Showing 171001 words to 174000 words out of 178828 words

Chapter 58 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt

18 Dec 2025

1466

kazar yana jin takaici ya rasa ma mai ya sa ita ko ɗan kawaicin nan ma na amare ba ta da shi, haka ya fito yana jin haushi, lokacin Mama Bilki ta fito daga banɗaki riƙe da buta ta ce

"Malam, Malam, Malam" Sainda ta kira shi sau uku sannan ya juyo, yana amsawa kamar an masa dole ta ce

"Lafiya kake ta zaryar fita daga gida ko siyan bakin ne bai kammalu ba" Ya kalle ta yana jin kamar ya wanka mata mari ya huce takaicin amaryar a kanta ya ce

"A,a siyan ƙafa ne bai ƙare ba, ba na baki ba, na ce siyan kai da ƙafa ake" Ta yanayin furucinsa ta gane a ƙufule yake ta ce

"Ba ni na kai zomon ba rataya aka bani" Wani tsaki ya ja yana juyawa ta sake cewa
."Ango ka taho min da maganin gudawa ka ganni tun daɗewa nake zarya banɗaki kamar angon da amarya take aike" Banza ya mata ya juya ya tafi tana jin lokacin da ya banko ƙofar gidan ta sheƙe da dariya a zuciyarta tana faɗin

'Kaɗan ma ka gani" Don ta fahimci akwai wani abun da yake faruwa duk da ba ta san mene ne ba, amma in tusa tana hura wuta za a gani.

Haka ya sake daɓawa a ƙafa domin dama a ƙafa ya je ɗazu saboda mammaƙon kuɗinsa ba zai hau mashin ba, ga shi kuma da ɗan tazara, ko da ya je mai kaza ya ce wallahi ba zai karɓi kazar da aka jawalwala ba tun da ya ga gabaɗaya ma cinyoyinta da ban suke ba sa jikinta. Kamar zai yi kuka haka ya cire naira dubu sha ɗaya ya siya kazar aka haɗa masa da waccan ya kamo hanya har ƙwallar takaici ya share.

Haka amarya ta zage ta ci kaza don ƙaramar nan sai da ta cinye tas, iyaka ta ciro ƴar ƙaramar tsoka ta saka masa a baki ya lamushe saboda ta hana shi ya saka hannunsa wai ba girmansa ba ne tana waje yake ciyar da kansa. Ita kuma sai ta yago ƙatuwar tsoka ta cika bakinta ta kalle shi ta ce

"An ce amarya in ba ta ci kaza ba ma dole a sha manta" Bai tanka mata ba illa dariyar yaƙe da yake. Haka ta ɗaure sairan wai ta ƙwayaenta ce idan sun zo gobe sai su haɗa da lemukan da zai kawo.

Haka Baba ya sha amarcinsa, yana fatan an samu ƙaruwa a ranar. Tun daga ranar yake lallaɓa amarya. Hankalinsa kwacakwam ya koma kan amarya dama shi bai damu da zuwa wajen mahaifiyarsa ba sai ya daɗe bai je ya ganta ba bai san cewa gabaɗaya albarkar rayuwarsa tana dangane da farincikin da ya saka mahaifiyarsa ba

Ranar da amarya ta cika kwana goma sha biyar a ranar ne bayan ta gama cin abinci ta fito tsakar gidan tana kelaya amai, lokacjn Baba shigowarsa kenam ya hange ta, da gudu ya yi wajenta yana zuwa ya faɗi ƙasa daga can gefenta ya yi sujada yana yi wa Allah godiya.Sai da ta gama ya bata ruwa ta wanke baki ya ce

"Sannu uwar maza, Allah raba lafiya kin gama min komai da za ki haifa min namiji" Langwaɓewa ta yi sai shi ya kama ta yana jera mata sannu. Washe gari da zai dawo daga kasuwa sai ga shi ya siyo rigunan jarirai maza guda biyar wai taro za a fara.
Amarya sai tsiyarta take tsulawa a gidan don dama tun da ta zo ba ta yi girki ba sai dai ta zaɓi abin da take so ya siyo mata. Ranar da ta cika kwana uku da yin aman tana kwance a saman doguwar kujera tana danna waya ya shigo ya ce

"Badary nah, tashi mu je za ki rakani" Haka ta yafo mayafi suka fito tare ya kulle ƙofar ɗakin nata yana faɗin da a ce yana da iko da ya hana ta ko da tafiya ce ahi zai ke yi mata tafiyar.

Napep ɗin da ya kira suka tarar yana jiransu suka shiga baya ya ja suka fara tafiya kanta ta kwantar a kafaɗarsa ta ce

"Wajen shaƙatawa za ka kaini Babban yaro?" Mai napep da sauri ya juyo jin furucinta ya kallesu shi ya ɗauka ƴarsa ce sai ya ji banbarakwai wai namiji da suna hajara ana kiransa da babban yaro.

Baba ya kalli mai adaidaita sahu ya ce

"Sanan,a ka fito ko kallon matan mutane?" Bai tankawa Baban ba ya ƙyale sai Baban ya ce

"Haba Badary nah ina na samu sukunin zuwa wajen shaƙadawa ni fa hankalina yana kan ki nan da abin da za ki haifa ai daga yanzu har zuwa lokacin haihiwarki ban ga ta zama ba an saci ɗan ɓarawo"

A ƙofar wajen scanning aka ajiye su, Baban ya ce
"Mu shiga"
Ta kalle shi za ta yi magana ya ja hannunta suka shiga sai da layi ya zo kansu Baban ya ce scanning za a mata a gano masa mai za ta haifa, ko da aka tambaya cikin watansa nawa sai Baba ya ce ai ba a yi sati uku ma da auren ba. Nana aka sanar da shi ba yanzu za a gane cewa ga abin da yake cikin ba saboda abin da yake cikin bai gama zama halitta ba har yanzu yana gidan jini.

Ko da aka faɗi haka Baba ya ce su tafi suna hanya yana ta mita yana faɗin ai dama ya san mai za a haifa namiji sai dai yana son a gani biyu ne ko ɗaya ne.

Amarya ta tsiro da rashin mutuncin cewa sai Baba ya aurar da duka ƴaƴansa tun da dai duka mata ne wai kakarta ta taɓa cewa idan mace mai ciki tana kallon abu to abun yana washe ta, wato tun da su mata ne za su washe ta ta haifi ƴa mace. Tun da Baba ya ji wannan batu hankalinsa ya tashi saboda shi kansa ya san ana cewa mace mai ciki ana wasar ta, amma dai bai san cewa gaske ba me ko kuma camfi ne, don haka maganin kar a yi kar a fara.

Haka ya tara gabaɗaya ƴaƴan masa ya ce su fito da miji ya basu sati guda. Kowacce jikinta ya yi sanyi dimin sun san ba su da wani tsayayye babu wani wanda za ka fitar ya aure ka tun da dama ba don aure suke son su ba kawai ana sheƙe aya ne.

Ko da sati ya cika babu wacce ta fito da miji kowacce sai ta ce saurayin bai shirya ba ita kuma amarya abu ya ci tura don har ƙin fitowa tsakar gidan take, kuma ba komai ya sa ta musu haka ba sai Arfat da ta ga tana mata wani kallon raini gabaɗaya ma ƴanmatan gidan suna mata gani-gani. Shi ya sa take so ta nuna musu ta isa da ubansu.
Yau ta kama alhamis Baba ya shigo da dare ya tattara su cike da masifa ya ce

"Na gaji da zamanku a gidan nan na ce ku fitar da miji kun ƙi kun zauna za ku washi Badary ta haifi mace, kun fi so na ƙare a wahale babu mai taimaka mini amma in ta haifa mini namiji ai shikenan na huta, tun ina siyan maganin farin jinin har na gaji saboda kamar ma baƙin jini nake ƙara muku, ku ba muni ba amma a ce gabaɗayanku babi wacce take da mijin aure yau na yanke hukunci kowacce ni zan zaɓa mata miji ba za ku rufa sati a gidan nan ba sai dai a gidan mazajenku"

Yana gama faɗar hakan fuuu ya yi hanyar waje. Washe gari da asuba aka ji sanarwa a masallaci cewa Malam Bala ya ce tun daga kan liman har ladan da sauran dattijan unguwa mai son ƴaƴansa da aure zai aura masa!.

Matan gidan sun yi takaicin wannan hukunci da Baba ya yanke sai ka ce mai neman kai da ƴaƴan. Babu wanda ya tanka masa don sun san babu wanda zai zo ya ce zai aure su. Amarya sai dariyar ƙeta take tana yada magana a tsakar gida wai gwara dai kowacce ta san na yi kar a saka ta haifi mace.

Da yamma sai ga shi ya zo ya tara su ya ce

"Kowacce ta samu wanda zai aure ta wallahi har raina ya yi fari sai na ji gabaɗaya zuciyata kamar an sauke mini dutse zan aurar da ku in huta da wahala" Ya faɗa tare da fara lissafo sunayen mutanen da suka sani a unguwar wanda manya ne ciki kuwa har d liman ko da ya zo kan Arfat ya ce

"Arfat ke Ayodele nw ya ce zai aure ki" Cike da mamaki kowa na gidan ya fito wanda suke ɗaki su kuma ƴanmatan sai suka fara kallon kallo, amarya kuma tana ƙofar ɗakinta ta kama tsantsa tana sakin murmushin ƙeta.

Arfat idanunta taf da hawaye ta ce

"Baba Ayodele fa ka ce wane Ayodelen?"

Cike sa masifa ya ce

"Ayodele nawa kika sani a unguwar nan? To Ayodele shugaban coci"
Mama Sa,ade ta ce

"Wallahi babu wanda ya isa ya aurawa ƴata arne" Baba cike da nuna isa ya ce

"Duk duniya babu wanda ya isa ya hanani aura masa tun da ƴata ce tun da ai ba a ce in ta aure shi ta koma kafirci ba kuma shi ma ya ce babu ruwansa da addininta kowa ya yi addininsa kin ga kuwa babu gudu babu ja da baya, tun da kaf unguwar nan babu wanda ya zaɓe ta sai shi kuma ba zan aurar da sauran ƴan uwanta ba ita ta zauna mini a gida domin haka babu gudu babu ja da baya!"



MAMY

Rai a matuƙar ɓace ta ce

"Dakata Zalika!. Kar ki raina min hankali mana, kenhar kin isa ki yinwasa da hankalina Zalika? Ita ƙawar taki ta rasa inda za ta yi ajiya sai a jakar ki, ta rasa mai za ta ajiye a jakar ki sai ƙwayoyin hana ɗaukan ciki?"
Zalika ganin Mamy ta rikice mata tana son janyo mata ruwa sai ta marairaice ta ce

"Wallahi Mamy ki yarda da ni ba ƙarya na miki ba, ko kaɗan ba da wata manufa ta ajiye ba, yanzu Mamy ni kika zargi da shan wannan maganin ko kuwa?"

Mamy a harzuƙe ta ce

"Dole ne na zarge ki Zakika saboda kin yi abin da za a zarge kin, shin idan babu rami mai ya kawo rami? Tun yaushe kika sauya Zalika mai zai sa na ƙi zarginki ai wannan ba ma zargi ba ne na tabbatar"

Kuka Zalika ta fashe da shi ta ce

"Mamy ko da wani zai zargeni na ɗauka ke ce za ki shaideni, kuma wannan abu ne da baki da tabbaci a kansa, kuma ko a musulunce zargin zina fa lamari ne baba kuma mai girma da yake buƙatar tabbatarwa, saboda ita zina ko za a zargi mutum sai an tabbatar sai an ga mutum turmi da taɓarya sannan sai an tara shaidu mutum ɗaya ba ya wadatar da ganin mazinaci...

Hannu Mamy ta ɗaga mata alamar dakatarwa, domin a furucin Zalika duk inda ta ambaci kalmar zina ran Mamy zafi yake sannan sai gabanta ya faɗi, ita a rayuwa babu kalmar da take jin nauyin furtawa a harshenta sama da kalmar zina, ta tsani kunnuwanta su saurari kalmar saboda nauyinta da kuma ƙazantarta don zina abun ƙyama ce, mai yinta abun ƙyama ne kuma abin a nisanci mu,amala da shi ne saboda zina Allah cewa ya yi ko kusantarta kar a yi bare a aikata ta.

Mamy ta ce.

"Zalika ni na haifeki ina so ki sani duk wani lafazi naki a tafin hannuna yake, na fi ƙarfin ki rufe ni da murfin ƙarya da yaudara, ina so ki faɗa mini tsawin wane lokaci kika ɗauka kina wannan mummunar ɗabi,ar?"

Zalika ta ɗaga idanu ta kalli Mamy ido cikin ido ta ce

"Mamy ki yarda da ni ban taɓa aikatawa ba idan kuma har kina kokwanton maganar ni zan kira wacce ta saka maganin ta zo har gida ta miki bayani" Ta faɗa tana kuka wiwi

Nannauyar ajiyar zuciya Mamy ta sauke tana jin wani zafi a zuciyarta ta ce

"Ba na buƙatarta duk bakinku ɗaya, kafin ta zo kun gama tsara yadda za ku faɗa mini ƙaryar da kuka shirya, za ki faɗa mini gaskiyar yaushe ne kika kai matsayin da har kika fara amdaninda ƙwayar hana ɗaukan ciki, ɗabi,ar da take lalata tarbiya ɗabi,ar da take lalata suna kina mace amma za ki lalata rayuwarki ki cuci kanki ki cucemu sannan ki bar wa ƴaƴanki baƙin fentin da har jikokinki sai abin ya shafa"

Baki Zalika ta buɗe za ta ci gaba da faɗin maganar da take alamta musu da zargin Mamy hakan ya sa zuciya ta ɗauki Mamy ta wanke fuskarta da ƙwararan maruka har biyu. Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Mamy da Zalika, Mamy tana hakin baƙinciki kamar wacce ta yi tseren gudu yayin da Zalika take dafe da kumatun ta.

Mamy ta ci gaba da faɗin
"Abin da kika yi irin na iyaye masu sakaci da tarbiyar ƴaƴansu ne duk da a lokuta da dama idan ƙaddara ta zo gifta maka babu yadda ka iya wajen kauce mata, amma na yi iya ƙoƙarina don baki tarbiya sannan ina komai naki kafin komai ya sauya"

Zalika ta ci gaba da kuka wiwi tana son yin wasa da hankalin Mamy, kallon ta Mamy ta yi tana rayawa a ranta cewa sai ta nunawa Zalika akwai bambanci tsakanin tunanin yaro da na babba.

Taku ɗaya biyu Mamy ta yi hannuqanra biyu suna goye a bayanta ta tsaya tarw da ɗaga kanta sama tana kallon silin hawaye suka wanke fuskarta masu matuƙar zafi, a hankali ta sauke kanta daga kallon saman silin ɗin ta juyo tana kallon Zalika da ita ma tuni nata idanun sun rine da saboda kukan da take yi don wasa da hankalin Mamy.

Ƙure ta da ido Mamy ta yi kamar mai tuna wani abu sai kuma ta fara magana cike da kaushin murya ta ce

"Zalika tun da har kin ƙi faɗa mini gaskiya kina wasa da hankalina zan yi abin da zai cire zargi da kokwanto a tsakanina da ke game da wannan maganar " Zalika ta ci gaba da yi wa Mamy kallon tsoro don ba ta san abin da za ta faɗa ba.

Mamy ta ce

"Zan duba ki Zalika, idan har kin taɓa sanin ɗa namiji ma daga na duba zan gane domin akwai bambanci da tazara mai tarin yawa tsakanin macen da ta taɓa sanin namiji da kuma wacce budurwa ce dal a led"
Zalika ta yi matuƙar razana da kalaman Mamy domin ta san an zo wajen da wayo da dabarar ta ba za su yi amfanin komai ba, matuƙar Mamy ta duba matantakar ta za ta san ta mu,amalanci namiji sai dai ta fara tunanin wace hanya za ta bi domin kaucewa wannan ƙudurin na Mamy shin Mamyn za ta yarda da wani wasa da hankalin kuwa anya?.




JIDDA


Zaman lafiya mai wanzar da nutsuwa suke yi tsakaninsu kasancewar ba ta mugun nufi ga kowa a rayuwa ahi ya sa ba ta taɓa kawowa cewa wani ɗan adam zai nufi rayuwarta da sharri, ɗan adam ɗinma wanda suka kasance na kisa da zuciyarta wato Aliya da kuma wacce take ganin ita ce ta maye mata gurbin uwa wanda ta rasa!. Sai dai kash rashin sani ya fi dare dunu domin zaton da take ba haka ba ne, saboda ta bar kashi ranar kwasa!.
Tun ran gini rana zane duk abin da bawa ya ƙaddara masa to sai ya faru da shi daɗi ko akasin haka, kyakkawa ko mummuna, wannan kaɗai ta saka a ranta take rayuwa hankali kwance ba tare da ta yi tunanin ta bar wani giɓi ba wanda ya kamata ta cike shi. Soyayya da ƙauna haɗe da kukawa da ba su da iyaka ko kuma hanyar misaltawa su ne abubuwan da ta yi amanna tana samun su daga Ibrahim sai dai ita ma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba tana ba shi kulawa daidai gwargwado domin matsayjnta na matarsa iya ma abubuwa da dama da ya shafe sa aun rataya a wiyanta.

Daga Umma har Aliya babu wansa ya saduda ko kuma yin da na sani ko kuma zuciyarsu ta rusuna game da mugun ƙudurinsu a kan Jidda wacce ba ta taka ko ta zubar musu ba. Suna nan suna ta shiri a kan yadda za su samu kuɗin da za su tafi ga mataki na gaba domin sun ci alwashin sai sun cika mugun burinsu banu gudu babu ja da baya. Sun yi ta buga buga inda za su samu kuɗi abin ya fassakara hakan ya sa suka yi dogon nazarin ganin inda ya dace au sosa, saboda Umma ta ce kar su tamabayi Jidda ba lallai ne ta basu kuɗi ba yun da ita tana ganin ba za ta iya ɗakko musu daloli a kuɗin mijin nata ba.


Umma ce zaune tare da Aliya su biyu a gidan sun haɗa kai suna shirya yadda za su samu kuɗi Umma ta ce

"Aliya sai kin yj taka tsantsan wajen yin abin da ya dace, kin dii ga yatinyar nan mai mugun hali matsawar za mu jira sai mun samu daga wajenta to tabbas za mu ci gaba da dawwama a talauci tun da ita sahegen sanabe ya sa ta je tana riƙon amana ni ban ga amfanin ta ba"


Aliya cike da sheƙiyanci ta ce

"To Umma ko a danganta ta da barzahu?" Ta faɗa.cike da ingilanci

Umma tana zare ido ta aika mata saƙon harara ta ce

"Baki da hankali Aloya, ai maƙiyi ka bar shi yake ganin ci gabanka, sai baƙinciki ya so halaka shi, bare mu ai tuggunmu na gaba a kan Jidda shi ne wulaƙanci daman ɗan hakin da ka raina.. "

Alia ta ce

"Watarana shi zai tsokane maka idanu"

Jinjina mata Umma ta yi suka ci gaba da tsara komai Aliya ta ce

"Umma ko dai set guda za a sato?" Umma ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login