Showing 66001 words to 69000 words out of 178828 words
Chapter 23 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
kayan sana'ar ruwa suna da riba sosai.
Bayan sati guda tana zaune bayan ta gama ɗura zoɓo da yamma, da yake yau ya ƙare tas har ana nema, yanzu pure water ne a ciki da zoɓon da ta saka yanzu, da sallama Nasir ya shigo bakinsa yana washewa, abin da ya bata mamaki har da ɗauka Kalifa shi kuma yaron ya ƙi sakewa da shi kasancewar ba sabawa ya yi da hakan ba. Mukulli ya ɗaga a hannunsa yana karkaɗa mata bayan ta masa sannu da zuwa duk da ta ga yau ya dawo da wuri sai dai tana mamakin fara,arsa. Cike da alamun tambaya a fuskarta ta ce
"Mukullin mene ne?"
Ya ce
"Sabuwar amarya na yi wato mota" Ya faɗa yana washe baki, sosai ta ji daɗin maganarsa, ba wai don ya ce ya yi mota ba, a,a sai don fara,ar da yake ko yaya ɓacin rai ko nuna isa da gadara basu da wani alfanu ga namiji yake yi wa iyalinsa.
Sosai ta nuna farincikin ta, dama ta san yadda kasuwa take gara masa ai yana samu sosai kawai dai don abin a zuciya yake wato mammaƙon nasa a zuciyarsa yake. Hijabi ta saka suka fito ƙofar gidan motar tana sheƙin sabunta dark blue ya juyo ya ga yadda take ta fara'ar sai maganarsa ta katse mata hanzarin fara,arta ya ce
"Na sayi motar nan ne saboda Meenal, Meenal ta faɗa min tana son duk inda za ta je in kaita a mota, sannan bata son ƙawayenta su rainata su ce mijinta bashi da mota!"
*BABA*
Gabaɗaya ya mayar da hankalinsa ga son banza, don yanzu kowa ya gane yana jin daɗin a masa abinci mai daɗi, don haka yanzu da daddare idan yana bacci cikin dare za a lallaɓa wata daga cikin ƴaƴan ko matan za ta sace mukullinsa, a je a auni shinkafa a store a mayar a rufe, don da abin nasu ma ya yi tsamari sai a auni kwano uku biyu a dafa a gidan kwano ɗaya sai a siyar a yi cefane da nama ko kifi a yi girki lafiyayye kowa ta ci Baba a yi masa zubi ya ci yana santi da saka albarka, har yau bai san cewa tanadin da ya yi domin ya siyar ba ne ake kwasa ana ci tare da shi.
Yanzu ma bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen bin malamai da masu siyar da maganin gargajiya yana siyan maganin farin jini domin ya samu ya aurar da ƴaƴan nasa, malamai kuma yana sakawa su yi roƙon Allah, amma shiru kake ji malam ya ci shirwa da alama dai addu'ar ta samu jinkiri ne, babban abin da ya ƙara tada masa hankali ma yanzu Sumy da Aisha da suka kammala karatun su na secondry yanzu kam waɗanda yake son ya aurar sun yi yawa. Shi ya sa ba ya ma son Sadiya ta kawo ƙorafi a ganinsa tun da dai ita Allah ya sa ta samu miji to duk wani ƙalubale ta haƙura ta rungumi ƙaddara!.
*MUBIN*
Da sanɗa ya shigo babban falon yana waige-waige sai dai ganin dalon wayam kamar yadda ya yi tsammani hakan ne ya sa ya ji ɗan daɗi a ransa, domin a ganinsa lokaci ne da kowa ya yi bacci idan ya shige ɗakinsa to zai zamana ko ma mene ne zuwa safiya Mamy ta huce daga fushin don ya san sai dai Mamy don Baffa ko a kwalar rigarsa. Takalmansa a hannu ya yi saɗaf-saɗaf kamar daga sama ya ga hasken fitila ya manaye falon, abin ya masa bazata hakan ya sa ya ji gabansa ya buga da ƙarfi, sai jin muryar Mamy ya yi kamar yadda ya tsammata ta ce
"Mubin daga ina kake?" Shiru bai bata amsa ba ta sake cewa
"Mubin irin tarbiyar da na baka kenan? Wannan ne sakayyar da za ka mini, maimakon ka zama ɗa nagari mai biyayya da bin umarnin iyaye, yi na yi bari na bari amma shi ne duk fadutukar da nake yi kake son watsa min ƙasa a ido" Ta faɗa lokacin zuciyarta ta fara karaya saboda tausayin kanta a nata ganin ba uwa ce kaɗai za ta kula da tarbiyae ƴaƴa ba haɗaka ya kamata iyaye mata da mazan su yi tarbiyar ƴaƴan amma shi ya bar mata komai ta yaya hakan zai yiwu gashi yaran suna neman kangare mata. Mubin cikin inda-inda ya fara maganar da rashin gaskiya ya hana shi furta abin da yake gaskiya ne dama hausawa sun ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake.
*JIDDA*
Gabaɗaya Ibrahim ya rikita mata lissafi ya sa duk tana jin wata muguwar kunyarsa, ya sa tana jin ashe ita ma tana da wani matsayi don yadda yake yi mata jin ta take tamkar wata sarauniya.
Ta tafi gajeran zancen zucin nan na wucin gadi kawai sai ta ji yatsansa a saman leɓɓanta, abin da ya dawo da ita hayyacinta kenan, tana dubawa sai ta ga tsokace ya gutsuro yake ƙoƙarin bata a baki. Cikin wata murya mai kwantar da zuciya ya ce
"Idan baka ci naman nan ba kuka zan miki Jiddanah" Yanayin yadda ya fara bata ga alamar wasa a tattare da shi ba hakan ya sa ta danne guntun kunyar ta buɗe masa bakin ya saka, yana sakawa ta saka hannunta na dama ta rufe bakin da tafin hannunta saboda duk kunyarsa take ji kasancewar rashin sabo. Idanunsa ta ji yana yawo a jikinta alama ce ta ya tsare ta da kyawawan idanunsa hakan ya sa ta kasa ɗagowa ta kalle shi shi kuma ji yake tamkar ya mayar da fuskarta cikin idanunsa ya zamana ita zai ke kallo a koyaushe.
Muryarsa tana sarƙewa saboda yanayin da ya tsinci kansa na kasancewa da ita a waje guda kuma matsayin mamallakiyarsa hakan ya sa ya ce
"Idan naman ya miki taurin da ba za ki iya taunawa ba, wallahi zan tauna miki shi Jiddanah, ji nake kamar don ni aka halicce ki wallahi ina jin kamar idan ban kyautata miki ko na faranta miki ba kamar dai na ci amanar ƙaunar da zuciyata take miki" Wani ruwa ne ya taru a ƙwayar idanunta, a zuciyarta tana godiya ga Allah da ya bata mijin marainiya, ita kuma ta yi alƙawarin ba za ta kasance daga cikin mata azzalumai ba wanda idan sun samu namiji yana ƙaunarsu suke cutar da shi ko su mayar da shi bawa, wata ma malamai take bi don ta samu yadda take so amma daga ta ga duniya a tafin hannunta sai ta fara gara mijin kamar ƙwallon ƙafa, bata san cewa duk abin da aka nema ta ɓarauniyar hanya ma'ana duk abin da aka yi ba ta hanyar Allah ba to ba zai taɓa dawwama ba!.
A kunya ce ta ce
"Zan iya taunawa, kaima ka ci" Jin furucin ta sai ya ji ya ƙara samun nutsuwa haka ya ringa ɗauka yana ci yana bata, don ya san a kunyar Jidda yau dai ba za ta iya bashi abu a baki ba sai ko nan gaba idan ta kwana biyu ta saki jiki da shi. Sun ci amma ba wani mai yawa ba, sai kuma ya tsiyaya musu lemon amma shi madara ya zuba, bakinta ya nufa da kofin amma sai ya ga ta miƙo masa hannun nan nata mai tafiya da hankalinsa wanda yake ɗauke da kyakkyawan jan ƙunshi da baƙi. Miƙa mata ya yi ta ɗan sha ta ajiye, shi kuma madarar ya shanye duka, ko da ya zuba mata sai ta girgiza kai.
Tana nan zaune ya kwashe duka kayan, sai ganinsa ta yi ya dawo, yana tsaye a kanta ita dai bata ɗago ba, kamar a mafarki kawai sai ta ji ya sure ta, ɗaukan jarirai ya mata, wata irin kunya da bata taɓa samub kanta a ciki ba ce ta ziyarce ta, hannunta biyu ta sanya ta rufe idanunta, bata ankara ba ta fara jin alamun sama suje haurawa, sai da ya gama hawa ta ji wani irin ƙamshi yana tashi na turarukan wuta, ƙaran ƙofar da ta tura da ƙafarsa hakan ta sa ta gane sun zo wani ɗakin ne daban, a wani lallausan gado ya mata masauki wanda ta ji tamkar dama katifar bata da tauri kawai wani irin laushi ne da ita tamkar auduga. Yana ajiye ta ya juya ta ji fitarsa, hakan ya sa ta janye tafukan hannayenta don yin tsegumin ɗakin da take ciki, ai kuwa ta ga aljannar duniya, tana cikin kallon ɗakin da yadda aka ƙawata shi hatta bedsheet ɗin ya sha lailaya a gadon. Ƙaran hayowarsa benen ya ankarar da ita ya dawk da sauri ta yi rubda ciki tana ambaton Allah, a zuciyarta don ta san dai an ce daren farko shi ne daren amarci kuma ango ba wai zai ɗaga ƙafa ba ne, bare wannan mijin nata yadda yake rawar ƙafa a kanta da yadda yake sonta tabbas zai famshe soyayyarsa.
Da sallama ya shigo amma bakinta ya mata nauyi bata amsa masa ba tana jin lokacin da ta mayar da ƙofar ya rufe tamkar da bugun zuciyarta ya rufe ƙofar, dilim ta ga ya kashe wutar ɗakin sai ta gefen gado wacce hasken nata yake blue wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke a ranta tana raya Aliya da Kasim suna can su ma suna soyewa.
Sai dab da asuba komai ya daidaita, wata irin kulawa da soyayya yake nuna mata, ita kuma tana narkewa kamar wata ƙaramar yarinya, shi kuma yana jin tamkar babu mata sun ƙare a duniya idan ya tuna yadda ya samu Jidda tabbas wannan rana ce mai matuƙar tarihi a rayuwarsa.
Shi ya taimaka mata ta tsarkake kanta bayan ta gasa jikinta sai sannu yake jera mata ita kuma tana raki. Sai da suka yi sallar asuba sannan ya sauya zanin gadon suka koma suka kwanta sanye da wasu kyawawan kayan bacci masu taushi da ya fito da su daga drower wanda iri ɗaya ne kawai bambancin nata na mata ne nashi na maza.
Wajen ƙarfe tara suna cikin ramuwar baccin da basu runtsa daren jiya ba wayarsa ta shiga neman ɗauki har ta katse babu wanda ya san mai ake yi, Mummy da take faman kiransa tana tsaye ga direban da za ta aika gidansa yana tsaye riƙe da kwandon da ta sa aka shirya musu lafiyayan abinci, don ta ce sai an kwana biyu za a kai ƴan aikin girki yanzu dai masu shara da goge -goge ne za suke zuwa suna gyara mata gidan, don bata so a je a dame su a hana su sakewa da juna, tun da shi ma Ibrahim ya ɗauki hutu a wajen aiki.
Ƙara kiransa ta yi cikin bacci ya ji ƙaran wayarsa a hankali ya buɗe jajayen idanunsa da suka masa nauyi ya miƙa hannu kan bed side drower ya ɗakko wayar tana saurin dannawa gudun kar ya tashi Jidda. Ganin Mummy ya ɗaga yana kai kunnensa ta ce
"Mu'azzam a kan mai za ka bar mini yarinya da yunwa tun yaushe nake kiranka baka ɗauka ba, kar fa ka bar yarinyar nan ta shiga kicin" Bai san lokacin da murmushin gefen baki ya suɓuce masa ba idanu ya mayar kan Jidda wacce take bacci cikin kwanciyar hankali hular kanta ta zame yana iya ganin gashin kanta ya ce
"Mummy masu ƴa, to ita ƴar taki ma bacci nake bata tashi ba" Mummy ta ce
"Ga direba nan zai kawo abinci" Ya ce
"To Mummy ina kwana, ina Daddy" Mummy ta ce
"Sai yanzu ne za ka gaishe ni? Daddynka gashi can yana karyawa bai fita da wuri ba yau"
Ibrahim ya ce
"To ai na ga ta ƴarki kike bakya ma ta ni"
*ALIYA*
Ganin ya zuba mata mayun idanunsa yana kallon ta sai ta ga ma tamkar baƙaƙen maganganun da ta faɗa masa sun zame masa busar sarewa, saboda ya shagala da kallon kyawun halittar ta, kyawun da take taƙamar tana da shi, ji take tamkar ta tauna ganyen maina( Dalbejiya) A bakinta saboda wani ɗaci da bakinta yake yi mata, kallo ɗaya ta yi wa Kasim ta ga bai cancanci ma ya zama mijinta ba, Ibrahim jawai take gani a ƙwayar idanunta kuma shi take da buri da kuma muradin samu, Kasim babu da wanda ya dace sai Jidda ita baƙa kuma mummuna marar gata wato wacce bata da galihu wato marainiya.
Wata tsawa da ta daka masa tamkar uwarsa ita ce ta dawo da shi daga zalamamman kallon da yake jifanta da shi. Har sai da ya runtse idanunsa sannan ya buɗe saboda yadda ta masa, tamkar wanda bakin uwa ya kama shi.
Murya ya sassauta don shi ko mai za ta masa ba ya son ta hana shi kanta a wannan ranar, ya ƙwallafa rai a cin amarci amma tana neman kawo masa cikas.
Yana ɗan haɗa hannaye biyu waje guda ya ce
"Aliya ki sassauta muryarki ko kuma ki dakata daga wannan lafuzan mararsa daɗin sauraro, ki bari in abokaina suka tafi ko me za ki min na amince ki mini" Ya faɗa yana magana kamar raɗa, wani haushi take ji in tana tozali da fuskarsa ji take tamkar ta wanke masa fuskar da gigitaccen mari ko ya dawo hayyacinsa ya gane Aliya ba tsararsa ba ce. Wani wawan tsaki da ta doka shi ne ya sa ya gane haƙarsa bata cim ma ruwa ba domin ya gane ihu ya yi a bayan hari da alama maganar da ya mata ta bi ta kunnen hagu ta fita ta kunnen dama.
Ya jima yana roƙon ta fito don saboda abokansa amma ta ba bango ajiyarsa, ganin wankin hula yana son kai shi dare ya fito jiki sanyi ƙalau yana tafiya kamar an yi wa ƙafarsa dabaibayi. Yana fitowa ya gansu a tsaye su duka da alama ma suna shirin tafiya ne, ji ya yi tamkar ya nutse saboda kunya, akwai damuwa a ce a ranar da amaryarka ta tare amma tana maka wannan cin fuskar a kan kunnen abokan ka.
Yaƙi ya yi da zuciyarsa da bakinsa ya saki wani murmushin yaƙe wanda iyakacinsa fatar baki, gabaɗaya sai ya lura babu annauri a fuskar kowa yana fitowa falon ya ruɗe da faɗin
"Kasim za mu wuce Allah sanya alkairi ya bada zaman lafiya da haƙuri da juna" Wannan furucin nasu ya tabbatar masa da cewa ai tun yau ya fara karyawa da haƙurin. Amsawa ya shiga yi yana ji kamar ya nutse haka suka fara fitowa yana biye da su a baya, har waje ya rako su. Suka masa sallama suna watsewa Salis ne kaɗai ya tsaya ya kalle shi cike da damuwa ya ce
"Kasim wannan wace irin baƙar rana ce a ce a ranar farkon aurenka da matarka da kuka yi auren soyayya amma ta watsa maka ƙasa a ido, ko ma mene ne ai duk gaggawar asara ta jirayi samu ko wato duk son ta buɗaɗa maka ƙasa a ido ta jira mu tafi" Iska ya hurar daga bakinsa ya ce
"Ni kaina ban gane kan gadon wannan lamarin ba har tsoron komawa nake cikin gidan, don da alamu babu sassauci a lamarin Aliya kamar wacce ta sha ƙwaya"
Salis ya ce
"Babu wata ƙwaya tsabar rashin mutunci ne" Sun jima suna jimantawa kafin Salis ya fito da wata ƙwayar magani ya ba Kasim tare da masa raɗa a kunne, daga bisani suka yi sallama, shigowa ya yi ya rufe ƙofar gidan ya tarar falon sai ledar kazar amarcin da abokansa suka yi haɗin gwiwar siya masa, da lemukan a ajiye.
Ko ta kansu bai bi ba ya nufi bedroom, samunta ya yi ta yi kaca-kaca da akwatin ta guda ɗaya ɗaya daga akwatunan da ya mata na lefe tana zuzzubar da kayan ganin kayan bacci a jikinta riga da wando hakan ya gane cewa kayan ta ɗauka a ciki, tattarewa ya yi ta rufe akwatin. Zaune take a bakin gado duk abin duniya ya ishe ta kawai falon Jidda ne yake mata gizo da kuma farfarjiyar gidan wacce ta fara tozali da ita ganinta take tamkar yanzu ne take ganin ta.
Muryarsa ce ta katse mata tunani ya ce
"Aliya amaryata" Watanuwar harara ta galla masa kamar idanunta za su faɗo, falon ya fito ya ɗauki lemon tana fakar hanyar ɗakin ya buɗe five alive ya jefa maganin da Salis ya bashi a ciki ya mayar ya rufe.
Duka ya ɗauka ya shiga ɗakin ya ajiye a gaban gadon ya koma falon bayan ya ce mata shi zai kwanta a falon tun da bata buƙatar ya zo inda take banza ta masa son ko magana ya yi haushi yake bata. A doguwar kujera ya kwanta yana jin duniyar ta masa zafi. Aliya kusan awa biyu ta ɗauka a zaune, cikinta da yake mata ƙugi ta ɗauki lemon da aka saka magani ta buɗe ta kafa kai ta sha ta ajiye ko rufewa bata yi ba, jim kaɗan ta fara hamma bata san ta kwanta a gadon ba bacci ya yi awon gaba da ita da mafarkin gidan Jidda, tana ta gani a mafarki gata nan a gidan Jiddansuna rayuwa da Ibrahim matsayin mijinta.
Zuwa can Kasim da ya yi tsai yana jin babu motsin Aliya a ɗakin, lallaɓawa ya yi ai kuwa ya ga ta yi bacci, hakan ya sa ya ci karensa babu babbaka a nan ya ɓingire bacci da mafarkin Aliya da take kusa da shi yau dai burinsa ya cika.
Aliya wacce maganin baccin ya saki, ta riga shi tashi a bacci don lokacin har gari ya fara haske, tana tashi ta ga abin da ya faru wanda ya ɗaga mata hankali sai dai a ƙwaƙwalwarta tana iya tuno kamar a cikin baccin ta ga ta