Showing 51001 words to 54000 words out of 178828 words
Chapter 18 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
a je ko ina ba har ya fara gajiyawa da wasu abubuwan duk da dama wani haƙƙin yana tauyewa ne.
Tana kallonsa ta ce
"Amma ni da ba zaman kaina nake yi ba zaman aure nake sai in ke ɗaukar ɗawainiyar kaina" Sheƙeƙe ya kalleta ya ce
"To Sadiya kar ki nemi sana'a ki zauna a haka" Yana gama faɗar hakan ya tashi ya nufi ɗaki da kallo ta bi bayanshi har ya ƙulewa ganinta, wani uban tagumi ta doka tana tunanin mafita, ita dama tana son sana'a sai dai rashin jari, ba ma wannan ba ita tun da ta yi auren nan tsawon shekara uku bata da wata nutsuwa sai dai damuwa.
Ko da ta shiga ta kwanta haka ya zo mata da buƙatarsa, babu yadda ta iya ta sauke nauyin haƙƙin duk da bata da wani ƙwarin jikinta sai dai tana tsoron kwanciya da nauyinsa sannan tana fargabar mala'iku su kwana suna tsine mata idan ta bijirewa umarninsa.
Washe gari da safe ta gama ɗumama tuwon ta zuba ta kawo masa har ta zubawa Kalifa ma, tana zaune ta yi shiru tunani ya yi awon gaba da ita ƙamshin miyar ne ya daki hancinta tana shaƙa kawai sai ta ji zuciyarta ta tashi, wani amai ta ji yana yunƙuro mata amma saboda ƙarfin hali take ƙoƙarin mayar da shi sai dai hautsinawar da cikinta ya yi shi ya sa babu shiri ta yi waje a gudu-gudu domin jin aman bashi da niyyar dakatawa.Tun da ta je bakin makwaranya take sheƙa amai kamar za ta amayar da ƴaƴan hanjinta, Kalifa ne jin ƙaran ƙololon aman tashi ya fito ya zo ya tsaya yana kallonta, har ta gama ta gyara wajen bayan ta wanke baki da fuskarta, duk sai ta ji jikinta ya mata nauyi hannun Kalifa ta kamo yana cewa
"Momma amai" Amsa ta bashi kawai, suna shigowa falon ta ga Nasir ya dakata da cin abincin da yake tana shigowa ya zuba mata idanu tamkar yau ya fara ganinta, ba ma wannan ba yadda yake mata wani irin kallon tuhuma shi ne abin da ya ɗaga mata hankali duk ta ji ta tsargu, duk da bata gama gane inda kallon nasa ya dosa ba.
Saurin kawar da kanta ta yi ta nufi inda ta tashi ta zauna, tana cewa Kalifa ya zauna ya ci gaba da cin tuwon. Kamar daga sama ta ji Nasir ya ce
"Kin san dai ba na son amai, a kan mai ina cin abinci za ki wani ƙwaƙulo amai kawai ki sa duk abincin ya fita daga raina, ai sai ki zo ki ɗauke tun da burinki ya cika na daina ci sai ki ajiye kw kya ci anjima" Danne abin da ta ji ya yunƙuro mata na takaici ta yi, ta tashi ta ɗauke ta fita ta kai kicin ta dawo, tana shigowa ya ci gaba da mata kallon ƙwaƙwaf sai da ya bari ta zauna ta ji ya jefo mata wata tambaya da ta saka ta tafi wata duniyar tunanin da bata yi shi ba, ya ce
"Wai aman mene ne kike yi Sadiya, kar dai ki ci min ciki ne da ke?" Wannan tambayar da ya mata ta sanya ta luluƙa duniyar tunani da zargin kanta, na farko tabbas wannan watan bata yi al'ada ba (priod) Sannan ta lura ma sai take ta jin kasala sannan kuma daga ta ci abu ma sai ta ji babu maganar da ya yi ce ta katse mata tunani ya ce
"Magana nake miki Sadiya" A tsorace ta ce
"Ni bani da wani ciki" Wani kallon ƙurilla ya mata ya ce
"Ai dama kar ma ki fara don ni ba na son haihuwa a kai a kai, yaro shekara biyu a masa wani ƙani, ai haihuwa ma kamar mage bashi da wani alfanu shi ya sa ake son tsarin iyali" Kallonsa kawai take bata ce komai ba, har ya tashi ya haɗa kan wayoyinsa ya ajiye ya je ya sake wanke bakinsa saboda tuwon da ya ci ya ɗauki abubuwansa ya juya zai fita ta ce
"Baka bada abinci ba" Ya juyo cike da gajiyawa ya ce
"Abinci, abinci, abinci" Sai da ya maimaita sau uku sannan ya yi wani tsaki, store ya je ya buɗe ya ɗakko taliya guda ɗaya ya rufe ya fito ya ce
"Gashi nan kuma wallahi kar ki juye duka, idan kika zuba rabi sai ki ɗan ƙara ki ajiye idan na dawo zan mayar store" Cikin sanyin murya ta ce
"Ka bada kuɗin cefane babu kayan miya sannan mai ma saura kaɗan, sai in ba almajiri ya siyo" Cike da tijara ya ce
"Wallahi naira biyar ba zan bayar ba wannan idan kina jero buƙatu ai sai ki talauta ni, wallahi shi ya sa nake so in yi aure ko na samu sassauci na san amaryar da zan auro za take tarairayar aljihuna tana buɗe bakin jakarta don ta tallafa mini" Yana kai wa nan ya saka takalmansa ya fice.
Bayan ta gama gyaran gidan ta yi wa Kalifa wanka ita ma ta yi, wanke wanke ta yi da wankin banɗaki ta gyara kicin tas. Ganin Kalifa ya yi bacci ta haɗa kayan wanki ta je ta wanke, duk abubuwan nan da take gabanta yana faɗuwa domin tana ta juya maganar Nasir a ranta a kan maganar ciki, ita kanta bata son ta samu ciki yanzu ba ma yanzu ba ita idan son samu ne Kalifa ya zama shi kaɗai ne wanda zai zama rabo tsakaninta da Nasir domin ta san gidan nan ba gidan dauwamarta ba ne, babu ma alamar zaman zai ɗore duk da ta san mutuwar aurenta tamkar rasa wani sashe na zaman lafiyarta ne a gidan mahaifinta amma dai tana zaman jiran tsammanin ta inda mafita za ta zo mata watarana!.
Tuno da tsinken pt na awon ciki wanda lokacin da take shayar da Kalifa Nasir ya zargi ciki ne da ita ya ringa mata rashin mutunci da hana rayuwarta sakat, shi ne da ya ga babu haza ya siyo pt ɗin ya ce ta gwada, tana dubawa babu ciki shi ne ya ringa jero hamdala kamar dai wani abu ne daban, sai ka ce ba shi ne mamallakin cikin ba, kamar dai ba shi ne yake lallaɓowa ya karɓi haƙƙinsa ba.
Kasancewar lokacin guda huɗu ne sai ta ajiye ukun yanzu ta ɗakko guda ɗaya domin ta gwada, sai ta ajiye masa idan ya zo ya ga layi ɗaya ne babu ciki sai ya sakar mata mara ta yi fitsari. Tana ɗakkowa ta je ta samu wani ɗan murfi ta shiga bayi ta yi fitsarin ta fito gabanta sai faɗuwa yake tana fargabar sakamakon.
Ko da ta zo ta ɓare pt ɗin ta tsoma a fitsarin ta ciro yayin da fitsarin yake tafiya a cikin pt ɗin domin fitar sakamako tare da matsananciyar faɗuwar gabanta yake tafiya. Lokacin da ya gama tafiya idanunta ra runtse da ƙarfi tana ta karanto addu'a a a zuciyarta a kan Allah ya sa ba ciki ne da ita ba, in ban da ma irin rayuwar da ta samu kanta a ciki a ce wai kana fargabar ganin kana ɗauke da ciki sai ka ce wani cikin shege!.
Hannunta karkarwa yake, kai gaba ɗaya ma sai jikin nata yake karkarwa shahada ta yi ta buɗe idanunta warai sai a kan sakamakon layi biyu ne a jiki raɗo-raɗo ƙafafunta da ta ji suna barazanar jumurin ɗaukar gangar jikinta da sauri ta zube ƙasa tana zaunawa zaman dirshan a fili tana furta
"Innalillahi wa inna ilahi raji'un"
*JIDDA*
Kunnuwanta ta sakawa auduga daga maganganun da su Umma suke yadawa a cikin gidan, duk wanda ya shigo gidan ganin kaya tana jin yadda Umma take nuna musu akwatuna 24 a matsayin lefen Aliya ta faɗa musu har da mota duk da motar Abba ya ɗauke ta ya kai gidan abokinsa aka ajiye ta, sannan sai ta nuna akwati biyu da kit a matsayin lefen Jidda mutane su yi ta faɗin Aliya ta yi goshi don wasu ma ganin kayan ya sa sun ɗauka wani hamshaƙin mai kuɗi ne Aliyar ta aura.
Umma duk ta kasa sukuni sun hana ransu sakat da ƙyashi da hassada ji take tamkar ta sauyawa Aliya da mijin Jidda a nata ganin ai Jidda ba za ta auri wanda ya fi mijin ƴarta Aliya ba.
Hassada suke nunawa a fili amma ita Jidda ko a jikinta, sai dai kuma da ya rage saura sati guda biki sai Umma da Aliya suka keɓe a lokacin da Jidda bata nan tana gidan su Salama sun tafi rabon cingam da kati, duk da har gidansu Ibrahim Salama ta rakata da Mummy ta ce sai ta je ta gaishe ta, sun ga tarɓa ta mutuncin kuwa a nan Jidda ta fahimci ta samu surukar arzii, sannan ta ƙara fahimtar ba ƙaramar ƙauna take yi mata ba, hakan ya sa ta ƙara jin hankalinta da kwanta da auren Ibrahim ko ba komai idan uwar miji tana sonka za ka samu salama a gidan mijinka.
Umma ce ta kalli Aliya da ta zuba uban tagumi, duk ta bi ta rame ta yi duhu ta ce
"Aliya na faɗa miki ki dajna saka damuwa a ranki, kar ki je ki samu wani ciwon kin san dai dama an ce hassada mugun ciwo ce bare kuma ta haɗu da damuwa a zuciya abin sai ya miki illa don abin sai ya yi yawa wai shege da hauka" Aliya ta buɗe bakinta da kuka yake son ƙwace mata ita damuwarta idan ta tuno kayan akwatin Jidda sai ta ji duniyar ta mata zafi, gani take gabaɗaya kayan da ita suka dace ba da Jidda ba saboda ita ce kyakkyawa kuma ita ce ma dai ta dace da auren miji kamar Ibrahim ba Jidda ba.
Tana jan hanci ta ce
"Wai Umma ya kike so in yi ne? Ina zan saka raina yanzu gwala gwalan da aka sakawa Jidda a lefe ni fa idan aka cire zoben ciki gabaɗaya sai ya saya kayan lefena har da canji, ga wasu miliyan uku a ajiye, sannan da kunnena na ji Salama tana cewa wai miliyan biyu ya bada kuɗin ƴanmatanci amma saboda Jidda matsiyaciya ce dakyar ta karɓi dubo ɗari biyu shi ma sai da Salama ta saka baki, yanzu da ni ce ba shikenan na samu wajen baje hajar karɓar kuɗaɗe ba, kina dai gani dakyar Kasim ya bani dubu hamsin shi ma yana min ƙorafin babu a rayuwa na tsani a furta min kalmar babu yanzu dubu hamsin mai za ta mana" Umma ta sauke ajiyar zuciya tana jin babu daɗi ta ce
"Ai ni yanzu ban san ba ya za a yi ma, wallahi na rasa mafita ko kaɗan gashi su Jidda ita da ƙawayenta Ibrahim ya biya musu kuɗin gyaran jiki ya kwaso kayan da za ta raba ya kawo mata suna nan jibge a ɗaki kamar babu gobe" Aliya kawai sai ta rushe da kuka ta ce
"Har kuɗin ƙunshi ya biya fa, jiya da dare ma kuɗin da ya bata ta miƙo min dubu ɗari wai ko za mu ƙara ni kuwa na jefa mata kayanta kar ma ta yi tunanin kuɗinta wata tsiya ne a wajena"
Umma tana zaro idanu ta ce
"Dan ubanku kika bata kuɗin? Wane shegen ya ce miki ana mayar da hannun kyauta baya, ai kai faƙiri baka biyewa mai arziƙi bayan kin san kina da buƙatar kuɗin"
Aliya ta ce
"Umma akwai damuwa fa a ce wai ni ce Jidda za ta taimakawa, ki ga wata shegiyar haɗaɗɗiyar mota wallahi da ni motar nan ta dace Umma" Ta faɗa tana kukan takaici.
Umma tana jin tamkar ta dishashe auren ma, amma abun da Allah ya nufa ya daɗe da yi, hakan ya sa ta ce
"Yanzu tun da dai Abbanku ya ce walima za a yi kin ga kayan can da Ibrahim ɗin ya kawo mata ya isa ku rarrabawa ƙawayenku to ya za ki yi tun da Allah ya ƙadarta miki talaka za ki aura, ai kawai mu bada kai bori ya hau"
Cikin rashin fahimta ta ce
"Umma ban gane ba"
Umma ta ce
"Aliya dole mu sauya taku, dole mu ɗauki haƙuri da jumurin halin da muka tsinci kanmu, ina nufin yanzu dole mu fito mu nunawa Jidda soyayyar ƙarya, mu danne duk wani ɓacin rai da za mu ji a tattare da ita, mu jata a jiki ta haka ne za mu samu shiga jikinta ta saki jiki da mu ko bayan an yi auren in ya so sai mu yi amfani da damarmakinmu wajen cika duk wani buri da muke da shi nan gaba!" Shiru Aliya ta yi tana nazarin maganar Umma duk da tana jin hakan da wuya ta iya amma kuma in har hakan ne dole ko da dariyar yaƙe ta yaƙi Jidda ta ga ko za ta yi nasara a kanta!
Tsaye Aliya ta tashi ta rungume Umma ta ce
"Umma ta kin fi ta kowa, Umma mikiya mai hangen nesa, tabbas ta haka ne za mu samu abin da muke so, don na ci alwashin sai na mallaki Ibrahim ko ta halin ƙaƙa, sai na zamewa Jidda ƙadangaren bakin tulu" Ta faɗa tana sakin Umma ta shiga juyi a tsakiyar ɗakin ta ce
"Umma kalli diri da kyauna ban dace da Kasim ba da Ibrahim na dace, ban dace da rayuwar talauci ba da gidan arziƙi na dace"
Umma ta ce
"Ai ki saka a ranki ƙwace goruba a hannun kuturu ba zai yi wahala ba, ke ko zaman kishi ne gwara ki yi da Jidda"
Aliya ta ce
"Wallahi kuwa tun da ba uwarmu ɗaya ba uban ma kowa da nashi, bare a ce auren miji ɗaya ya haramta a garemu!".
Haka suka ringa tsara yadda abubuwa za su kasance wajen yaƙi da zukatansu ganin basu nuna ƙiyayya a fili ba.
Da daddare Ibrahim ya zo wajen Jidda bayan ta fita sun gaisa suna ɗan tattaunawa tana zaune kan wani dakali da yake daga can ƙofar gidan shi kuma yana tsaye ta jingina da jikin motarsa, hira suke cikin natsuwa da kwanciyar hankali, tsaftatacciyar hira ba irin hirar da wasu ƴanmata da samarin zamani suke yi ba wacce hira ce da ta saɓawa addini da kuma al'ada, wanda yawanci wasu samari da ƴanmatan sun ɗauki hakan a matsayin wayewa, bayan ba wayewa ba ce jahilci ne da rashin tsoron Allah da kuma tuna makoma.
Hira da taɓa jikin juna, ko hirar marar kyaun sauraro, gabaɗaya ya saɓa addini sannan daga ke har shi ba za ku yi daraja a idanun junanku ba sannan ko da Allah ya yi kun yi aure za kuke zama da zargi!.
Cikin hirar tasu ne Ibrahim ya ce
"Jiddanah!" Murmushi ta yi ta ɗago tana kallonsa ta ce
"Na'am" Ya ce
"Ina so na miki wata tambaya amma ina jin nauyi" Ta ɗan yi shiru tana jin babu daɗi a ranta don ta yi tunanin ko magana zai mata a kan lamarin Aliya sai da ta ɗan ɗaure fuska don ita bata son wai don za ta auri namiji ko kuma bayan ta aure shi, ta tsaya yake sanin sirrin gidansu ko kuma yake faɗawa wasu daga danginta magana ba za ta lamunci hakan ba, ko yaya naka-nake ne sannan duk daren daɗewa ana iya sauya miji amma ɗan uwa ba a sauya shi, don haka duk yadda nake yake to naka ne idan ka ba namijin ƙofar ya san sirrin gidanku to tabbas wataran gori ko wulaƙanci zai iya biyo baya idan ma hakan bai samu ba babu wani alfanu ga mace take kwashe sirrin gidansu tana faɗawa miji.
Ta ɗan sauke ajiyar zuciya ta ce
"Ka faɗa in har da sarari zan faɗa maka" Ya hurar da iska daga bakinsa ya ce
"Kawai idan ba damuwa ne ina son sanin tarihinki ma'ana ina son sanin asalin labarinki na san mahaifanki sun rasu amma bayan haka ban san komai ba, kuma ba don wai wani abu ba kawai dai ina son sani" Sai da ta kalle shi sannan ta mayar da idanunta tana kallon ƙasa ta ce
"Sunana Hauwa ana kirana da Jidda, mahaifina ɗan asalin ƙasar Niger ne a wani gari da ake kira Doso, mahaifina saboda halin babu da kuma wasu matsalolin wanda yarinta bata bari na san su ba kasancewar lokacin shekarata goma. Wannan dalilan ne suka saka ya baro ƙasarshi ya dawo Nigeri'a , lokacin da ya zo ya dira a garin Kano bai san kowa ba cikin ikon Allah suka haɗu da Abba ya taimaka masa, ka ga wancan gidan shi ne gidan da muka zauna da mahaifana a ciki muka rayu" Ta faɗa tana nuba masa wani gida da yake kallon gidan Abba, wanda gidan yanzu a rufe ma yake babu kowa a ciki, waiwayawa ya yi ya kalli gidan kafin ya juyo yana kallonta ganin idanunta sun cika da ruwa, bata yi ƙasa a gwiwa ba ta ɗora da faɗin
"A kwana a tashi abota mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu don Allah har kasuwa tare suke zuwa da mahaifina Malam Abdullahi, koyaushe mahaifina yana faɗawa mahaifiyata girma da darajar Abba a wajensa a ganinsa ba kowane mutum nr zai nuna karamci kamar yadda Abba ya nuna masa ba, abotarsu ta saka ƙawance mai ƙarfi ahiga tsakanina da Aliya, koyaushe muna tare muna son junansu sanann mahaifanmu mata ma basa nuna mana bambanci gidanmu tamkar gidansu Aliya haka nima. sai dai ita Umma bata ƙawance da mahaifiyata sai dai in an haɗu a gaisa ko wani dalili mai ƙarfi" Ta faɗi hakan tana jan hanci da alama dai akwai wani abu da take kusa zuwa wajen faɗa yadda ya ji muryarta tana rawa, ko kuma labarin da take bashi ne yake taɓa mata zuciya.
Ta ci gaba da faɗin
"A watarana wacce ba zan taɓa mantawa da ita ba, ita ce ranar babu makaranta domin ranar asabar ce, muna zaune muna ta hira da mahaifiyata na ce mata wajen Aliya zan