Showing 36001 words to 39000 words out of 178828 words

Chapter 13 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt

18 Dec 2025

1455

tabbas ya san Jidda tana masa wani ɓoyayyan so duk da tana bayyanawa amma ya san baki ba zai iya furta yawan son da take masa ba. Duk da ya san wanda take masa ba zai kai wanda yake mata ba.


A can gidan su Kasim, Kasim ne tsaye a ɗakinsa ya rasa yadda zai yi saboda ya faɗawa mahaifinsa cewa ga abokansa nan za su zo su kai su a motoci shi ne yake ta masa faɗa yana mene ne wani abin motoci kar wani mai motar da ya zo masa ƙofar gida, a ƙafafunsu za su je suna tafiya suna hira, haka yana ji yana gani Baban nasa ya kirawo wani mai ruwa ya ce ya zo da zai yi hayar baro, haka ya ɗakko baron aka ɗora akwatuna biyu sai ƙaramin kit guda ɗaya suka nufi gidan su Aliya.


Mai baron yana gaba maza guda uku suna binsa a baya shi kuma Baban Kasim ɗin ya koma cikin gidan.


MAMAN AFRAH
09025576222





https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=ems_copy_t


*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)


NA


MAMAN AFRAH


. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 9️⃣


*SADIYA*

Ta daɗe tana nazarin rayuwa kafin daga bisani ta tashi ta haɗa kayan wanke-wanke ta wanke. Kalifa da ya ƙi kwanciya saboda zafin jikinsa ta ɗauke shi ta goya shi zuwa can ta ji yana mimmiƙewa alamar tana son sauka ga wani ƙananan kuka da yake tana sakko shi ta ga har ya fara kashin kamar ta yi kuka haka ta je ta gyara shi ta dawo dasho ta kwantar ganin ya kwanta ta je ta yi wanka ta fito ta shirya. Sai neman magani take amma babu na zazzaɓi babu na gudawa gashi bata da kuɗin da za ta saya masa maganin hakan ya sa take ta takaicin rashin sana'a domin sana'a makami ce kuma jigo a rayuwa in har kana yi ko yaya za ka fi ƙarfin abubuwa.

Nasir tun da ya fito ya turawa Baba wannan kuɗin bayan sun yi waya, gidan Hajiya ya nufa ana sauke shi a mashin ya shiga da sallama. Bayan ya zauna ya gaishe da Hajiya Husna da Hibba suka gaishe da shi, ya amsa suna ta raha abinsu.

Hajiya ta kalle shi yana cin abincin ta ce

"Gaskiya wannan matar taka an yi makirar mata wallahi, ita kullum bata da aikin sai son ta ɓanɓari kuɗi a jikin ka, ai wallahi an kusa dai yin ta ta ƙare daga ka auri Meenal ka huta yarinya mai hankali da sanin ya kamata kuma ka ga ita ko nawa ka kashe mata baka yi asara ba amma wannan ita ƴar gidan faƙirai ba wani saba kama kuɗi ta yi ba sai shegen munafurci" Ta faɗa tana yatsina fuska. Karaf Husna ta ce


"Hajiya ai daga matar nan ta Yaya sai baya wallahi sumi-sumi kamar munafuka ko kaɗan bata da hali" Hibba ta ce

"Ai gwara ya auri Meenal ƴar ƙwalisa ta zo gidansa ya huta ita ma ta huta"

Hajiya ta ce

"Wallahi kuwa abinsu tuwona maina"

Sai da ya kurɓi shayinsa ya ce

"Ai ni in ban da ƙaddara babu abin da zai saka na auri Sadiya, kuma yanzu ma tun da har ubanta ya nuna zaman auren yake so ta yi to za ta rayu a wahala kuwa"

Hajiya ta ce

"Ai karka saurara mata, dama mashinshi ne ta rasa ya yaɓa maka da yake kai ne mai tsautsayin"

Suna ta faɗin maganganu a kan Sadiyar har ya gama cin abincin yana faɗar ya yi daɗi sosai, Hajiya tana faɗin ai shi ya sa ta ce ake yin abincin da shi yake ci yana murmurewa tun da bakinsa ya saba da cin mai daɗi da mai maiƙo saɓanin Sadiya da dama ta saba da cin tuwo, dubu ashirin ya fiddo ya ba Hajiya dubu goma su kuma kowa dubu biyar sai wata tsohuwar ɗari biyi da Hajiyar ta ce ya bada za a siyowa Kalifan magani, daga haka ya musu sallama ya ce ya tafi kasuwa. Almajiri aka ba ya je maƙota ya siyo maganin rana da maganin kashi na gargajiya Hajiya ta ce su je su kai mata ta haɗa musu da fanadol ta ce su kai a jiƙa a ɗura masa maganin zazzaɓin, bayan ta san maganin yara ya kamata a bashi ba na manya ba.


Basu tashi tafiya ba sai da suka gama ɓata lokaci, lokacin da suka zo ƙofar gidan da ƙafa Husna ta tura ƙofar gidan har sai da ƙofar ta bugu da jikin bango da ƙarfi wanda hakan ya falkar da Kalifa daga baccin da yake a tsorace yana kuka, ko ba a faɗa ba ta san mai mata wannan ɗabi'ar don haka kawai sai ta shiga jiran zuwan su don ta san ƙannen mijinta ne.

Hibba ta ce

"Gafaranmu dai" Ta faɗa a gadarance, amsa musu ta yi domin ta san rainin hankali ne maimakon su yo sallama shi ne suka yi hakan, tana kallonsu ta window tana jijjiga Kalifa suna ƙarewa gidan kallo labule suka bankaɗo suka shigo ɗakih suna wani yatsina suka zauna.

Babu wacce ta yi magana cikinsu Sadiya ta ce

"Su Husna ne yau a gidan namu"

Hibba ta ce

"Gidanku ai yana can gidanku sai ko ki ce yau mu ne a gidan yayanmu, kuma zuwa gidan nan ai ya zama farillah saboda gidan ɗan uwanmu ne sannan kuma ki sa a ranki nan ba da jimawa ba za ku zama ku biyu don yayanmu dole a gallo sabuwar amarya irin matan da ake yayi wayyayu" Ta ji ciwon maganar amma sai ta basar ta ce

"Gidansa ne kam, to Allah ya kawo ta" Daga haka babu wacce ta tambaye ta ya maia jiki Husna ta dangwarar mata da maganin a tsakar ɗakin ta ce


"Saƙo daga Hajiya ta ce gashi nan in dai magani ne da na kashin da na rana har da na zazzaɓi ki jiƙa amma batun wai kike cewa Yaya za a kai shi asibiti bai taso ba" Ɗago idanu ta yi ta kalle su kowacce ta tamke fuska a gadarance amma Sadiya bata ce komai ba sai Husna ta ce

"Wato a faɗa miki saƙon uwar tamu amma ki wofintar saboda ba saƙon taki uwar ba ne" Sadiya ta ce

"Karki zageni Husna, kuma ai na ji saƙon ta ko kin ga na yi musu" Basu bata amsa ba suka ce uhm a tare suna masu tashi suka fita, tana ji suka fice daga gidan babu wacce ta yi ƙoƙari rufe mata ƙofar gidan!.

Ledar ta ɗauka ta duba abubuwan da suke ciki tana jin babu daɗi a zuciyarta tabbas duk macen da bata yi dacen miji ba kuma vata dace da uwar miji ba, sannan dangin miji basa ƙaunarta lallai ba za take jin daɗin zaman gidan aurenta ba.


Nasir soyayya suke shi da Meenal kamar su haɗiye juna, sai dai yanayin yadda take zuwar masa da buƙatar kuɗi abin yana damunsa sai dai da ya faɗawa Hajiya sai ta ce wuyarta a yi auren za ta daina wataƙila da yarinta duk da yarinyar tana da tunani da hangen nesa in ji Hajiya.

Yau ya kama talata inda Hajiya ta sanar da ƙawarta mahaifiyar Meenal za ta kai musu ziyara. Da yammacin ne Meemal da mahaifiyarta suna zaune a falo suna hirar bikin da ake son saka rana Meenal ta ce

"Ni wallahi Momi ba don dai saboda ke ba da babu yadda zan yi in aure wannan Nasir ɗin" Ta faɗa tana jan dogon tsaki, baki Momi ta taɓe ta ce

"To ya za a yi tun da ya nuna yana son ki kuma mahaifiyarsa ma ta nuna tana ƙaunar wannan haɗin, ai sai a yi tuwona maina" Ta faɗa tana wata ƴar bazawarar dariya.

Ƙwafa Meenal ta yi ta ce

"Hummm!. Yaro bai san wuta ba sai ya taka, ni wallahi ba zan ɗauki raini da cin kashin da suke yi wa wannan Sadiyar ba, tsaf za mu raba raini don wallahi ko ita Hajiyar ba saurara mata zan yi ba bare wannan riƙaƙun ƴanmatan ƙannen nasa duk sai na gasa musu ƙasa a hannu, shi kuma Nasir hummm sai ya zama mijin ta ce"

Momi ta dara har da ƴar shewa ta ce

"To Meenal idan baki yi wannan abubuwan da kika zayyano ba kenan ma baki cika ƴar halak ba, ai ba baiwa na kai musu ba ki ƙwatawa kanki ƴanci a gidan miji karki yarda da rainin kowane shege" A daidai nan kiran wayar Nasir ya shigo a inda hakan ya yi daidai da tsayawar napep ɗin da ya ɗakko Hajiya a ƙofar gidan su Meenal ɗin. Da sallama ta shigo gidan Momi ta amsa tana mata maraba tare da cewa ta shiga, ita kuma Meenal da sauri ta tashi ta shige bedroom tana kashe murya suka fara magana da Nasiri.

Nasir ya ce

"My love na matsu mu yi aure ko ma zama tsintsiya maɗauri ɗaya, ke ce taurauwa a gidana ke za kike murza kambunki wancan ta cikin gidan ma karki ba kanki wahala wajen sakata a layin kishiyarki don daga kin zo gidan komai ya dawo hannunki" Ya faɗa yana jin tamkar ya janyo ranar auren nasu da ba a saka ba duk da ana dab da sakawa. Wannan dariyar tata mai ƙaramib sauti wacce take nuni da tana jin kunya ita ta sakar masa tare da cewa

"Ni ka sa ina rufe fuska kunya nake ji Allah" Wani daɗi ne ya lulluɓe shi ya ji tamkar ya yi ihun daɗi don yana mugun son mace mai kunya duk da ya san Sadiya tana da kunya da kawaici amma dai shi yanzu hankalinsa yana kan Meenal ɗinsa wacce yake ji ɗaya tamkar goma, wacce kuma yake riritawa kamar ƙwai.

Hira suka ci gaba da yi tana ta nuna masa tana jin nauyinsa a inda shi kuma yake ji babu ya shi don yadda Meenal take bashi girma sai yake jin ladabin Sadiya kamar dai ma ba wata biyayya ce take masa ba, sun jima suna hirar daga bisani suka yi sallama ya kashe wayar yana sauke nannuyar ajiyar zuciya a inda a wani ɓangaren na zuciyarsa yana jin daɗi yau har sun yi waya sun gama bata buƙaci wani kuɗi daga gare shi ba, saboda ya lura ita bata san yawan tambayar abu kima yake zubarwa da mace!.Don roƙo yana taka muhimmiyar rawa wajen daƙile mutucin wanda yake roƙon, shi ya sa ma wani ya tambayi manzo S.A.W shin mai zai yi Allah ya so shi sannan mai zai yi mutane ma su so shi. Manzon Allah S.A.W ya cewa mutumin ka guji duniya Allah zai so ka, sannan ka guji abin hannun mutane mutane ma za su so ka, kenan duk wanda kake son abin hannunsa yau da gobe kimarka raguwa take a wajensa.

Suna yin sallama ta saki wani gajeran ɓoyayyan tsaki ta ture wayar gefe tare da kwantawa male-male a kan gadon a fili ta ce

"Wahalalle kawai, mutum kai baka son ka ɓamɓaru wato ka ji yau ban roƙi kuɗinka ba shi ne gudun kar na roƙa har wani saurin yi min sallama kake, ai zan shigo cikin gidan" Ta faɗa tana janyo wayat ta shiga wtsapp take ta chart ɗinta.

A falo cike da fara'a Momi ta tarɓi Hajiya a inda suka gaisa daga nan hirarsu ta ƙawaye ta ɓarke e tsakaninsu, Hajiyar tana faɗin cewa ƴan uwan mahaifin Nasir za su ji dangin mahaifin Meenal su kai kuɗin gaisuwa, saboda daga Baban Nasir har na Meenal basa raye.

Suna ta tattaunawa zuwa can sai gashi Meenal ta fito falo tana taku cike da nutsuwa, gaban kujerar da Hajiya take zaune ta je ta tsugunna tana mai sunkuyar da kai ƙasa ta ce

"Hajiya ina wuni" ,Hajiya cike da farinciki ta ɗora hannu a kan Meenal tana amsa gaisuwar tare da yaba hankalin Meenal ɗin, tana ganin idan suka samu Meenal a family nasu sun warke.

Cike da ladabi ta tashi ta fita, Hajiya ta kalli Momi tana murmushi ta ce

"Ƙawata wallahi kin iya haihuwa sannan kin iya tarbiya, haka kawai ya je ya kwaso masa jangwam ai wallahi Nasir da Meenal ya fara aura babu dalilin da zai sa ya auri wata Sadiya kuma wallahi yanzu ma ruwanta ne bai ƙare ba daga zama ya ƙare dole ta fita ta bata waje saboda gidan Nasir na Meenal ne ita kaɗai" Dariya Momi ta yi ta ce

"Ai ƴarki ce komai kika yi daidai ne!." Dariya suke suna ci gaba da tattaunawa, a inda Meenal ta dawo ɗauke da ruwa da lemo a faranta sai kofi ta zo ta durƙusa cike da ladabi da zubawa Hajiya ruwan ta tashi ta bar wajen Hajiya tana ta yabawa Meenal ɗin bata san cewa lumbu-lumbu ce wutar ƙaiƙayi ba.

Ta jima a gidan sai la'asar liss sannan ta musu sallama ta fito za ta tafi lokacin Meenal tana ta aikin munfurci ita kuma Hajiya tana yaba mata a nata ganin taimakawa Momi take. Bayan tafiyarta suka zauna suna ta tsara yadda abubuwan za su kasance idan Meenal ta shiga cikin gidan.

Hajiya tana fita daga nan gidan da ta tari napep sai gidan Sadiya, Sadiya tana tuƙa tuwo lokacin Kalifa yana wasa saboda ya ɗan ji ƙwarin jikinsa ta jiyo Hajiya tana kwaɗa sallama, amsawa ta yi tana mai tasowa daga bayan ta rufe tukunyar dama ta gama tuƙa tuwon. Tun da ta shigo take yi wa gidan wani kallo na rainin wayo tana wani tattaɓe baki Kalifa kuwa kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai shi kuwa da yake ba wani shaƙuwa ya yi da ita ba wasan sa yake ko wajenta bai nufa ba.


Sadiya cike da ladabi ta ce

",Sannu da zuwa Hajiya" Bata amsa ba ta ce

"Ke dai Sadiya ki ji tsoron haɗuwarki da Allah"Sadiya tana kallonta tana jiran ƙarin bayani don ita bata ga abin da ta yi da za a mata wannan furucin ba a nata ganin ita ce ya dace da ta jefe su da wannan kalmar. Hajiya bata jira cewar Sadiya ba ta ɗora da faɗin

"In banda shegen son kuɗi kike ɗorawa yaro jinya ga yaro nan yana wasa amma har kina ikirarin kai shi asibiti wannan da maraya ne Nasir ba na raye kika aure shi da ya taɓa ya ji gabaɗaya sai kin talautashi a shegen kawo buƙatun naki!" Sadiya kai ta sunkuyar ƙasa ta rasa ma abin da za ta ce mata amma duk da haka sai ta yi ƙarfin cewa

"Wallahi bashi da lafiya ai shi Abban nasa ya...

Hannun da Hajiya ta ɗaga mata ne ya saka ta haɗiye sauran maganar da ta guntso a bakinta. Hajiyar ta ce

"Ai komai ya kusa zuwa ƙarshe zai auro mace mai ladabi da tsoron Allah, mai tattala masa dukiya wacce ta san darajar dangin miji wacce za ta ɗaukeni tamkar ni ce silar zuwanta duniya" Idanu Sadiya ta ɗaga ta kalleta ta haɗiye ɓacin ran da ya ziyarci zuciyarta, don ta ji ba daɗi da ta lissafa abubuwan kenan duk waɗannan abubuwan ita bata da shi, ta ce

"Hajiya ki shiga ɗaki mana baki zauna ba kina tsaye" Baki ta taɓe ta ce

"Ai tuni aka bani wurin zama a inda aka san darajata, aka bani ruwa ana girmamani ai in sha Allah shekara ba za ta rufa ba sai Meenal ta tare a gidan Nasir!" Tana faɗar hakan bata jira komai ba ta juya ta fice daga gidan ta bar Sadiya tsaye tana maimaita sunan Meenal a zuciyarta ita dai Meenal ɗaya ta sani ƴar gidan ƙawar Hajiyar don ta taɓa zuwa gidan ma ita da su Husna lokacin tana amarya suka zo.


Juyawa ta yi ta nufi wajen tukunyar tuwonta, a ranta tana mamakin mutum nawa take aure, Nasir ya ci zarafinta ƴan uwansa ga kuma mahaifiyarsa su basu ma san auren ya fice mata a rai ba don bata da yadda za ta yi ne.



*GIDAN BABA*

Wajen ƙarfe goma na safe Baba ya fito daga ɗaki yana gyara zaman babbar rigarsa ya janyo ƙofar ɗakinsa ya rufe ya kalli Mama Habiba da take wanki ya washe baki ya ce

"To mu fa Allah ya yi aure da marar kwabo za mu tafi na san yau dai ɗari biyar ɗina da nake sayan awarar rana ta huta" Ɗagowa ta yi daga wankin da take tana masa kallon rashin fahimta ta ce

"Yau ɗumaman tuwon safen ne ya ƙosarka sosai da gar ba za ka buƙaci abincin rana ba?" Wata dariya ya yi irin ta ba za ki gane ba ne ya ce

"Ana ga yaƙi ke kina ga ƙura!. To Baban abokin abokina ne ya rasu kuma gidansu masu mugun kuɗi ne wato uban ya bar tarin dukiya kin san kuwa wajen zaman makokin za a ci jar miya, ni ban ma taɓa ganin wanda Baban nasa ya mutun ba kawai dai labari abokina ya bani cewa jiya sun yi ciye-viye da suka je gaisuwa shi ne na masa Allah annabi ya rakani in yi gaisuwa, kin ga gwara mu tafi tun da wuri da zafi -zafi ake bugun ƙarfe sannan da sanyin safiya ake kama fara" Duk abin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login