Showing 57001 words to 60000 words out of 178828 words
Chapter 20 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
tamkar zai tashi sama, ɗaki ya shiga jim kaɗan sai gashi da rigar a hannu haɗe da singlet, a ƙofar ɗakin ya saka singlet ɗin ya ɗora rigar hannunsa riƙe da waya ko maɓallin rigar bai ɓalla ba hatta takalminsa tana gani a baibai ya saka, ƙofa ya nufa sai jin rufowar ƙofar gidan ta yi gararaf!.
Kalifa ta kama ta tsayar a gefe ta wanke wajena ta ɗakko shi suka nufo ɗakin, tana zuwa ta zauna a kan kujerar Kalifa yana kan cinyarta, bata ankara ba sai ta ji hannun Kalifa a kan fuskarta yana share mata hawaye, kallonsa ta yi tare da rungume shi, tana jin son ɗan nata har ciki ranta, tana rayawa a ranta ta san komai daren daɗewa za ta fita daga cikin wannan uƙubar, sannan tabbas ta san Nasir ranar nadama tana zuwa zai gane shayi ruwa ne, amma dai a juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe, don rayuwa tana cike da darasi ne sai dai mutum bai ga damar ɗauka ba, amma a kowane sakan a kowace awa akwai abubuwan da mutum zai koya kuma ya gane sai dai ruwansa ne ya yi aiki da shi ko kuma ya watsar amma dai shi ubangiji mai yin hisabi ne a kan komai!.
Wajen ƙarfe goma ta ji an turo ƙofa, sallamar Hajiya ce ta fara tashi a cikin gidan, cike da ladabi Sadiya ta amsa, sai dai fitowarta daga ɗakin domin yi wa Hajiya iso lokacin Kalifa yana biye da ita dama wanka ta masa tana shafa masa mai. Gabaɗaya fuskar Hajiya a haɗe take tamkar an faɗa mata mutuwa ko wani mugun abu, amma sai Sadiya ta daure ta ce
"Sannu da zuwa Hajiya bismillah ki shigo" Wani kallo ta jefi Sadiyar da shi ta ce
"Ba abin da ya kawoni ba kenan, ko an ce miki zama na zo idan zaman nake son yi in zauna a gidana a ɗakina mana, kin san dai ai kujeruna sun fi naki komai sau miliyan" Sadiya ta ji babu daɗi a ranta amma sai ta danne ta yi murmushin yaƙe wanda iyakarsa leɓe ta ce
"Haka ne sun fi nawa " Wani kallon ke kika sani Hajiya ta mata ta ce
"Nasir ya je mini da wata maganar banza wai ciki ne da ke" Abin ya yi wa Sadiya ciwo wato cikin sunna ne ma maganar banza hakan ya sa ta ce
."Eh gaskiya ne" Hajiya ta ɗan yi mamakin amsar da Sadiya ta bata duba da Sadiyar bata fiya kausasa harshen ba amma amsar tata sai ta ji tamkar dai a fitsarance ta yi amma sai ta ce
"To abin da nake so da ke shi ne, mun yanke shawara da Nasir da ƴan uwansa cewa wannan ciki zubar da shi za a yi" Da sauri Sadiya ta ɗago kai tana kallon Hajiya cike da mamakin kalamanta.
*BABA*
Duk kiran da yake yi wa Sumy tana jinsa amma ta ƙi amsawa hakan ya sa ya fara rafkawa Mama Talatuwa kira, Mama jin kiran ta tunkari ɗakinsa tana zuwa ta ganshi a ƙasa a kwance yana sharɓa uban gumi ta ce
"Subhanallahi Malam lafiya" Baba da ya buɗe baki zai bata amsa jin gudawar ta taho sai ya ji tamkar idan ya buɗe baki kashin zubowa zai yi bai yi wata-wata ba ya sake komawa banɗaki, sai gashi yana tafiya yana ɗan sunkuyawa yana dafa bango yana faɗin
"Wayyo Allah, gaskiya gudawa bata da daɗi ko in ce bata da imani, kalli yadda ta ƙarar min da ƙarfi lokaci guda, ɗan katan daɗi da na ci duk ta saka na kai masai(Toilet ) Haba ai sai na gwammace daman awara na ci don ji ba don idan ban yi gudawar nan ba a wando za ta zubo da ba zan yarda in yi kashin abinci ƴan gayun nan da na ci ba" Tana ta kallonsa har ta samu ya zauna tana son amayar da magana amma tana tsoron masfifarsa sai da ya zauna da sauri ya zame ya kwanta yana cew
"Ni wallahi ina ga mazaunan nan nawa ba za su zaunu ba ma, kai jama,a lokaci guda mutum lokaci guda ba mutum ba"
Mama Talatuwa ta ce
"Dama haka cuta take yanzu mutum yanzu gawa... Kafin ta ƙarasa ya ce
"A bakin ki Talatuwa kuma sai kin rigani mutuwa, ni nan tsawon rai zan yi sai na haifi na miji ko kangararre ne ya taimaka min na san daɗin haihuwa sannan zan mutu" Cike da mamakin maganarsa ta ce
"Allah ya huci zuciyarka dama ni ban maka fatan mutuwa ba, ai cuta ba mutuwa ba ce" Shiru ya yi don jin cikinsa yana kartawa ya ce
"Ki nemo Sumayya ta kawo min maganin gudawar da Habiba ta bata ta saya da safe" Da to ta amsa ta tashi ta fito, ɗaki ta nufa ta samu Sumy ta ce
"Sumayya Babanku ya ce ki kai masa maganin gudawa" Shiru ta yi sai kuma ta tashi ta fita, tana zuwa ɗakinsa ya fara masifa
"Ke saboda ke shegiyar yarinya ce ina wannan halin amma ba za ki kawo min maganin ba?" Tana danne ƴar dariyarta ganin Baban ya yi zuru-zuru don ta tuna matsayinsa na mahaifinta bai nuna tausayawa ba gareta ya bata kuɗin maganin ba sai yanzu kuma zai ce ta bashi hakan ya sa ta ce
"Baba dama fa guda huɗu ne ni kuma duka na shanye" Cike da masifa ya ce
"Si kike dai in fitar da kuɗi ko in banda ma almubazzaranci a ce magani biyu ma bai isa ki shanyw ba sai kin sha huɗu" Bata yi magana ba ya ce
"Ai kuwa da in banda hamsin ko ɗari a siyo min maganin gwara na zauna gudawar da kanta in ta gaji da fitowa ta tsaya min"
Haka Baba ya yi ta gudawa har dare amma bai sha magani ba, sai da ya ga yana dab da rasa ransa sannan ya bada naira hamsin aka siyo masa ya sha.
Washe gari ma haka gudawar ta dawo don haka ya galabaita ma, sai masifa yake yana cewa ƴaƴansa basu da amfani da a ce maza ne da yanzu sun kai shi asibiti Arfat ce ta lallaɓa lokacin baccin wahala ya ɗauke shi ta je ta auno shinkafa kwano biyu ta ɗora ta dafa ta lallaɓa aljihun rigarsa ta ɗauki dubu biyar ta yi miya har da naɓa don dama mahaifiyarta ce da girki.
Aka dafa shinkafar nan har dare kowa yake wadaƙa da ita ya ci ya ƙoshi don dama cikin wacce ya noma ce da ya jibge sai kayan abinci sun yi tsada zai fito da ita ya sayar, shi ma da ya tashi haka Mama Bilki ta kai masa shinkafa da miya da nama ya karɓe ya ci yana ta saka albarkar cewa ashe tana son sa tun da har bakin girkinta tana sayen abinci ta dafa kowa ya ci lallai yana alfahri da ita.
Ko kaɗan bai san cewa abincinsa ba ne kuma a aljihunsa aka samu kuma a aljihunsa kuɗin cefanan ma ya fita, yana da halin da zai wadata iyalansa amma ya gwammace ya musu ƙwauro ya ce kowacce ta je ta nema ba ya musu kallon su mata ne kuma ba ya tsoron hakan ya zama hanyar lalacewarsu.
*JIDDA*
Daga ita har sauran wanda suke kusa da su na motar kallon Aliya suke, hatta direban motar sai da ya taka wani uban birkin da sai da wanda yake bayansa ya kusa buga masa tasa motar, Allah ya rufa asiri ma lokacin ba wani gudu ake yi ba tun da suna ƙoƙarin kutsa kai cikin gidan Jiddan ne. Kowa ya hau tambayar ko lafiya, shi dai direban ƙarasawa ya yi ciki ya yi parkin don duk girman gidan sai da gabaɗaya motocin suka shiga ciki.
Ƴar uwar Ummar ce ta ce
"Lafiyarki Aliya mai yake damunki" Aliya da shigowarsu cikin get ɗin gidan ya sa ta sake susucewa hankalinta ya ɗuguzuma da tashi, ganin gidan da ƙwayaye tarrr ya haske ko ina kamar rana ga motoci ne tamkar wajen aiyar da su suna gefe a lulluɓe, hakan ya sa ta ji kamar ta haɗiye zuciya ta mutu. Ita ma ƴar uwar Abban ta ce
"Ko dai jifa aka yi wa yarinyar nan ne a kan aure in ba haka ba yanzu nan take lafiya ƙalau amma kuma a ce ta gigice haka?" Ƴar uwar Umma wacce ranta gabaɗaya ya ɓaci na ganin gidan Jiddan ta ce
"Allah ne ya san karatun kurma" Jidda kuma duk ranta ya sosu ta ce
"Aliya mene ne ?" Aliya ji ta yi da Jidda ta yi magana tamkar ta ɗauki wuƙa ta daɓawa Jiddar ai dai dole idan Jiddar ta mutu Ibrahim ya aure ta, ta zauna a wannan gidan mai kyau wanda a ganinta kowacce mace za ta yi buri da mafarkin samu!.
Direban ma gabaɗaya ya maido hankalinsa kansu shi da abokinsa na gafensa, Aliya kuma da sauri ta danne abin da take ji ta tattaro nutsuwar ta ta buɗi baki tana mai miƙa hannu wajen ƙafarta ta ce
"Wani abu ne na ji ya cije ni a ƙafa ta" Ƙofofin motar aka buɗe suka suka fito sauran jama'a kuwa da basu san mai yake faruwa ba duk sun fito daga motocinsu suna shige ciki suna son ba idanunsu abinci domin su kashe ƙwarƙwatar idanunsu, haske-haske aka shiga yi ƙasan kujerun amma ba a ga komai ba, har ma ana tunanin ko kunama ce amma ta ce ba kunama ba ce. Ƴar uwar Umma ce ta kama lafayar ta rufa mata tare da riƙe hannunta, a inda ƴar uwar Abba ta kama Jidda wacce duk ta shiga damuwa da yanayin da ta ga Aliya.
Ƙofar sa za ta sada su da ainihin cikin gidan suka nufa mata sai sakin guɗa ake yi, amma Aliya suna dab da shigewa ƙofar ta ja ta tsaya ta ce
"Aunty ni ba zan shiga ba" Ƴar uwar Umma ta ce
"Me ya sa mu shiga mana ki raka ƴar uwarki kin san dai ba zama za a yi ba yanzu za a fito a tafi raka ki naki ɗakin, kuma kin san dai Abbanku yance hatta ƙawaye kar a bar kowa a gidan amarya su zauna wani siyan baki gabaɗaya za a tafi a bar amarya" Aliya wacce take jin idan ta shiga ciki ta ga ɗakunan tamkar za ta haɗu da taɓin hankali hakan ya sa ta ƙara togewa duk wanda ya zo sai ya raɓe su ya wuce. Ƴar uwar Umma ta rasa ya za ta mata gashi dai ita bata shiga ba, suna nan sai ga wasu daga cikin matan sun fara fitowa suna shiga mota hakan ya sa Auntyn ta kama Aliya ta mayar da ita motar duk da motar ma tana ɗaya daga cikin motocin da suka zo ɗaukan Jidda daga ɓangaren Ibrahim.
A can ciki kuwa tun da aka shiga da Jidda bata bari addu'a ta kufce mata ba, don sai da ta yi lokacin fitowa daga gida, da za su shiga gidan nata ma ta yi a zuciyarta duk da lokacin ne Aliya ta tada musu hankali. Har aka zaunar da ita a bakin gado tana ta maimaita addu'o,in neman tsari inda mutane suke ta mata sam barka da addu'ar zaman lafiya, wasu kuma ƴan baƙin ciki suna taɓe baki musamman Amatullahi ƙawar Aliya wacce take jin haushin ni'imar da Jiddar ta samu, wasu kuma suna mata fatan alkairi, wasu suna jin dama su ne suka samu wannan daukar da wannan kyakkyawan mijin, don kana shigowa babban falon da tangamemen hoton Ibrahim za ka ci karo yana wannan kyakkyawan murmushin nasa mai tafiya da zukatan ƴan mata da yawa!.
Jidda tana bakin gadon a zaune tana lulluɓe kanta a sunkuye sai wasa take da yatsunta da suka sha kyakkyawan ƙunshin baƙi da ja duk da kasancewarta baƙa amma lallan ya haska hannun tamkar ka gudu da hannun. Sai dai idanunta yana ta hawaye rana ta tuna mahaifanta sannan zuciyarta a cunkushe da damuwar da ta lura ƴar uwarta Aliya. Salama ce ta je ta dafa ta ta ce
"To amarya za mu tafi sai mun sake dawowa, a toh wallahi ba don Abba ya hana a zauna ba da sai na jira zuwan abokan ango!" Ta faɗa tana dariyar wasa Jidda ta buɗe dashashshiyar muryarta ta ce
"To yanzu ma sai ki zauna" Murya Salama ta rage tana magana ƙasa-ƙasa ta ce
"Ko na zauna na miki zaman ɗaki?" Daga cikin lafayan take kallon ta Jidda da take kallonta don ta san zolayarta ne take yi.
Jin Jiddar bata ce komai ba sai ta ɗora da faɗin
"Taɓ ba zan zauna ba wannan angon naki ya yi ƙuli-ƙulin kubra da ni don daga gani ya shiryawa wannan ranar a toh za a kashe arna" Wata ƙawarsu da ta zo kusa da su ta ce
"Ai yau angon nan va arna kawai zai kashe ba musulmin ba ba zai barsu ba" Suka fashe da dariyar zolaya ita da Salama duk Jidda tana jinsu. Jin ana ta horn suka fara mata sallama suna fitowa.
Ƴar uwar Abba ko da ta fito ganin Aunty da Aliya a tsaye a gefe da Amatullahi ta ce
"Haba Aliya ai dai kin raka ƴar uwarki ɗaki kun yi sallama amma ji zo har cikin gidan baki shiga ɗakin ba wannan ai sai wani ya ɗauka wani abu ne, kin san dai mutane ba a iya musu" Jin hakan sai Aliya ta yi tunanin kar Jidda ta yi tunanin wani abu da ban hakan ya sa ta ce za ta shiga don yanzu ba ta son wani abu da zai nuna rashin ƙaunar Jidda a tattarw da ita, duk da ta ciki na ciki, ta fi so suke basaja kamar yadda suka shirya hakan da Umma.
Ƴar uwar Abban ce ma ta kama hannunta suka nufi ciki, Aliya daga cikin laffayar ta kafe hoton Ibrahim da yake kafe a falon a take ta ji wani abu ya tsarga mata, tana tunanin da a ce ita ce yau a wannan gidan da kuma wannan mijin lallai da ƙawaye da dangi sai sun raina kansu amma dai gashi Allah ya san halin jaki da bai bashi ƙaho ba!.
Dakyar take taka ƙafafunta daurewa kawai take, a haka suka wuce ɗakin da Jidda take wanda a ƙasa yake ba a sama ba, wani sanyi da ni,imtaccen ƙamshin turarukan wuta wanda aka siya a wajen Zainab Muhammad tahir wacce take da zafafan turarukan wuta ƴan sudan kowa ya san yadda turarukan wutan sudan suke da ƙamshi nata sun sha bamban domin turarukan wutan suna kama ɗaki ƙamshin su mai daɗi da sanyaya rai 0814 209 8878 ta number wannan suka mata magana suka mallaki nasu ga duk mai buƙata zai mata magana tana siyar da ɗaya tana bada sari a farashin sauƙi siyan na gari mayar da kuɗi gida!.
Yanayin yadda kayan ɗakin suka karɓi ɗakin tamkar dama don su aka ƙera ɗakin tangameman wadataccen ɗaki, Allah ne kawai ya sa Aliya bata yanke jiki ta faɗi ba, ko da suka shiga ɗakin cikin ƙarfin hali ta furta
"Jidda!" Jidda ta ɗago kai tana kallon Aliya ta amsa kawai sai Aliya ta je gaban gadon ta rungume Jidda tana sakin kuka, a zahiri kukan rabuwa ne amma a baɗini kukan baƙin ciki ne. Jidda ma ta fashe da kukan sai da suka yi mai isar su ƴar uwar Abban tana basu haƙuri kafin Aliya ta ce
"Jidda ƴar uwata ƙawata da bani da tamkar ki, mun zauna shekara da shekaru amma yau aure zai raba tsakaninmu sai dai zumunci amma babu kwanan gida ɗaya a ɗaki ɗaya, ina roƙon ki yafe min iya zamanmu sannan ina miki fatab alkairi" Jidda jin kalaman bogin da Aliya ta yi sai zuciyarta ta yi rauni hakan ya sa ta fashe da kuka mai tsuma zuciya tana cewa ta yafe mata ita ma ta yafe mata, haka aka fita da Aliya rai cike damƙuna da hassada!.
Sun saka ta a mota tana ta kuka wanda kukan ya zame mata biyu, hassada babban ciwo da kuma kukan zuwa gidanta da take ganin bashi da maraba da kurkuku a wajenta ita yanzu sam Kasim ba ya birgeta. Jidda lokacin da ta ji rufowar get sai gabaɗaya ta fashe da kuka har da sheshsheka.
Bayan kamar minti hamsin ta ji horn da kuma ƙaran buɗe get, shigowar motoci ta ji amma dai ba za ta bambance biyu ne ko uku ba, jim kaɗan ta fara jin ƙaran rufe ƙofofin alamun fitowar wanda suke cikin motar. Hayaniya ta fara jiyowa a falon inda take jiyo muryar Ibrahim yana faɗin
"Daga na kirawo ta kun gaisa za ku fita ku tafi gwauraye su je ɗakin gauranci masu aure su tafi wajen matansu" Ya faɗa cike da zolaya. Tana jin yadda falon ya kaure da maganganinsu amma bata iya gane mai suke cewa sai dai ta san tsiya ce suke masa don ta ji sai dariya suke yi.
Shigowarsa ɗakin ya sanya gabanta faɗuwa, sai ta ji duk wani nauyinsa take ji tamkar dai ba wannan Ibrahim ɗin nata da suke kasancewa kullum a waya suna magana ba ko idan sun haɗu kamar ba za su rabu ba.
Duk wata kunya ta rufe ta sai take jin dama su Salama basu tafi ba duk da ta san umarnin Abba ne hakan, amma a ganinta da suna nan za ta ji sauƙin kunyar da ta mata ƙawanya a zuciya duk da ta san dai ko suna nan dole za su tafi ba za su kwana a gidan ba. Abin mamaki lallai sai lokacin ta tabbatar maza basu da kunya ita tana jin nauyinsa da kunyarsa da ya shigo ɗakin amma shi kuma yana kusanto kansa gareta, domin bai yi wa kansa masauki a ko ina ba sai a kan gadon inda take zaune ya zauna dab da ita kafaɗarsa tana gugar