Showing 168001 words to 171000 words out of 178828 words
Chapter 57 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
faɗuwa jin za a ƙulla mata wani sharri wato ana ƙoƙarin watsa mata tsaba kaji su bita. Cike da tausasa murya ta ce
"Wallahi ban san da zaman hular nan a nan ba na rantse da Allahn da ya halicceni ba ni na ɗakko ta ba"
Nasir da ya gaji da abubuwan nan ga shi ya ga sirikar tasa ma kamar ƙoƙarin ƙara kunna wutar bala,in take sai ya ji duk ransa ya ɓaci hakan ya sa ya ji haushin Sadiya domin dai hakan yana tabbatar masa da cewa abubuwan da ake zargi a kanta haka suke tun da ga shi an ga hular Meenal a ɗakinta kuma tana rainawa mutane hankali a fusace ya ce
"Hular ce ta zo da ƙafarta" Kallonsa ta yi idanunta taf da hawaye ta ce
"Wallahi Abban Kalifa ba ji ba ce"
Momi ta ce
"Sadiya ya kamata ki daina yi wa mutane wasa da hankali kawai ki fito fili ki faɗi gaskiya dama an san gaskiya ciwo ne da ita, don haka kawai ki faɗa kanki tsaye ni kuma na miki alƙawarjn za a rufa miki asiri matuƙar kika amsa laifinki"
Sadiya kallonta ta mayar kan Momi ta ce
"Wallahi duka abubuwan da ake zargina ban aikata ba hasali ma na je ɗakin Meenal don na taimaka mata amma shi ne take mini bita da ƙulli dukan kabarin kishiya"
Meenal ta ce
"Allah sarki ni, wato Sadiya saboda kin ga mu biyu ne a gidan nan babu na uku wanda zai yi shaida shi ne kike faɗar son ranki"
Sadiya ta ce
"Ni Allah ne shaidata kuma tun da nake ban taɓa zuwa wajen boka ko malam ba, bare na faɗa masa buƙatata ni Allah na dogara, kuma shi ne shaidata cewa ban ɗauko hulamdon na yi magani ba kuma ban ɗauki filo na je don na rabata da numfashinta ba"
Momi ganin ramin da ta yi wa zSadiya don ta rufta ba ta rufta ba sai ranta ya yi mugun ɓaci ta ce
"Mu da wa muka ce miki muka dogara? Mu ma Allahn dai ne abin dogaranmu" Meenal ta durƙusa za ta ɗauki hularta sai Nasir ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu ya ce
"Meenal karki kuskura ki taɓa hular nan"
Sadiya ta kalli yadda fuskarsa ta sauya lokaci guda ɓacin rai ya baibaye fuskarsa.
Meenal ɗagowa ta yi da mamaki tana kallonsa kowa ma shi yake kallo hatta Momi sai da ta ji shayin yanayinsa ta ce
"Kai Nasir lafiya kuwa, ya haka yarinya da hularta kuma ka hana ta ɗauka?" ,Sadiya kuwa har fuslarta ta jiƙe da hawaye ta san shikenan hukuncin kanta zai sauke tabbas ita dai tana ganin jalala a gidan aurenta sai dai ta san duk wanda ya jura wahala ko ƙalubale a rayuwa to tabbas watarana nasara za ta zo, watarana zai taka tudun tsira, saboda hausawa ma suna cewa mai haƙuri yakan dafa dutse, duk wanda ya yi haƙuri zai samu sakamako duk daren daɗewa.
Nasir ya fara magama cike da ƙaraji tamkar ba da Momi yake magana ba ya ce
"Momi ana batun kisan kai ne fa wannan abubuwan da muke yi gabaɗayanmu ba aikinmu ba ne"
Momi a tsorace da lamarin ta c
"To aikin su waye"
Ya ce
"Aikin hukuma ne mana, hukuma ce ya kamata ta yi bincike don tabbatar da gaskiya, wannan lamarin dole sai hukuma ta shiga" Ya faɗa yana saka hannu a aljihu ya fito da waya, Momi dakyar ta haɗiye tsoron da ta dirar mata ta ce
"Kai haba dai Nasir wace hukuma ana zaune lafiya, ai abu ne na gida, da Sadiya da Meenal ai duk ƴan uwana ne ba kishiyoyi ba ai an zama ɗaya, in zama ya haɗa da aure da haihuwa ai sai an ruguma haƙuri da dangana"
Meenal ta karɓe da faɗin
"Ai dama abin bai kai nan ba" Suka faɗa kowa yana tsoron furucin da Nasir ɗin zai yi game da maganar da suka yi, domin sun san muddin ya sako hukuma su ne a ciki, domin daga an cika bincike su za su kwana a ciki shi ya sa suke ƙoƙarin naɗe tabarɓar kunya da hauka. Sadiiya ta ce
"Ni wallahi na amince a kira hukumar saboda in har za a yi bincike za a gani gaskiya"
Safiyya ta ce
"Ke Sadiya ya ana so a kashe wuta kina rurata, shi fa bincike ba shi da wata rana ko da a addini"
Sadiya ta ce
"Addini ma ba irin wannan binciken ya hana ba, amma ni dai in har za a cire zargin da ake min to na yarda a saka hukuma"
Nasir ya ce
"In dai hukuma ce an saka ta ma an gama don ni ba zan iya wannan abin ba, ina zamana lafiya a zo ake jaza mini gwara...
Momi ta ce
"Nasir ni ai tamkar mahaifiyarka nake, kuma Sadiya ai yarinya ce magana ta ya dace ka bi kawai a kashe maganar a gida ba sai an fitar ba wani ma ya ji, kawai Sadiya ta karɓi kuskurenta"
Sadiya ta ce
"Wallahi ni dai ba zan taɓa karɓar aikin da ba ni na aikata ba, kawai a saka hukumar don ba na so a zo a ɓata mini suna ana cewa na yi yumƙurin kashe kishiyata saboda kishi ko kuma na ɗauki hularta zan mata asiri in raba ta da miji amma in hukuma ce in har jna da gaskiya za ta wanke ni"
Momi a zuciyarta ta c
"Wannan ƴa ƴar bala,i ce, neman since mini zani a kasuwa take dole na samu mafita tyn kafin ranar jin kunya ta bayyana'
A fili ta ce
"Lallai Sadiya dama haka kike da kafiya da taurin kai? To mu ba damu ba ni ba tsohuwar banza ba ce ba zan je ina yawon bin hukuma ba duk su ƙwace mini kuɗi a karshe babu biyan buƙata"
Sadiya ta ce
"Ai ba kowace hukuma ba ce take karɓar kuɗi akwai wanda gaskiya kawai za su fitar"
Meenal ganin Nasir yana bin Momi da kallon kamar bai yarda da ita ba da take maganar rashin kai wajen hukuma da sauri Meenal ɗin ta ce
"Wai mene ne ake ta jayayya to a je wajen hukumar ma wane shegen yake tsoron ra mutu bare ta yi rai," Ta faɗa tana kallon Momi da ta mata alama da ido a kan ta ɗauke hularta ta ƙara sunkuyawa Nasir ya hana ta ɗauka a karo na biyu sai Momi ta sunkuya da kanta za ta ɗauka da sauri Nasir ya hana ta ɗauka yana faɗin
"Ai babu wanda zai taɓa hular nan sai hukuma sun zo"
Momi da sauri ta ce
"To uban mai zai haɗa hukuma da hula?"
"Nasir ya ce na gaji da wannan jayayyar da ake yi gwara a je wajen hukuma kawai ta nan ne za a tabbatar da gaskiya, kuma wannan hular babu mai taɓawa, hukuma ne kaɗai za su yi aikin su, za su tabbatar da mai laifi za a su gane idan har Sadiya ce ta kawo hular za su gane idan kuma Meenal ɗin ce ta shigo ɗakin da kanta ta jefar da hular shi ma za su gano" Gaban Meenal ne ya bada saurin rasss aka fara kallon kallo a tsakaninsu
Nasir ya ci gaba da magana babu alaɓun wasa ko sasaauci ya ce
"Za a ita ganowa ta hanyar fingerprint (Yatsun hannu) Idan Meenal ce ta taɓa hular za a gano idan kuma hannun Sadiya ne a jiki shi ma duk za a gano, kenan ta hanyar gano hannun jikin hular ne za a bambance tun da yanzu filon da aka yi amfani duk yataunmu suna jiki"
Momi ta ce
"Ikon Allah"
Ya ci gaba da faɗin
" Za a iya gano cewa Meenal ce ta ajiye hular a ɗakin Sadiya ta hanyoyi biyu da suka shafi DNA da binciken yatsun hannu (fingerprint)
Fingerprint Analysi idan Meenal ta taɓahular da hannunta kai tsaye, za a iya samu yatsun hannunta a jikin hular
masu bincike za su ɗauki hular, su fitar da fingerprints da ke jiki, su kwatanta da na Meenal. idan yatsunta sun bayyana, to shikenan hujja ce kai tsaye cewa ta taɓa ko ta bar hular a can.
DNA Analysis idan akwai gashin kanta a cikin hular (ko 'yan ƙwayoyin fata), za a iya fitar da DNA
Sannan a gwada da nata idan ya dace, to lallai ita ce ta bar hular wannan hanya ce mafi ƙarfi wajen tabbatar da asalin mai abu musamman idan babu fingerprints., Idan kuɓa Sadiya ce ta taɓa ma duk za a gano" Su duka sun tsorata da furucinsa sai dai Momi da ta san duniya ta lalace ana iya siyan komai da kuɗi wato tana iya sayen gaskiya da kuɗi ma amma kuma furucin da ya yi yanzu ya tarwatsa ƴaƴan hanjin su dukansu.
Yana tabbatarwa da faɗin
"Ba zan ba kaina wahala a kan wannan ba sai da sharaɗi wallahi wallahi kowacece aka gano ita ce da laifi sai na yanke duka igiyoyon aurena a kanta, ina nufin idan har aka yi bincike duk wacce ita ce da laifin sai na sawwaqe mata aurena, zan raba alaƙar aurena da ita saki ɗai-ɗai ha uku!"
Gaban Sadiya ya fi na kowa bugawa duk ta san tana da gaskiya, amma yanzu gaskiya ta yi ƙaranci a duniyar nan ,don tana tunanin idan har aka tauye mata haƙƙi tabbas ita ce za ta samu takardar sakin ina za ta je da wannan tsohon cikin bare ta san halin Baba.
BABA
Tun yana jiran taimakon mutanen unguwa har ya cire rai kasancewar babu wamda ya ɗakko ko naira biyar bare a ɗakko ko da ƙwayar hatsi ko shinkafa a bashi haka ya sha baƙaƙen maganganun a kan cewa duniya ta lalace yanzu mutane ba sa taimakawa, bai san cewa kowa ya san abubuwan da yake yi wa iyalinsa ba na tauyewa domin yanzu an daina kiwon dabba an koma kiwon mutum. Haka ya ci gaba da fafutukarsa ta zuwa kasuwa dama kuma yana da kuɗi kawai dai rashin wadatar zuci ne sai dai kuma tun da wannn gobara ta faru sai lamuram gidan suka sake caɓewa ba ya bada ko kwabo iyakarsa idan an tambaye shi abinci sai ya cw shi da tsautsayin gobara ya faɗawa ina ya ganshi, sai dai su bari har wata damuna ta zo idan ya yi shuka ya samu sannan zai ci gaba da basu abinci ko da kuwa iya na dare ne.
Yanzu kowa ya zage dantse yana nema da masu sana,a da kuma masu bada kansu a basu kuɗi shi dai burinsa ya aurar da su ya huta, duk da yanzu ya mayar da hankali ne ga nasa sabin auren da yake son ya yi, don ya ɗora rai a kan sai ya auri namiji. Babu wanda ya san Baba yana neman aure wata yarinya ce ya samu budurwa mai rawar kai kuma idanunta a buɗe suke tas. Tun da ya ƙyalla idanu ya ga yarinyar ya ɗora rai a kanta ba komai ya fi tafiya da shi ba irin farar fatarta da ta sha mayukan bilicin sannan uwa uba kaf gidansu maza ne ita kaɗai ce mace, wannan ya sa yake ganin zai samu irin haihiwa tun da an ce ana gadon haihuwa, sannan ko mahaifiyar yarinyar ma su biyu ne mata a gidansu ƴan uwan mahaifiyar tata maza har goma, sannan ita ƴar uwar mahaifiyar tata ma kaf ƴaƴanta maza ne ba ta taɓa haihuwar mace ba wannan ya sa Baba ganin kakarsa ta yanke saƙa.
Duk wani burin Baba yana kan Badariyya wacce ta gama gano lagon Baba na son haihuwar namiji sannan ta gane tsantsar jahilcinsa da rashin godiyar Allah na ƴaƴa matan da ya bashi. Gabaɗaya sai take masa wayo da kuma kawo masa buƙatu shikenan duk da son kuɗin Baba amma haka yake kashe mata kuɗi musamman da yake ganin samari suna zuwa wajenta don ya ɗauke mata hankali daga kansu. Bai san cewa su samarin nata ƴan rage dare ba ne babu wani na aure sai an ce su fito sai a neme su a rasa yanzu shi kaɗai ne wanda take jalabtawa don shi ne na auren. Hatta wayar hannunta Baba ne ya saya shi ya gwammace ko nawa ne ya kashe tun da dai zai samu cikar burinsa na haihuwar ɗa namiji tun da yana ganin zai auri tsatson haihuwar maza.
Jarabawarsa a kan Badariyya shi ne soyayya gabaɗya sai ya ji yana ƙaunarta kamar ma a kanta ne ya ƙara tabbatar da mene ne so duk da kasancearta yarinya. Sai ya zamana tana juya shi kamar waina a tanda saboda soyayyar da yake mata hidima tamkar dai ba Malam Bala mai mammaƙo da son abin duniya ba. Babi wanda ya san wainar da Baba yake toyawa sai da ya zamana biki saura sati biyu sannan ya tara matan nasa ya sanar da su babu wacce ta yi wani baƙinciki kowa ta ce masa Allah kawo amarya lafiya, domin dama tun da suka ga ana gini sun san a rina wai an saci zanen mahaukaciya. Ƴaƴan gidan kuwa ya tara su yana gindaya musu sharuɗɗa kasancewar Badariyya ta gama faɗa masa abubuwan da take so da wanda ba ta so, haka yake ta kumfar baki ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.
Ranar ɗaurin aure ya sha farar shaddarsa sai sheƙi take tana baza ƙamshin turarensa, Allah ne kaɗai ya san iya farincikin da yake ciki domin yana ganin kukansa ya ƙare nan da watanni tara cif yana da ɗa namiji mallakinsa. Sadiya ko da ta ji labarin auren Baban haushi da takaici ya baibaye ra son ta san saboda haihuwar namiji ya yi auren,, ita dai da farko ma ta ji haushin sakon Mama Habiba da ya yi amma yanzu daɗi take ji don ta san Mama Habiba albarkacin haƙurin da ta yi a gidansu to tabbas Allah zai musanya mata da mafi alkairi tun da ba wani wuce aure da haihuwa ta yi ba.
Ɗakin amarya ya sha jere da dare aka kawo amarya, ko da ƴan kawo amarya suka watse Baba ya je ya bankawa gidan sakata, ya shiga ɗakin amarya ya banke ƙofa ya shiga bedroom yana washe haƙora, amarya tana ɗan jin kunya haka ya ce su yi alwala su yi sallah, bayan sun yi sallar nafila Baba ya hau cire Babbar riga ya rataye, ya kalli amarya ya ce
"To amarya Bismillah" Ta masa kallon sheƙeƙe har sai da ya sha ruwan jikinsa ta ce
"Ban gane Bismillah ba, banga kayan maƙulashe ba" Ya ɗan yi jim yana kallonta ya ce
"Wane kaya kenan?"
Ta ce
"Ina kazar amarci sa sauran kayan sanyi?" Ya dafe kai ya ce
"Kash!. Ai kwata kwata na sha,afa wallahi garin saurin in zo wajenki na manta ana kawowa amarya wani kayan maƙulashe kuma laifin su malam Lurwanu ne da ba su tuna min ba" Tsaye ta miƙe tana cewa
"Ni Badariyya aka manta kazar amarcina sai ka ce wata amaryar kyankyaso"
Baba ya ce
"Haba an Badry nah ai kaji a gidan nan sai kin ture, ki yi haƙuri mantuwa ce kuma kowa ma yana yin mantuwa yanzu dai ki mini afuwa zuwa safiya sai in rama miki" Wani kallo ta masa ta ce
"Bari ka ji Bala" Da sauri ya kalle ta ganin yau babu ɗan sunan soyayyar ma ta faɗi sunansa gatse-gatse cike sa rashin ta ido yarinyar da ya haife ta ta ci gaba da faɗin
"Ni Badariyya ƴar Mama ban san babu ba koɓai da nake so ake min ko ka manta ƙanwar maza ce ni, kowa ji yake da ni saboda ni kaɗai cw macw in za ka buɗe bakin aljihu ka buɗe" Wani yawu ya haɗiye yana fatan dai kar wannan yarinya da niyyar talauta shi ta zo ga shi kuma sonta yana ɗawainiya da shi. Haka ya lallaɓa ta ya saka babbar rigar ya fita ya buɗe gidan ya fice duk mutanen gidan suna jin fitarsa. Haka ya je wajwn mai kaji aka faɗa masa kuɗaɗensu, kamar ya yi kuka haka ya duba wata ta dubu biyar kamar tattabara saboda ƴar ƙarama ce, haka aka sako masa a leda ya ratsa ta siyo mata lemon roba guda ɗaya ya tafi.
Sai da suka zauna tana ƴar dariya ganin an kawo mata kaza ƙawayenta in sun zo gobe ai babu raini ana fito da kaza sai ta ga lemo ɗaya tana mamaki ta ce
"Babban yaro ya na ga haka kuma lemo ɗaya kamar ka roƙo ko dai alakoro aka saka maka?" Ya kalle ta yana washe baki don Allah kaɗai ya san daɗin da yake ji in ta ce masa Babban yaron nan sai ya ji ya koma yaro ɗanye sharaf yake jin kansa ɗaya da samari.
Yana kallon ta ya ce
"Ai da yake ni ba sha zan yi ba cikin ki dai ke kaɗai ya ishe ki"
Ta ce
"A,a wannan ai sai a ce mini marowaciya baka san ƙawaye suna zuwa su ga ƙwaƙwaf washe garin kawo amarya ba, so kake ake cewa da saurayi na aura da sai na ture lemuka kuɓa bayan na san an ce ku manyan kun fi ba macw kulawa da nuna soyayya da bautata mata" Murmushin ƙarfin hali ya yi ya ce
"In dai lemo ne da safe zan siyo miki kafin su zo" Amincewa ta yi sai da ya buɗe ledar kaza ta ga ƙaramar kaza wani salati da ta kwasa sai da ya ji tamkar mutuwa aka sanar mata, yana kallonta ya ce
"Lafiya?"
Ta ce
"Wannan ƴar tsakuwar kazar fa? Haba Babban yaro kamar wanda dai baka sona ka da za ka samo ƙosasshiya" Ta karɓa tana murɗe cinyar kazar duka biyu ta cire su tana ɗagawa tana nuna masa, ta ce wallaho sai ya canjo kazar in ba haka ba ita a gado za ta kwana shi a ta saka masa katifa a ƙasa tun da bai kawo kazar amarci ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya shiga lallaɓa ta don ba zai yarsa ranar yau ta wuce bai yi sunna ba saboda yau ma tana cikin lissafinsa don ya fara sakawa a ransa ma a yau za a aamu ƙaruwa.
Haka ya buɗe ƙofa ya fito da ledar