Showing 114001 words to 117000 words out of 178828 words

Chapter 39 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt

18 Dec 2025

1456

ban jima da fita ba kuma Amatullahi ce ta ɓata mana lokaci yanzu ma ko asibitin bamu ƙarasa ba" Fatan alkairi ya mata yana faɗa mata yadda ya yi kewarta baki ta taɓe a zuciyarta tana raya shi aka bari da yawo da zance don ita yanzu tana nan tana yaƙin yadda za ta samarwa kanta kyakkyawar rayuwa.

Ƙaramar ƙofar get ɗin ta tura amma sai ta ji a rufe gam hakan ya sa ta yi nocking. Mai gadi da yake zaune kan benci yana ɗann gyangyaɗi ya taso ya buɗe mata tun da lokacin ƙarfe ɗaya saura. Yana ganinta amma bai bata hanya ba sai ya tare ta da tambayar

"Baiwar Allah wa kike nema?" Maimakon Aloya ta bashi amsa sa ta shiga ƙarewa kanta kallo tana duba ko akwai wani waje da ya gani wanda ta yi kama da mai neman taimako da har zai jefe ta da wannn tambayar cike da gadara ta ce

"Matsa min in wuce ko ka ɗauka irin mutanen da suke neman taimako ne ai ban maka kama da mai allazi ahidin ba " Ta faɗa tana neman bangaje shi ya ƙara tare ƙofar yana cewa shi a kan aikinsa yake, nan ta shiga ɗaga murya tana faɗin gidan ƴar uwarta ne, shi dai bai kulata ba ya fito da waya a aljihunsa ya kira Jidda yana faɗin

,"Hajiya akwai wata baƙuwa a waje tana cewa sai ta shigo kina da baƙuwa ne Ta ce ƴar uwarki ce?" Jidda da take kicin ta ɗan yi jim sai ta ce

"A,a amma ka barta ta shigo" Cike da girmamawa ya amsa.

Matsa mata ya yi ta wuce tana faman faɗin da bai matsa ta shiga ba da sai ya rasa aikinsa. Nocking ƙofar ta yi jim kaɗan Saude mai tayata aiki ta zo ta buɗe dama tare suke da Jidda a kicin tana taya ta aiki. Buɗe mata ƙofar ta yi tana mata sannu da zuwa Aliya ko amsawa bata yi ba ta ce ta wuce cikin babban falon inda tana shiga wani ƙamshi mai daɗin gaske ya baibaye mata hanci, fitowar JIdda ta hango Aliya a tsakiyar dalon da sauri ta ƙaraso fuska cike da fara,a bakinta ya ƙi rufuwa. Aliya kuma ganin Jidda ta yi ƴar ƙiba ta murmure ga wani kyau da fatar ta ta yi tamkat wacce take rayuwa a ƙasar waje wani tuƙuƙin baƙin ciki ya cika mata ciki tana tunanin da yanzu ita ce a wannan daular ita ce ta yi kumari ta warware.


Danne abin da ya ɗarsar mata a zuciya ta yi domin ta san wannan damar tana dab da zuwa gare ta ta kusa ta shuga tsakanin ma,auratan biyu wato ta zo ta kafa tata fadar a birnin zuciyar Ibrahim ba tare da wani ta kawo mata cikas ba.

'Oyoyo Aliya shi ne ma ko sanarwa " Ta faɗa tana ƙarasowa suka zauna a kujera a tare Aliya sai yaƙe take, don ita zuciyarta cike take da yadda za ta ɗauki cokali.
Tana ƴar dariya ta ce

"Yanzu don zan zo ganin ƴar uwata jinina sai na sanar da ita? Ai dama na ce bari na zo tun da ke har yanzu kin gagara zuwa na ce wataƙila ku masu kuɗi bakwa ziyartar gidan talakawa" Jidda tana mata ƴar hararar wasa ta ce

"Haba dai wannan wace irin magana ce dama ranar juma,ar nan nake cewa zan je gida in gaishe su sai na ratsa gidanki, daga nan sai na je gidansu Ibrahim na gaishe da ita" Ta faɗa tana kallonta.

Nan suka shiga ƴar hira Jidda tana jin kamar ta goya ta saboda daɗin sa ta ji. Saude ce ta zo da sallama tana ɗauke da plate wanda yake ɗauki da lemon roba guda biyu da ruwan roba guda ɗaya masu sanyi, sai kofi ta zo ta durƙusa ta ajiye a gabanta tana ƙara gaishe ta amsawa ta yi hankalinta a kan Jidda tana ta ƙare mata kallo kamar dai ba wannan Jiddar wulaƙantacciya ba a wajensu amma yanzu gashi ta samu ƴanci, ƴancin ma mai lasisi.


Lemon ta tsiyaya mata ta miƙa mata da hannu biyu kafin ta tashi ta bar wajen, Jidda ta ce

"Saude ki goge kan cooker gas ɗin idan wajen ya huce sannan ki kwaso kwanukan ki jera a kan dining" ,Cike da ladabi ta amsa ran Aliya yana ƙuna wai yau Jidda ce da mai aiki bayan a gida ita ce baiwar gidansu lallai wannan bahaushe yake kira rana ɗaya Allah kan yi bature.

Suna hira inda Jidda take tambayar Kasim wani ɓacin rai ne ya zicyarci zuciyarta ita ba don larura ba ta tsani a kira sunan Kasim ma. Ita ma ta daure ta tambaye ta Ibrahim kafin ra bata amsa wayar Jiddar da take kan ɗaya daga cikin kujerun ta shiga ringing, tashi ta yi ta tafi za ta ɗauko gabaɗaya idanun Aliya a kanta tana ganin yadda doguwar rigar rantsatstsan leshin ta kamata daga baya tamkar dama a jikinta aka yi ɗinkin tana murmushi ta amsa wayar, Aliya tana jin yanayin yadda suke wayar cike da kulawa ta gane da Ibrahim take magana. Sai bayan sun kammala wayar ta ce

"Kin ganshi ma ɗan halak shi ne ya kira ai yana office" Ɗan runtse idanu Aliya ta yi ta buɗe tana tunanin yanzu shi yana can a office cikin AC ita kuma nata mijin yana can cikin rana a kasuwa yana fafutuka.

Sun jima suna ɗan taɓa hira ita dai Saude ta koma ɓangaren su na ƴan aiki inda suke tare da wata dattijuwa kakarta mai suna Baba kuluwa. Kiran sallah ya sa Jidda ta ce su je su yi sallah, bedroom ɗin da aka ajiye ta ranar da aka kawo ta suka shiga Aliya ta shiga banɗaki ita kuma ta fito ta hau sama jim kaɗan ta dawo ta tarae tana sallah ita ma alwalar ta yi ta zo ya kabbara tata sallar. Bayan ta idar suka fito falo ta kawo musu abinci suna cikin ci Ibrahim da ya taho daga office yau da wuri kasancewar kansa yana ciwo bai faɗa mata ba sai ya taho don baya so ta tada hankalinta.

Da sallama ya shigo gaban Aliya y buga da ƙarfi Jidda kuma ganinsa yanzu ya sa ta gane akwai damuwa musamman da ta kalli yanayinsa, cokalin hannunta ta ajiye ta miƙe tsam Aliya kuma ta gaishe da shi fuska babu walwala ya amsa kawai sai take ganin kamar dai ya gane ita ce take kiransa ko kuma ya san ƙudurinta, da sanyin jiki Jidda ta nufe shi yana kallon yadda yanayinta ya sauya da idanunta ta shiga isar da saƙon tambayar dawowarsa a wannan lokacin amma maimakon ya furta mata komai sai kawai ya langaɓar da kai gefe yana lumshe kyawawan idanunsa da suka ɗan kaɗa suka ja tana ƙarasowa sai ta karɓa jakarsa ta office ɗin amma shi ba wannn tallafin ya fi buƙata ba ya fi son jin fatar jikinta a jikinsa ko ya ji sassauci don ya yi ammana Jidda wani tsagi ce na jikinsa yana ji a jikinsa tabbas idan babu Jidda ba zai rayuwa ba ko da ya rayun zai yi rayuwa ne irin ta akwai ruhi amma gangar jiki kamar gawa!.

Hannunsa ya kai ya rungumota jikinsa yana sakin ajiyar zuciya, hannunta ta saƙala a bayansa suka shiga takawa a hankali don ita tuni har yanayinta ya sauya ta fara jinta tamkar marar lafiya, ita da take ji ana cewa idan ɗa bashi da lafiya mahaifiyarsa tana jin jikinta tamkar marar lafiyar wani lokacin ma tare ake yin jinyar da uwa da ɗan ashe dai gaske ne tun da gashi ita ma da yae mijinta har ta ji nata jikin ya amsa.

Aliya kuma sai suka zame mata TV don sai ta zama tamkar mutuntumi a wajen tamkar dai ma basu san da ita a wajen ba, suna riƙe da juna suka fara haurawa sama, Aliya ta kafe su da idanu, har suka ɓacewa ganinta, wani haushi ya cika mata zuciya tana tunanin da yanzu ita ce wannan kyakkyawan yake gwadawa wannan soyayyar wannan a gaban mutane ma yana yi wa matarsa haka ina ga in suka keɓe a ɗaki ɗaya ta san ai sai dai a kira matarsa ƴar gata, don a haka ta fahimci tsantsar kulawa ce da soyayya.
Da nannuyar ajiyer zuciyar da ta sauke ta dawo hayyyacinta tana sakin wami tsaki a fili, duk da daɗin abincin da take ci a take ta ji ya zame mata maɗaci a fili ta furta

"Zan farraƙaku nan ba da daɗewa ba dole za ku rabu, ni kuma in gina fada ta" Ta faɗa a fili tana tunanin tashi ta yi abin sa ya kawo ta gidan amma kuma tana tunanin ya za a yi ta gane cokalin. Ƙaran wayarta ne ya katse mata tunanin da take tana dubawa ta ga Umma ɗagawa ta yi tana ɗan waiwayawa ta ga tabbas babu kowa dama wannan ƴar aikin take ji tana karawa a kunne ta ce

"Hlo Umma"

Umma ta ce

"Aliya ke kaɗai ce?" Aliya ta ce

"Eh Umma amma ban koma gida ba"

Umma ta ce

"Ayyo dama ina son jin kanun labarai ne to na tambaya cewa ke kaɗai ce don kar in je ko wannan mata mazan yana kusa" Wani takaici ne ya turnuƙe ta da aka ambaci sunan mijinta tana sassauta murya ta ce

",Umma ina gidan Jidda zan kira ki"

Umma da mamki ya gama ɗarsarwa a zuciya na tambayar kanta mai ya kaita gidan Jiddar sai dai tun da ta ce tana can babu damar tambaya sai ta fara ƴar dariyar yaƙe wacce ta soyayar ƙarya ce ta ce

"Kuma yanzu Aliya kina gidan ƴar tawa shi ne kike sanya baki haɗamu a waya ba maza bani ita" Aliya ta ce

"Hmmm! Umma bata kusa fa sun hayr sama ita da mijin" Umma ta ce

"Aikin banza da wofi idan tusa tana hura wuta ai za mu gani" Tana faɗar hakan ta kashe wayar tana tunanin dole a samo maƙarƙashiyar da za a yankewa Jidda jin daɗin da take ciki domin ita Umma saboda hassada mugun ciwo ko gidan Jidda bata taɓa taka ƙafarta ba tana ta faɗar wai ɓanya basu fiya zuwa gidan yara ba sai da dalili.

Tana ajiye wayar ta tashi tsaye gabanta yana faɗuwa za ta tafi neman cokali hanyar kicin ɗin ta kama har ta tafi ta dawo jin ƙaran wayarta ta ɗauka ma Umma ce sai ta ga sunan Amatullahi ta ɗaga Amatullahi ta ce

"ƙawata ya ake ciki ne Allah sa dai aikin gama ya gama?"

Aliya ta ce

"Ina nan yanzu na samu dama zan je in duba"

To mai kike jira ko sai kin rasa damar da kika samu"

Aliya ta ce

"Ni wallahi tunanina ma wanne ne cokali" Amatullahi ta ce

",Dalla malama ki yi aiki da hankali da tunaninki " Tana faɗar hakan ta kashe wayar ita kuma ta ajiye ta nufi kicin ɗin da sauri,sai kuma ta dakata ta yi wajen dinning ɗin sai kuwa ta ga gabaɗaya kayan abincin ne ba a ajiye plate da cokula ba tsaki ta yi ta je ta tura kicin ɗin wani ƙamshin girki da bai gama barin kicin ɗin ba ne ya ziyarci hancin ta, amma ba wannan ne a gabanta ba sai ta shiga wurwurga idanu manyan kwanduna ne gasu nan da dankali da doya kainiya ganinta komai gashi na a wadace ban da ma ita ai babu wani abunda zai bata mamaki domin gidan dukiya ta zo mai za ta gani ƙwai ma kamar abin banza gashi nan kiret kiret ita kuwa tun da ta ragargaje na amarcin yanzu sai dai ranar da ya ga yana da kuɗi ya siyo guda biyu wasu manyan robobin spices da curry masu ɗauke da sunan MAMANA AFRAH SPICES ta gane jere da nauikan abubuwa da ta tabbatar duk kayan girki ne, tsaki ta yi ta je inda ta ga cokulan ta fara tunanin wanne za ta ɗauka kar ta je ta ɗauki wanda ba nasa ba a samu matsala babu zato da tsammani ta ji an turo ƙofar wanda hakan ya sa ta tsorata sosai hantar cikinta ta kaɗa sai ta ga wannan ƴar aikin ce da ta ji an kira da Saude.


Cike da girmamawa ta ce

"Ayya ban san kina ciki ba shi ya sa ban nema izini ba" Kallon ƙasƙanci Aliya ta jefe ta da shi ita Saude tana mamakin matar tun da ta san Jidda bata wulaƙanta su tamkar ma ba ƴan aiki ba amma ita wannan sai hararrata take frige ɗin kicin ɗin ta buɗe ta ɗakko ruwan roba guda biyu ta rufe har ra je bakin ƙofa sai Aliya ta ce

"Ina za ki kai ruwan wato kin ga bata nan za ki yi sata"

Saude ta ce

"Sha za mu yi fa"

Aliya ta ce


"Lallai samun wuri har ruwan roba kuke sha?"

Saude ta ce

"Aunty Jidda ta ce bata mana shamaki da duk wani abu ba" Tana faɗar hakan ta juya ta bar kicin ɗin.

Jidda ko da suka shiga ɗakin ta ajiye jakar a kan ƙaramar lokar gefen gadon bayan ta taimaka masa ya zauna, yana dafe kai duk sai tausayinsa ya kamata.

Cike da kulawa ta ce

"Kanka ne yake ciwo?" Kai ya gyaɗa mata, taimaka masa ta yi ta kwanta bayan ta ja masa filon ya kwanta sai ta shiga masa addu'a bayan ta masa cikin sanyin murya mai cike da nuna kulawa da kuma damuwa da wanda ake yi wa magana da muryar ta ce

"Mu tafi a kai ka asibiti ina direban ne" Dakyar ya mata magana ta hanyar faɗin

"Ba sai na je asibiti ba, direbana na aike shi a bakinnget ma na ce a ajiyeni"

Ta ce

"To ba ga direbobi a gidan ba"

Ya ce

Ki bar batun asibitin nan"

Ta rausayar da kai kamar za ta yi kuka ta ce

"To a kira likita ko in kira Mummy sai ta faɗawa Daddy?" Maimakon ya bata amsa sai ya saka hannunsa ya riƙe dantsen hannunta kawai ya mayar da idanunsa ya rufe yana faɗin

"Ki bani magani bana son kowa ya sani idan na sha magani na samu bacci zai daina" Shiru ta yi tana bhn kyakkyawar fuskarsa da kallo yadda zara zaran gashin idanun da suka ƙawata idanun suka ƙara masa kyau sai kuma yadda fuskar ta yi fayau da ita.

Tana cikin kallon ta ji cike ta kulawa ya ce

"Kar ki saka damuwa a ranki kin ji Jiddana" Idanun ta lumshe ta buɗe ta ce

"Ita damuwar da kanta ta san na cancanci na saka ta a raina domin da kanta ta ziyarce ni tun a kallon farko da idanuna suka maka, a inda ƙwaƙwalwa ta harba saƙon kana cikin damuwa tun a lokacin gaɓɓaina suka yi sanyi yanayin jikina ya sauya" Furucin da ta yi ya tabbatar da sun zama hanta da jini shi da ita, don shi ma haka ne yake faruwa da shi idan ya ganta a damuwa!.

A hankali ta zame riƙon da ya mata fitowa ta yi domin ta samo masa abinci kaɗan ya ci ya sha maganin, sai da ta sakko ƙasa da ta ga kwanukan abincin da suke ci da Aliya sannan ta tuna cewa Aliya tana gidan don gaba ɗaya ta manta damuwar Ibrahim ɗinta ya dishashe tunanin komai.

Tunaninta ko ta shiga bedroom ne za ta shiga bayi, dining ta nufa tana zuwa sai ta ga ashe bata ajiye masa plate da cokula ba hakan ya sa ta nufi kicin ganinsa a ɗan buɗe ta tura sai kawai ta ga Aliya tana tsaye, Aliya kuma sai da ta ji gabanta ya faɗi domin bata tsammaci zuwan Aliya a yanzu ba don ita zuciyarta ma tana faɗa mata cewa suna can suna soyayya saboda bata san cewa bashi da lafiya ba.

Cike da wayuncewa ta ce

"Kawai kicin ɗin nake ƙarewa kallo kin san ina son ganin jeran kicin, nawa ma sai na yi ta kallonsa duk da bai haɗu kamar wannan ba" Jidda bata san lokacin da ta yi dariya ba ta ce


"Kina da abin daariya yanzu saboda kallon kicin ɗin ne kika bar cin abinci?"

Aliya ta ce

"Haba Jidda ya za a yi in iya ci bayan tare muke ci kika haura sama"

Jidda ta ce

"Ai da kin ci ni yanzu abinci zan kai masa kaɗan ya samu ya ci ya sha magani ba ya ɗan jin daɗi ne"

Aliya ta ce

",Wayyo Allah sawaqe" Jidda ta amsa da amin

Kicin wear ta nufa ta ɗauki plate guda biyu, sai kuma ta je wajen na cokula ta ɗauki cokali a inda gabaɗaya cokulan iri ɗaya ne a wajen sai kuma ƙasan wasu ne amma masu mariƙa ja ne wanda ta ɗauka kuma coffee ne jikin inda ake riƙewar. Ta haɗa da saving spoon suka fito tare tana tsokanar Aliya wai har ta gama kallon kicin ɗin ita kuma sai take ta murna a ranta ta gane cokalin da yake amfani da shi.

Ita ta tsaya a dining tana zuba masa abincin ita kuma ta ƙarasa ta ci gaba da cin abincin amma naman kazar take ci don ta yi amanna ba za ta rage naman ba saboda ta san idan ta koma nata gidan miya ce zallah ko naman miya babu sai ranar da ya ga da sarari ta siyo naman miyar ko kifi a saka, in kuma kasuwa ta yi kyau sai ya siyo naman a dafa ita a da ne ta matsu ya samu aiki amma yanzu da samun aikinsa da rashinsa duk ɗaya tun da dama tana so ne tun da ta ga yanzu shi yaron kasuwa ne ba wai hamshaƙin ɗan kasuwa ba kenan duk abin da yake nemowa buga-buga ne.


Jidda tana gama zubawa ta rufe da ɗaya plate ɗin ta haura sama Aliya tana raka bayanta da harara kamar idanunta za su faɗo. Tana gama daina hangota da sauri ta tashi ta nufi kicin ɗin ta ɗauki cokalin ta tsaya tana kallon cokalin tana dariyar cin nasara kasancewar bata rufe ƙofar ba Saude da ta dawo ta ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login