Showing 33001 words to 36000 words out of 178828 words
Chapter 12 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
ɗin guda biyu Husna da Hibba karyawa suke dankalin turawa ne da wainar ƙwai sai shayi mai kauri da kuma farfesun kifi suna ci suna hira wayar Hajiya ta yi ƙara ɗagawa ta yi ta ce
"Hello Nasir" Nasir ya ce
"Hajiya ina kwana" Amsa masa ta yi tana faɗin ga abincinsa ya amsa mata da gashi nan zuwa sai ya ce
"Kalifa ne yake kashin haƙori da amai da zazzaɓi shi ne Sadiya ta ce za ta kai shi asibiti"
A harzuƙe Hajiya ta fara faɗa tana cewa
"Wai Nasir sau nawa zan faɗa maka cewa wasu matan munfukai ne, suna faɗar jinyar ƴaƴansu ne kawai don su tatsi kuɗin miji, wato ta ɗauka kai sokon namiji ne to ahir ɗinta wallahi wani kashin haƙori ne za a kaiwa likita to likita ya bashi mai, sau nawa zan faɗa maka laulayin haƙori ba ya jin magani, shi ne za a wahalar da kai a yaudare ka ai wallahi ɗana ya fi ƙarfin mace ta ci kuɗinsa rabu da ita naira ɗari ta isa ta biya buƙata zan bada maganin a kai mata" Sosai ya ji wani daɗi a ransa yana son yadda mahaifiyarsa take taya shi tattalin kuɗinsa, ya gama wayar lokacin ta dawo falon ya kalle ta a wani wulaƙance ya ce
"Hajiya ta ce za ta bada maganin a kawo" Sai da ta kai zuciyarta nesa sannan ta ce
"To"
Store ya je ya ɗakko shinkafa da wake daidai wanda yake bayarwa a dafa ya kawo ya bata ya juya ko sallama bai mata ba ya fice ya banko ƙofar gidan. Shiru ta yi tana ta tunanin rayuwarta a ce kai baka da wata kima ko daraja a wajen miji bare ƴan uwansa ɗanka bashi da wata daraja yanzu a ce ɗansa bashi da lafiya amma ya hana a kai shi asibiti sai mahaifiyarsa ce za ta ce masa za ta bada maganin, kwanciya ta yi a kusa da Kalifa tana ta tunani.
Zuwa can ta tashi ta fita ta fara wankin banɗaki tana cikin yi ta fara jin ƙaran wayarta, kafin ta zo har kiran ya katse wani ya shigo, tana ta tunanin ko lafiya sai ta ga sunan Babanta gabanta ne ya faɗi ta fara tunanin Allah sa alkairi ne.
Jiki sanyi ƙalau ta ɗaga wayar ta gaishe shi ya amsa tana jin muryarsa raɗau babu alamun damuwa hakan ne ya bata tabbacin babu wata damuwa ko matsala.
Baba Ya ce
"Sadiya kiranki na yi in ce ki tayani godiya wajen mijinki kai Allah sakawa Nasir da alheri" Shiru Sadiya ta yi sai dai bata bayyanawa Baba mamakinta ba ta ce
"Godiyar mai Baba?"
Baba ya ce
"Ka ji yaron arziƙi ashe ma bai faɗa miki ba, shi ya sa fa ake so in mutum zai yi alheri ya yi tsakani da Allah ba sai wani ya sani ba, shi ya sa aka ce hannun hagu kar ya san na dama ya miƙa" Sadiya ta ce
"Haka ne Baba"
Baba ya ce
"Wallahi Sadiya wayata na ji tana ta ƙara ina dubawa na ga mijinki ne bawan Allahn nan na gaishe shi" Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tsayawa Sadiya jin Baba ya ce wai shi ya gaishe shi ba ma Nasir ɗin ne ya gaishe da Baban ba.
Baba ya ci gaba da faɗin
"Kawai bayan ya amsa gaisuwata sai ya ce Baba ka tuwo akawun lamba, bai jira na ƙara magana ba ya yanke kiran, ni kuwa ban yi bori da sanyin jiki ba na kwashe lambobin akawun ɗina na tura masa, ina turawa na kira shi ban san lokacin da na ce ranka ya daɗe na tura ba" A take hawaye suka fara sartu a fuskarta wai Baban ne ya cewa sirikinsa ransa ya daɗe saboda kawai ya ji maganar kuɗi wannan wace irin zubar da kima ce.
Baba ya ce
"Da to ya amsa min ya kashe ana jimawa sai ka dubu ɗai-ɗari dubu na dukan dubu har dubu goma ya ce in ɗauki dubu biyar in ba tsohuwarki dubu biyar, na rinƙa masa godiya, yanzu dai na bata dubu uku ni na ɗauki bakwai shi ne na kira ki kema ki tayani gode masa, yaron arziƙi ai ke da shi sai mutuwa ce za ta raba"
Sadiya a zuciyarta ta ce
',In sha Allah ba zan mutu a gidan Nasir ba ina saka ran wataran zan fita daga wanna rayuwar marar ƴanci rayuwa marar galihu, rayuwa marar daraja' A fili kuma ta ce
"Amma na ji daɗi Allah saka masa da alkairi kuma in ya dawo zan yi ta gode masa tare da yaba masa" Haka Baba ya mata sallama cike da jin daɗi. Tana ajiye wayar za ta juya wani kiran ya shigo, ta ɗauka Baban ne amma tana dubawa sai ta ga Mama ɗauka ta yi bayan sun gaisa ta ɗauka Mamar za ta tambaye ta yaya aka ƙare jiya da ta dawo ko dai wani abu makamancin haka, ko ma dai ta tambaye ta damuwarta kamar yadda ta je mata da ƙorafin jiya ko ba komai sai ta lallashe ta ta tausasa mata yadda za ta rage mata raɗaɗi a matsayinta na uwa amma sai ta shiga faɗa mata alkairin da Nasir ɗin ya musu tana ta msta godiya da musu fatan haɗin kawunansu, haka dai Sadiyar take bata amsa cikin ƙarfin hali daga ƙarshe suka yi sallama.
Tana kashe wayar ta koma ta zauna daɓas tana tunanin kenan dai Nasir ya ƙara ƙirƙirar wata hanyar toshe duk wata ɓaraka, ita tana gidan yana musguna mata ko kuɗin kai ɗanta asibiti bai bata ba gashi a can kuma yana bajinta wato zai wanke laifinsa ko da ta je musu da magana ba za suke amincewa ba, tun da suna masa kallon mutumin kirki wannan alama ce ta sun zaɓi farincikin ɗan wani a kan farin cikin nasu ƴar!.
*JIDDA*
Ranar da aka kawo kayan saka ranar Aliya da yamma, guɗa ƙawayen Umma suka cika gida da shi Umma tamkar za ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, saboda ganin kowacce a wajen ana kawo mata kayan saka rana sallayoyi dabino, kuɗi, wasu ma kuɗin ake kai musu amma sai gashi Aliya har da ƙaramar akwati wannan dalilin ya sa maƙota suke ta zuzuta abin har kan Mama da Aliya ya fashe. Da dare bayan an watse Aliya sai gwada takalman take tana wani bada faɗi a tsakar gida lokacin Abba baya nan yana waje tare da baƙi sai murna Aliya take tana cewa
"Umma na wuce raini a unguwa, na kere sa'a wallahi Kasim yana matuƙar sona, ya kankaro min mutunci a wajen ƙawaye irin wannan takalma kala goma atamfofi kala biyu da turaruka ina ga in aka ga lefe ai ina jin ƴan baƙin ciki sai sun zauce" Ta faɗa tana ɗaga murya.
Umma ta ce
"Aliya kin yi sa'ar miji, mijin nunawa sa'a mijin bugar ƙirji ki nuna a ko jna saboda duk namijin da aka ce miki zai iya bugun ƙirji ya faranta miki to tabbas yana da kyakkyawan buri idan ya samu maƙudan kuɗi ina ga sai kyautar miliyoyi" Suka kwashe da dariya duk abin da suke Jidda tana ji don ita tun da aka kawo kayan da aka buɗe a gaban mutane ta gani bata sake gani ba, don ko bayan mutane sun watse da ta je ta fara ɗaga takalman Umma ta ce
"Jidda kar ki ƙara ɗaga kayan nan, wato kina ɗagawa zuciyarki tana ƙuna ko? Abu ne da ba za ki taɓa samu ba, wataƙila ma mijin naki ya ƙoƙarta ko dubu talatin ne kuɗin lefen da na saka ranar har ma sadaki tabbas aurenki bashi da maraba da sadaka Jidda" Lokacin d Umma ta mata wannan furucin ta ji ciwo amma kuma tuno yadda take jin Ibrahim a ranta da zuciyarta sai take gani ko babu ko kwabo za ta aure shi ta zauna da shi tsakani da Allah, kuma za ta masa matuƙar biyayya har ƙarshen numfashinta!.
A fili kuma sai ta tashi siyam-siyam ta nufi ɗaki tana jin babu daɗi a lan abin da Ummar ta mata ko don ba ita ta haife ta ba, amma ita Jidda a zuciyarta daɗi da farinciki take na kayan da aka kawowa Aliya kuma bata jin ƙyashi ko baƙinciki kuma bata wani tunani a kan cewa tana jin tana son wani abu makamancin abin da aka kawowa Aliyar bare ma ita kamar yadda Ummar ta faɗa ta san ma hakan ne tun da a yadda take kallon Ibrahim bata taɓa zaton zai ce da aure yake son ta ba, tunaninta bai shirya auren ba duk da baka san tanadin mutum ba amma ita bata da buri a haka take son kayanta.
Abba yana wajen yake ganin matan jefi-jefi suna zuwa suna gani tare da yin Allah sanya alkairi. Abba bayan baƙin sun tafi ya jima zaune yana ta jimami da mamaki sai dai ya san ba a mamaki da jimami da lamarin ubangiji hakan ya sa ya rasa ma wa zai tunkara da wannan magana, jin wai ashe ɗan gidan Alhaji Sule ne ya zai auri Jidda, mutumin da babu inda za a ambaci sunansa a kasa gane shi babban mutum mai dukiya da ya yi shura, lallai Allah, Allah ne yana yin yadda ya so a lokacin da ya so, yana ba wanda ya so sanda ya so Wayo ko dabara ba ya ba mutum abu Allah kaɗai yake bayarwa, Allah shi yake bayarwa a gode masa ya ƙara!.
Abba ya nisa tare da sakin wata ajiyar zuciya yana duba naira miliyan uku a gabansa wanda 500k guda shida kowanne nannaɗe da kyaure, yana tunano yadda suka gabatar masa da kansu a matsayin baƙinsa da suka yi waya cewa za su zo bayan sallar isha'i bai taɓa saka ran zai gansu ba shi ya sa da ya ga zuƙeƙiyar mota ma bai kawo cewa baƙin nasa ba ne.
Yadda suka karrama shi duk da yana da labarin Alhaji Sule bashi da wulaƙanta ɗan adam ya san mutuncin mutane amma sai ya ga abin ya fi yadda ake faɗa, tabbas zai yi alfahri a ko ina da mijin da Jidda za ta aura saboda ko da ya zo ya gaishe shi haƙiƙa ya yaba da hankali da tunaninsa, kuma a yadda ya ganshi bai taɓa tunanin masu hannu da shuni ne har haka ba, amma ya zo gidan talakawa neman aure haƙiƙa duk wanda ya auri Jidda ya dace da mace kamila kuma ta gari, duk da ba shi ya haifi Jidda ba amma yana alfahri da ita, kuma ya yi wa su Alhajin bayanin wace ce Jidda kuma sun ji sun gani.
Kuɗin ya fara tattarawa yana tunanin yadda zai yi da wannan kuɗin, tun da shi kaɗai ya karɓi baƙin nasa, duk da naira miliyan goma suka bayar a matsayin kuɗin gaisuwar uwa da uba da kuma kuɗin kuɗin saka rana gabaɗaya suka kawo amma ya ce shi ba zai karɓi miliyan goma ba ya yi yawa dakyar ma ya ɗauki miliyan uku.
A fili ya furta
"Alhamdulillah, Allah na gode maka da ka bani iko zan sauke nauyin marainiyar nan, zan damƙa ta a hannu na gari Allah ka taya mijinta riƙo ka bashi ikon kulawa da ita!" Gabaɗaya ya kwashe kuɗin ya saka a babbar riga bayan ya ware dubu goma ba don komai ya yi hakan ba sai don kar ya saka Umma ko Aliya jin wani abu marar daɗi a ransu saboda shi kansa bai zaci haka ba kuma ya ga suna farinciki da abin da Kasim ya mata, kar su fara raina abin da ya yi.
Gidan ya shigo ya same su suna zazzaune, suna cin abinci ɗaki ya shiga ya ɓoye gabaɗaya kuɗin yana sakawa a ransa cewa bayan bikin zai samu kadara ya sayawa Jidda da kuɗin wannan don bai yarda ya ba kowa kuɗinta ba.
Bayan ya fito ya zauna ana hira yana cin abinci sai da ya kammala ya yi gyaran murya ya ce
"Ummar yara" Umma ana washe baki aka ce
"Na'am" Ya ɗan nisa kaɗan tare da zaro dubu goman aljihunsa ya ajiye ya ce
"Ga kuɗin gaisuwa da saka ranar ƴarki Jidda!." Gaban Jidda ne ya bada wani rasss a inda Umma da sauri kafin ta furta komai ta miƙa hannu ta ɗauki kuɗin a fili ta fara irgawa tana cewa
"Dubu ɗaya, dubu biyu, dubu uku, dubu huɗu, dubu, biyar" Da ta zo kan dubu biyar sai da ta ɗago kai ta kalli Jidda wacce kanta yake sunkuye saboda kunya ita kuma Aliya bakinta washe tana kallon hannun Umma saboda tana ganin kuɗin hannun Ummar da take irgawa ya kusa ƙarewa. Umma ta ci gaba da irgawa tana murmusawa cike da ƙeta a ranta ganin dai kuɗin bashi da maraba da sadaka, da ta zo dubun ƙarshe sai da ta ƙara sautin ta ta ce
"Dubu goma cass" Ta faɗa tana kallon Abba da yake murmushi kafin ya furta wani abu Jidda ta tashi da sauri saboda kunya ta nufi ɗaki. Umma a zuciyarta ta ce
'Shegiya aniyarki ta biki wato ba za ki iya kukan baƙin ciki a gaban mutane ba sai kin shige ɗaki taɓɗi lallai iska tana yawo da mai kayan kara in banda matsiyaci kika kwaso har yaushe zai kawo dubu goma' Maganar da Abba ya mata ne ya dawo da ita daga maganar zucin da take ya ce
"Kin gama irgawa" Tana dariya mai sauti ta ce
"Wallahi na gani abin arziƙi yarinya ta yi goshi" Aliya ta ce
"Umma dubu goman ne goshi" Ta faɗa tana ƴar dariyar yadda Jidda za ta ji, Abba ya ce
"Ke ba na son shashanci tashi ki tafi ki ba mutane waje" Da sauri ta tashi ta shige ɗaki tana shiga ta rungume Jidda ta ce
"Amarya ta ango ya kawo mata dubu goma" Jidda duk sai ta ji kamar ta nutse ita kuma Aliya murna take ganin ta fi Jidda komai dama ta san babu yadda za a yi ita kyakkyawa mummuna ta fi ta komai na aure!.
Tun da aka saka rana wata guda sai soyayya da shaƙuwa suka ƙara tsananta a tsakanin masoyan biyu wato Jidda da Ibrahim, kowa ƙoƙarinsa ya ba ɗan uwansa kulawa tamkar ƴan biyu haka suke rayuwarsu kamar dai ƴan uwa ba wai wanda soyayya ce ta haɗa ba!.
Abba ya yi ƙoƙari ya saya musu kayan ɗaki iri ɗaya daidai ƙarfinsa, a inda ya saya kayan kicin ma komai babu bambanci. Sai dai Umma tana ta sayan kayan kicin tana turawa ƙasan gado don bata yarda a ce da Jidda marainiya da kuma Aliya mai uwa a raye an musu komai da komai iri ɗaya ba.
Jidda sosai suke murna ita da ƙawarta Salama Jidda za ta yi aure!.
Mummy yau saura kwana biyu su dira a Nigeri'a za su dawo daga Dubai inda suka tafi sayyayar kayan lefe.
Yau saura kwana biyu a kawo lefe don ranar ta kama gabaɗaya tare za a kawo domin Abba ya sanar da kowanne ɓangare na maza cewa rana ɗaya za a kawo. Aliya da Amatallahi suna ta rawar kai sanadin wasu hotuna da Kasim ya turawa Aliya na wasu lesuna ya ce kaɗan daga cikib kayan da aka saka a lefe ne sauran sai an kawo ta kashe ƙwarƙwatar idanunta. Wannan dalilin ya sanya Amatullahi da Aliya cewa ranar kawo kayan lefen a ɗakin Umma za su ɓuya babu inda za su tafi domin a kawo a kan idanunsu saboda Aliya ta sanar da Kasim cewa a samo motar da za ta kawo masu kawo kaya, hakan ya sa ya ce ai dole ma ya samo motoci, kanta ya fashe suna ta yadawa Jidda magana wacce ita bata wani damu da abubuwan da suke faɗa ba. Har yau bata san waye Ibrahim ba shi kuma yana jin daɗin mu'amala da ita a hakan rayuwar duniya bata dame ta ba kuma har yau ko ɗankwali bai bata kyauta ba bare naira biyar sai dai yana mata wani tanadi na musamman a cikin gidanta wanda farinciki ne da kwanciyar hankali in sha Allah.
Yau ya kama alhamis ranar da za a kawo lefen Jidda tun da rana ta shirya ta cewa Umma ta tafi gidan su Salama, suna can suna ta murna da kuma sakawa a ransu cewa duk abin da aka kawo za su karɓa su yi farinciki!.
A zaure Abba da ɗan uwansa da kuma amininsa da maƙota guda biyu. Umma ita da ƙawarta sun kasa zaune sun kasa tsaye suna ta tunanin yadda za a kawo kayan nan sun da Umma tana ganin kayan saka rana ma an yi musu bajinta bare kuma lefe mai kankat.
Kuɗi ma sai da aka ɗora dubu ashirin.
A can gidan Daddy zuƙa zuƙan motoci kuma galla galla sabbi dal, sai sheƙi suke na sabunta da kuma gani ka san sun ci kuɗi. Guda uku aka ware inda ma'aikatan gidan suke fito da wasu kyawawan kwatuna suna lodawa a motocin sai da suka gama saka wa tas, maza biyar ne wanda za su tafi kai kayan inda kowacce mota da direba. Wata baƙar mota sabuwa wacce ita ma gabaɗaya kujerunta ledojin sabunta ne za an buɗe get motocin za su fita Daddy ya zaro mukullin daga aljihu ya miƙawa wani direban da yake a tsaye karɓa ya yi ya shiga motar suka jera suna tafiya a laye sabuwar baƙar motar ce a tsakiya suna fita aka rufe get ɗin suka lula a saman titin da tamkar domin su aka yi shi, suka tasamma gidan su Jidda.
Ibrahim da yake kallonsu ta saman windown a bene ganin fitarsu ya ɗaga hanni yana godewa Allah tare da fatan Jidda ta ci gaba da amincewa da shi don ya san yau kayan lefensa za su tabbatar mata da waye shi, tun da ta faɗa masa an kawo dubu goma kuma bai ga alamar rainuwa a tare da ita ba,