Showing 60001 words to 63000 words out of 178828 words

Chapter 21 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt

18 Dec 2025

1452

tata kafaɗar, wani ƙamshin turarensa wanda take jin na yau ya sha bamban da na kowacce rana ko don kasancewar yau ranar ta musamman ce a tarihin rayuwarsu Allah masani. Yana zama sai ta ji tamkar ta nutse jin jikinsa yana gugar nata, abu ne sabo tsakaninsu da bai taɓa faruwa ba ko ta ce abu ne sabo wanda a iya rayuwarta bata taɓa kasancewa da wani ɗa namiji da kusanci kamar hakan ba, sai ta ji duk jikinta ya fara wata irin tsuma.

Tana cikin wannan tunanin sai kawai ta ji ya ɗora hannunsa a kan hannuwanta da take wasa da su, wani irin yammm ta ji tamkar an haɗa shokin bata san lokacin da ta yi saurin janye hannun ba, sai dai saurin ƙara riƙo hannun nata wannan karon hannu biyu ya saka ya riƙe nata, cikin wata murya mai sanyi da daɗin amon a kunnen mai sauraro kuma ga ma,abota soyayya ya ce

"Habibty an zo lafiya?" Bakinta bai bata haɗin kai ba wajen bashi amsa sai ta ji ya sake ɗorawa da faɗin

"Ina fatan kin zo da shirin tarɓar mai gidan naki domin kuwa zai zame miki raƙumi da akala, sannan zai zama tamkar ƙaramin yaro a wajenki karki manta sarauniya kike a fadata, amma ni zan zama tamkar bawa a fadar sarki a gare ki wallahi ina sonki Jidda ba zan iya daina sonki ba har ƙarshen numfashina!" Kalmomin nan da ya ambata sun sanya kunnuwana yin dummm har lokacin ban ce komai ba sai ya saki hannun ya ɗage laffayar da ta masa shamaki da ganin fuskata, yana buɗewa ya yi saurin saka hannu yana share lemar hawayen da suke kwance a fuskata sannan ya ce

"Karki ƙara zubar mini da hawayenki, hawayenki suna da matuƙar muhimmanci Jidda kin zo inda ba za ki sake zubar da su ba sai dai kukan daɗi amma ba na baƙin ciki ba, aure ana yinsa ne don faranta ran juna ni kuma zan zamo mai faranta miki, zan zama daban a cikin maza je, don sai na saka kin zama da ban a cikin mataye" Mainakon in daina kukan kamar yadda ya ambata sai wasu sabbin hawayen
suka zubo don in har abin da yake faɗa haka ne haƙiƙa na yi dace da miji na gari kuma mijin ƙwarai.

Ban yi zato ko ankara ba sai na ji ya rungumeni wani irin fargaba na ji kasancewar karo na farko a rayuwata da faruwar hakan, ɗiff na yi ina jin yadda ƙirjina yake dakan lugude, shi kuma Ibrahim bai ma san mai take yi ba abu ɗaya ya sani hakan ya haifar masa da wata irin nutsuwa mai wuyar misaltawa.

Kiran da Abeed ya shiga masa shi ya ankarar da shi, da sauri ya sake ni yana faɗin

"Taso mu je kar wannan ya fasa min dodon kunne" Yana faɗar hakan ya miƙe tsaye, tare da kama hannuna na miƙe ya saka hannu ya lulluɓe min fuskar kamar yadda ya same ta a lalluɓe yana faɗin

"Kar a gane min fuskar amaryata, ni dama in ban da sun kafa min tsiya da babu wanda zai rako ni" Ni dai ban ce komai ba kawai dai na ji hannunsa cikin nawa ya kama, babu yadda na iya haka na biyo shi muka fito kunya duk kamar na nutse. Tun da muka zo falon suka mana caaa wai mun Ibrahim ya ƙule da amarya a ɗaki ya manta da su, shi dai cewa yake

"Ko ma mai na yi ai ba haramun ba ne" Suna ta wasa da dariya, ya zaunar da ni tare da zama a kusa da ni, nan aka shiga yin addu'o i da kuma mana ƴan nasihohi daga ƙarshe suka mana fatan alkairi suka mana sallama suna cewa ya zo ya raka su yana faɗin ai ko nan da ƙofa ba zai fita ba, haka suka tafi suna mana tsiya, ina jin lokacin da suka fice mai gadi ya rufo get ɗin.

Suna fita ya buɗe min fuskar ya kama ni, wani ɗaki muka shiga kusa da ɗakin da aka kaini, komai na ɗakin sabo dal amma ba kayan ɗakin da Abba ya saya min ba ne na ɗakin da aka kaini nan ne kayan da Abba ya saya mana, haka ma kujerun falon, banɗaki muka shiga tare bayan mun saka takalman da suke ƙofar bayan sabbin silifas ne yellow da kuma ja. Ni dai na tokare a bakin ƙofa na sunkuyar da kai ganin haka ya shiga yin uzurinsa ni dai ina jin ƙaran ruwa amma ban san ruwa yake kamawa ba ko kuwa alwala, jim kaɗan ya ce

"Wuce ki yi alwala ko kuma ni in zo in miki... Tun kafin ya ƙarasa na rama gefensa na wuce kasancewar banɗakin ma yana da girma tamkar ba banɗaki ba.

Shi kuma dariya na ga ya min sai ya ɗaga hannu ya fatsa min guntun ruwan hannun nasa a fuska, har hakan ya sa na murmusa, juyawa ya yi ya fita yana dariya ni kuma na yi tsarki tare da yin alwala na fito, a ɗakin na ga ya shimfiɗa sallaya gida biyu, ɗaya tashi a gaba tawa a baya haka ya yi kabbara muka gabatar da nafila raka'a biyu bayan mun salance ya ɗaga hannu ya yi addu'a muka shafa. Bayan ya juyo ya dafa kaina ya yi addu'a sannan ya tashi ya fita jim kaɗan ya dawo ɗauke da leda babba sai kuma plates.

Bayan ya ajiye ya fita sai gashi ya dawo da lemuka da madara masu sanyi ya jera ya koma ya ɗakko kofuna na glass duk tana kallonsa sannan ya dawo ya zuba komai sai ya ce

"Ki sa hannu mu ci" Ta ce

"Na ƙoshi" Hannu ya kai ta lakato hancinta ya cr

"Yau akwai ɗura kenan" Idanu ta ɗaga tana kalle shi tare da sauke idanun a kan gasashshsiyar kazar da take ta turiri kai ta shiga girgizawa kafin ta samu furta wani abu sai gani ta yi ya yago naman kazar tsoka ya nufi bakinta tare da faɗin

"Jiddanah yi bismillah" ,Yadda ya yi furucin kawai ya isa ya nuna maka tabbas yana cikin mazan da zai ba mace kyakkyawar kulawa da nuna soyayya a zaman aure!.


*ALIYA*


Tun da suka fito daga gidan Jidda ranta yake suya ji take dama a ce mafarki ne take ba wai zahiri ba. Motoci suna ta wulwula gudu saman titi tana zancen zuci cewa yanzu duk rabi da kwatan motocin na domin ɗaukan Jidda suka zo ita kawai albarkaci take ci.


Sun yi tafiyar mai nisa kafin suka kusa wata unguwa da hasken fitilun motocin ne kawai suka haske unguwar, motar gaba wacce ita ce abokin Kasim yake ciki su ne jagora zuwa gidan amarya Aliya, Aliya sai saukar guɗar mata take ji kamar za su cire hanci ita kuma tana jin guɗar har tsakiyar kanta.

Wani gida madaidaici wanda yake ɗan sheƙin fenti don yanzu tana satar kallon windown don ta ga gidan da za a kaita hasken fitilun ne suka nuna mata sabon fentin da aka yi wa gidan, don motocin da suke gaba sun fara tsayawa a saitin gidan, idanu ta runtse da ƙarfi tana jin tsanar Kasim a ranta, ganin gidan Jidda duk yawan motocin sai da suka samu matsugunni a cikin gidan amma sai gashi ita babu get ɗin da ko mota ɗaya za ta samu mafaka, hasali ma ƙaramar ƙofa ce a gidan, ba ma wannan ne abin mamaki ba yadda bata hango hasken ƙwan fitila a gidan ba sai ta fara zancen zuci tana faɗin


'Kar dai Kasim don baƙin talauci inji ma bai saya ba, saboda babu nepa a ce gidan amarya, amaryar ma kamar ni amma babu haske?' Ta faɗa a zuciyarta tana saka haƙorin sama na bakinta ta dantse leɓenta na ƙasa bata ankara ba ta ji Aunty ƴar uwar Umma tana faɗin

"Fito da Bismillah Aliya, kin zo gidanki, ki shiga da addu'a Allah sa gidan zamanki ne Allah sa abokin rayuwa ne sai mutuwa ce za ta raba" A fili Aliya ta sako ƙafarta ta fito a zuciyarta kuma ta ce

'Ba amin ba' Ƴar uwar Abba ita ce ta amsa da amin, mata kuwa sai guɗa suke rafkawa an samu abin da ake so, mata kenan akwai son shagalin biki su dai su je biki (Lol)

An fara cusuwa zauren gidan inda ake ta faɗin

"A jira wasu su gama shiga mana, ai zauren ne ƙarami" Aliya da ake riƙe da ita kamar ta kurma inu haka take ji, sun shigowa gidan hakan ua yi daidai da jan ƙaramin inji da aka yi wato aka tada, amma wajen ja uku injin bai tashi ba, a ja na huɗun ne sai ga haske tarrr ya haske gidan, mata aka fara faɗin

"Haba haske ai rahma ne" Wata mata da Aliya bata gane wace ce ba sai ji Aliya ta yi ta
ce

"Gidan Jidda kuwa haske tarr har muka tafi bamu san ma ta inda hasken yake zuwa ba babu ƙara injin" Wata ta kusa da ita ta ce

"To ko sola ce"

Sai matar ta ce

"Abinki da babban gida wataƙila wajen injin ma da aka tanafa na musamman ne yadda ba zai damu masu gidan ba" Aliya kamar ta zazzage su haka ta ji.

Falon aka shiga da amarya, hakan ya yi daidai da mutuwar injin sai fitulun waya aka kunna wata mata tana faɗin

"Gyara fa ake yi shi ya sa"

Ɗakin aka wuce da amarya tana ganin ɗakin na Jidda ya yj biyar ɗin nata, Jidda ta samu komai idan ta ce komai tana nufin komai ciki kuwa har da kyakkyawan miji.

Har aka watse in ji bai tashi ba tana jin ƙaran ƙwale-ƙwalen ƙarafe a tsakar gidan da tashin maganar mutanen guda biyu, da alama ma in jin ba sabo ba ne ko kuma dai matsala ya bayar.

Tana jin motocin suka tashi suka tafi, tana zaune dilim a duhu sai hasken fashashshen screen ɗin wayarta. Lulluɓin ta fisge tana ƙarewa ɗakin kallo ɗakin ya yi kyau babu laifi har jeren da aka yi amma saboda hassada da hangen na sama da ita gabaɗaya baƙin gidan da ɗakin take gani Sai da aka yi wajen minti talatin kafin suka samu injin ya tashi, sallamar Kasim da wasu da bata san su waye ba ta ɗauki dai muryar abokinsa Salis, tana ji masu gyaran injin suka tafi su kuma suka shigo falon suka zazzauna, suna ta yi masa tsiya ango na amarya tana jin suna faɗin

"Wai ina amaryar ne?" Kasim ya ce

"To ku haka za ku ga amarya ba a muku iso ba, ai sai na nema muku izini sannan zan kawo maka ita" Gabaɗaya suka hau masa tsiya shi dai ya nufi ɗakin domin kawo amarya.

Maimakon ya ganta a lulluɓe sai ya ga fuskarta warai babu lulluɓi abin ya ɗaure masa kai ma tamkarnwata zararriya haka ya ganta, mamakinsa ya danne ya ƙarasa yana sakin yaƙe duk da gabansa yana faɗuwa don ya san ko kaɗan Aliya bata ɗokin aurensa tun daga ranar da ya kai lefe a baro.

Zaunawa zai yj sai ya ji a faɗace ta ce

"Karka zauna a kusa da ni don ban gayyatoka ba" Fasa zaman ya yi ya shiga mata nuni da hannu yana mata alama cewa da mutane a falo a gefe ɗaya yana mata alama da cewa ta yi ƙasa da muryarta. Cikin hargagi ta ce

"Ina ruwana da mutane, ko akwai wanda na kaiwa katin gayyata, da suka kwaso koɗaɗɗun ƙafafu suka zo, to yadda suka zo haka za su ɗauki ƙafa su koma inda suka fito" Kalamanta sun kusa saka ya zauce saboda ɗimuwa, ya san dai duk abokansa sun ji abin da ta ce, bai taɓa zato ko tsammanin hakan ba, wannan ranar babbar rana ce a gare shi mai ɗimbin tarihi amma yanayin Aliya ya nuna so take ta rusa komai, so take ta tada fitina, so take ta shayar da shi ruwan guba mai ɗaci ba ruwan zuma ba, a ce a ranar farkonta a gidansa tana magana kamar za ta kai masa duka anya zaman zai iyu?.


Kafin ya gama shan ruwan mamakin da Aliya ta shayar da shi, ji yake kamar ya nutse don kunya shi bai ma san ta ina zai fita falo kuma da wane ido zai kalli abokan nasa ba don ya san sun ji komai, kawai sai ya ga ta miƙe tsaye ta shiga warware laffayar jikinta, ya zamana daga ita sai leshin jikinta, wanda ya matuƙar amsar kyakkyawar fatar jikinta baƙin lalle da ja da ya ƙara haska kyakkyawar fatarta, ji yake yana son kaɗaicewa da ita a wannan daren mai ɗimbin tarihi amma hakan zai iyu?.


Na ce muku hakan zai iyu😃😃😃 ku bani amsa wato cmmnt ma sai kun bushi iska kuke yi a toh nima ai kuna gani a ƙwaryar shanku sai na bushi iska nake typin😒😕 labarin nan yana da tsayi akwai darasi akwai cakwakiya, abubuwa masu kamar almara za ku ji yadda.... Ba zan dai faɗa ba kawai ku biyoni mu cigaba da tafiya ko ni ina jin labarin a cikin raina.

MAMAN AFRAH
09025576222



https://chat.whatsapp.com/I3Lo5jRFh1CDcU1leu8VXW



*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)


NA


MAMAN AFRAH


. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 1️⃣3️⃣


*SADIYA*

Maganar Hajiya ta saka Sadiyar shiga ruɗani sannan abu ne wanda bata taɓa zaton cewa ko a mafarki Hajiyar za ta ambata ba, domin cikin ai ba na shege ba ne da za a yi maganar zubar da shi. Maganar da Hajiya ta ƙara yi ne ya dawo da ita hayyacinta jin Hajiyar tana faɗin

"Don haka ki ɗakko mayafi ki zo mu tafi a cire cikin, saboda gidan nan ba matattarar yara va ce ta yaya za a ce daga yin yaye har kin sake ɗurar wani cikin " Cike da jin nauyi da kuma jin kunya Sadiya ta ce

"Hajiya ni ma Allah ne ya ƙaddara ya bani wallahi ba da sani na ba ne...

Hajiya tana ɗaga mata hannu a harzuƙe ta ce

"Sadiya an ce miki jahila ce ni ban san Allah yake bayarwa ba?" Kai Sadiya ta shiga girgizawa alamar a'a, Hajiya bata jira cewar Sadiya ba ta ɗora cike da ɓacin rai take faɗin

"Ke duk ƴan dabarun nan na mata bakya yi, shin mai ya sa vaki saka tsinke a hannu ba ko kuma kin je an saka miki na bakin mahaifa, ko ki sha magani abubuwan tsarin iyali gasu nan barkatai amma kika yi hirim da ke kika sake ɗaukar ciki, saboda baƙin hali da mugun kishi saboda za a yi amarya ku mata dama damuwarku gado shi ya sa baku da aiki sai gasa a haihuwa so kike kafin ta zo kin tara bataliyar ƴaƴa yadda ba za ta taddo ki ba, to albishirinki ba wani dogon lokaci za a ɗauka ba da har kike tunanin tara ƴaƴa a kwana kusa Nasir zai angwance" Idanu Sadiya ta ɗaga ta kalli Hajiya sai kuma ta sunkuyar da kai.

Hajiya ta ƙara kallon Sadiyar kallo irin na ƙasƙanci don ita duk ladabi da biyayyar Sadiya da kuma haƙuri ba wani birgeta yake yi ba ta ce

"Ina so ki sani ciki dole a zubar da shi idan kuma har ƙin ƙi to shawara ta ragewa mai shiga rijiya, ko ya faɗa ko kuma ya sauya shawara, zaɓi biyu ne ko dai ki yarda a zubar ko kuma ki zauna ki raini cikin amma ki sani ɗawainiya ce kika ƙarawa kanki, don Nasir bashi da ƙarfin riƙe mata biyu da yara biyu a yanzu ga kuma hada-hadar shirye-shiryen aurensa shin da wanne zai ji? Wallahi wasu matan baku da lissafi"

Sadiya a fili ta ce

"Ki yi haƙuri Hajiya amma ba zan iya kisan kai ba"

A zuciyarta kuma ta ce

'Duk irin rufin asirin da yake da shi ai a samun Nasir ko ƴaƴa goma ne ba zai gagara ya riƙe ba amma saboda son zuciya da sarewa sannan kuma bai yi dacen mahaifiya ba shi ne kuke raina ni'imar da Allah ya bashi'

Hajiya ta sake cewa
"Dama na zo in kai ki a zubar ne amma tun da kin ce kin ji kin gani to ga wajen nan"

Tana faɗar hakan ta juya ta fice, zuwa jimawa can sai ga Nasir kamar an jefo shi mamaki ma take dama bai tafi wajen kasuwancin ba, ko arziƙin sallama basu samu ba haka ya shigo kamar wanda ya zo filin yaƙi, yana shigowa ya ce

"Sadiya wato kin rainani kin raina mahaifiyata, Hajiya ta zo har gidan nan amma ki ambula mata ƙasa a ido ke ga ishashshiya da mai ko? To ki sani tun da kika ƙi zubar cikin nan ni ba zan dawwama da wahala ba kullum kuna jinya ke da yara ga shirin auren nan" Ya faɗa yana tada jijiyoyin wuya.

Sadiya a zuciyarta ta ce

'Wai namiji da Allah ya ɗora masa gabaɗaya ɗawainiyanda kulawa da iyalansa amma shi ne yake gajiyawa, bayan babu wani abu da Allah ya ɗorawa mace ta sayawa kanta ko ta sayawa ƴaƴa sai dai don kyauatatawa gabaɗaya ɗawainiya kan namiji take kama daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login