Showing 6001 words to 9000 words out of 178828 words

Chapter 3 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt

18 Dec 2025

1431

da aka ba ɗan ƴat uwarta Kalifa saboda rashin mutunci.


Tana fita tsakar gidan Baba ya fara sababi yana faɗin

"Saura in ga kin kwaso min ƙafafun ki a kwana kusa kin dawo min gidan nan, idan ba dubiya ko wani gagarumin dalili ba" Ya faɗa yana ɗaga murya, hakan ne ya ankarar da mutanen gidan zuwan Sadiya don lokacin da ta zo kowa yana ɗaki, amma yanzu kowa ya san ta zo.

Mama Bilki da take zaune a ɗakin ta tana cin garin kwaki da suga jin furucin Baba ta sheƙe da dariya ta ce.

"Wato ƴar da ake tunƙaho ta samu miji wasu basu samu ba, ita ce ake yi wa kashedin dawowa gida hummm a yi dai mu gani in tusa tana hura wuta, da yake mijin ma ɗan tijara ne ba wani mai hannu da shuni ba ne da mai kuɗi ne in sau ashirin za ta zo gidan ai ba za a gaji da ita ba saboda an san nauyi za ta rage in ta zo, amma da aka san talaka ne mijin ita ma Allah baku mu samu ce ai gashi nan da tsakar rana ana korarta" Ta faɗa tana dariya Aisha da take danna waya bata ce mata komai ba.

A can tsakar gidan Sadiya ta juyo ta ce


"Baba don Allah ka barni in an yi la'asar rana ta yi sanyi sai in tafi, amma rana a buɗe kuma wallahi gori yake min duk ranar da na koma gida da wuri bare yau da tsakar rana"

Baba ya ce

"Ya miki goriba ba gori ba, ba mijinki ba ne ai in baki sani ba ki sani baki da gidan da ya fi gidan mijinki"

Haka ta juya ta tsaya a zaure ta goge hawayen duk da kowa yana ganinta zai gane ta yi kuka, gashi Baba ya ƙi barin ta zauna a gidan ma bare ta yi ɗan zance nauyin zuciyarta a ragu. Baba kuwa har bayanta ta bi sai da ya zo har ƙofar gida ya tsaya ya hange ta ta kama hanyar gidanta duk da akwai tazara sosau daga gidansu zuwa gidan nata. Cikin gida ya koma ta ƙara zuwa ɗakin Mama Talatu ya ƙara kora mata kashedi sannan ya buɗe ɗakinsa, ruwa ya ɗauka tare da awararsa ya zauna ya shiga ci.


A zuciyarsa yana faɗin

"In banda abin Sadiya ke da Allah ya dube ki a haihuwar fari ya baki ɗa namiji yanzu wannan yaron yana tasowa ba kin huta ba, zai ke ɗaukan ɗawainiyarki, ni ba gashi nan ba sau mata rigis nake haifa"

A ɓangaren Sadiya tun da ta kama hanya take ta zancen zuci, ta san yau sai dai ta tashe kunnuwanta don Nasir sai ya yayyanka mata baƙaƙen maganganu, ya faɗawa iyayenta maganar da take sosa mata rai kwata-kwata bai san darajar mutane ba. Gabaɗaya ta gaji a haka ta ƙaraso unguwar tasu, tana shawo kwanar gidan nata, sai ga Nasir a bayan mashin za su wuce ta, da alama daga gidan yake, amma kallo ɗaya ya musu ita da Kalifan ya ɗauke kai tamkar bai san su ba, kai tamkar ma babu wata alaƙa a tsakaninsu, a nata ganin ko da ita bai nuna ya santa ba, ai ya nuna ya san ɗansa tun da jininsa ne, duk da ta san ɗan nasa ma ba wani son sa yake ba.

Haka ta daure ta cigaba da tafiya ga zafin rana, jikinta tana jin yadda gumi yake zuba a bayanta duk rigarta ta jiƙe. Da yake a ƙofar gidan nata akwai matakala guda biyu wanda sai ka taka sannan za ka buɗe ƙofar gidan, har sai da ta taka matakalar tana tsaye a ka ta buɗe jakarta pose wacce mukulli ne kaɗai a ciki ta zaro mukullin tana shirin saka mukulli ta buɗe jamlock ɗin amma sai ta ga wani abu a jikin ƙofar wanda ya yi matuƙar bata mamaki...

MAMAN AFRAH
09025576222
[10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/IQU3wL7NUTCCqrbtxkJaaz?mode=ems_wa_t



*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)


NA


MAMAN AFRAH


. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 3️⃣


Fitowarsa kenan daga wanka jikinsa ɗaure da towel inda kansa yake tsane ruwan da yake jikin kwantaccen gashin kansa, ƙarasowa ya yi tsakiyar ɗakin har lokacin yana goge gashin kan nasa gaban madubi ya ƙarasa ya ahiga shafawa fatarsa mayukan da suka dace da ita mayukan da suke jibge da turaruka a kan madubin tamkar an buɗe shago.

Ibrahim kenan ɗa ɗaya tilo a wajen Alhaji Sule wanda yake kira da Daddy ɗa kuma a wajen Hajiya Faty wacce yake kira da Mummy. Fari ne dogo sannan ba siriri ba ne faffaɗa ne mai yalwar kwantaccen gashin kai, yana da manyan idanu wanda suka ƙawatu da zara-zaran gashin ido da gashin gira yana da ƙaramin baki pink lips, sai dai bashi da hayaniya.

Ɗan gata ne na ajin ƙarshe a wajen iyayensa mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne kuma tsohon ɗan siyasa, iyayen Ibrahim suna matuƙar son sa, basa son ɓacin ransa, sai dai bashi da mata hatta budurwa ma bashi da ita, tun da ya dawo daga ƙasar america da ya kammala karatunsa yake kula da kamfanonin mahaifinsa.

Burin iyayensa yanzu su ga ya yi aure domin su ga sun samu jika, kasancewar shi kaɗai Allah ya basu. Sai da ya gama shiryawa tsaf ya saka fararen wando da riga sai dai rigar tana da dogon hannu, kayan sun yi matuƙar amsar jikinsa ya ƙara komawa gaban madubi ya taje gashin ya kwantar da shi da brush kumb. Turaruka ya sake fesawa kafin ya ɗakko wayoyinsa da jakarsa da zai tafi kamfani kasancewar Daddy ya ce za su fita da wuri akwai baƙi da za su yi yau, za a tattauna a kan wasu kayan.

Wayarsa ya duba sai ya ga ƙarfe tara hakan ya bashi tabbacin ya sha baccin bayan komawarsa da gari ya waye, ganin miss call ɗin Daddy a ransa ya ce

"To fa! Daddy ina ga ya fita ma ya barni" Ya faɗa yana ɗakko takalminsa a wajen takalma ya saka ya shiga sakkowa daga matakalar benen, a hankali cikin hutsuwa, Ibrahim mutum ne nutsatstse kuma yana da ibada.

Yana baro part ɗinsa direct part ɗin Daddy ya nufa, sai dai ya samu babu kowa sai ƙaran AC da tv a falon, fitowa ya yi ya nufi part ɗin Mummy da sallama ya tura ƙofar falon, sai dai babu kowa sai mai aiki tana goge -goge, cike da girmamawa ta shiga gaishe da shi ya amsa ko kallon inda take bai yi ba amma dai a muryarsa da ta saurara babu wulaƙanci kuma kowa ya san shi ko a bayan idanunsa suna yabonsa domin ya san daraja da muhimmancin ɗan adam.

Sai da ya je tsakiyar tangamemen falon ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu ya ce

"Ina Mummynah" Dakatawa ta yi da goge -goge ta ce

"Yanzu ta haura sama"

Iska ya hurar daga bakinsa ya ce

"Ki mata magana bana son haurawa saman" A ladabce ta amsa masa tana tahowa za ta yi w Hajiya Faty magana, ganin yana danna waya ta saci kallonsa a ranta tana kissima cewa tabbas duk macen da ta samu Ibrahim a matsayin miji haƙiƙa ta dace.

Kusan tare suka sakko da Hajiyar lokacin yana waya da Daddy Mummy ta ƙaraso ta zauna a kusa da shi, har ya gama wayar ya kashe yana kallonta da murmushi a saman fuskarsa ya ce

"Ina kwana Mummy nah" Dariya ta yi tana masa kallo mai cike da ƙauna irin ta uwa da ɗa ta ce

"Ka manta da asuba ma da kuka dawo daga masallaci ka gaishe da ni?" Ta faɗa tana dariya mai bayyana haƙora.

Shi ma murmushin ya yi ya ce

"To Mummy ko sau nawa ɗa ya gaishe da mahaifiyarsa ai ba wani abu ba ne" Kai ta gyaɗa masa ta ce

"Mai za ka ci?"

Fuska ya shagwaɓe ya ce

"Ni ba na jin yunwa, tun da kuka rigani karyawa"

Mummy ta ce

"To Mu'azzam rigimamme, ai kai tun da sarkin bacci ne waye zai jira ka yunwa ta masa lahani, Daddyn ka ma da ya ce za ku fita gajiya ya yi da maka waya ya ce in ka tashi ka bi shi"

Yana ɗan yatsina fuska ya ce

"Yanzu na kira shi ya ce yana kamfanin siminti kin san baƙin nan da za a yi magana da su ba ƙaramin kaya za su saya ba"

Haka suka ci gaba da tattaunawa ta zubo masa abincin ya zauna a kafet ya ci ba wani da yawa ba, dama dankali ne da wainar ƙwai sai shayi da ya sha shi ma kaɗan. Bayan ya gama ya mata sallama ta masa addu'a ya fito riƙe da jakar da wayoyinsa, ya samu an wanke gabaɗaya motocjn da suke wajen an goge sai sheƙi suke, direba da sauri ya matso ya karɓi jakar ya saka a baya yana gaishe da shi da girmamawa ya amsa, da kansa ya buɗe bayan ya shiga ya zauna direban ya rufe masa marfin ya shiga ya tada motar mai gadi ya wangale musu tangamemen get ɗin suka fita yana ɗaga musu hannu ya mayar da ƙofar ya rufe.

Sun haura titi suna tafiya sai karatun qur'ani da yake tashi a ciki, wanda duk direbobin sun sani idan Ibrahim ne a mota ba a kunna masa waƙa. Sun kusa ƙarasawa kamfanin inda direban ya gangara gefen titi kasancewar ba a farko bakin titi kamfanin yake ba sai an gangara.

Gangarawar da direban ya yi ya fara tafiya kaɗan akwai akwai wani wuri da ruwa ya ɗan taru da yake wajen daga gefen car wash ne da alama ruwan wajen ne ya ɗan gangaro, wasu ƴanmata guda biyu sun taho ɗaya tana ɗagawa wani napep hannu, direban cikin rashin sani tayar ta shiga cikin ruwan, sai ruwan nan ya fantsala bai yi masauki a ko ina ba sai a jikin ƴanmatan nan guda biyu, farar ita kawai ruwan ya fatsu da jikin takalmin ta ne, inda baƙar kuma gabaɗaya ruwan ya ɓata mata rigar jikin ta.

Direban ne cikin nuna rashin jin daɗin abin da ya yi ya ce

"Subhanallah" Ibrahim da yake danna waya ya ɗago shi sai lokacin ma ya ga abin da yake faruwa, amma sai ya rasa ma mai zai ce. A waje kuwa Aliya ce cike da masifa ta danƙaro wani ashar mai gunna ta yi tana kallon motar ranta yana matuƙar ɓaci ta ce

"Wannan daga gani ƴan Allah baku mu samu ne, wato karere masu cin arziƙi don babu yadda za a yi wanda ya taka arziƙi ya san darajar wannan kyakkyawar motar ya saka ta a cikin ruwan caɓali" Ta faɗa tana kama tsantsa, yayin da direban ya yi parking a gefe yana neman izinin Ibrahim a kan zai fita ya basu haƙuri. Ibrahim ne ya ce

"Sai ka kula ka ga Daddy yana kirana tun ina gida, gashi ka zi ka janyo wannan duk ta cikawa mutane kunne da hayaniya" Da to ya amsa, ita kuma Aliya kasancewar bata ganinsu da yake glass ɗin baƙi ne baka ganin wanda yake cilin motar.

Jidda wacce take kallon rigar jikinta yadda ruwan nan ya ɓata, fuska ta ɓata ba tare da ta ce komai ba tana tunanin yadda za ta koma gida ba ta sauya kaya saboda duk sun jiƙe, kuma gashi makarantar fa za su je exam za su shiga.

Direban yana fitowa tun kafin ya buɗe baki Aliya ta fara zaginsa tana cewa

"Ai dama na san sai dai direba wanda ba a gaji arziƙi ba kuma ba a san darajar kuɗi ba, shi ya sa kake zunduma wannan kyakkyawar motar a ruwa marar kyau, da a ce ma kuɗi ne za ka biyani ladan mata min takalmin da ka yi da ba haka ba, to yanzu dai na san haƙuri ka fito ka bani kuma wallahi ina so ka sani ko za ka tafi tsirara sai ka biyani diyyar ɓata min takalmi" Ta faɗa tana ɗaga jijiyoyin wuya, shi kuma direba ya dage sai bata haƙuri yake kamar zai ari baki ya ce

"Haba baiwar Allah, yanzu ki kalli ƴar uwarki ita ce aka yi wa abin da ya cancanci a bata haƙuri, kalli yadda aka ɓata mata jiki amma ke da ruwan ma kaɗan ne ya taɓa ki kike wannan abin" Jidda ganin suna hayaniya ta ce

"Kai Aliya dan Allah ki yi haƙuri mana, kin zauna kina ta ɗaga jijiyoyin wuya a kan wannan abin ƙanƙ... Hannu ta ɗagawa Jidda ta ce

"Dalla malama rufewa mutane baki, ana maganar waɗanda suka san ciwon kansu a kan haƙƙi ai ke bakya saka baki ba, ni idan ni ya ɓatawa kaya kamar yadda ya ɓata miki da tuni na sharara masa mari" Da sauri direban ya kai hannu ya dafe kumatunsa tamkar dai an mare shin.

Jidda kuma ranta ne ta ji babu daɗi jin an ce mata bata san ciwon kanta ba, kuma dama ta san za a rina wai an saci zanen mahaukaciya.

Aliya ce ta ɗaga hannu ta miƙawa mutumin a kan ya bata kuɗi, ɗari biyun da ta rage ya fito da ita ya miƙawa Jidda, yana cewa

"Baiwar Allah ki karɓa ki saya omo ki wanke kayan da na ɓara miki" Kafin ya kai kuɗin saitin Jidda Aliya ta saka hannu ta warce tana cewa

"Matsiyaci wai ɗari biyu, to na karɓe dama an ce sata a gidan ɓarawo rance ce, kuma raba arne da makami ibada ne" Ta ce tana saka kuɗin a jakar hannun ta.

Jidda ce ta buɗe baki ta ce

"Bawan Allah da baka wahalar da kanka wajen bayar da kuɗinka ba, da ka bari za su maka amfani amma ka ɗauka ka bayar, kuma ai kowane ɗan adam ajizi ne sannan yana iya yin laifi" Kai direban ya shiga gyaɗawa jin maganar hankali da hikima duk abin da ake yi Ibrahim yana kallonsu ta glass daga cikin motar.


Ya yaba da hankali da nutsuwar Jidda, sannan ya lura ta san daraja da muhimmancin ɗan adam kamar yadda shi ma ya sani.

Aliya kuwa ta wuce Jidda tana aika mata harara a inda da za ta wuce ta saka hannu ta daki bayan motar, napep take tsayarwa amma bai tsaya ba hakan ya sa ta tsallaka titin ta koma ɗaya ɓangaren, a nata tunanin ta tafi ta bar Jidda don ba za ta juri har sai ta jira ta ta koma gida ta sauya kaya ba, ba ma wannan ba ita a rayuwa ta tsani take tafiya da Jidda kasancewar Jidda baƙa kuma mummuna a zahiri Jidda bata da wani kyau, baƙa ce tana da faɗin fuska sannan tana da matsakaicin tsawo, tana da manyan idanu sai daj hancinta gajere ne kuma mai faɗi. Saɓanin Aliya da take fara tas kyakkawa ajin farko, tana da tsayi sannan tana da doguwar fuska dogon hanci wanda ake yi wa laƙabi da kamar biro duk wani abu da ya danganci kyau Aliya tana da shi wannan dalilin ne ma ya sa take ganin ta ciri tutar da sai ta zaɓi miji ta darje, miji ma na nunawa sa'a mai hannu da shuni wanda take ganin ko da ɓarawo ne in dai yana da kuɗi kuma yana da kyau to fa ta ga mijin aure don shi ne zaɓi kuma burinta.


Tana daga can inda ta tsallaka tana hango direban nan da yake ta faman ba Jidda haƙuri kafin ya juya zai je ya shiga mota, ita ma Jiddan tana ta ƙoƙarin tafiya Aliya a zuciyar ta ta ce

'Hmmm! Ka ji da shi cuwon ajali a ɗan yatsa, tun da dai ka gama jiƙa mutane ai sai ka san inda dare ya maka, baka san cewa wannan baƙar mummunar da ita da bola mu duk ɗaya muke ganinsu ba, ni ma nan da ka ganni ƙaddara ta haɗani tafiya da ita, saboda kan nan nawa dusa ce ko in ce fanko ne babu komai a ciki, ko bihim ban sani ba wamda zan rubuta a exam ɗin da za mu yi, shi ya sa ma nake so mu tafi tare da ita tana rubutawa ina copy, dama ita take goyani a kowacce exam' Ta faɗa tana ɗan taɓe baki, tare da duba agogon da yake hannun ta.


Ibrahim kuwa da sauri ya saka hannu ya buɗe ƙofar ya fito lokacin Jidda ta fara tafiya, yana zuro ƙafafunsa farare tas da suke cikin baƙin takalmi mai yatsa, Aliya tun daga tsallaken titin da take ta hangi an buɗe bayan haɗaɗɗiyar motar wannan wacce ta gama yi wa direban motar ɗiban albarka, mamaki haɗe da al'ajabi suka haɗe suka cunkushe kwanyarta, wani irin bugawa ƙirjinta ya yi da ƙarfi lokaci guda zuciyarta ta aiko mata da wani saƙon tambaya kamar haka

'Dama akwai wani a cikin motar ba direban ba ne kaɗai, kenan mamallakin motar ne wannan ya fito?' Ta tambaya kwata-kwata ta gagara ƙifta idanunta don gani take idan ta ƙifta tamkar wanda take hangowar ɓacewa zai yi.

Ibrahim kuwa lokacin da ya fito Jidda ta masa ɗan nisa, domin ta saka gabata can tana ta zabga sauri, sannan shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login