Showing 147001 words to 150000 words out of 178828 words
Chapter 50 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
ka bani," Sai kuwa Meenal ta fara masifa tana cewa ta msta gorin sana,a shi kuma yana tsaye ya kasa crwa komauɓi don Sadiya ta goge masa hadda bai zaci za ta rikice har ta ƙwatawa kanta ƴanci ba.
Faɗa ne ya kacame a tsakanin su amma Meenal ce take ta kumfar baki a dole sai an cirewa Sadiya nepa ita kuma Sadiya ta ce wallahi babu wanda ya isa ya cire mata nepa.
Haka ta koma ɗaki tana faɗin
"Wallahi idan aka cire mini nepa sai na kirawo ƴan nepa sun cire wutar gidan gabaɗaya sai dai kowa ya zauna babu nepa, in kuwa har wani ɓangare na gidan nan zai zauna da nepa to dole ya kasance nawa ɓangaren ma akwai wuta, domin ni ma mutum ce kuma ni ma matar gida ce kamar yadda kike matar gida" Tana jin su suna ta bala,i ita dai gabanta ma faɗuwa yake lokacin da take yin faɗan, amma ta daure ne saboda ta lura matsawar bata ƙwatawa kanta ƴanci to tabbas shan ruwa a gidan ma sai ya gagare ta, ga shi yanzu za ta yi haihuwa ta biyu kenan ita da ƴaƴanta za su rayu babu ƴanci a cikin gidan.
Nasir ya sha masifa a wajen Meenal don tana faɗin ya zaɓi da Sadiya a kanta. Ranar a kan gado ya kwana shi kaɗai ita kuma a ƙasa don kawai ta nuna masa tana fushi, ta ɗauka zai saka a cire nepar washe gari sai ta ga ɗiff bai yi maganar ba ma hakan ya sa ta saka a ranta dole ta je gida domin ta kaiwa Momi kuɗi a je a yi aiki a kansa wato ya dawo sai abin da ta ce masa.
Sadiya kuwa a daren ta haɗa mango juice da zoɓo ta saka a frezer ɗinta. Tana ta addu,ar Allah ya ɗota ta a kansu, tun da ta ga dole sai tana kataɓus wajen ƴancinta tun da babu mai bin bayanta ya ƙwatar mata haƙƙinta daga gidansu har gjdansu Nasir ɗin.
Tuni kasuwar kayan sanyi ta dawo, bayan kwana biyu aka sake kafe sunayen ƴan tallafi Allah da ikonsa sunan Sadiya ya sake fitowa amma wannan karon ban da Noor dama an ce wasu hsr sau uku ma sunan su yana fitowa haka ta je ta karɓo kuɗin nan, tana ta al,ajabi duk da ba a mamaki da lamarin ubangiji ga shi dai ta yi asara amma da yake Allah maji roƙo ne ya mayar mata a lokaci ƙanƙani, sai ta sauya wajen ajiya kawai ya zamana ƙananan kuɗi take ajiyewa a gida, su manyan kuɗin kawai sai ta ba almajirinta ya je pos ta rubuta masa acc no ta a je a tura mata, ya zamana ba ta ma ajiye cash ɗin bare a ɗauke.
Meenal kuwa wuni ta tambaya zuwa gidansu, ta haɗa kan kuɗin wajen Sadiya wanda ta sata, da na wajen Nasir da take masa sata yadda ba zai gane ba, ko ya ce zai sauke ta a gida sai ta ce masa ya je za ta hau napep. Waya suka yi da wani Alhajinta cikin wanda suke holewarsu kafin ta yi aure sannan suna shirmensu a waya ma, haka suka haɗu a hotel ya kama musu ɗaki suka sheƙe ayarsu, ya mata alƙawarin za ta ji alert mai nauyi domin a lokacin wai bankinsa ya samu matsala kuma ba shi da cash.
A ƙofar gidansu ya sauke ta, dama ta yi wa Momi waya haka suka fito Momi ta tare musu wani mai napep, su biyu ne a ciki mai napep da kuma wani a gefensa a zaune, Momi ta kwatanta musu inda za su kaisu, don sosai sai an fita ma daga gari wani ɗan ɗauye ne haka suka yi ciniki, sai suka yanka musu kuɗi da yawa Mominta dage tana neman ragi buɗar bakin Meenal tana dariya ta ce
"Momi akwai kuɗi fa, kuɗi ba matsala ba ne kawai mu je ai biyan buƙata kawai ake so, ai tun da Nasir har ya fifita wanann ƙazamar matar tasa marar aji sai ya gwamamce kiɗa da karatu"
Momi ta ce
",Yaushe ta zama ƙazama bayan na ji ana cewa tsaftar masifa gare ta"
Meenal ta ce
",A,a kawai na faɗa ne"
Haka suka ci gaba da tafiya suna tafiya su Meenal da Hajiya suna ta tattauna zancen kuɗin da yake a jakar.
Momi ta ce
,"Wallahi gwara da kika raba shegiya da kuɗin ai da sannu zaman gidan zai gagare ta,"
Meenal ta ce
"Ai bokan nan ko nawa ya buƙata zan basho, dama akwai ma wani alƙawarin kuɗi da aka mini" Sun saki baki suna ta zuba, basa lura da cewa basu san su waye masu napep ɗin ba, kawai mutane in suka shuga napep ko motar haya sai su saki baki suna ta zance, wani ma sirrinsa zai ke faɗa abubuwa dai barkatai ba a takatsantsan.
Duk abin da suke masu napep ɗin suna jin su, sannan suna ta yi wa juna magana da ido don sun gama shirya komai ba tare da su Meenal sun sani ba. Sai da suka yi nisa a tsakiyar daji gaba babu kowa haka ma baya sai kawai mai napep ta taka birki ya tsaya Momi ta ce
"Ya dai?"
Sai ya ce
"Mai ne ya ƙare shi ne zan zuba wani"
Meenal ta ce
"Don ma kana da akwai da yanzu a nan ina za a samu wani mai"
Mai napep ta ɓangaren Momi ɗayan da ya fito ta ɓangare Meenal dama majiya ƙarfi ne, hasali ma ba masu napep ba ne arowa suka yi a wajen abokinsu don su yi damfara sai kuma tsautsayi ya faɗa a kan su Momin.
Duka suka yi wa su Momin suka ƙwace jakar Meenal da wayoyin su, sai da suka musu lilis sannan suka shiga napep ɗin suka kwasa a guje, suka bar su yashe a nan tsakiyar hanyar tsakar daji, kowacce tana murƙususu don hatta bakinsu da hanci ya sha naushi, basu ma da ƙwarin gwiwar hadda ce lambar jikin napep ɗin!
Yau Sadiya kawai muka taɓo ina da uzuri ne.
MAMAN AFRAH
09025576222
https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=hqrt1
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 2️⃣7️⃣
UMMA
Da tsananin faɗuwar gaba take kallon ƙullin maganin guda biyu da bokanya ta bata, tana jin tsoron tunkarar sabuwar gawar tare da taraddadin kar ta je asirinta ya tonu domin tana ganin ta yaya za a ce daga ka fesar da magani ya bi iska kowa zai suma? Wannan lamari ne mai girma sai dai tun da ta yarda da aikin sihirin bokanya sai ta cire kokwanto a ciki tana rayawa a ranta wannan lokacin sai an samu nasara fiye da lokacin da aka faɗi babu nasara wanda Aliya ta yi aikin cokali, sannan wannan lokacin ba za ta yarda ta yi asarar kuɗin da aka biya na maganin ba.
Sai da ta sakko daga barandar ƙofar ɗakinta ta shiga tunanin ya za ta yi da Abba? Tun da dai ta san yana masallacin sai dai tuna sai an yi sallar isha yake dawowa hakan ya sa ta ji dama dama wai kibiya a ido. Fitowarta daga gida kenan ta tsaya tana kalle-kalle tun da dai ta san ita inda za ta je aiwatar da aikin nata aiki ne mai haɗari, sai dai dole ta yi takatsan tsan waje tafiya gidan Malam Kalla saboda yanzu dai ai maganin bai fara aiki ba tun da sai ta je ta fwsa maganin ne kowa zai suma sannan bakin kowa ya mutu komda wani ya gani bau mai tambya kamar yadda bokanya ta faɗa.
Ko da ta tafi tana jin tsoron yana ƙara mamaye ranta, sai dai mugun nufinta a kan Jidda na sai ta dawo ƙarƙashinsu sun ƙasƙantar sa ita, Ibrahim ɗin da ya zama gatanta sun maido da shi soyayyar Aliya ce take mulki a cikin zuciyarsa, hakan ya sa ta ji wani irin ƙarfin gwiwa a zuciyarrta ta ce
'Jidda dole ne ki ƙarƙanta! Dole ki zama abin tausayi kuma abin kwatance amma ba kwatance mai kyau ba sai dai kwatance na tausayawa, ko maƙiyinki sai ya tausaya muki Jidda, domin yanzu ƙiyayyar da nake miki ta linku ba zai taɓa iyuwa ba ke kina rayuwa a cikin daula ke da baki da wani gata ko galihu, baki da wani kyakkyawan asali ke asali mai munin ba babu shi, har ki fi ƴata samun gata da kulawa kina rayuwa a haɗaɗɗan gida mai cike da ƴan aiki ana miki hidima ana girmamaki, kina juya kan naira ta yadda kika so, kina ado da zinare hmmm wai ke ce har mijinki yake yi wa uban da ba shi ne silar dirowarki duniya ba kyautar mota, ni tawa ƴar tana can mijinta yana yawo ranar duniya tana ƙarewa a kansa a kasuwa, tabbas da sake!' Ta faɗa tana ƙara sauri don ganin ta aiwatar da abin da ta yi niyya domin maganar zucin da ta yi ya ƙara ingizata a kan aiwatarwar.
Tun da ta fito take cin karo da mutanr jifa jifa ana tafiya gidan, da alama jajanta mutuwar ne ko dai mutanen suna da alaƙa da mamacin wato ƴan uwa na kusa tun da dai an ce sutura sai gobe.
Ta kusa ƙarasawa gidan ta hangi su Abba su uku shi da ladan ɗin masallacin nasu da kuma liman sun nufi gidan rasuwar, da sauri ta faɗa gidan ta tsaya daga bayan ƙofar gidan a cikin zauren ta laɓe a jikin ƙofar tun da ta san maganin bai fara aiki ba Abba yana ganinta zai tambaye ta ba,asi duk da mutuwa ce a maƙota yana da kyau a yi haƙƙin maƙota don jajantawa amma sai ya san ai duk gaggawar asara ta jirayi samu, ma,ana duk saurin zuwan da take ta jira ya dawo daga masallacin ta tambaye shi.
Tana ganinsu suka shige, baki ta taɓe zuciyarta tana ingizata. Ƙullin maganin ta buɗe hannunta saboda ɗan duhun da ya fara ratsa duniya na magriba sai ra kasa tantance wanne ne na fesawa a cikin gidan wanne ne na sakawa a hancin gawar!.
Gudun kar ta yi ɓaran ɓarama ta fesa na hancin gawa su ƙi suma mutanen gidan sai ta yi saɗaf saɗaf ta fita dagan zauren, tana fita ta ga wata yarinya tana tafiya tana ƴar waƙa da fitila a hannunta, kiranta ta yi ta ce ta ara mara fitilar ta karma ta haska maganin ta bambance sai ta ba yarinyar fitilar ta juya cikin gidan.
Tana iya jiyu yadda ake ta koke-koke a cikin gidan, amma son zuciya ya hana ta yi tunanin cewa, idan gawarta ce ko ta wani nata za a yi wa hakan ba za ta ji daɗi ba, shaiɗan ya hana ta fahimci aairi babu kyau saɓon Allah ne, ta kasa fahimtar haɗarin da yake tattare da neman biyan buƙata ta haramtacciyar hanya, wato aiki da maganar boka da kuma amfani da gawar da a yanzu babu abin da take buƙata sai addu,a da neman gafara sannan kowa yana iya zama gawa a kowane lokaci, da ciwo ko babu, babu jinkiri ga wanda lokacinsa ya yi sannan babu gaggautawa ga wanda lokacinsa bai ƙarasa ba!.
Zuwa wurin boka haramun, aiki da maganarsa ya saɓa da addini, sannan ba ta ma tunanin shi aure lokaci ne bare ma ƴarta tana da auren sun raina samun mijin ne da kuma matsayinsa, kuma hakan yana nuni da yin aure ta tilas domin shi wanda za a yi aikin a kansa tilasta masa za a yi, kuma akwai haɗari ga aiki da bokanci ko yin sihiri.
Da sauri ta zazzage maganin a tafin hannunta tana fatan Allah sa dai babu ita a suman da aka ambata mutanen za su yi tun da idan aka suma har ita yaya kenan.
Babu ɓata lokaci ta zage murya ta ce
"Malam Kalla" Tana faɗa ta shige tsakar gidan ta hura maganin gabaɗaya ya bi iska. Kamar almara take ganin kowa ya zube a inda yake ya sume, tamkar gawarwaki haka ta ga mutanen babu wani mai motsi. Daga can gefen wata tabarma ta hangi Abba da su Liman suna yashe tamkar gawar su ɗin ma. Ba ta hira komai ba ta nufi ɗakin Malam Kalla, malam kalla malami ne mahaddacin qur,ani sannna mai ruƙo da addini.
Ɗakin a cike yake da mutane matansa ne sai manyan ƴaƴansa amma kowanne babu bambanci da gawar domun duk sun sume. Yana kwance a miƙe zumbet an lulluɓe shi da zanen gado, yanayin yadda suke ya nuna ba a daɗe da yin rasuwar ba ma wataƙila ma yana rasuwa akan sanar a masallacin.
Ta na nufarsa gabanta yana tsananta faɗuwa sai dai ba za ta yi wasa da wannan damar da ta samu ba din ta san tana gama yin aikin komai zai daidaita su fara cin duniyarsu da tsinkena tsire. Ba ta tunanin su ko za su tsallake wannan rana ba su mutu ba tub da ajalin ba sallama yake yi ba, kowa mutuwar tana zuwar masa ne bagatatan.
Tana taugunne a gabansa ƙafafunta na karkarwa amma haka ta saka hannu ta buɗe gawar ta ganshi idanunsa a rufe ruf kamar mai bacci. Maganin ta buɗe daga leda ta saka yatsu biyu ta tsakuro, ta nufi hancin gawar za ta zuba sai dai me sai ta ga gawar kamar ta ɗan motsa, gabanta ya bada rass amma sai ta saka a ranta cewa tsabar ruɗanin da take ciki ne domin gawa ai ba ta motsi duk wanda ya mutu ya mutu.
Ƙara nufar hancin nasa ta yi ta ƙara ganin gawar ta ɗan motsa hannun gawar ne yake ɗan motsi amma kaɗan sai ka lura za ka gani, ɗan jim ta yi amma sai kawai ta ƙara nufar hancin gawar za ta zuba maganin sai kuwa ta ga kan gawar ya ɗan motsa Umma ta tsaya cak! Ta juya ta dubi ƙofar shigowar amma babu kowa kuma gidan shiru sannan har lokacin babu wanda ya ƙara shigowa gidan. Kallon mutanen ɗakin ta yi don ta tabbatar da cewa ita kaɗai take ganin gawar tana motsi ko akwai wanda yake tayata gani amma ta ga babu kowa sai ita kaɗai.
Kawai sai zuciyarta ta raya mata cewar gizo ne idanunta suke mata domin su hana ta aiwatar da ainihin abin da ta zo yi wanda ta samu wata dama, tana tono kuɗin da ta bayar na aikin sai kawai ta ajiye ledar a gefe ta saka hannun ɗaya ra riƙe hancin gawar ta nufi hancin da ɗaya hannun mai maganin.Kamar daga sama kuma kamar almara Umma ta ga hannun gawar nan mai motsi ya ɗago kafin ta gama tantancewa hannun gawa ya damƙe hannunta!
Tashin farko ta ji kufcewar fitsarin da ba ta shirya masa ba, a yadda take a tsugunne ta ji zaninta jagaf, ga tsananin tsoro da tashin hankali da kuma da na sanin yin wannan aikin tun da dai ta san gawa ba ta motsi amma ita bayan motsin da gawar ta yi ga shi har hannun ta ta riƙe.
Jan hannunta take amma sai ta ji tamkar an saka mayen ƙarfe domin gawar ta riƙe hannun gamgam kamar tare da hannun aka halicce ta. Umma abin ya fara wuce gona da iri domin abin ya fara wuce hankali da tunaninta, ita da ta zo don aiwatar da aiki a cikin ƴan mintuna amma ga shi wankin hula yana so ya kai ta dare.
Ganin abin ba na ƙare ba ne ta shiga ture gawar amma gawar tana ƙame kawai dai ta riƙe hannun Ummar ne. Umma ta fara tunanin kar fa asirinta ya tonu tun da dai sai ta ambaci sunan mamaci sannan kowa zai dawo daga suman da ya yi ga shi kuma yanzu gawar ta ƙi sakin ta kenan hakan yana nuni da tonuwar asirin ta ko yaya?.
Abu dai ya faskara!. Don yanzu Umma kokarin kwatar kanta kawai take ta ma saddaƙar cewa yiwuwar aikin da ta zo yi sai sa,a. Tana kiciniyar kwakwace kanta ta zubar da maganin hannun nata wanda za ta zuba a hancin gawar, amma ba ta shi take ba wannan lamari ya girmi tunanin ta.
Jan hannun ta yi da ƙarfi aikuwa sai ta ji gawar ta saka ɗaya hannun ta damƙi ƙafarta guda ɗaya shikenan sai Umma ta sare cewa asirinta rana dab da tonuwa, don ta san ida har wani ya shigo gidan wanda shi ba ta yi aikin watsa magani da shi ba to ta fara zargin zai ganta wannan yana nufin Abba zai san abin da ta zo yi kuma sakamaon ta ta sani ba sai an faɗa mata ba kuma kowa zai san mai ta zo aikatawa tun da gawar ba ta wani nata ba cw sannan mai ya kaita wajen gawa da har ta riƙe mata ƙafa da hannu!?.
Wajen kiciniyar ƙwaƙwace kanta ɗan sauran maganin da ya rage a ledar wanda take ganin shi ne ya rage mata tun da na hannun ya zube, tana rayawa a ranta idan ta samu kwace hannunta sai ra tura maganin a hancinngawar amma a kokarin ganin ta tsira ta ture ledar gabaɗaua ya zube dama ba wani yawa ne da shi ba don