Showing 111001 words to 114000 words out of 178828 words

Chapter 38 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt

18 Dec 2025

2393

tsawar da aka mata ta matsa gaba da sauri sai da ta musu umarnin juyowa sannan suka juya suka zauna. Kafin su fara bayani ta sanar da su ta san da abin da suke tafe, Aliya sai kallon baƙar matar take wacce babu alamun ɗigon imani a wajenta nan ta ce

"Zan yi miki aiki kuma za a samu biyan buƙata idan har buƙata bata biya ba to ba daga garemu ba ne kin saɓa lamba ne, amma matuƙar kika yi yadda na ce to an wuce wajen" Kai Aliya take kaɗawa kamar ƙadangaruwa sannan sai bokanya ta ce
"Za ki kawo mini cokalin da yake cin abinci da shi a jikin cokalin zan yi aikin, sai kuma ki mayar da cokali a tabbatar ya ci abinci da shi idan haka ta faru to ƙurunƙussss!.

Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Amatullahi da Aliya jin wata gadar zare da aka musu, ita Aliya tunanin da ta farw ta yaya za ta gane cokalin da yakencin abinci sannan har ta mayar ta tabbatar ya ci abinci wannan ai abu ne mai wahala tana cikin wannan maganar muryar bokanya ta katse ta da faɗin

"Ba ma magana a musa mana, komai muka faɗa sai an aikata in ba haka ba akwai yiwuwar ciwon hauka ga mutumin da ya zo neman taimako wajenmu kuma bai yi abin da aka ce ba"
Didididiiimmmm gaban Aliya ya buga da ƙarfi idanunta suka ciko da ƙwalla.


MAMAN AFRAH
0902557622






https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=hqrt1



*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)


NA


MAMAN AFRAH


. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE2️⃣1️⃣



MEENAL

Rai a ɓace ta saka hannunta ta riƙe hannun Hajiya wanda takaici ya sa Hajiya ta fashe da kukan takaici bata taɓa zaton akwai irin wannan tanar da har matar ɗanta za ta riƙe mata hannu ba. Nasir da sauri ya fito daga motar ya nufi su yana faɗin
"Meenal ki saka mata hannu" Haka Meenal maimakon ta saki hannun sai ta warɓar da hannun, ita kuma Hajiya sai ta fara tunanin tun da har Meenal ta iya riƙe mata hannu ta warɓar da alama ko marin nata ta yi ba za ta ajiye hannunta ba za ta rama. Faɗa Hajiya take yi kamar za ta ari baki sai Meenal ta kalle ta ta ce

"Hajiya da kin adana kalamanki wataƙila nan gaba za su miki amfani, don yanzu aka fara wasan, sannan ki mayar da wuƙar ni ba zuwa gidan ki zan yi ɗaukan dankali ba, amma ki sani ɗan naki dai da bakya so a ɓanɓare shi, shi zai ƙara cire wasu kuɗin ya siyo kuma muddin kuna so ku ci dankali sai dai ƴaƴanki su zo su soya a tsakura muku don ni ba baiwa kuka ajiye ba" Tana faɗar haka ta juya ta shige gidan. Bak sake Hajiya ta bi bayan Meenal da kakko yadda ta tafi tana karkaɗa mazaunai irin na yaran da suka riƙa a rashin ta ido.
Nasir ne cikin sanyin murya ya ce

"Ki yi haƙuri Hajia... Kafin ya gama faɗa ta katse shi da faɗin

"Haƙurin da ta mutu sadakar nawa ka bani? Kana raye za a yi min cin kashi Nasir har ni matarka za ta ce wai za ake tsakurawa abinci kamar wata almajira" Shi dai baki yake bata amma ta yi banza da shi hatta motar tasa ta ƙi shiga.

Napep ta tare ta nufi gida ta je tana ta kumfar baki su Husna suna taya ta, sai da yamma ya shirya ta nufi gidan ƙawarta mahaifiyar Meenal ko da ta je baƙi basu gama watsewa ba wasu kuma suna ya shigowa yin Allah sanya alheri.

Tana shigowa Momi ta hau mata lale marhabin tana faɗin

"Ka ga manyan mata maganin ƙanana ƙanana, ka ga ƙirjin biki uwar amarya uwar ango"Dariyar yaƙe kawai Hajiya ta yi ta nemi wuri ta zauna sai da aka kira magriba ƙafa ta fara ɗaukewa sannan Hajiya suka keɓe da Momi Hajiya ta ce

"Ƙawata akwai matsala wallahi" Cike da nuna damuwa Momi ta ce

"Subhanallahi Allah rabamu da matsala mai ya faru?"

Hajiya ta ce

"Wallahi yarinyar nan Meenal ina ga an samu wasu ƙawaye mararsa imani da tarbiya sun bata sabon darasi da shawarwari a kan zaman gidan miji da kuma uwar miji ganaɗaya ta sauya halayya"

Momi ta hau faɗin
"Innalillahi wa inna ilaihi raji,un wane ƙawaye ne wannan waye ya miki wannan bayanin"

Hajiya ta ce

"Ni da idona na gani" Ta faɗa tana kwashe komai ta faɗawa Momo, Momi ta ringa tafa hannuwa tana salallami tana faɗin amma dai bata ɗauki shawarar ƙwarai ba. Hajiya sai ta ga ma yadda take zaton Momin za ta ɗauki maganar sai ta ga bai kai hakan ba, sai ta fara tunanin ko dai son kai ne.

Hajiya ta ce

"Yanzu mene ne mafita?"

Momi ta ce

"To wace itin mafita kuma ai tun da har ƙawaye suka ɗorata a kan wata turba wacce ba tarbiyar gidansu ba sai dai a hankali a fahimtar da ita kin san yaran yanzu, dama fa kana tarbiya sai kana haɗawa da addua amma ƙawaye da abokai su ne matakin farko na warware saƙar da ka ɗauki lokaci kana yi shi ya sa ake so iyaye sukr saka idanu a kan ƴaƴa su ga waye abokinsu kuma su waye ƙawayensu" Baki ta saki tana kallonta ai a ganinta wannan son kai ne ta ɗauka Momin za ta kira Meenal ko a waya ne ta kutuntuma mata ashar ta ƙara fahimtar da ita matsayin Hajiya amma sai ta ga abin ya sha bamban.

Haka ta baro gidan ranta babu daɗi tana tunanin mafita don ba za ta ƙyale wannan abinnya tafi a haka ba amma za ta ɗauki mataki kawai bata so ne zumuncin su ya yi rauni amma duk da hakansai dai zumuncin ya gurɓace.

Ko da Hajiya ta tafi Momi ta kira Meenal ta faɗe mata biri har wutsiya nan ta ƙara zugata da jaddada mata kar ta sake ta saki jiki a rainata, kar ma ta yarda a ga makwancinta ta ƙwaci ƴancin ta duk wanda ya ce kule ta ce casss!.


A haka rayuwar gidan Nasir ta ci gaba da kasancewa sai abin da Meenal ta ce ake zartarwa don sun gama barbaɗawa Nasir magani a abinci ya cinye yanzu sai abin da ta zartar ake yi. Sadiya bata ma su take ba ta saka sana,arta a gaba duk yadda Meenal ta so takalar ta da faɗa bata kula ta sai ta yi kamar bata ji ba gorin duniyar nan babu wanda bata mata ba na cewa ai babu abin da bata sani va game da halin gidansu kawai bata biya ta su yi faɗa nr don tana tsoron komawa gida mahaifinta ba zai bari ba.

Hatta abinci ita take aunaw Sadiya tamkat ba ita ce uwar gida ba, sannan a ba Meenal kulin cefane ita a hanata, duk wani abu na bambanci ko rashin adalci shi ake yi a gidan, ita ta yi girki da gawayi ita ta ɗora a gas sannan ita Meenal tana da mai wanke wanke almajiri ita kuma Sadiya da kanta take yi.

Hajiya sai da ta ga dankali da kayan shayi ya ƙare kaf sannan ta ce Nasir ya siyo wani buɗar bakinsa ya ce

"Hajiya yanzu idan akamce zannke siyan ƙwai doya dankali da kayan shayi ruɓi biyu gaskiya za a samu matsala ga mota ta yanzu tana yawan bani matsala sai kuɗin gyara take ci sannan yanzu Meenal bata taɓa yin girki babu nama"

Hajiya ta ce

"To mai kake nufi yanzu?"

Nasir ya ce

"Sai dai idan har kuna sona dankalin su Husna suke zuwa suna aikatawa sai Meenal take ɗauka musu suna kawo muku kamar yadda Meenal ta tsara, amma na san ita Meenal ba za ta yarda ta girka muku ba" Da bala,i Hajiya ta ce

"Bata isa ba dole ta girka don na fahimce ka na rashin siya a can gidan da kuma nan ni ma bana so ka wahalta aljihunka saboda auren ƙanannka amma dai tun da ita uwar muyane ba za bari a dafa a nan a bata ba dole ta dafa" Nasir jikinsa ya yi sanyi hakan ya sa ya ce

",Ba komai kawai zan saya muku " Yana barin gidan ta kira Meenal tana ɗagawa ta ce

",Hajiya ya ne? Ƙalau dai ake kirana" ,Ran Hajiya ya sosu da ta ji wannan batu amma sai ta ce

"Fitsararriya mai ido a tsakar ka, ina so in ƙara tabbatar miki da cewa ɗana ni na haife shi dole ya mini abin da nake so gashi can zai sayo mana kayan kari in kin isa mu zuba ni da ke!" Tana faɗar hakan ta kashe wayar ta bar Meenal da waya a kunne. A ƙufule Meenal ta kira Nasir ta ce


"Yanzu kai baka isa da ƙannenka ba saboda na ce suke zuwa suna mana girkin safen kawai shi ne za ka je ka siyo wasu kayan saboda ka nunawa ƙanennka ban isa da mijina ba su rainani na gode" Tana kai wa nan ta fashe da kukan kissa ta kashe.. Nasir ya kira ta yana ta aikin lallashi ya ce ya fasa siyowa zai tilasta su Husna zuwa.


Kawai Hajiya sai kiran Nasir ta gani tana ɗagawa ta ce

"Yawwa ka kira a kan gaɓa dama yanzu nake son kiranka in ce mun fi son dankalin mai manya manya douar kuma sabuwa muke so ta fi daɗi" Nasir ya ce

"Hajiya ya za a yi a ce ni ban isa da su Husna ba bayan an ce babban wa uba, kawai suke zuwa gidana suna girkawa" Salati ta hau yi ta kashe suka hau jajantawa ita da su Husna Hibba sai ɗurawa Meenal ashar take yi suna cewa ta mallake musu ɗan uwa Hajiya kuwa har da kukan takaici wai an fi ta iko da ɗa.


Washe gari suka ƙi zuwa sai Hajiya ta yi musu tuwon shinkafa suka ci kaɗan sun saba da kayan dankli da kwai da shayi mai kauri yau kuma sai bunu suka sha wato lipton.

Haka suka yi ta mita wata washe garin saj suka kwashi ƙafa suka tafi gidan sun daɗe zaune a ƙofar ɗakin Meenal suna jiranta kafin ta fito a shelaƙe ta basu kayan da za su yi aikin kuma din takaici ta ce kar su taɓa mata cooker gas ta ce su yi da gawayi haka suka yi wahala suka gama ta zo ta ɗauro musu kayan shayin kamar wani ƙullin roƙo kuma a waje ɗaya ta haɗa madara da milon. Basu gama sanin bata da mutunci ba sai da ta ce sai da su koma su kawo kwanon sa za a zuba ko ta zuba a leda haka suka tafi suna ta tsene mata har da uwar ta sai da suka tsinewa haka ma Hajiya ta ringa zaginta da ta ga kayan shayin ta ɗakko wani ramgameman fulas ta basu, suna kaiwa Meenal ta tsakura musu wani a ƙasan kwano ko Hajiyar ba zai isa ba bare su.

Haka suka tafi ransu duk a ɓace sai da suka je sai suka fara zancen da a ce Sadiya ce ta samu wannan damar da ba za ta musu haka ba.


Kullum haka suke zuwa su girka ta basu su tafi dama yanzu da kwano suke tafiya Sadiya kuwa babu ruwanta da sabgarsu ko Nasir rabon da ya taka ƙafarsa a tsakiyar falonta ma tun kafin Meenal ta tare bare a yi zancen biyan haƙƙi. Ga cikinta ya tsufa tana dab da haihuwa. Wata ranar laraba sai kawai Meenal ta ce Nasir ya sa maau aiki su buga kicin na langa langa Sadiya ta kwashe mata kaya daga kicin haka kuwa aka yi, Sadiya ta kwashe komai nata, don ita yanzu in banda gayan kayan abinci babu abin da ake bata a gidan shi ma ba ishashshe ba.


Yanzu da ta lura Kalifa yana ganin dankali da ƙwan da ake soyawa sai ta saya kokai ta ajiye su ma take soya musu tun da Allah ya rufa mata asirin da sana,ar da take yi wanda wannan abu shi ne ya tsayewa Meenal a rai don ko buga gidan aka yi za a saya abu ta ringa masifa tana cewa ana katse mata bacci.

Yau lemon mango tun safe ake saya haka ya sa gabaɗaya ma kayan sanyin suka ƙare da yake tana da ƙanƙara kuma akwai nepa sai ta zauna ta haɗa wani tana zubawa a robobi. Gidan da aka buga ya sa ta yi magana aka ce ƴan nepa ne bill ne muka kawo, ta je ta karɓo yana nannaga mata idan ba a biya yau ba gobe za su dawo su yanke.


Za ta zuna sai Meenal ta fito a gadarance sanye take da baƙin wando da ya kamata tree quarter da farar riga kai babu ɗan kwali sai wani kaɗa jiki take tana fitowa ta ce

"Kawo wannan bill ɗin tun da ba ɗakin ki zai shiga ba tun da ma ke ai baki da bakin kwana a gidan nan" Sadiya bata ce komai ba ta ba Kalifa ta ce ya kai mata, haka ta karɓa ta shige ɗaki.

Ko da ya dawo gidan suna zaune da daddare ta yi filo da cinyarsa sai ta ce

"Ga bill can ƴan nepa sun kawo, sun ci gobe za su yanke in baka biya ba"

Ya yi shiru ya ce

"Ni yau kasuwar nan bata yi kyau ba" Wani daɗi ta ji don an zo wajen da take fatan a zo

Sassauta murya ta yi cike da kissa ta ce

"Honey ni kana bani mamaki ya za a yi a ce wai kullum kai kake biyan nepa" Da mamaki ya ce

"Wa zai biya min"

Ta ce

"Sai kuke raba daidai da Sadiya ai ta fi kowa morar nepa a gidan nan, amma yanzu idan ka tunkare ta da maganar ba lallai ta bada kuɗi ba kawai idan ƴan nepa sun zo sai su tanke mata ɓangarenta in ya zo nan gaba idan aka ce ta bayar ba za ta yi musu ba" Shiru ya yi sai kuma ya miƙa mata hannu suka tafa yana jin lallai shawarar ta yi daidai da ma,ana sai ya ce

"Wallahi ƙwaƙwalwarki tana aiki ban taɓa wannan tunanjn ba" Murmushin cin nasara ta yi.

Da safe kafin ya fita ya bata kuɗin nepa ya ce idan sun dawo ta basu, amma sai ya yanke wani kaso daga kuɗin ya ce ta ce su yanke ɓangaren Sadiya.

Sadiya yau tun da almajirinta ya ɗauki kayan yake dawowa yana ƙarawa gashi daga unguwa ma sai zuwa ake nan da nan ya ƙare tas. Ta zauna ta sake wani ta jera a frige. Ta gama zubawa kenan sai ta ji ana bugawa da aka yi magana aka ce ƴan nepa ne a kawo kuɗin wuta, Meenal ta ɗauki kuɗin ta je da takardar ta basu, ta musu bayani babu musu suka yanke ɓangaren Sadiya, Sadiya tana tsakar gidan tana jin ƙaran tvn Meenal kasancewar ta ƙure ƙara, amma tana shiga falonta sai ta ga ƙwayayen basu kawo ba ta duba ko ina ta ga babu nepa ta ƙara fitoea ta ci gaba da jin ƙaran tv a ɗakin Meenal a nan take ta fara tambayar kanta

"Ya haka?"



ALIYA

Amatullahi ce take mata alama da ido alamar ta amince a take ta shiga kaɗawa bakanya kai, sai kuma suka tambaye ta kuɗin aikin ta ce sai sun kawo cokalin an yi aikin tukunna. A tsorace suka baro wajen suna tafiya har suka fito daga surƙuƙin dajin suka zo bakin titi sun daɗe suna tsaye suna tattaunawa Amatullahi tana faɗawa Aliyar kawai daga nan ta wuce gidan Jidda ta san duk yadda za ta yi ta ɗakko cokalin tun da gobe dole su dawo su kawowa bokanyar cokalin.

Bayan sun sauka a motar suka shiga napep kowa daban ta shiga tun da Amatullah gidansu za ta tafi ita kuma gidan Jidda. A ƙofar gidan Jidda napep ya sauketa ta fito ta bashi kuɗin tana lissafin sauran kuɗin nata ya kusa ƙarewa gashi bata san ma da mai za ta biya bokanya kuɗin aikin ba, duk da bata san nawa ne kuɗin ba sai dai ta san za ta yi ƙaryar da za ta yi ta ɓanɓari kuɗin aikin a jikin Jidda tun da ita ita ce mai kuɗi ita kuma Allah ya tauye mata nata samun sannan shi ma mijin fuƙara,u ne. Tana tsaye gaban tangamemen get ɗin tana ƙarewa gidan kallo ranta tana ƙuna tana ƙiyasto ranar da za ta tare a cikin gidan.

Ƙaran sohuwar wayarta ne ya dawo da ita daga tunanin ganin sunan Kasim ta doka wani uban tsaki, a zuciyarta tana faɗin

'Ɗan anace uban shegen naci ko mai zai bani zai kafa mini kira' Ta faɗa sai dai kiran yana dab da tsinkewa ta ɗaga tana karawa a kunnenta ta ji hucin iskar sa ya busa yana faɗin

"Aliyata sarauniyata" Wani ɗaci ta ji a zuciyarta tana galla masa harara tamkar yana ganinta, sai kuma kamar an mata dole ta ce

"Uhmmm" Ya ce

"Fatan kina cikin ƙoshin lafiya, baki koma gidan ba?" Ya tambaya yana sararon amsar ta. Ɗan jim ta yi sai kuma ta ce

"Eh dama ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login