Showing 102001 words to 105000 words out of 178828 words

Chapter 35 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt

18 Dec 2025

1435

ba Meenala" Ta faɗa tana buɗe jakarta ta ɗakko wani ƙullin magani a leda fara da baƙa. Ta ce

"Wannan na farar ledar ki jiƙa a ruwa ki yi wanka, shi kuma na baƙar ledar sai ki sha a shayi" Ta faɗa tana bata amma bata karɓa ba ta jefe mata tamabayr

"Maganin mene ne?" Hajiya sai da ta ɗan waiwaiya gudun kar wata ta taho daga cikin ƙawayen ta ji ta juya tana fuskantar Meenal tana sassauta murya gudun ma kar Sadiya ta musu laɓe ta waje ta ce


"Maganin karayar asiri ne, da alama jifanji aka yi Meenal tun da safe bakya cikin hayyacinki" Wata bazawarar dariya Meenal ta yi ta ce


"A hayyacin wa nake to? Mai ma na yi?"

Hajiya ta ce
"Meenal maganganu karazube kike yi babu taunawa bayan ba haka kike ba duk kin sauya ko ni kina min magana kamar sa,arki, haka su Hibba da suka zo da safe ma kika ƙi ganinsu ina jin ma baki san sun zo ba saboda bakya cikin hayyacinki, dama zama da kishiya sai da takatsantsan babu abin da ba za ta yi ba din ganin ta dusashe haskenki a idanun mutane da na dangin miji, jin an ce kina da ladabi da biyayya da girmama na gaba da ke ta shiga ta fita za ta ɓata miki asali"

Meenal ta ɗan lunshe idanu ta buɗe ta ce

"Bari ki ji in faɗa miki rasss nake, ke baki san a zamanin da ake ba ne yanzu? Ya za a yi kyakkyawa da ni yarinya ɗanya sharaf ƴar zamani in zauna miji ko uwar miji suna juyani kamar wata waina? Idan ma za ki ɗauke idanunki daga sabgar gidan ɗanki to ki kauda idanunki ki bar mu mu shaƙata mu more amma in kika ce za kike shiga sabgar da ba ruwanki ki yi uwa da makarɓiya wallahi hawan jini fa ciwon zuciya zai kashe ki" Meenal ta faɗa cikin halin ko in kula tana cikin faɗa wayarta ta yi ƙara ta duba ta ga Nasir ne sai da ta shawaɓe fuska alamar shagwaɓa ta kara wayar a kunne tana wani buga ƙafa kaɗan a ƙasa ta ce

"Baby ka je ka zauna ka barni da kewa" Hajiya neman mai Jijjigata take yi don ta tashi daga mafarkin da take don abin ya shallake tunaninta an barta riƙe da ledojin maganin da sai da ta zare naira na gugan naira har naira dubu goma aka bata, duk don a dakatar da rawar kan Meenal a dawo da ita hayyacinta take mata biyayya ya zamana ita take jan ragamar gidan ɗanta amma sai gashi Meenal tana tababtar mata cikin hayyacinta take da alama ma inda kunya take Meenal ko ta wajen bata bi ba.


Daga ɗaya ɓangaren Nasir ya ji wani daɗi da ta masa magana shi dama ba ya son wannan gadarar da take masa hakan ya sa ya washe baki daidai nan Meenal ta danna handsfree Hajiya ta jiyo muryarsa yana faɗin


"An ciko gas ɗin taɓ kuwa amma ya ci kuɗi ko dama tsada yake ko don na daɗe ban saya ba na saba siyan buhun gawayi kuma Sadiya da adani sai ki ga ya daɗe tana amfani da shi" Hajiya jin an ce gas ya ci kuɗi ranta ya ɓaci ta fara tunanin yawan kuɗin kamar a aljihunta aka fitar tana tunanin yanzu idan hsr haka gidan Nasir zai ci gaba da kasancewa a hannun ƴan sari to ya za a yi da auren Hibba da Husna bayan shi ne komai nasu.

Meenal bata amsa masa maganar wancan ba ta ce

"Sweet heart lemukan nan fa ba kala ɗaya za ka siyo ba ka haɗo kaloli, sannan ka ƙaro da mararsa sanyi kamar katan biyar sai a saka a frige saboda baƙi" Da to ya amsa mata sai da ta saci kallon Hajiya da take cike kamar za ta yi bindiga ta sassauta murya ta ce

"Ka taho min da fanadol jikina duk ya ɗau zafi saboda aikin da ka kwana kana yi

Shi kuma ya ce

Ai kam jiya na... Kafin Hajiya ta gama jin mai zai ce ta juya har tana haɗawa da gudu ta yi hanyar falo....


MAMAN AFRAH
09025576222
[11/19, 6:12 PM] 😍: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=hqrt1


*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)


NA


MAMAN AFRAH


. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 2️⃣0️⃣




*HAJIYA*

Har tana tuntuɓe a ɗan tudun ƙofar da ya raba falo da bedroom sai da ta zo falon ta ja birki kamar wacce aka biyo da gudu ko kuma wacce aka saka tsere. Mutanen falon da kallo suka bita suna tunanin dalilin gudn nata don duk a firgice take, sai da ta ga sun zuba mata ido ta gane ashe dai a guje ta fito. Wani takaici da haushin Meenal ne ya turnuƙe mata zuciya tana ganin ta yaya ma za a yi a ce tana surukarta take maganar kwana da miji, ba ma wannan ma ko da an ɗauke matsayinta na suruka ai tana matsayin uwa a wajenta tun da ƙawar uwarta ce.
Meenal kuma tana ganin abin da ya faru sai ta fara danne dariyarta marar sauti don abin ya bata dariya ta tabbatar duk tijarar hajia matsayinta na uwar miji ba za ta so jin yadda daren farkon ɗanta ya kasance ba kuma ma a kan kunnen nata ɗanta ne zai ja ragamar bayanin. Ɗan wayincewa ta yi tana faɗa masa ya taho da panadol ɗin kafin ta yanke kira a fili tana furta

"Wallahi in dai ni ce mu zuba ni da ku ɗan halak ka fasa don wallahi ba zan ɗauki rajnin hankali ba sai dai mu yi ta bugawa ni da ku muna fafatawa domin idanuna a buɗe suke rasss."
Hajiya ɗan wayuncewa ta yi ta nemi waje daga can ƙaramar kujera ta zauna tana jiran Meenal ɗin ta gama wayar don ta fara tunanin ba hayyacinta take ba har yanzu domin da a hayyacinta take yarinya me kunyar kamar Meenal ba za ta yi magana da mijinta irin wannan a gabanta ba, shi ya sa har yanzu take ƙarfafa cewa bata san ina kanta yake ba.

Abu na gaba tana tsoron ta fita tsakar gidan ta ci karo da abin da aka ɗakko a store ɗin ɗanta gani take zuciyarta bindiga za ta yi, in akwai abinda ta tsana a duniya bai wuce a ce wani abu da zai taɓa lafiyar kuɗin Nasir ba shi kaɗai ta haifa namiji kuma shi ne nauyin dukkan ɗawainiyarsu idan har ya haɗu da kangararriyar mata ta san shikenan sun shiga uku a yadda ta fara ganin take-taken Meenal in har a zahiri ne daidai take gani ba wai jifanta aka yi ba wato ba asiri ba ne gaskiya babu tantama sun faɗa hannun ƴan sari!.
Meenal tana gama wayar ta zauna ta ɗora waya da dadironta suna ta shan soyayyarsu don tana ƙara tabbatar masa babu rabuwa tsakaninta da duk wani abokin holewarta don ta yi wani aure, babu abin da za a fasa. Zaman da ta yi ta san duk ƙwawar hajia dole ta gaji ta haƙura domin ta san za take ta tunanin bata gama wayar ba.

Hajiya kuma sai jera hamma take don da yanzu a gida ne da ta fara haramar cin abincin rana amma yanzu babu hali bata ma cikin nutsuwa da kwanciyar hankali an barta tana ta tangaririya a titi tun da sanyin safiya tana zuwa wajen malami tare da kashe naira dubu gomar magani bayan gashi shi kansa maganin ba a karɓa ba bare ta saka ran Meenal ɗin za ta yi amfani da shi.

Suna gama wayar sai kiran Mominta ya shigo hakan ya sa ta ɗauka cike da farinciki suke waya Momi ta ce
"Ta gaban goshi fatan dai babu matsala" Meenal ta ce
"Momi ki bar batun matsala ko a mafarki ai tun da dai ni ce ƴarki to kin yi bakwana da matsalar damuwar ƴa mace a gidan aurenta don kin san babu wanda zan yarda ya yi awon gaba da ƴancina a gidan miji" Momi ta jinjinawa ƴarta tana ƙara bata ƙarfin gwiwa da jaddada mata kar ta kuskura ta bada fuskar da za a rainata a gidan aure!.
Meenal ta ce

"Momi ni dai zan yi iya iyawata don ganin ba a tozarta ni ba duk da na san wani lokacin duk ƙoƙarin mutum na gujewa natsala sai ta afka masa sannan matsaloln gidan aure ba kidahumanci ne yake kawo su ba ko rashin wayo, sai dai ya danganta da wanda ka dace da shi a matsayin abokin rayuwa ko kuma suruka da dangin miji, duk da akwai matan da suke bayar da kansu suka sakin jiki a musu kowane cin kashi duk da cewa mace ƴar biyayya ce amma ba ce ta bada fuskar da za ta zama baiwa ko kuma abar wulaƙantawa ba" Tun da ya fara bayani Momi take jinjina mata daga na ta hau faɗin
"Kar ki kuskura ki ragawa Hajiya na faɗa miki daga ita har ɗanta ki koya musu karatun ta nutsu don na ga da sauransu a karatub duniya sun ɗauka don kina ƴata za su ci kashi a kanki ko su juye kowace bola a kanki to ba haka take ba"
Meenal ta hau ba mahaifiyarta labarin yadda abubuwa suka wakana tsakaninta da Hajiya da Nasir har ma da zuwan Hajiyar gidan ta kawo mata magani wai bata cikin hayyacinta sai dai bata faɗawa Momi wayar da ta yi a gaban Hajiyar ba.
"Magani Meenal hauka ake za ki karɓi magani a wajen wani barw ki yi amfani da shi, karki manta ni da Hajiya tif da taya muke hakan ba zai hana ta tarwatsa ko farraƙa tsakaninki da ɗanta ba don son zuciya irin nata kin sani bata ƙaunar a ɗanɗani arziƙin ɗanta ta fi son koyaushe daga ita sai ƴaƴanta don haka tana iya karɓo maganin da za ta rage miki matsayi a wajensa don kar yake kyautata miki, ko kuma ta yi maganin da za ki koma kina mata biyayya kamar vaiwa ta taka ki yadda ta so kamar yadda suka mayar da wannan uwar gidan marar ƴanci da galihu a wannan gidan"

Meenal ta ce

"Momi dama ina sane ba zan yarda ma na yi amfani da shi ba, sai faman faɗi take wai bana hayyacina ta fi so in ci gaba da ƴasƙantar da kai irin yadda nake nuna mata kafin ya aureni bata san kawai shigo shigo ba zurfi ba ne"

Momi ta ce

"Ai na san kin haifu a cikina gwara ki nuna mata shayi ruwa ne, sannan ki nuna mata tsakanin zuma da maɗaci akwai bambanci, kuma dole ne ki bambanta mata tsakanin aya da tsakuwa banda zubar da girma mai za ta je yi gidan yara a ranar farko ga ƙawayenki nan bata tunanin za a rainata duk son abin ɗanta ya rufe mata idanu""

Meenal ta ce

"Ai da ni take zancen sai na gasa mata aya a hannu in shayar da su ruwan mamaki in bata kauda idonta ba sai na bayar da darasi a kanta yadda uwayen miji za suke barin matan ƴaƴansu su sake da mijinsu, ni ba zan lamunci cin mutunci ba ni babu wanda zan ragawa ko ita matar tasa sai ta san da zamana" Suna cikin haka Meenal daga wutsiyar ido ta hango Hajiya ta leƙo kanta cikin ɗakin, da sauri ta yi sallama ta kashe wayar ta nufi wajen tana faɗin

"Hajiya dama baki tafi ba?" Wata ajiye zuciya da har sai da Meenal ta ji ita Hajiya ta yi a fili kafin ta ƙaraso tana faɗin

"Ƴata Meenal baki karɓi magani ba ina na samu damar tafiya, kuma bakya tunanin ƙawayen can naki su yi aika-aika a store da kika basu mukullin?" Hajiya ya faɗa don jikinta sai yake bata kamar za su yi sata a store ɗin ko su yi almubazzaranci don ta ga ita Meenal ɗin bata ma damu ba da mukullin da ta basu.

Ɗan yatsina fuska ta yj ta ce

"Hajiya bari na miki gwari gwari yadda za ji fahimta, wallahi summa tallahi rass nake babu wani fitar hayyaci idan kuma akwai wani abu da kike so in tabbatar miki ki yarda za ki iya faɗar abin da kike so na faɗa miki, sannan kuma mukullin store ɗin ne sai an bi mutum don an bashi aika-aika a kan abinci sai kamce wasu ɓarayi to ni ko ɓarawo in ya saci abinci gani nake ba sata ba ce tun da idan ya ci ma maganin yunwa ya yi kuma za ka samu ladan sannan ai abinci kashinsa za a yi ba kadara ba ne da za ake alkintawa"
Tsabar mamaki Hajiya kallon Meenal kawai take dakyar ta yi yaƙi da bakinta ya iya furta

"Abincin ne ba kadara ba Meenal baki san mace ana so ta zama mai adana dukiya da komai na miji ba yanzu idan abincin ya salwanta a taron nan na amarcinki sai fa Nasir ya sake fafutukar kawo wani ai a tausayawa miji, sannan da kike batun ɗaukan abinci ba sata bane ai duk abin da mutum zai ɗauka in har ba nashi bane kuma ba a bashi ba sunansa sata k...

Meenal hannu ta ɗagawa Hajiya wanda ya sa ta dakata da maganar cike da mamakin hannun da ta ɗaga mata tamkar wata sa,arta sai kawai ta ji ta ce

"Hajiya ya kamata kisan inda dare ya miji karki manta nan gidan mijina ne ina da damar yin komai, sannan ba huruminki bane da zaki baro naki gidan sabodan zubar da girma ki zo kina bin diddigin abin da yake faruwa a gidan ɗanki sannan shi Nasir ɗin ai tun da kika ga ya yi aure ya shirya tarɓar kowace buƙata dole ta nemo idan babu kuma wallahi summa tallahi babu mai mini shamaki da abinci ko wani abu a gidan mijina, yadda kike taƙama ɗanki ne haka nake taƙamar mijina ne na ma fiki iko da shi yanzu" Furucin Meenal na yanzu ya sa Hajiya ta yi tsai tana lura da yanayin maganar ta a nan ta fahimci cewa tabbas a hayyacinta take babuwwasu alamu na fitar hayyaci a tare da ita kawai tsabar rashin kunya ne da fitsara hakan ya nuna ba ma sai ta ɓata loakci wajen cewa Meenal ta yi wani abu da zai nuna tana hayyacin ta hakan ya sa a zafafe Hajiya ta ce


'Wallahi ƙarya kike Meenal! Babu wanda zai yi iko da Nasir sama da ni"

Meenal ta kalle ta ido cikin ido ta ce


"Kina musu da hakan?" Bata jira amsar Hajiya ba ta ce

"Idan kin musa ki zo ɗakin nan da daddare akwai wata shegiyar rigar bacci da nake da ita da kuma shu,umar humra mai tada kan maza zan saka rigar in shafa humrar zan faɗa wa Nasir ya zauna a wuri ke kuma ki ce ya tashi in zai bi umarninki mu gani!." Wani salati da Hajiya ta kwasa sai da ya so ba Meenal dariya son ta lura Hajiya ta shaƙi takaici kuma abin ya ɗaure mata kai Meenal ta murmusa ta ce

"Ki saka takalmanki ki koma gidanki sannan ki ɗauke idanu a kan lamuran gidan nan idan kina son kanki da girma da arziƙi in ba haka ba wallahi takaici sai ya kusa kasheki" Tana gama faɗar hakan ta fito falo ta bar Hajiya tsaye kamar ta saki ihu tana fitowa falon ƙawayenta suka hau mata kirarin amarya har da masu mata waƙar amarya da Ali Jita ya yi wa amarya. Suna ta abin su Hajiya tana bedroom tsaye da jaka maƙale a hamata ƙullin magani guda biyu a hannu, waiwayawa ta yi ta kalli ɗakin ta ƙare masa kallo sai ta hangi gajeran wandon Nasir da rataye saman ƙofar banɗakin juyowa ta yi ta fito falon ko kallon tarkacen ƙawayen Meenal na falon bata yi ba ta yi waje don zuwa lokacin ma Meenal ɗin ta yi tsakar gidan.


Sadiya tana alwalar azahar a famfo Meenal tana tsaye wajen ƙawayenta da suka ɗakko kayan abincin a store suna nuna mata, suna cewa abincin da yawa tana faɗa musu dama fa ba wai za a kai gidansu ba ne yau kawai ta faɗa ne don ta cusawa Hajiyar haushi. Fitowar Hajiya daga falon Meenal za ta saka takalmi ya yi daidai da shigowar Nasir da ya kinkimo silindar gas yana tafiya a ɗan duƙushe alamar mutum ya ɗaga abu mai nauyi bayansa wasu matasa ne guda uku suna ɗauke da katan ɗin lemo coca cola biyu mirinda ɗaya sai fanta biyu.

Hajiya tsabar yadda ta ruɗe da ganin lemukan da ya siyo ga gas tana tunanin kenan dai maganar Meenal ta zama zanen dutse sai da ya aikata, a ƙwaƙalwarta tana ƙiyasin kimanin nawa aka kashe a hakan ta saka takalminta ɗaya nata ɗaya kuma na wata daga cikin ƙawayen amarya sannan kowanne ba ƙafarsa ba ce.

Kiran sunan Nasir take Sadiya da ta gama alwala dariya tana neman ƙwace mata da ta ga ƙafar Hajiya ta yi saka takalmi kamar ƙafar ƙananan yara sannan takalman daban-daban ne uwa uba yadda ta tikce tana kiran Nasir.

Nasir faɗi yake

"Ina zuwa Hajiya" Ya yi hanyar kicin ya daidaita musu silindar a jikin gas ɗin, tsakar gidan kuma samarin nan suna tambayar inda za su ajiye lemukan Meenal ta yi karaf ta ce

"Ku kai ƙofar wancan ɗakin" Ta faɗa tana musu nuni da ɓangarenta sannan ta hau ƙwalawa wasu daga cikin ƙawayenta ta ce su karɓa su saka a frige har tana musu tsiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login