Showing 78001 words to 81000 words out of 178828 words
Chapter 27 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
ƙarfi ta ɓangaren maza, za ki ga ma ko breast ɗina sak na maza ne bai fito irin na mace ba, kin san shi mata -maza ana samunsu da breast su girma sak na mace sannan al'aurarsu ma waje biyu ne ɓangaren mazantaka da kuma ɓangaren matantaka sai dai kowa da ɓangaren da ya fi ƙarfi" Ganin ta zuba masa ido tana sauraron abin da yake cewa sai hakan ya bashi tabbacin tamkar dai abubuwan da yake faɗa suna shigarta hakan ya da ya ɗora da faɗin.
"Idan har aka yi wa mata -maza aiki su ma za su rayu kamar kowane mutum wanda ba mata-maza ba, sannan suna haihuwa kamar kowa daɗin daɗawa ba a gadon haihuwar mata maza, wato a ce mata maza ya haifi wanda yake mata maza" Idanu ta runtse don idan tana jin kalmar mata -maza ji takr kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, gashi ya karɓe ɗan budurcin da take alkintawa tana jin yadda ƙasanta yake mata zafi da raɗaɗi amma sanin jinsin Kasim ya daƙushe kowane ciwo da take ji, tabbas don ya shammace ta amma da bai isa ya karɓi budurcin nan ba
Lokacin da ta runtse idanunta babu abin da take hangowa sai Jidda kwance a lallausan gado, mai kyakkyawar shimfiɗa da zanin gado mai laushi, tana kwance a lallausar fatar Ibrahim. Hakan ya sa da ta buɗe idanun sai ta ga Kasim ya zama wani baƙiƙƙirin. Idanu ta ɗaga sai ta ga ashe ma wandonsa ya shimfiɗa a kan gadon ya gabatar da sunnar a ka don tana iya hangar abubuwa masu wuyar faɗuwa a jikin wandon.
Juyawa kawai ta yi ta fita wanka ta yi amma na farin ruwa wato wanlan janaba, tana gamawa ta ɗauro alwala ta fito, a bakin ƙofa suka ci karo da Kasim ya matsa mata ta wuce, sallah kawai ta yi ta sake sauya wata rigar ta koma falo ta zauna ta harɗe ƙafa, har ya gama abin da zai yi ya zo ya yo sallar ya koma ya zauna a kan sallayar ya jingina da bango. Wajen ƙarfe tara ya fito ya zo ya ce
"Aliya mai za ki ci" Ko kallo bai iishe ta ba, ya ɗauki filas ɗin ruwan zafi a kicin ya jona ruwa a kyatil ya kunna ƙaramin gas ɗin ya ɗauki ƙwai guda uku ya fasa ya saka maggi da albasa ya shiga soyawa don shi ba ya jin ma zai iya cin wani abu. A lokacin da yake kicin lokacin ne kiran Umma ya shigo wayar Aliya Umma da ta ƙule a ɗaki saboda kar baƙin da suke tsakar gidan su ji wayar da za ta yi don Abba ya fita, bayan Aliya ta ɗauka Umma ta ce
"Aliya ya fita Kasim ɗin?" Aliya ta ce
"Umma babu inda zai je yana nan fa" Umma ta ce bari na kira ki an jima" Tana faɗar hakan ta kashe wayar. Shayi ya haɗa mata ya ajiye a gabanta da wainar da ya yi amma ta saka ƙafa ta ture kofin shayin ya zube ta saka ƙafa ta taka wainar, wannan abin da ta yi ba ƙaramin ƙonawa Kasim rai ya yi ba har ta ga gabaɗaya fuskarsa ta sauya, amma sai bai ce mata uffan ba ya ɗauke ya zo ya gyara wajen, ɗaki ya koma ya kwaso kayan shimfiɗar ya wanke ya shimfiɗa wani zanin. Ganin goma ta yi ya saka takalminsa ya fita daga gidan ko magana bai mata ba.
Don yanzu zuciyarsa ta fara masa wasi-wasi a kan Aliya ya ga abin nata ba na ƙare ba ne, ya san a iya saninsa Aliya ita ta amince da aurensa ba ya manta ranar da aka kai mata kayan saka rana yadda ta yi ta gode masa kamar ta goya shi amma yanzu komai ya sauya tun daga ranar da aka kai kayan lefe kenan dama abin hannunsa take so ba shi b?
Ko da ya fita wuri ya samu ya zauna a waje ya kira Salis yana faɗa masa cewa Aliya ta ga halittarsa tana masa tijara sannan ya faɗa masa abin da ta masa da ya mata girki.
Salis cike da ɓacin rai ya kawo wani zagi mai maiƙo ya danƙara ya ce
"Wai wannan yarinyar mai take nufi da kai, ya za ka je kana neman zama matar kana neman bata matsayin naka da Allah ya baka na namiji, ai mace ita ce a ƙasan namiji amma kana neman mayar da kanka wani nusari, a wannan zamanin har ta samu namijin da zah shiga kicin ya sama mata abinci amma take neman ta yi wasa da damarta na lura Aliya ba albarkar zaman aure take nema ba, wallahi jiya sai da na zo na kwanta abin da ta maka a kunnen abokanmu ya ɓata min rai" Kasim kamar zai yi kuka ya ce
"Wallahi na ga abin nata ba na ƙare ba ne abin ma kamar dai ci gaba yake" Suka ci gaba da tattaunawa.
Aliya kuwa yana fita ta ɗaga wayarta mai fashashshen screen ta shiga kiran wayar Amatullahi, bayan ta ɗauka ta ce
"Ƙawata amarya wato an kwana ana kwasar amarci shi ne yanzu da aka wartsake aka kirani" Ta faɗa cike da zolaya Aliya ta ce
"Dalla can malama rufewa mutane baki ana ga yaƙi kina ga ƙura, mutumin da ya min fyaɗe" Amatullahi ta fashe da dariya ta ce
"Batun nawa dai ya zo wato an ci amarcin dai ai ni dama na san duk wayon amarya dole sai an sha manta" Wani tsaki Aliya ta doka ta ce
"Idan kika ƙara ambaton amarcin nan sai mun ɓata, na kira ki ne in faɗa miki wani sabon tashin hankali da na tsinci kaina a ciki"
Cike da ɓacin rai ta ce
"Subhanallahi Allah rabamu da tashin hankali ni fa dama jiya ganin kina kumbure-kumbure shi ya sa ban tsaya yi miki sallama ba, saboda na ga sai ki mini rashin m... Aliyanta katse ta da faɗin
"Amatullahi Kasim mata maza ne" Amatullahi zaune ta tashi daga kan doguwar kujerar da take kwance a falon gidansu tana mai saka hannu ta toshe bakinta ta ce
"Mata maza fa? Ke yanzu Aliya duk bita da ƙullin da kike yi wa mutumin nan sai kin bishi da sharri?" Aliya cike da haushi ta ce
"Wai sharrin mai kike nufi? Ina miki maganar tsakani da Allah mata maza ne Kasim amma kina wani batu" Amatullahi ta ce
"Innalillahi mun shiga uku, kuma kika zauna a gidan Aliya?" Aliya ta ce
"To ya zan yi?" Amatullahi ta ce
"To ke ba shikann ba kin samu maƙalar rabuwa da shi sai ki ce ya yaudare ki bai sanar da ke ba in ya so kin ga kin samu hanuar yakice shege daga rayuwarki dole ya sake ki tun da babu wacce za ta zauna da mata maza, kin ga burinki yana dab da cika na auren mijin Jidda tun da ba uwa kuka haɗa da ita ba, sannan ba uba kuka haɗa ba bare a ce ya hakan ya haramta" Dididim gaban Aliya ya buga a take ƙwaƙwalwarta ta fara mata safa da marwa lokaci guda wani abu ya ɗarsu a zuciyarta, sai dai furucin Amatallahi ya katse matq hanzari in da ta ce
"Ina fatan dai babu abin da ya shiga tsakaninku, don mar a je yin abu sau ɗaya ya ɓata miki abubuwa dubu!" Aliya cikin rashin fahimta ta ce ban gane ba?"
Amatallahi ta c
"To idan yi ɗaya an samu ƙaruwa fa kin ga ko sakin ki ya yi ya barki da jelar goyon ciki da reno"
MAMAN FRAH
09025576222
[11/7, 9:00 PM] 😍: https://chat.whatsapp.com/GTq4oSxwxZfLKU7Amx5My1?mode=wwt
*RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka)
*NA*
*MAMAN AFRAH*
BOOK 1️⃣
PAGE 1️⃣6️⃣
Wannan grp ni
MAMAN AFRAH na buɗe shi ne domin masu soh saya kayan sallah su yi adashe, za ka zaɓi abin da kake so ka zuba kuɗinka ya danganta da yadda kake so. Duk abin da ka zuba a rubuce yake daga ka gama za a baka kaya.
1-Leshi 4-abaya
2-Atamfa. 5-kayan yara
3-shadda 6-Mayafai
7-Takalmi da jaka
8- Takalman yara
Da sauransu idan har kin san ba yi za ki yi ba karki shiga min grp don cire ki zan yi, ba wasa ya taramu a ciki ba.
Maman afrah
09025576222
*SADIYA*
Tun da suka ɗauki hanyar gidan gabanta yake faɗuwa, tunaninta ɗaya kar Nasir ya yi wa Baba tijara a gabanta domin ba za ta ji daɗin hakan ba, duk da shi Baban yana ganin yana musu ruwan kuɗi amma da alama har yau bai san waye Nasir ko kuma dai ya sani takewa yake yi. A ɓangare ɗaya na zuciyarta yana cike da fargabar ko dai Nasir ya sawwaƙe mata ne babu laifin fari bare na baƙi duk da cewa ita ba tsoron sakin take yi ba kawai tana shayin halin Baba ne yadda yake da son aurar da ƴaƴa tamkar rai da mutuwa. Duk da yanzu ta samu sassauci na zaman gashin ƙumar da Nasir yake mata a cikin gidansa kuɓa ba komai ba ne ya kawo mata wannan sauƙin sai sana'ar da take yi don ta lura da cewa idan har kana da sana,a to baka ma jin zugin ɓacin rai idan an maka saboda wani sa,in rashin zaman lafiyar da yake wanzuwa tsakanin wasu ma,auratan har da ganin matayensu basu da sana,a bare aikin yi, suna ganin duk wata ɗawainiyar mace su za ta ɗorawa amma ba duka aka taru aka zama ɗaya ba wani namijin ko kina sana,a ko aiki babu ruwansa da harkar kuɗinki kuma zai yi abin da ya dace da ɗaukan gabaɗaya ɗawainiyarki da sauke haƙƙinki da ya rataya a wuyansa. Wani namijin kuma shi yana jin daɗi ya ga matarsa tana da abin yi wato ta tsaya da ƙafafunta har ma da kansa zai ke ƙara mata ƙarfin gwiwa, wani kuma sai dai ma ya san duk yadda zai yi domin ganin ya murƙushe komai don kar ki ci gaba saboda yana baƙjn ciki wani kuma yana tsoron ki samu wani ci gaba ko ɗaukaka ki fi ƙarfinsa kowa dai da yadda ya ɗauki rayuwa kuma da yadda yake kallon ta.
Sadiya bata san sun shigo layin gidan nata ba domin ta yi nisa a duniyar tunanin da ta lula maganar Baba ce ta katse mata tunanin har hakan yansa mai napep ɗin jan wani uban birki don ya tsorata da furucin Baba ya ɗauka ma wani gagarumin abu ne ya faru, jin Baba ya ce
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Wannan furucin da ya yi da ƙarfi tamkar wanda ya hango wani gagarumin haɗari ya tunkaro su,shi ne ya sanya Sadiya dawowa hayyacinta a kiɗime tana ciccira ido domin ganin abin da yake faruwa, shi kuma mai napep har da sauri kashe kiɗan da ya ƙure ya tsayar da napep ɗin tare da juyowa ya ga abin da ya faru. Baba kuwa kuwa babu ruwansa da kiɗimar da ya saka su bai yi bori da sanyin jiki ba ya ce
"Wai don Allah mai ya sa Nasiru yake son tona mini asiri ne? Ya zai mayar mini da ƴa gida kuma ya garƙamawa gidan mukulli gidan uban wa ya tafi to?" Ya faɗa ya ɗorawa Sadiya Kalifa a cinya, ita Sadiya sai lokacin ta lura da gidan a kulle kuma ta gane duk wannan ɗaga jijiyar wuyan da Baba yake saboda gidan a rufe ne da yake ma basu gama ƙarasowa gaban gidan ba, dogon wuya Baban ya yi ya hango.
Baba kuwa fita ya yi daga cikin napep ɗin duk ya gama tada hankalinsa sai baza uwar babbar riga yake tana neman taɗe shi, Sadiya ta ma rasa bakin magana ikon Allah kawai take kallo, shi kuma mai napep da ya gane mai Baban yake yi wa baloƙoƙon sai ya ja wani ƙaramin tsaki ba tare da kowa ya ji ba. Baba kuwa ƙarasawa bakin ƙofar ya yi ya taka matakalar ƙofar gidan ya taɓa kwaɗon (Padlock)Ɗin da aka rufe gidan cike fa faɗa ya ce
"Sadiya wai ni kika rako ko kuwa ke na rako da kika zaune a adaidaita sahun? " Cikin sanyin jiki Sadiya ta fito tana cewa
"Baba gani na yi gidan a rufe" Yana harararta ya ce
"Kuma don gidan a rufe sai ki zauna a ciki kamar wanda dai so kike ki koma gidana" Bata tanka masa ba ya tsaya tare da kama ƙugu yana hangen ta inda Nasir zai fito. Mai napep kuwa ya wani sako ƙafa waje ya ɗauki mataji(Kumb)Ya ɗan taja gashin kansa cike da tantiranci ya ce
"Yallaɓai karka manta dai duk tsayuwar da nake yi a wajen nan a kuɗi take don haka yawan jiran da zan yi yawan hauhawar farashin kuɗina" A zuciye Baba ya ce
"Abin da ya fi hauhawar farashin kuɗinka, sai ka ce sata kana tsaye ba tafiya kake yi ba bare ka ce mai kake ƙonawa amma kake batun kuɗi yo ba zan biya ba, bayan ma zuwan nawa babu biyan buƙata" Wani irin durowa ya yi daga napep ɗin ya tsaya Baba yana jifansa da wani kallo, mai napep ya waiwaya ya ga layin ba kowa yana ɗaga rigarsa sai ya zaro wata zarɓeɓiyar wuƙa soke a jikin wandonsa, da sauri Baba ya matsa a kiɗime har yana zamewa ya surmiyo daga saman dakalin ƙofar gidan, mai napep ya ce
"Bani haƙƙina, in ba haka ba in farɗe maka ciki daga kai har ƴaƴan naka" Da sauri Sadiya ta ƙanƙame Kalifa cike da tsoro dama ita sai ta ga ma tamkar wani ɗan shaye-shaye ne Baba hannunsa yana rawa ya saka a aljihub babbar rigarsa sai ga kuɗi ya fito da su ƴan dubu-dubu kusan dubu ɗari biyu bakinsa yana rawa yake faɗin
"Nawa ne kuɗin naka har na jiran da ka yi" Mai napep ya ce
"Dubu da ɗari biyar" Baba hannu yana rawa ya ce
"Ga dubu biyu ka riƙe canjin" Karɓa mai napep ɗin ya yi ya mayar da wuƙar ya koma cikin napep ya ɗakko ɗari biyar ya jefawa Baba ya ce
"Ni da kake ganina haƙƙina nake nema, babu ruwana da sai na karɓi haƙƙin wani shi ya sa ba na sata, na gwammace duk runtsi na nemi na kaina na kaucewa wulaƙanci, kuma ni da kake gani ko akuya ban taɓa kashewa ba ita ce dai dabba bare kuma mutum kawai barazana ce saboda masu ci da haƙƙin wani" Yana gama faɗar hakan ya shiga napep ɗinsa ya tada ya kunna waƙa ya yi kwana ya bar wajen a guje.
Baba ɗari biyar ɗin ya ɗauka ya zauna a kan dakalin yana faɗin
"Wasu yaran zamanin fitsararru ne, ashe ma duk bige ne ba iya caka wuƙar zai yi ba, ai wallahi da na san haka ne da dubu ɗaya zan bashi" Ya faɗa yana haɗa kan kuɗin ya mayar aljihu, Sadiya kawai kallonsa take da mamakin kalamansa duk da babu wani abu sabo a lamarin Baba.
Ranta ƙuna yake bai dace a ce ya yi mata abin da ya mata ba, ta yaya za a yi a ce mijinta ya kaita gidan ya tafi ahi kuma ya dawo da ita. Waje ta samu ta zauna take ganin ikon Allah sun kwashe ya fi minti arba,in amma babu alamar Nasir sai mutane da suke wucewa, Baba sai hamma yake a jere can da ya gaji ya ce
"Tashi mu je gidan mahaifiyarsa ki zauna w can ki jira shi, ai in ya dawo ya je can ya ɗakko ki" Wasu hawaye ne masu zafi suka kwaranyo mata, jin wai gidan sirikarsa zai kaita, sirikar da ita ce silar duk wasu abubuwan da suke faruwa, sannan ta yi imani da Allah sai sun yi wa Baban wankin babban bargo sannan kuma ya bar mata abin gori na cewar ubanta ne ya dawo da ita. Kamar daga sama ƙwaƙwalwarta ta kai mata wasu tunani a take ta zaɓi ta yi wa Baban ƙarya don tsira da daraja da mutuncin ta, duk da ƙarya ba ɗabi'arta ba ce kuma ba halayyar ta ba ce.
Cike da danne abin da ya ɗarsu a zuciyarta ta ce
"Baba ai Hajiyar bata gari ta yi tafiya" Kamar wanda ta faɗa masa saƙon mutuwa ya ce
"Subhanallahi bata gari kuma? Amma ai ba za a rasa sauran ƴaƴan nata a gidan ba" Da sauri ta ce
"Tare suka tafi" Ya numfasa ya ce
"Kai ni dai na ga ta kaina wallahi yaron nan yana son tada mini hawan ruwa, to ke dama baki ɗauki mukulli ba" Sadiya ta ce
"Shi ya datse gidan da kansa"
Baba ya ce
"Dama ya shirya shuka tsiyar nan amma dai mu je gidan, kuma wallahi sai dai mu tafi a ƙafa ba zan biya kuɗin adaidaita ba" Yana faɗa ya fara tafiya, haka Sadiya ta bi bayansa tana ɗauke da Kalifa a kafaɗarta, ranta har ya mata daɗi ganin Baban bai zubar mata da mutunci a wajen Nasir da mahaifiyarsa ba, duk da ta san da wuya ne idan bai faɗa masa cewa ya rakata gidan a rufe ba.
Suna tafiya yana masifa wayar Nasir kuwa ya kira ya fi a ƙirga amma bata shiga, ko da suka koma gidan ɗakinsa ya shiga ita kuma ta je ɗakin Mama Talatu.
Mama ta ce
"Sadiya yankuka dawo har gabana ya faɗi ko dai dama yaji kika yi shi ne kika yi ƙaryar tare kuk?" Kai kawai ta girgiza.
Sai a ɗakin Mama Habiba suka kwana saboda Sumy ta kafa rashin mutuncin Kalifa ba zai kwamta a katifa ya musu fitsari ba, shi kuma ɗakin ƴanmatan dama bata ma tarki zuwa ba saboda ta san rashin kunya za su mata.
Baba washe gari bai