Showing 120001 words to 123000 words out of 178828 words
Chapter 41 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
ya kaita ɗakinsa a lokacin da shi da Jidda basa wajen. A gefe ɗaya tana tunanin idan Jiddar ce kuma fa? Wace amsa za ta bata shin mai Jidda za ta ɗauka dangane da sauya akalar tsanarta zuwa tsantsar ƙaunar ƙarya da suka yi don kawai ta auri mai dukiya, tabbas ta san duk wanda ya yi ido huɗu da ita yanzu to haƙiƙa sai ya mata kallon tuhuma domin gabaɗaya alamomin rashin gaskiya sun bayyana ƙiri-ƙiri a tare da ita.
Jin takun yana matsowa dab alama ce ta mai hayowar ya kusa ƙare tako matakalar da sauri ta koma ta shiga waige waige tana son gano inda za ta ɓuya ta gwammace ta kwana a ɓoye idan har hakan zai yiwu a kan a ganta zargi marar adadi ya hau kanta!.
Abin da yake kai kawo aranta shi ne idan kuma Jidda ce dole ai za ta ga bata falon sannan komanta tana falon ita cw bata nan mai za ta ce mata kai abin ya haɗe mata goma da ashirin. Amma hakan ba zai sanya ta karaya ba don cikar burinra da na Ummarta ya fi komai a halin yanzu. Kaf ɗakin bata ga wajen da za ta ɓoye ba tare da an ganta ba hakan ya sa ta yi wajen drower za ta shiga tsakanin drower da bango ta takure ko Allah zai tseratar da ita kar a ganta, sai daj tana zuwa ta ga wajen ya yi mata kaɗan ta shige domin dole za a hango ta a kiɗime ta fito ganin babu mafaka sannan sirinta yana dab da tonuwa sai kawai ta buɗe ƙofar banɗaki ta shige tana shiga ta mayar da ƙofar ta rufe. Jikinta har karkarwa yake da ta ji an turo ƙofar ɗaki ta shiga fargabar sa sai take jin tamkar ko numfashi ta yi sai an ji.
A ɗarare ta samu wata tula a jikin ƙofar ta leƙa taakar ɗakin gabanta ya bada sautin dimmmm ganin Ibrahim ne ya shiga a nan ta tabbatar kashin ta ya bushe domin ta san tun da ya dawo ɗakin dole Jidda ma ta yi wa ɗakin kutse. Yana shigowa ya ajiye wayoyinsa a kan gadon ya hau cire rigar jikinsa a take Aliya ta yi wa idanunta masauki a kan kyakkyawar lallausar fatarsa kasancwar ya bata baya nw yana juyowa sai da ta kusa zaucewa ganin kyakkyawan gargasa shimfiɗe a faffaɗan ƙirjinsa ya kwanta lifet kallon tsari na kyawun halittar da Allah ya masa kawai take a take ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin lallai Jidda ta more da samun kyakkyawa kuma nagartaccen miji kowacce mace ta samu miji irin wannan tana ganin a duniya an sallame ta ta wannn ɓangaren.
Gaban ta ne ya buga da ƙarfi da ta yi wani tunani cewa ko dai wanka zai yi a take ta ji shagalar da ta yi da kallon nasa tana yaba kyawunsa ta ji ya ɓace mata yawun bakinta ya ƙafa ta ji bakin ya bushe. Jikinta ne shiga karkarwa tana hangowa cewa idan ya buɗe banɗakin ya same ta ya za ta yi tana cikin wannan tunanin sai ta ga ya juya ya nufi wajen drower ya buɗe ya ɗakko wasu kayan ƙanana ya saka coffe ɗin wando da wata farar riga mai hoton damisa coffe a jiki a hanzarce ya ɗauki wayoyinsa tana jin yana waya ya buɗe ƙofar ya fita.
Bayanta ta juya ta jingina a jikin ƙofar bayan ta rufe idanunta tana sauke ajiyar zuciyar tsalllake rijiya da baya, yanzu abin da ya rage sai ta bari idan ya ɗan jima da fita sai ta fito ta lallaɓa ta koma falon ƙasa.
A haka ta lallaɓo ta fito tana sauri sai da ta leƙa daga jikin ƙofar ta ga tana hango step ɗin na benen alamar Ibrahim ya fita sannan ta buɗe ƙofar a hankali ta fito kamar wanda aka jefo Jidda haka Aliya ta hango ta gashi ta riga ta fito daga ɗakin har ta rufe ƙofae babu damar ta koma hakan zai sa Jiddar ta ji ƙaran ƙofa da hanzari Aliya ta ji gefen jikin bangon da yake gefe ta laɓe, haka Jidda ta hayo tana sanye da wata doguwar riga mai tattara a hannun wacce gabaɗaya rigar kamar an halitta ta a jikinta yadda ta kama jikinta dole kowane namiji mai lafiya ya kalleta ba zai iya ɗauke idanunsa ba sannan dole sai wani abu ya ɗarsar masa a zuciya, tana riƙe da fulas ɗin tuwon don dama na miyar ne ta kai da plate da cokulan.
Addu,a take a zuciyarta kada Allah ya sa Jiddar ta waiwayo bayanta don tana juyowa za ta ganta sai dai Jidda da hankalinta yake a gaba bata waiwayo ba ta wuce tana takunta ta nutsuwa wanda gabaɗaya rigar da ta kamata duk takun da za ta yi sassan jikinta suna rausayawa. Tana tura ƙofar ta rufe ta nufi inda ya cire kayansa ya ajiye ta shiga linkewa za ta saka a kayan wanki don ita al,adarta ce kaya ko na wanki ne saj ta linkeshi.
Aliya tana shirin kama gabanta ta sauka ƙasa sai kawai ta ji ƙaran takalmi ana hayowa sama, idanu ta zaro da sauri ta lallaɓa ta tura ƙofar ɗaya ɗakin a hankali ba tare da ƙofar ta yi ƙara ba ta shige ta rufo gabaɗaya ta haɗa gumi tana leƙowa ta hango Ibrahim yana hayowa, duk ta haɗe gumi na tsurewar da ta yi,. ta ji lokacin da ya tura ƙofar ɗakin Jim kaɗan ta ji an sake buɗewa sai ta fara jin maganarsa yana cewa
"Ba jimawa zan yi ba ina ɗakko saƙon zan dawo na yi tunanin ma a mota na bar shi amma da na duba ban gani ba na san yana office"
Sai ta ji Jidda cikin wata sassanyar murya mai tafiyar da nutsuwar miji tana cewa
"Yanzu wannan tuwon da ka sa na maka haka zai yi ta jiranka" Ta faɗa ta karashe tana wani yin kamar ƙaramar yarinya ta ji lokacin da ya ce
"Kin san dai wannan tuwo dole ne ma in ce ai har ɗumame zaki min da safe ko Jiddana?" Ya faɗa cikin sigar wasa da lallashi. Wani daɗi a cika ran Aliya jin yana batun cin tuwon sai kuma ta ji Jidda ta ce
"To ni dai karka daɗe ka ji" Ya kalle ta yana dariya ya ce
"Idan na daɗe tsallan kwaɗo za ki saka ni" Tana kumbura baki ta ce
"Kuka zan yi" Hannunsa ya saka a bakinsa yana ɗorawa a kan laɓɓansa guda biyu ya ce
"Karki yi min kuka da wannan idanun naki in ba haka ba zan rama da tsakiyar dare" Da hannu biyu ta rufe fuskarta tana jin yadda koyaushe son Ibrahim yake ƙaruwa a zuxiyarta saboda ya iya tafikar da mace ya san kalamai da ayyukan da zai yi mace ta so shi tabbas Ibrahim ya iya koyawa mace yadda za ta so shi.
Aliya duk da bata ganinsu amma tana jin yadda tattaunawar tasu take gudana haka nan kuma ranta yana ƙuna da abin da suke faɗa, sai dai ta sa duk ihu ne bayan hari, sannan saura ƙiris tarayya da alaƙarsu ta zama tarihi babu abin da ya fi faranta mata irin da ta ji ya ce sai ya ci tuwon nan har da ɗumame da safe ai kuwa ta san shikenan burinta ya cika!.
Tana jin yana mata sallama har yana cewa da dare za su je su gaishe da Mummy duk don ya farwntawa Jiddan tun da ya san tana ƙaunar Mummy ita ma Mummy tana ƙaunarta. Tana jin ƙaran saukarsa daga benen sannan ta ji lokacin da Jidda ta koma ɗakin ta rufo. Aliya tana maƙale a ɗakin a jikin ƙofa kamar wata ƙadangaruwa, sai da aka ɗan jima ta tabbatar yanzu Ibrahim ya bar falon ƙasa wato ya fita kafin ma ta gama wani tunani ta jiyo ƙaran buɗe get ɗin gidan haka ya bata tabbacin ya fita ma.
Yanzu ne take so ta shammaci Jidda ta fito ta yi saurin sauka ƙasa tun da ta tabbatar yanzu Jidda ta san bata falon thn da ta fito ta ga bata ganta ba, saboda haka dole ta tanadi hujjar da za ta kare kanta da ita duk da wannan ba matsalarta ba ce a halin yanzu matsalarta ta fi karkata ga sauka daga saman wannan kafin asirinta ya tonu. Juyawa ta yi tana kallon ɗakin da take ciki tana ƙiyastawa a ranta yanzu haka Jidda gyaran ɗaki take ta san kuwa abu ne mawuyaci ta kasa shigowa ɗakin da Aliyar take ta gyara.
A zuciyarta ta ce
"Uwar shegiyar tsaftar jaraba, dama wannan bata dace da ƴan aiki ba ni ce na fi dacewa a kawowa ƴan aiki wannan kalar ma,aikata ce ba kalar hutu ba ma,aikatan ma ƴan wanke-wanke' Ta faɗa tana jan ƙaramin tsaki.
Cikin sanɗa ta buɗe ƙofar a hankali ta mayar ta rufe ta fara lallaɓawa tana takawa a hankali sai da ta je tsakiyar benen kawai ta ji ta yi wa ƙafarta masauki a cikin lema, kafin ta tantance sai ji ta yi suuuuuu ta yi wata uwar sufer da ta ganta zaune jaɓar tana gangarawa bata yi masauki ba sai a step na ƙarashe jin ƙaran buɗe ƙofa a sama ya sa ko hutawa bata yi daga gangarowar ba ta tashi da sassarfa ta tashi jin ƙugunta ya riƙe ta miƙa hannu ta riƙe tsantsa tana takawa dakyar da sauro ta yi tsakiyar falon Saude da take haɗa kayan wanke wanke a kicin tana ganin abin da yake faruwa a idonta ta shiga dariya marar sauti har da riƙe ciki.
Aliya kuma sai ta shiga sauri-sauri gudu-gudu ta yi hanyar ɗakin da yake kusa da wanda Jidda ta shiga yin wanka, tana wani cangala ƙafa kamar kwaɗo, don tafiyar kamar tsalle haka take tana shigewa ɗakin ta rufo. Saude kuwa har lokacin tana ta dariya duk da bata san dalilin da ya kai Aliya saman ba amma kuma dai ta san ba wani abin kirki ba ne tun da babu yadda za a yi take sauri tana son guduwa alamun bata so a ganta duk da faɗuwar da ta hanga ta yi daga saman benen amma ko fatsarwa bata yi da jin ciwon ta tashi tana tafiya kamar wata sabuwar yar shayi tana tale ƙafa tana riƙe ƙugu ga wani ɗan tsalle da take tana cangala ƙafa.
Akiya tana shiga ɗaki kawai sai ta kwanta a ƙasa sa,arta ɗaya ma kafet ɗin ɗaki da yake da laushi sosai, birgima take tana ambaton wayyo a hankali ji take kamar ta yi ihu amma babu hali don gwiwar hannunta ma da ta bugu ciwo take mata. Haka ta daure ta shiga banɗaki ta wanke ƙafa sai fuskarta ta fito sai da ta ɗan ji jikin nata ya ɗan koma daidai ta buɗe ƙofar ta fito tana ƙoƙarin gyara ɗankwalin kanta. Jidda kuma tana ɗakin bayan ta ɗan ƙara ɗame gadon duk da shimfiɗar bata waji ɓaci ba. Dama cikin zannuwan gadon da Mummy ta aiko mata ranar nan ne wanda ta ce a wajen MAMAN AFRAH marubuciya ta saya domin babu abin da bata sayarwa, guda huɗu ta bata zanjuwan gadon da mai haɗe da labulaye da mai bargo sai mai filo huɗu dukka na ɗinkawa ne sai kuma wani lumtsumeme shi kuma na kamfani ne. Sun yi kyau sosai don da ta kira Mummy tana mata godiya sai ta ce za ta bata lambar MAMAN AFRAR ko za ta saya wani abu saboda kayanta suna da inganci tana siyar da labulaye zannuwan gado, takalman yara da manya, kayannyara ɗinkakku da na kamfani mayafai atamfofi lace abaya hijabai tutaren wuta, magungunan mata maganin sanyi, kayan sanyi, kayan kicin da sauransu.
Tana cikin gyarawar ne ta ji rigif alamar faɗuwar wani abu dalilin da ya sa ta fito kenan sai dai abin mamakin tun daga can saman take waige -waige har ta zo ƙasa bata ga alamar komai ba, sai dai ta ji ta taka lema da bata san ya aka yi hakan ta faru ba. Tana zuwa tsakiyar falon hakan ya yi daidai da zuwan Aliya ma sai kawai Jidda ta kalle ta ta ce
"Wai ina kika shige ne ni wallahi na ɗauka ma fita wajen kika yi ko saƙo aka kawo miki" Tambayar nan ta sake saka Saude a shakku don yanzu ta ƙara tabbayarwa Jidda bata san da zuwan Aliya sama ba, hakan ya sa ta fara hasashen dama ko sho dalilin da ya saka ta taho a gaggauce har tana faɗowa daga matakalar, don dama ita ta taho daga ƙofar da take sada ta da falon Jidda idan aka taho daga ɓangaren su na ƴan aiki lokacin sa ta yi wa falon tsinke ta hangi wulgin Aliya ta yi sama to duk tunaninta Jidda ma tana saman, sai bayan tana kicin kuma ta ga fitowar Jidda daga ɗaki ita ma ta zo ta nufi saman, don ta ji lokacin da Jidda take cewa Aliya ina ta yi kuma. Dama ita Saude tana zargin Aliya da wani abu na rashin gaskiya don yanayin da ta ganta ranar nan a kicin ma rashin gaskiya ne ɓaro ɓaro iya nazari da tunaninnta tana ganin tsantsar tsana da kuma ƙyashi a idanun Aliya da take yi wa Jidda.
Da gangan ta ɗauki ruwa ta je ta zuba a matakalar don ta san tun da har Jidda bata san ta hau saman ba bayan a can turakar mai gidan take to ta san tabbas akwai wata maƙarƙashiya. Shi ya sa ta zuba tuwan domin ta san tun da Jidda ta hau samn to Aliya za ta yi ƙoƙarib kuɓuta, bayan ta zuba ne kuma ta ga Ibrahim ya dawo ga hau saman tana ta addu,ar Allah ya sa kar ya ga ruwan ko kuma ya taka, duk da ma akwai takalmi a ƙafarsa ba lallai santsin ya kwashe shi ba, bayan ya fito ne kuma sai ta ga ma yanayin yadda Aliya ta taho kaɗai ya isa ta gangaro idan ta samu kufcewar take matakala sai kuma Allah ya sa ta taka ruwan ta faɗo. Ta so a ce Jidda ta ganta sai dai kash an samu akasin lissafi.
Amsar da Aliya ta ba Jidda ya ƙara saka Saude a tarkon mamaki domin cewa ta yi
"Dama na san idan baki ganni ba sai kin tambaye ni cikina ne ya hautsina min, ganin kina banɗakin wancan ɗakin shi ne na je na shiga na wancan ɗakin" Ta faɗa tana ƴar dariya Jidda ma dariyar ta yi ta matsa kusa da Aliyar ta ce
"Ki ce rage ciki kika tafi, Allah sarki har na tuna rayuwarmu ta yarinta idan na je gidan Umma daga na ce ina jin kashi sai ke ma ki ce kina ji, in riga ki shigewa banɗaki kike ta cewa in yi sauri karki yi a wando" ,Ta faɗa tana dariya sosai, Aliya ma daeiyar take duk da hannun Jidda da ya taɓa kafaɗarta ji take tamkar an ɗora mata garwashi saboda tsantsar tsanar Jiddar da take ji amma babu halin nunawa.
Aliya ta ce
"Umma sai ta ce ku dama kamar ƴan biyu ɗaya ba zai yi abu ba sai ɗayan ma ya ce zai yi Allah na tuba kashi dai ba a matse shi ba sai a ce ana ji idan ɗaya ya ce zai yi wa ya sani ma ko da kanku kuke ƙwaƙulowa" Aliya ta maimaita maganar cikin kwaikwayar muryar Umma suke dariya.
Kan kujera suka ƙarasa har lokacin hannun Jidda rataye a wuyan Aliya kamar yadda suke dafa kuna lokacin da suke yaran, Jidda tana jin wani daɗi da farincikin ganin sauyawar rayuwarta a ƙanƙanin lokacj, wato a da ta rasa duk kulawa da soyayyar ƴan uwantaka da ta ƙawance tsakaninta da Aliyarta uwa uba tsantsar tsana daga Umma amma yanzu gashi komai ya shiga littafin tarihi.
Suna zama Jidda ta ɗauke hannunta tana cewa
"Ni wai har alwala kika yi ne " Ta faɗa ta sigar wasa dariya Aliya ta yi don dama da gayya ta wanke ƙafa da fuska don ta cirewa Jidda shakku a kan cewa daga banɗaki take sai da ta gyara ɗaurin ɗankwalinta ta ce
"Kawai dai fuska tw ce na wanke"
Saude an barta da tsantsar mamaki tana tunanin makirce da ƙarya irin na Aliya hakan yansa ta ɗarsa zargin akwai wani abu da ya kai Aliya saman wanda kuma bata jin alkaiti ne don ta san dai ai Aliya bata ce zuwa ta yi kawai don ta ga saman ba idan har ganin saman take son yi ai ba sai a ɓoye ba sai dai za ta yi amfani da hankali da basira don ta gane inda Akiya ta dosa sannan ta yi alƙawarin duk wani abu da Aliya za ta yi ga uwar ɗakinta Jidda to ba za ta bari ba matuƙar tana numfashi sai dai abu wanda yake dama Allah ya rubuta a littafin Jidda wanda yake ƙaddara ne ita kuma ƙaddara duk runtsi babi mai guje mata.
Ƙaran wayar Aliya ne ya katse tana ɗago wayar ta ga sunan Kasim dimm ta ji faɗuwar gaba don bata san dalilin kiran ba, sai kuma ta maje don kar Jidda ta fahimci wani abu tun da dai ta faɗa mata baya gari duk da shi bata faɗa masa za ta fitan ba sai kuma wani tunani ya faɗo mata tana jin Allah ya sa tana ɗaga wayar ta ji muryar wani daban wato a ce mata mai wayar sun yi haɗari ya mutu, shikenan ta jefar da kwallon mangwaro ta huta da ƙuda.
Tana ɗagawa ta kara a kunne tare da yin shiru tana jiran jin labarin mutuwar Kasim
Sai ta ji muryar wani yana cewa
"Ai abin babu kyan gani gabaɗaya babu wanda ya tsira a motar duk sun mutu"
Aliya bata san lokacin da ta ce
"Alhamdulillahi ba" Don tsabar son ta ji sanarwar mutuwar Kasim bata gane cewa wani ne a gefe yake maganar ba, ba wai a wayar da