Showing 18001 words to 21000 words out of 178828 words
Chapter 7 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
ya buɗe masa ƙofa yana ɗaga masa hannu da masa fatan alkairi, don da gani an ga tafiya ta musamman saboda ko direba bai bi ta kansa ba, horn kawai ya yi wa mai gadin shi ne amsar maganar da yake masa a zuciyarsa kuma yana amsa addu'ar da mai gadin ya masa.
Kan titi ya nausa motar yana tafiya a hankali karatun qur'ani yana tashi a motar, tun da ya zo inda zai gangara gidan da yakr tsammanin gidan su Jiddan ne, inda ya hanga ta shiga ranar nan, gabansa yake tsanani da mummunar faɗuwa bai san dalili ba amma ya alaƙanta hakan da SO.
Misalin ƙarfe biyar ya zo wajen amma kuma har biyar da rabi babu wanda ya fito ko ya shiga gidan da yake tsammanin ganin Jiddan. Dama ba a ƙofar gidan ya yi parking ba daga can gefe ne, har biyar da arba'in babu kowa sai mutane da suke ta hada -hada da kuma yara suna ficewa sai dai shi bai san ya zai yi ya ce a mata magana ba. Yana nan sai ya hangi wata budurwa ta taho rana zuwa ta nufi gidan, zuciyarsa tana raya masa ya fita ya tambaye ta amma kuma shi ko kaɗan ma yarinyar bata masa ba yanayin shigarta da ma tafiyar da take, hakan ya sa ya koma ya jingina, don hatta karatun ya kashe kawai zaman jiran tsammani yake. Bayan ta shiga gidan jim kaɗan sai gasu sun fito su biyu ransa ne ya ɓaci a lokacin da ya ga Aliya wacce suka fito da Amatullahi wacce ta shiga gidan yanzu. Ko kaɗan ba ya son ma'amalar Aliya da Jidda don a ganinsa basu dace da yin ƙawance ba ji ya yi kamar ta fito ya ce daga yau kar su ƙara zuwa gidan su Jiddan.
Har suka ɓacewa ganinsa ransa a ɓace, daga can ya hango wasu ƴanɓata guda biyu sanye da dogayen hijabi, suna tahowa, idanunsa ƙurrr a kan Jidda don tun daga ganin da ya mata na farko bai taɓa manta kamaninta da kuma yanayin tafiyarta mai nutsuwa ba, ko ƙiftawa ba ya yi gani yake idan ya ƙifta zai rasa ganinta har abada. Zuciyarsa tana masa zillo so yake ya yi amfani da wannan damar ya fito daga motar ya tunkare ta ya faɗa mata sirrin zuciyarsa amma faɗuwar da gabansa yake ba ya ji ma idan ya fito bakinsa zai bashi haɗin kai na gabatar mata da kansa. Jidda wacce suke tafiya da Salama ƙawarta haka suka taho har suka zo daidai motar da Ibrahim yake ciki, dama hira suke abinsu amma maganar da suke basu gama ba kuma za su rabu domin gida Salamar ma za ta wuce.
Ganin motar da take gefe a ajiye kasancewar gilashin baƙi ne basa ganin wanda yake ciki, ƙarasawa suka yi suka jingina da motar, Ibrahim da yake ciki gabaɗaya an dagula masa lissafi da farko ma da ya ga sun nufo motar ga ɗauka suna ganinsa domin ya manta cewa gilashin na waje ba ya ganin wanda yake cikin motar. Kamar ya fito ya gudu haka ya ji sai da ya ga sun tsaya a jikin motar hankalinsa ya kwanta, ya rasa dalili amma dai yana tunanin saboda bai taɓa tunkarar wata ƴa mace da sunan so ba ne. Kasancewar Jidda ba baya ta juyawa motar ba gefen kafaɗarta ne ta jingina ita kuma ƙawar ta juya baya, yanayin tsayuwar da Jidda ta yi ya ba Ibrahim damar kallonta sosai.
Salama ce ta ce
"Ke ma Jidda na faɗa miki ki daina damuwa kike addu'a kawai Allah zai baki mafita...
'Jidda?" Ibrahim ya furta a zuciyarsa
'Dama sunanta Jidda,.kenan Hauwa'u ce?' Ya tambayi zuciyarsa.
Yana ƙara jefawa zuciyarsa tambayar
'To mai yake damunta ake bata haƙuri?' Ya jefawa kansa tambayar da bashi da mai bashi amsa. Hannu ya kai jikin gilas ɗin saitin inda take tsaye ya dafa wajen.
Jidda idanunta cike da ƙwalla ta buɗe baki ta ce....
Furucin da Jiddar ta yi suka daki kunnuwan Ibrahim lokaci guda ya ga duhu ya maye hasken da yake gani, gabansa yana faɗuwa jin tashin hankalin da ya kai masa ziyara lokaci guda, da sauri ya koma ya zauna jingine da kujerar saɓanin da da ya ɗan taso yana taɓa jikin gilashin. Kansa ne ya sara da mugun ƙarfi yana jin ba zai jure wannan furucin na Jidda ba...
Wayyo hannuna🥺 10 readmore😫
*Mata masu aji akwai kayayyaki na tashin kan oga fa, akwai haɗaɗɗun tsumi da daka, da matsi ba na sakawa ba matsi da za ki tasafa ki shiga hajia, akwai na gyaran breast wacce breast nata ya kwanta lifet ta zo mu saka labule idan bata son dama kunu ina da na kwaya amma ba ƙwayar bature ba ƙwaya ta gargajiya, ingantattun itace haɗaɗu masu nagarta ki min magana in kina so ga no wayata a ƙasa*
MAMAN AFRAH
09025576222
Shin kinason hadaddun hijabs Wanda zaki ratsa ko Ina dasu?❤️kinason sanya hijabs masu fitarda asalin kyau da kyawun fuska?😹hijab din da Ana Ganinki ansan hijab neh?🥰 Anything hijjabs ask FUA ✅ got you covered.💃…Ba hijab kadai ba muna saida: inner caps, jersey veils, chantally veils and materials gowns ,jalbab,Hijab,Umrah set,lefe package,walima anko and lots more✨Muna bada sari a aika maka koina cikin Aminchi.
(location; kaduna,zaria and Gumel jigawa State,Muna delivery koina,niger,Ghana,saudia)
let us be your surest hijjabs plug,we give deliver the best.
[10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=ems_copy_t
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 6️⃣
*SADIYA*
Ranta ne ya mata ƙuna tana jin wani zafi da raɗaɗi a zuciyarta, ta fara tunanin shin mai Nasir yake nufi da ita ne? Ta yaya za a yi mace ki dawo gidanki ki haɗu da mijin ki amma ko kallo baki ishe shi ba bare ki sa ran zai miki magana ko ya yi wa ɗan da kika haifa masa.
Kallon ƙaton kwaɗon da ya datse ƙofar ta yi a karo na biyu, tana jimami a zuciyarta ta ce
'Ya san ya sauyawa gidan mukulli amma bai bani ba to mene ne nufinsa? ' Ta faɗa a zuciyarta tana saka hannu ta riƙe kwaɗon tana tunanin yadda za a yi ta buɗe ta shiga gidan, tun da babu gidan wanda take shiga a umguwar bare yanzu gidan wa ma za ka je da tsakar ranar nan, to idan ka je ma ka ce mai?. Ɗan sakin kwaɗon ta yi ya bugu jikin ƙofar yana sakin wani ɗan ƙara, kanta ta jingina a jikin bangon ƙofar daga gefe tana jin ita daj bata dace sa miji ba a gefe ɗaya zuciyarta tana faɗa mata hatta mahaifin ma bata yi dace da shi ba.
Ta jima a haka tana jin irin yadda gumi yake sartu a jikinta saboda zafin ranar da ake gabaɗaya ranar a buɗe take. Motsin da Kalifa ya yi ne ya dawo da ita daga duniyar saƙa da warwarar da take yi a zuciyarta. Ɗagowa ta yi tana ƙarewa layin nasu kallo babu kowa sai mutane da suke ficewa jefi-jefi idanu ta mayar hanyar da ta biyu ko za ta hango mashin ɗin da Nasir suka wuce amma ko alamarsa, ta daɗe a tsaye ko za ta ga ya dawo amma shiru tamkar maye ya ci shirwa!.
Zafin rana ga goyo shi kansa Kalifa so yake ta sakko shi, ganin abin ba na ƙare ba ne, don a ƙalla ta yi kusan minti talatin a wajen a tsaye amma babu alamar Nasir zai kawo mukullin. A hankali ta sakko daga matakalar gaban gidan tana jan ƙafa ga yunwa ga baƙin ciki da takaicin ɗa namiji da yake ƙunsa mata, ga rashin adalcin da iyayenta suke mata, na rashin jin damuwarta da kuma magance mata ita.
Gidan da yake kallon gidan ta, nan ta hangi inuwa da ɗan dakali a wajen, haka ta cira ƙafafu tamkar iska za ta ɗauke ta, suna zuwa inuwar ta zauna har lokacin bata sauke Kalifa daga bayanta ba. Bayan ta zauna sai ta kifa kanta a gwiwarta tana jin babu daɗi ganin duk wanda zai wuce sai ya kalle ta, har ta fara zargin ko daj sun zata mahaukaciya ce. Maganar Kalifa ta katse mata tunani jin ya ce
"Mom a sakko ni" Ya faɗa cikin maganrsa ta gwaranci da bata fiye fitowa raɗau ba, hannu ta kai ta sakko shi, sai lokacin ta lura da hannunsa da ba a wanke masa ba lokacin da ya ci tuwo. Tana sakko shi ya fara ɗaga hannu yana nuna hanyar da suka baro yana faɗin
",Abba" Wani iri ta ji a zuciyarta don wannan maganar da ya yi hakan yana nuni da cewa ya ga mahaifinsa lokacin da suka wuce, baki ta buɗe cikin sanyin murya ta ce
"Abbanka yana zuwa ya ke siyo maka alewa ne, kana son shan alewa?" Kai kawai ya gyara mata.
Zuwa can tana zaune Kalifa a cinyarta jakarta ƙarama a gefenta a ajiye, ganin yara suna wucewa da uniform a jikinsu ta tabbatar yanzu ƙarfe uku ta yi.
Wani yaro ɗan maƙotanta daga can gefe ya fito sanye da unifort riga pink me ɗigo-ɗigo yayin da wandon yake purple, tun da ya hange ta yake dariya har ya ƙaraso ya ce
",Auty Sadiya" Ya faɗa yana cike da fara'a amsa masa ta yi ya shiga gaishe ta sai kuma ya ce
"Aunty ya kike zaune a waje?" Ya tambaya yana kallon ta da yake da ɗan wayonsa don zai yi shekara tara zuwa goma, rasa ma mai za ta ce masa ta yi duk ta ɗan diririce sai kuma can dabara ta faɗo mata sai ta ce
"Tare da Abban Kalifa muke to mukullin ne ya faɗi shi ne ya koma ya dubo?" Ta samu kanta da sharara masa ƙarya. Dariya ya yi bai ce komai ba don shi ko kaɗan ba ya son wannan mutumin bashi da kyawun hali ya yi ta korarsu idan suka je gidansa. Wasa ya yi wa Kalifa ya fito da alewa a jakar makarantarsa ya bashi yana ɗaga masa hannu yana masa bye-bye shi ma Kalifan bye-bye ya masa.
Alewar ya miƙa mata ta karɓa ta ɓare masa ya fara sha, shiru babu amo ba labarin Nasir har aka fara kiran la'asar abin ya ɗaure mata kai don ta san ko ma ina zai je ya ci a ce ya dawo tun da dai ta san ba kasuwa ya tafi ba tun da gashi nan da kasuwa zai je da wuri zai fita. Abin ya fara bata tsoro tana zaune babu sallar azahar babu ta la'asar gashi tana tsoron shiga gidajen maƙota cibi ya zama ƙari don matsawar ta shiga ya zo ya ganta tabbas akwai gagarumar matsala. Kalifa sauka ya yi daga cinyarta saboda ya gaji da zaman waje ɗaya, ya shiga kewaya wajen, yana ɗan wasa.
Ta buga uban tagumi ta yi nisa cikin tunanin lamuran gidan aurenta, tana tuna irin wulaƙanci da tozarcin da Nasir yake mata, ƙaran wani birki da mai mashin ya ja shi ne ya dawo da ita hayyacinsa, a kiɗime ta tashi ta je gaban mashin ɗin da ta hangi Kalifa kwance a wajen, mai mashin ɗin wanda yake ɗauke da ƴan makarantar islamiya da ya ɗakko, kanta a take ya shiga juyawa ta yi kan Kalifan da gudu ƙirjinta yana bugu tamkar zuciyarta za ta fasa ƙirjin ta fito tana faɗin
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
*JIDDA*
Idanunta cike da hawaye ya cigaba da magana don don duk abin da take faɗa iya gaskiyarta take faɗa komai daga ƙasan zuciyarta yake ta ci gaba da faɗin
"Ni ba damuwata rashin mijin ba damuwata ɗaya yadda Umma za ta takura min idan aka yi auren Aliya ba a haɗa da nawa ba, kuma kin ga Abba ba zaman gidan yake ba, sai na gwammace kiɗa da karatu in ma bata kore ni ba, don ba gori ba har goriba sai ta min a kan rashin auren"
Shiru Salama ta yi tana nazari da tunanin maganganun ƙawar tata a lokaci guda tausayin Jidda yana mamaye mata zuciya da ruhi.
Ibrahim wanda ya cika da zufa tun furucin Jidda na farko wanda shi ne ya saka shi a ɗimuwa, kuma shi har ga Allah a yadda yake jin Jidda ta gama bin jijiyoyin da jinin jikinsa ba zai iya rayuwa ba sai dai ita sai dai furucin ta ya nuna masa da sauran rina a kaba, domin kuwa da wuya wai gurguwa da auren ne, shiru ya yi ƙwaƙwalwarsa tana tuno masa haɗe da dawo masa da tunanin abin da ta furta wanda shi ne ya saka shi a ɗimuwar da yake ganin dab yake da ya rasa Jidda wanda hakan kuma babban ƙalubale ne a rayuwarsa.
'Salama damuwar yawancin ƴanmtan yanzu shi ne auren namiji mai kuɗi kuma kyakyawa, yawancin kowacce burinta ne wannan, ni kuma inda muka sha bamban da saura kenan tunanina burina haɗe da ƙudurina basa kan namiji kyakkyawa kuma ba wai don hakan ya haɗa nasaba da munin da nake da shi ba, uwa uba dukiya basa gabana don ni a ra'ayina in auri talaka kuma mummuna in da zan samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta yadda kyawunsa ba zai ruɗi ruɗaɗɗun ƴanmata ba, sannan dukiyarsa ma ba za ta tsone musu idanu ba, kin ga burin Aliya ne wannan ni kuma bani da ra,ayi a kan hakan, amma zan ci gaba da addu'a Allah ya bani miji na gari daidai ni' Wannan su ne furucin da ya hargitsa tunanin Ibrahim da sauri ya saita madubin motarsa ƙan ƙarami na ciki wanda yake maƙale fuskarsa ya kalla a ciki, ganin irin kyawun da Allah ya yi masa sai da ya ƙara jin gabansa ya faɗi tamkar dai a yau ne ya taɓa ganin kyawun fuskarsa.
Zuwa yanzu duk ba ya fahimtar maganganun da suke tattunawa, hankalinsa ya yi bala'in tashi yana ta tunanin ya zai yi ya mallaki Jidda, tun da gashi ba ya ma cikin mazan da take da burin aurr, na farko dai shi yana da kuɗi sannan uwa uba Allah ya hore masa kyau shi kyakkyawa ne ajin ƙarshe, zai iya tabbatarwa ya cika dukkan abin da ta lissafa zai samar mata na kwanciyar hankali a gidan aure sai dai kash! Bai sani ba ko za ta karɓe shi a matsayin kyakkyawa kuma mai kuɗi don ya tabbata shi dai sai dai a saka shi cikin masu kuɗi pan ajin farko ba ma ajin ƙarshe ba.
A fili ya furta
"Ya zan yi?" Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsar ta bare kuma mafita. Yana cikin wannan tunanin kamar an ce ya ɗago sai ya ga wayam babu kowa a jikin motar, dama ya ji ba ya jin maganarsu kasancewar a ruɗe yake bai yi tunanin dajna jin muryarsu da ya yi ba. Idanu ya hanga sai kuwa ya ga Jiddan za ta shige gida ta juyo tana yin bye-bye kasancewar ita yake kallo sai ya ga tamkar shi take ɗagowa hannun bai san lokacin da ya ɗaga nasa hannun ba yana mata bye-bye tamkar wani soko. Ganin ta shige gidan ya dawo hayyacinsa sai a lokacin ya yi tunanin ashe ma bata ganinsa kasancewar baƙin gilashin motar, sannan ma shi da ba saninsa ta yi ba shi kaɗai ne ya san ta ya san matsayinta a zuciyarsa. Can da ya hanga sai ya ga ashe Salama ƙawarta ta ɗagawa hannun, huci ya busar mai zafi daga bakinsa ya ɗan kwantar da kujerar tare da mayar da bayansa ya kwanta ya rufe idanunsa kawai ita yake hangowa lokacin da take yi wa ƙawarta bayani, yadda take bayani cike da damuwa shi ne abin da ya fi tsaya masa a rai.
Idanun ya runtse da ƙarfi a fili ya furta
"Jiddaaaa" Yana mai jan harafin ƙarshe na sunan nata, ya jima a haka har sai da aka fara kiran sallar magriba ya tashi tare da gyara kujerar ya mayar da ita daidai ya mayar da hannunsa kan mukullin motar ya kunna tare da fara ƙoƙarin janta duk da yana jin tamkar jijiyoyin jikinsa sun daina aiki, kamar dai ba zai iya jan motar ba, yana ƙoƙarin yin kwana, sai ya ga wani mai mashin da yake ɗauke da wani mutumi ya tsaya a take mutumin ya sauka yana sanya hannu a aljihu ya ciro kuɗi ya miƙawa mai mashin ɗin, yana bashi ya juya ya fara tafiya mai mashin ɗin yake miƙa masa canji amma sai ya ɗaga masa hannu alamar ya bar shi, haka ya shiga magana shi dai Ibrahim kasancewar ba a kusa yake ba bai ma san mai yake cewa ba sai dai ya san godiya yake masa.
Mai mashin ya ja mashin ɗinsa ya yi gaba, a inda Ibrahim ya bi bayan Abba da kallo har ya shige cikin gidan da ya ga Jidda ta shiga.
Sosai ya yaba da yanayin dattijon kuma daga