Showing 9001 words to 12000 words out of 178828 words
Chapter 4 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
bai ma san sunanta ba abu ɗaya kawai ya sani shi ne saboda ita ya fito daga motar. Direban ne ya buɗe ya fito, cikin hanzari ya gewayo inda Ibrahim ɗin yake cike da girmamawa ya ce
"Yallaɓai kana buƙatar wani abu ne?" Ɗan shiru ya yi kafin daga bisani ya ce
"Kawai na ga baka kyautawa yarinyar can ba ne, kuma na ga ita ko uffan bata ce maka ba" Cike da alhini direban ya ce
"Wallahi yallaɓai ta san darajar mutane, duk da na yi abin ne cikin rashin sani kuma dama ɗan adama ajizi ne amma sai na ji ko kaɗan ban kyauta mata ba" Iska ya huro daga bakinsa yana sanya haƙorin gaba na cilin bakinsa ya dantse leɓansa na ƙasa, idanu ya mayar hanyar da Jiddar ta yi yana iya hango gidan da ta shiga daga can gefe wasu gidaje da suke a jere, sai ya ɗan jujjuya kamar mai neman wani abu, sai kuma ya kama ƙofar zai shige motar.
Aliya kuwa da take jin duk kan motsinsa tamkar da bugun zuciyarta yake, hakan ya sa ta fara tunanin ita yake nema, bata yi ƙasa a gwiwa ba ta fara ƙoƙarin tsallakowa, garin sauri har wata mota ta kusa kashe mata ƙafafu, amma hankalin ta ya yi gaba, tana fatan wannan mai kuɗin ya zamana cikar burinta da kuma mafarkinta da na mahaifiyarta, don yanzu ne take ganin za ta cika burin kyawun da Allah ya bata.
Garin sauri har harɗewa take, sai gata ta ƙaraso wajen a 360, Ibrahim ya ja ƙofar yana shirin rufewa don direban tuni ya shige mazaunin direba, kawai sai ya ga mace kamar an jefo ta, tana zuwa ta kama hannun ƙofar motar ta ce
"Gani" Cike da mamaki yake bin ta da kallon rashin fahimta, kunnuwansa suna dawo masa da sautin furucin da ta yi ɗazu tun daga kan ashar da kuma cin mutuncin da ta yi wa direbansa, cike da takaici ya ce
"Wa yake neman ki?" Inda-inda ta fara jin tambayar da ya mata, rai ya haɗe ya ce
"Dalla matsa zan rufe mota" Da baya ta ja tana jin ƙamshin turarensa na masu aji, ya kaure ko ina na mashaƙar numfashin ta, ba ma wannan ba tsananin kyau da farin da yake da shi gashi kuma a gefe ɗaya ɗan gayu ne wannan ne abin da ya damfaru a zuciyarta, tana jin inama wannan ya zama mallakin ta tabbas da ta huta, babu ita babu kukan muni ko talaucin miji, don ta raɗawa zuciyarta wannan shi ne mijon da ake kan yayi, kuma shi ne wanda za a yi ta yayi har abada!.
MAMAN AFRAH
09025576222
[10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/B6ZgynXRCc3LWNggTkzg7X
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE4️⃣
IBRAHIM
Yana gama rufe ƙofar ya ba direban umarnin su tafi, jan motar direban ya yi suka ƙarasa ƙofar tafkeken get ɗin kamfanin yana zuwa ya danna horn aka buɗe musu, ya cilla hancin motar cikin get ɗin.
Aliya da take tsaye a wajen kamar an dasa ta, idanunta ƙurrr a kan motar da take sheƙi tana ɗaukan idon sabunta, har suka shiga bata ɗauke idanunta ba, sai da ta ga an rufo get ɗin sannan ne ta dawo hayyacin ta, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, tana rayawa a zuciyarta cewa tabbas idan da rai da rabo ta ci alwashin mallakar wannan kyakkyawar halittar inda kuma take ganin za ta huta domin muddin ta auri wannan ta yi ban kwana da wata kalma wai wahala ko rashin kuɗi. Idanu ta lunshe tana hango kyakkyawan farin hannunsa mai ɗaure da tsadadden agogo a idon zuciyarta, tana iya hango yadda kwantaccen gashin hannun yake a jikin hannun yanayin fatarsa kaɗai tamkar wanda ba a Nigeri'a yake rayuwa ba, bata san lokacin da wani murmushi ya suɓuce mata ba don har ta fara hango irin soyayya da kulawar da za ta samu idan suka mallaki juna a matsayin ma'aurata.
Jidda kuwa lokacin da ta ƙarasa gida da sallama ta shiga, amma maimakon Umma ta amsa mata sai ta mata banza, sai da ta yi sau uku amma Umma ko ɗagowa bata yi ta kalle ta ba, bare ta saka ran za ta amsa mata, hakan ya sa cikin sanyin jiki ta shiga gidan tare da nufar ɗakin nasu don ta sauya kayan ta san matuƙar ta tsaya jiran sai Umma ta amsa mata sallama to har rana ta faɗa bata samu hakan ba. Gashi kuma tana son ta je kar a shiga jarabawa.
Tana shiga ɗakin ta nufi wajen jakar kayanta, dakyar ta ɗakko wata doguwar rigar atamfa roba ta saka duk atamfar ta koɗe, amma a haka ta saka saboda duk kayan nata idan Abba ya ɗinka musu Umma take ƙwace nata ta bayar sai ta sayi mai araha ta bata wani lokacin ma sai ta hanata mai arahar, shi kuma Abba da yake ba a gidan yake wuni ba kullum yana kasuwa ba sanin mai yake faruwa yake yi ba. Hijabi ta ɗauka ta saka shi ma duk ya ɗan yi fari, kayan ta mayar ta rataya a saman ƙofa a cewarta idan ta dawo daga makaranta sai ta wanke tun da yau jarabawa biyu za su yi.
Fitowa ta yi da jakarta a hannu, ganin Umma tana zuba ruwa a buta, ta ce
"Sai mun dawo Umma" Wata uwar harara Umma ta jefa mata, da ba za ta yi magana ba ma sai dai ta ce
"Ko ki dawo ko ki dawwama a can duk uwar ubansu ɗaya" Jikin Jidda sanyi ya yi hakan ya sa ta kalli Ummar kamar za ta yi kuka duk da wannan kalamai ne wanda ta saba jin su amma a koyaushe aka mata su sai ta ji su tamkar sabbi ne dal a leda aka buɗe, suna zame mata sababbi a koyaushe domin kalamai ne mararsa daɗi ƙiri-ƙiri ake nuna maka an tsane ka.
Ganin yanayin da Jidda ta shiga Umma ta ce
"To baƙa mai baƙar zuciya, kun ƙura min ido ni kar ki cinye ni kurwata kurrr, ni wallahi ban san dalilin da mutum zai ɗakko bare ya kawo cilin iyalinsa ba, ina dalili kawai a ɗakko mana annoba a kawo mana gida shekara da shekaru, ni yanzu ban ma san ranar da zamanki a gidan nan zai yanke ba, to wannan abu baƙiƙƙirin hanci kamar ƙofar gari abu babu fasali ta ko ina wane namijin ne ,ai kwasa? Tun da dai aure shi ne mafita ɗaya da za ki bar mana gida tun da babu dangin iya bare na Baba, babu inda za a kai ki ko ki raɓa mu ɗin dai mu ne ƙaryar taki, amma wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, dole idan kuka ƙarasa makarantar nan tun da yanzu jarabawa ta rage idan baki samu mashinshini ba ko sadaka ce ba bayar da ke ko ga ladanin masallaci ne" Umma ta faɗa tana tashi tsaye daga sunkuyon da ta yi tana zuba ruwan a buta.
Jiki sanyi ƙalau Jidda ta juya tana ɗaga ƙafa kamar an mata dabaibayi a ƙafafu, fitowa ta yi daga gidan tana ɗaga ƙafa ta kamo hanya fito da wayarta keypad ta yi daga jaka ta duba ta ga lokaci ya kusa tana fatan kar a samu goslow a hanya.
Hango Aliya tsaye idanu a rufe ya bata mamaki, tana ƙarasowa ta ce
"Aliya lafiyarki kuwa?" Da sauri Aliya da idanunta suke rufe babu abin da take hangowa sai gasu nan sun yi aure da wannan kyakkyawan matashin tana cikin daula tana wulaƙanta ƴan aiki da kuma dangi ƴan uwa, hatta Jidda sai da ta ganta ta zo gidanta tana saka masu tsaron ƙofa su yi waje da ita wai bata santa ba.
Yatsina fuska Aliya ta yj lokacin da ta buɗe idanun, a maimakon ma ta ba Jidda amsa sai ta juya ta fara tafiya, ita Jiddar sai ta take mata baya suka ƙarasa bakin titin, napep suka tsayar suka shiga. Sa'adatu Rimi suka nufa domin a can ne suke karatun N.C.E suna shekararsu ta ƙarshe saura jarabawa biyu ma su kammala karatunsu.
Lokacin da suka tashi ƙarfe biyu na rana ne, lokacin rana ta take, dakyar suka samu napep ɗin, sai dai kuɗin da ya yanka musu na Jidda naira hamsin bata cika ba hakan ya sa ta nemi alfarmar ya rage mata amma ya ce ba zai rage ba saboda shi ma ba ruwa yake zubawa a napep ɗin ba mai yake zubawa, suka tsaya a kan cewa idan an kusa zuwa za ta sauka haka ta amince. A daidai wani gidan mai ya sauke Jidda saboda har rance ta ce Aliya ta bata amma ta ƙi bata kuma akwai kuɗin a wajen Aliyar. Tana ji tana gani haka ta sauka da ranar nan ga yunwa da suka kwaso.
Aliya har da wani taɓe baki ta yi da sakin murmushin mugunta, dama da a tafiya ne sai ta ranta mata ko don saboda ta bata amsar exam tun da idan basu tafi tare ba sun zauna a kujera ɗaya ba sai dai ta bayar da takardar a haka ba tare da ta rubuta komai ba, kasancewar banda dusa babu komai a kan nata hasali ma bata karatun shiririta kawai take a makarantar da biyewa ƙawaye ƴan ƙarya, ita kuma Jidda karatun take yi gata da ƙoƙari kanta yana ja sosai da sosai saboda tana da mayat da hankali.
Tafiya take har ta ƙaraso wajen kamfanin simintin nan nasu Ibrahim, tana tafiya sai gumi ne kwance a fuskarta kasancewar ranar da ta take, Ibrahim wanda tun zuwansu da direban ya ce direban ya tafi da motar gida, saboda da Daddy za su tafi gida, ƙarfe biyu da rabi suka tashi Daddy da Ibrahim ne a baya sai direba yana jan su, mai gadin ƙofar kamfanin ya buɗe musu get suka fito, Ibrahim wanda tun bayan zuwansa kamfanin yake ta tunanin Jidda duk da bai san sunanta ba amma tabbas ya yaba da hankali da tunaninsa yarinyar ta birge shi sosai.
Suna fitowa kamar an ce ya ɗago fuskarsa sai kawai ya sauke a kan Jidda wacce take tafiya cikin natsuwa kanta a ƙasa, gabaɗaya ya mayar da kallonsa kwacakom kanta, yana ganin yadda hijabin ya mata kyau, shi dama yana son ya ga mace tana suturta jikinta, tambayar zuciyarsa ya fara yi yana cewa
'Ko ina fitsararriyar ƙawar nan tata, wacce bata san darajar ɗan adam ba, wannan ko kaɗan baku dace da zama ƙawaye ba, ana cewa sai hali ya zo ɗaya ake ƙawance amma dai ku kun sha bam-bam a halayya' Ya faɗa yana bin bayanta da kallon don lokacin ta gifta, ta kama hanyar gidan da ya ga ta shiga lokacin da ta tafi da safe, kuma yana ji a jikinsa inda ya ga ta shiga da safen nan ne gidansu, ko yanzu ya so a ce babu Daddy da sai ya tambaye ta ko da sunanta ne.
Direba yana ɗan waige-waige domin zai haura hancin motar saman titi, a daidai nan Daddy ya lura da Ibrahim ya juya bayansa yana kallon waje daga cikin motar, a nutse Daddy ya ce
"Mu'azzam" Amma da yake ya yi nisa bai san Daddy ya kira shi ba, duk da suna zaune a kusa da juna, sai da Daddy ya maimaita ya ce
"Mu'azzam" Ya faɗa yana ɗan taɓa shi, sannan ne Ibrahim ya juyo da sauri yana ɗan murmushi ya ce
"Na'am Daddy" Daddy da ɗan mamaki a fuskarsa ya mayar da hankalin wajen da Ibrahim ɗin yake kallo a ƙoƙarinsa na ganin ya hangi abin da ya ɗaukewa tilon ɗan nasa hankali. Sai dai iya ganinsa bai ga kowa ba, saboda wajen akwai mutane kowa yana dabgar gabansa sannna ita wacce Ibrahim ɗin yake kallo wato Jidda ta riga ta miƙe ta yi ɗan nisan da Daddy ba zai fahimci ita Ibrahim yake kallo ba, kuma ko da a ce ya hango ta ba lallai ya kawo cewa ita ɗan nasa yake kallo ba kasancewar ba halayyar Ibrahim ɗin ba ce kallon mata don su a halin da ake ciki ma yanzu burin su bai wuce ya fitar da mata su masa aure ba, amma ya ƙi sai ya ce wai akwai lokaci!.
Daddy kallonsa ya mayar kan Ibrahim lokacin har sun haura kan titi direba ya ɗau hanya ya ce
"Mu"'azzam mene ne ya ɗauke maka hankali har ya hana ka jin kirana?" Murmushi Ibrahim ɗin ya yi ya ce
"Kawai dai ina kallon jama'a ne Daddy" Ya faɗa saboda ba ya son ya faɗawa Daddy cewa mace yake kallo ya san idan ya faɗa masa gaskiyar abin da yake kallon shikenan kuma yau haka za su wuni suna tsokanarsa shi da Mummy.
Ɗan zantawa suka shiga yi a tsakaninsu irin na ɗa da uba.
A ɓangaren Jidda kuwa lokacin da ta isa gida ta tarar Aliya da Umma suna zaune a baranda a tabarma suna hira, Aliyar tana cin abinci, babu wanda ya amsa sallamar da ta yi sai ma wani kallon tsana da ƙasƙanci da Ummar take bin ta da shi.
Ɗaki ta nufa ta ajoye jakar hannun ta, ta cire hijabin ta fito ta ɗauki ruwa a buta ta shiga banɗaki, ruwa ta kama ta fito dama fashin sallah take shi ya sa bata ma yi sallah a makaranta ba. Sai da ta zo saitin su Umma ta ce
"Umma ina abincina?" Kallon sheƙeƙe Umma ta mata ta ce
"Wanda kika kawo na ajiye miki?" Ta faɗa tana kallon Jidda da take wasa da yatsun hannun ta.
Jin bata amsa mata ba ta ce
"Na ce wanda kika kawo min in dafa miki?" Kai ta girgiza, sai Ummar ta ce
"Tun da kin san baki kawo ba kar ki tambayeni"
Aliya jin ta ƙoshi sai ta ajiye cokalin ta ture plate ɗin gabanta ta saki wata gyatsa, haɗe da komawa ta kwata tare da ɗora kanta a kan cinyar Umma tana mai cewa
"Wash Allah na ƙoshi kuma na gaji"
Umma ta ce
"To ba sai ki huta ba, dama an je ana taa gwagwarmayar jarabawa, Allah dai ya baki sa'a"
Aliya ta ce " Amin Ummana, ai daɗin mai uwa a gaban murhu sai ya ci ya ƙoshi"
Jidda jin wannan furucin ya sa ta tuna da tata mahaifiyar hakan ya sa ta ji ƙwalla ta taru a idanunta yanzu shekara goma sha ɗaya kenan da ƙada ta rufe idanunta idan ta tuna lokacin mahaifyarta tana raye duk abin da ta ci sai ta ajiye mata, ko da bata nan haka za ta ajiye mata wani lokacin ma ita ta haƙura ta ajiye mata, amma yanzu mutuwa mai rabawa ta raba su, mutuwa mai yankan ƙauna ta raba tsakani.
Ɗaki ta nufa ta je ta hau kan ƙaramar katifar ta, kwantawa ta yi rubda ciki ta ɗora kanta a kan filo, idanu ta lumshe tana jin yadda yunwa takr addabar ƴaƴan hanjin ta, wanka ma take son yi amma kuma yunwa ba za ta barta ba.
Idanu ta rufe wasu zafafan hawaye suna gangarowa, tana jin tamkar yau ne ta rasa mahaifanta, tana jin kewarsu a zuciya da ruhinta, abubuwan da suke faruwa bayan mutuwarsu masu ɗaure kai da kuma al'ajabi su ne suke saka take ta tunanin shin dama haka rayuwa take?.
Juyi ta yi sai kuma ta ji Umma tana ƙwala mata kira, da sauri ta tashi zaune tana goge idanun ta, sai da ta tabbatar cewa babu hawayen sannan ta fito ta ce
"Gani Umma"
Umma ta ce
"Gashi nan sai ki ɗauka, wato kin je ɗakin kin ƙule sai ya dawo ya zaci wani abun aka miki ya ishe mutane da tambaya" Ta faɗa tana turo mata plate ɗin da Aliya ta ci abinci ta rage, kaɗan aka ƙara abincin a kan sauran Aliyar, ba tare da ta ce uffan ba ta ɗauka ta juya tana dab da shiga ɗaki Aliya ta ce
"Eh mana kya ɗauki ki tafi ai ko godiya babu, tun da ga baiwar ki da kika ajiye ta girka miki ta dafa ta baki" Juyowa Jiddan ta yi ta ce
"Na gode Umma Allah ya saka fa alkairi" Ta faɗa jin Ummar bata amsa ba kuma dama ta san hakan ba mai yiwuwa ba ne, sai ta juya ta shige ɗakin.
Tas ta cinye abincin duk da bai wani ishe ta ba, amma dai ta ji yanzu ta dawo dai-dai shiru ta yi tana tunanin mai ya sa Umma ta sauya, mai ya sa a da can baya lokacin iyayenra suna raye bata nuna ta tsane ta ba sai yanzu? Mai ya sa a da take nuna mata ƙauna daga ita har Aliya amma yanzu tamkar basu taɓa son ta ba ma. Ta jima tana saƙa da warwarar kafin ta fito da kwanon lokacin ana kiran sallar la'asar banɗaki ta shiga ta yi wanka ta fito Umma ta kalle ta ta ce
"Haka kawai kike yi wa mutane wasan ruwa da sabulu, abin da duk wankan da za ki yi ba sauyawa ,a ki yi ba kina nan a baƙar ki" Bata ce komai ba ta shige ɗakin.
Bayan