bar wajen nan, kuma maganin da kuka sha na farin jini duk wacce ta amayar min shi wallahi sai ranta ya ɓaci, mu ga zuwa gobe ko maganin zai yi aiki a fara min kayin neman aurenku" Ya faɗa yana miƙewa tsaye ya gyara rigarsa ya juya ya nufi hanyar ɗakinsa yana ta ƙananan maganganu da babu wanda ya ji mai yake cewa amma da alama faɗa ne yake.

Mama Talatu ce ta ɗan matsa kusa da Mama Bilki ta ce

"Bilki don Allah yarinyar nan ki saya mata audugar mata, wallahi babu daɗi jinin al'ada yake kunyata mace kaima babba da yaya bare kuma yaro duk sai mutum ya ji ya tozarta duk ya rasa sukuni, in har baka kintsa kanka ba sai kake ta tsarguwa ko ka ɓaci... Kafin ta ƙarasa Mama Bilki ta ɗaga mata hannu tana faɗin


"Talatu bana son iyayi, idan ba za ta saka tsumma ba to ta zauna a haka, ita ba shegen girman kai ba idan aka ce ta fita waje ta soya awara ta siyar sai ta ƙi wai bata son talla, waye ubanta? Uban nata da ba ya iya ɗaukan ɗawainiyarta tun da ba za ta zage ta nema ba ai ta yi ta ganin takaici" Tana faɗar haka ta juya ta kama hanyar ɗakinta.

Mama Sa'ade baki ta taɓe ta juya ta shige nata ɗakin, Mama Takatu a zuciyarta ta ce


'Wannan rayuwa ban san ina za ta je da mu ba, duk wanda ya ce ƴa mace ta ɗauki ɗawainiyar kanta ai hanyar lalacewa ya nuna mata, yanzu a ce uwa ba za ta siyawa ƴarta mace auduga ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login