Showing 69001 words to 72000 words out of 178828 words
Chapter 24 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
bashi haɗin kai, kamar kuma ba a bacci ba ne kamar dai a zahiri ne kallo ta shiga ƙarewa Kasim da yake shararar bacci ko kayan jikinsa bai mayar ba. Hannu ta kai ta rufe bakinta gudun kar ihun da take ƙoƙarin wwace mata ya fita, a kiɗime ta sauka daga kan gadon tsabar ruɗani bata san ma ina take jefa ƙafafunta ba, ko kaya babu a jikinta haka ta ɗakko wayarta da ta gani a kan madubi da hanzari ta fito daga falon tsakar gida ta nufo tana fitowa ta yi tozali da injin da bashi da maraba da tsoho wani haushi ya turnuƙe ta duk da halin da take ciki ya doke wannan.
Kicin ta nufa ta kamo sunan Umma, Umma da take kan sallaya Abba bai dawo daga masallaci ba, tun da ta idar da sallah take zaune a kan sallayar ta doka uban tagumi tana tunanin Aliya da gidan da ta tafi zaman aure babu abin da ya fi ƙona mata rai da akance gidan Jidda haske ral amma gidan Aliya ana shiga da amarya inji yana mutuwa dakyar aka samu ya tashi sai da masu gyara suka masa ribdugu. Tunani da damuwarta ɗaya Jidda tana can ta kwana a gida mai kyau Aliya kuma a gidan ya ku bayi.
Tana cikin wannan tunanin ta ji ƙaran wayarta gabanta ya yanke ya faɗi da sauri ta nufi wayar don tana tsoron ko sanarwae mutuwa za a faɗa mata, sai dai ganin sunan Aliya ya sa ta danna Ok da sauri tana karawa a kunn Aliya ta fashe da kuka ta ce
"Umma kin san wa na aura?"
Gaban Umma ya bada dididdimdimmm a tsorace ta ce
"Aliya ba Kasim kika aura ba"
Aliya ta ce
"Umma ki bar maganar wai Kasim na aura eh shi na aura amma Umma akwai ɓoyayyan al'amari wallahi mai firgitarwa Innalillahi wa inna ilaihi Umma ... Na aura!".
Umma da take tsaye sai gata gata ta yi zaman ƴan bori idanunta tamkar za su faɗo numfashinta yana barazanar guduwa ya barta...
*KU JE KU DISKANTA SHIN WACE CE A CIKIN KU ZA TA BANI AMSAR WA ALIYA TA AURA? NA BAKU GARI😃* *AMMA* *KO NI NA TSORATA SA ABIN DA TA FAƊA LALLAI KASIM YA SHAMMACE MU, SAI DAI AMSAR TANA NEXT PAGE IN MUNA RAYE*
Shin wai bakwa neman maganin mata mai inganci don ku birge mazajenku? Ku kankarowa kanku mutunci da magungunan sa nake siyarwa akwai maganin sanyi akwai atamfofi lesuna zanin gado takalma kayan yara akwai plazzo set na yara da manya kai komai ma akwai mai so ya min magana don mallakar nasa har kayan kicin duk akwai a farashi me sauƙi
MAMAN AFRAH
09025576222
https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=ems_copy_t
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 1️⃣4️⃣
*SADIYA*
Duk da kasancewar ta mai haƙuri da kawar da kai, komai ya farutana yin kamar bata gani ba idan kuma ta ji tana yin kamar bata ji ba, sai dai wannan furucin nasa ya taɓa mata zuciya. Ta yaya za a yi ya faɗa mata cewa saboda Meenal ya saya mota ita da bata zama matarsa ba duk da za ta zama, wato su iyalinsa basu kai matsayin da za a sayi mota saboda su ba, har ya duba ƙwayar idanunta yana faɗar saboda Meenal ya sayi mota don kar ƙawayenta su ce bashi da mota. Danne abin da ya ɗarsu a zuciyarta ta yi tare da ƙoƙarin ƙirƙirar wani murmushi don a a rayuwa ba komai ba ne sai mutum ya magantu a kansa, ba komai ne sai ka yi magana ba, ba a kowane abu ake ƙorafi ba!.
Tana murmusawa ta ce
"Amma fa ka yi namijin ƙoƙari!.Gaskiya gwara da ka siya ko don ka fitar da ita kunyar ƙawaye"Ji ya yi kansa ya masa wani girma yana riƙe da Kalifan ya washe baki ya ce
"Ai kam kin san an ce amarya sai da lallashi" Tana dariya ta ce
"Gaskiya kam amarya ai hukuma ce sai da lallashi" Yana kallonta don ya ji daɗin furucin ta ya ce
"Uwar gida fa?" Wani murmushin ta sake yi ta ce
"Uwar gida sai haƙuri" Ya ɗan yi jim sai ya ce "Kenan ita uwar gida sai haƙuri mai ya sa kika ce haka?" Ta ce
"Kawai dai na ga dacewar hakan" Iska ya ɗan hurar ya ce
"Kuma maganarki haka take"
Sadiya ta ce
"Dama mana" Kalifa ya miƙa mata ya juya ya ce mata yana zuwa ya rufo ƙofar, cikin gidan ta dawo tana jin lokacin da ya tada motar ya yi gaba, don dama ya iya mota, Kalifa ta ajiye ta ɗauki abin wasa ta bashi, ta cigaba da uzurinta don ita yanzu sana'ar nan ta fiye mata komai don ta lura ita ce gatan ta kuma rufin asirinta.
Kwanci tashi asarar mai rai yanzu cikin jikinta yana da wata bakwai, ya fito sosai, sana'a kuwa yanzu ta kafu, duk unguwa an san ta wasu ma daga wani wurin suna zuwa siya, don yanzu har da nono take ɗaurawa mai kyau sannan ribar da take ɓoyewa ta haɗa ta siyar da frige ɗin ta cika ta saya freezer amma ba sabuwa ba sai dai babu abin da ya same ta. Da yake Allah ya saka mata albarka sosai ta bunƙasa, yanzu duk ƴan ƙananun kayan jarirai tana saya wanda za a iya sakawa maza da mata, duk da tana zuwa awo amma ita take yi wa kanta komai kama daga kuɗin napep zuwa asibiti da kuma abubuwan da za ta buƙata har magunguna, tun da idan ma ta faɗa masa cewa za ta je asibiti iyakarta ya ce
"Sai ta dawo" Har ta saba da wannan furucin ita yanzu tun da dai tana sana,ar nan kuma tana rufa mata asiri bata damuwa ma da watsi da kuma wofantar da haƙƙoƙinta da yake yi. Yanzu ta fara siyar da farin man Ok da kuma manja, curry da sauran kayan miya na amfanin gida, yanzu gidan koyaushe baka rasa wanda zai zo siyan abu. Hatta kayan gwanjo siya take nata da na Kalifa sai ta saya kamar sabbi ta wanke ta goge suke saka abin su don haka dogayen riguna da wando da riga da kuma riga da skirt duk ta saya tana kwalliyarta a cikin gidan ta fito abinta tsaf idan ma tana marmarin abu sai ta siya ta dafa kayanta shi ma Nasir ɗin ya ci, hakan ya sa yake ba su Hajiya labarin ai kuwa Hajiyar take ce masa dama ai ta faɗa masa idan ma tana sana'ar duk a hidimar gida kuɗin zai ke ƙarewa, basu san sana'a sirri ba ce, tana yin alherinta a ciki.
Yau ta kama juma'a bayan ta gama ayyukanta, lokacin Kalifa ya yi bacci, tana so ma ta tashe shi saboda yamma ta yi amma kuma gudun rigima sai ta ce idan ta yu wanka ta shirya sai ta tashe shi. Bayan ta yi wanka ta shafa fowder ta lips stick, riga da wando na plazzo ta saka da hularsu kalar dark blue kayan sun karɓe ta ta shafa turare sai ƙamshi take buɗaɗawa. Cikn ta da ya fito ya yi ɗas a cikin rigar, ta je kusa da Kalifa za ta tashe shi don lokacin miyar dare ce kawai take dahuwa a kan gawayin ta gama tuwo. Sallamar wata yarinya ce ta dakatar da ita, inda ta ce ta bata farin mai kwalba guda da kuma curry ɗaurin ɗari biyu guda biyar sai zoɓo na ɗari uku, kasancewar dama man ɗaurawa take ta ajiye kowane awo ta bata duka ta bata canjin, ta karɓa ta juya ta fita ita kuma ta je za ta ajiye kuɗih kawai sai ta ji ƙaran tsayuwar mota a ƙofar gidan, ƙaran rufe ƙofofin motar ta ji sai kuma ta ji an turo ƙofar gidan, muryar Nasir ta fara jiyowa yana ɓaɓɓaka dariya, sai ta ji yana shigowa sai kuma take jiyo takun takalmi ƙwas-ƙwas wanda hakan yake nuni da ƙaran takalman mace ne, sai kuma zuciyarta ta bata tare da su Husna yake ƙannensa, har ta fara fargabar zuwansu saboda rashin arziƙinsu kar su mata halin nasu na rashin mutunci tun da su ba sa tunanin makomar nasu auren idan sun yi tun da su ma mata ne watarana gidan miji za su je!.
Wasu muryoyi ta ji sun sallama a gadarance, muryar ɗaya ta so ta san mai ita sai dai bata gama tantancewa ba, sai kawai ta jiyo muryar Nasir yana faɗin
"Haba ku da gidanku, sai wani rafka sallama kuke yi kamar baƙi"
Wata murya ta jiyo ta ce
"Gaskiya dai ai gidanta ne kuma gidan yayanta abu ne ya haɗe mata biyu" Duk wannan maganar da suke kafin su shigo tsakar gidan ne wato daga zauren gidan, kafin ta gama dawowa daga shan ruwan mamakin maganganunsu ta yi saurin amsa sallamar tana fitowa daga falon nata.
Hakan ya yi daidai da shigowarsu tsakar gidan suka yi ido huɗu da Sadiya wacce shigar da ta yi ta ɗauki hankalinsu ganinta tsaf tamkar ita ce amaryar ta yi ƙiba abinta kamar bata da wata damuwa, don dama ita damuwa sai idan mutum ya buɗe cikinsa ake sanin yana da ita duk da a lokuta da dama tana iya bayyana kanta a gangar jikin mutum.
Ba ma wannan ne ya ɗan taɓa musu zuciya ba, yadda cikin jikinta ya mata cif-cif shi ne abin da ya ɓatawa Meenal rai, a take ta ji wani kishi ya baibaye mata zuciya tana jin tamkar ta maƙure Sadiyar ita bata ma san tana son Nasir haka ba sai da ta ji kishin Sadiya ya tokare mata maƙoshi ya ƙi gaba kuma ya ƙi baya!. Basu kaɗai lamarin Sadiya ya tafi da su ba hatta Nasir ta shammace shi, saboda kayan jikinta bai taɓa ganinta dansu ba sabbi ne, da ta saya wajen maman afrah don tana siyar da set ɗin plazzo na yara da manya sannan tana siyar da iya wandon plazzo ɗin. Ba wai don bata yin kwalliya ba sai dai don ɗinkin ya fita ne yadda wandon ya baje sosai ya ƙara mata kyau rigar kuma cif kamar don ita kaɗai aka ƙirƙire ta.
Sadiya ganin su Meenal ya taɓa mata zuciya a nata ganin ba ƙaramin cin fuska ba ne namiji ya shigowa da mace matarsa da zai aura, kuma bai sanar da ita ba sai dai kawai ta gansu sun shigo, duk da cewar Babarsa da Babar Meenal ƙawaye ne amma ai ya kamata a ce an sanar da ita, kai ita gaba ɗaya ma bata ga alfanun hkan ba domin mai suke ci na baka na zuba ai in dai gida ne kamar yau ne za ta shigo shi, tun da yanzu biki bai fi sati uku ba kuma an kammala mata komai na ɓangarenta. Sadiya bata so su ga lagwanta daga su har Nasir ɗin don haka sai ta ƙirƙiri bariki kamar yadda su ma suka mata bariki cikin wani salon murya ta ce
"Oyoyo baby sannunka da zuwa, kenan dama ba sai an yi sallar magribar za ku zo ba, ka ce mini sai an yi sallar magriba za ka kawo su?" Ta faɗa tana wani rausaya kai gefe tare da yin fari da ido, mamaki al'ajabi ne ya kama kowane ɗayansu, musamman Nasir da hakan ya fi kasancewa baƙon abu a wajensa hakan ya sa ya saki baki galala yana bin ta da kallo. Meenal kuwa wani takaici ne ya turnuƙe ta tana jin tamkar ta kurma ihu tana ganin Sadiya bata isa ba bare ta kai har Nasir ya yi wata magana da ita musamman yadda ƙannensa suke sanar mata ita ba komai ba ce a cikin gidan, amma yanzu gashi ta ga akain haka, don bata taɓa tunanin Nasir zai sanar da Sadiyar zuwanta ba, ta so a ce Sadiyar bata san da zuwanta ba domin ta ƙona mata rai sai gashi sun samu saɓanin abin da suke zato, wato ma yadda ta so ta ɓatawa Sadiya rai na zuwanta gidan sai gashi ta ga ko a jikin Sadiyar wai an tsikari kakkausa.
Maganar Sadiya ce ta katse su da faɗin
"Sannunku da zuwa amarya bakya laifi" Wani irin haɗe rai Meenal ta yi ita kuma ƙawarta ta ɗauke kai tamkar ta ga kashi tun da sun gama shiryo yadda za su ƙular da Sadiya ta yadda abin zai tsaye mata a rai har ya hanata sukuni. Shi kuma Nasir sai ya tsinci kansa da faɗin
"Eh dama yanzu ne za su zo" Shi kansa vai san dalilinsa na faɗin hakan ba tun da ya san basu yi maganar da Sadiyar ba. Murmushi Sadiya ta yi ta ce
"To ai ita da gidanta ma za ta iya zuwa koyaushe duk da dai ba a kawo ta ba" Kallon kallo aka shiga tsakanin Meenal da ƙawarta Meenal a zuciyarta tana rayawa a ranta cewa dole idan ta shigo gidan nan Sadiya ta faɗawa aya zaƙinta.
A hankali ta fara wani taku tana jijjiga jiki yadda za ta ɗauki hankalin Naair ɗin ta yadda zai shagala da kallonta har Sadiya abin ya bata haushi sai dai aka samu akasi shi kawai sai ya ji kamar wanda aka jarabce shi da kallon Sadiya kawai ji ya yi tamkar an sanya maganaɗisu a tsakaninsu wani abu yake ji yana fusgashi dangane da ita. Ƙawar Meenal ta ja wani gajeran tsaki ta kama hanyar ɓangaren Meenal ɗin kamar yadda ta ga Meenal ta yi sallamar wani yaro ya katsewa kowa hanzari inda ya ce a bashi farin mai na dubu biyu da ɗari biyu, kasancewar a ƙulle suke a wajen sannan kuma gashi kuɗin nasa ba canji banne dubu biyun ce da ɗari biyun sai Sadiya ta ce
"Ɗan yi haƙuri ka ji ka zo a daidai lokacin da zan nunawa ƙanwata ɗakinta, bari in zo in baka" Shi kuma Ibrahim jin wannan furucin sai ya ce
"Bari in bashi" Ya faɗa yana nufar wajen zai ɗakko masa man, shi ya yi hakan nr don ya birge su Meenal su ga kamar dai ba ya wulaƙanta matarsa saboda ya san an ce wasu matan sun tsani namiji mai wulakanta matarsa ya gida, saboda suna ganin su ma wataran idan sun shigo gidan zai musu hakan. Da to ta amsa masa ta fara bin bayansu don lokacin Meenal har ta murɗa ƙofar za ta buɗe, zuwan Sadiya ya sa ta dakata da abin da take a ƙufule ta ce
"Ba ma buƙatar taimakon ki" Sadiya sai ta saki murmushi ta ce
"Ayya!. Dama don an ce baƙon ka annabinka amma tun da haka ne babu damuwa s fito lafiya" Nuna rashin damuwa a kan lamarin abin da ta faɗawa Sadiya ya sa ta ƙara jin zafi a ranta, ita kuma Sadiya ta juya ta koma lokacin har Nasir ya ɗakko man yana nuna mata cewa wannan ne? Su dama tsabar ma ransu da ya ɓaci suna shiga suka fito na farko dai yanayin yadda suka samu akasin yadda suka yi zato daga matar gidan da kuma yanayin ginin da aka yi sai ta ji bai wani kwanta mata ba tun da lamarinta akwai ƙarya a ciki, haka ya sa suka fito buguzum-buguzum Sadiya kuma da ta bashi amsa da shi ne man sai ta je za ta karɓa ta tsaya dab da shi wani ƙamshin turarenta ya buge shi, bai san lokacin da ya yi murmushi ba ita kanta Sadiyar abin ya bata mamaki sai dai sakin murmushin da ya yi a kan idanun Meenal wacce ta ƙara cin karo da haɗuwar hannayen Sadiya da Nasir a daidai lokacin da zai bata man, ko kallo basu ishi su Meenal ba sannan ta yi da na sanin zuwanta gidan, don tana ganin cin fuska Nasir ya mata da gangan. Hanyar waje suka nufa, Nasir ya shiga kiransu amma ko waiwaye babu wacce ta yi a cikinsu.
Bao bi ta kan Sadiya ba wacce ta karɓi man ta ba yaron a take ya takewa su Meenal baya yana faman rafka musu kira, yaron ma fita ya yi Sadiya a fili ta ce
"Ku kuka sani ku ƙare ƙalaw" Ta faɗa tana mai shigewa ɗaki hannunta riƙe da kuɗi.
Su Meenal ko kallon inda motar Nasi take basu yi ba, haka suka fara tafiya kamar za su tashi sama, Meenal ta ce
"Wai ni Nasir zai yi wa barikanci,saboda na ce zan je in ga ɗakina saboda tsare -tsaren kayan da za a saka a ciki shi ne har zai ke kula matarsa da ya san yana son ta uban wa ya ce ya ce zai aure ni?" Ta faɗa tana yin ƙwafa tare da raya cewa zai san ya yi da ƴar halak. Ƙawarta Huzaifa ta ce
"Wai baki ga har wani yauƙi take ba, yanzu wannan matar ce za a ce tana fuskantar wulaƙancin ɗa namiji anya ba rufarki aka yi ba?" Ran Meenal ne ya ƙara ɓaci tana cin wani alwashi a kan komai kamar ta yi kuka ta ce
"Abin ya zo da rainin wayo, wai ni ba ma wannan ba sana'a take yi fa da alama kina gani ana sayen mai, ni da babu uwar da