Showing 72001 words to 75000 words out of 178828 words
Chapter 25 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
nake siyarwa kuma wallahi ba zan siyar ba amma zan ɗauki mataki bari na shiga gidan, ai duk wanda ya iya allonsa wankewa yake yi" Huzaifa ta shiga zuga ta tana ta jin kanta dole ta yi wani abu duba da yadda shi ma Nasir ta ga yana yi wa Sadiya wani kallo tamkar bai san da su ba a wajen.
Nasir tun da ya fito ya hangi sun kama hanya sun tafi, daga haka ya gane akwai gagarumar matsala, hakan ya sa ya fara sauri ya take musu baya, yana tunanin abin da ya musu don shi kansa ya sha'afa da yadda ya mu'amalanci Sadiya a gabansu. Yana binsu yana magaiyar su tsaya amma basu saurare shi ba suka ba banza ajiyarsa. Yana dab da ƙarasowa da yake sauri suke kamar su tashi sama, kawai sai gani ya yi sun tsare mai napep, sun shiga da ɗan gudunsa ya taho sai dai kafin ya zo mai napep ɗin ya tada sun tafi, ya san kuwa hakan ba ya rasa nasa ba cewa umarni su Meenal ɗin suka baiwa mai napep ɗin.
Tsaye ya yi a wajen yana riƙe da ƙugu ya rasa mai yake masa daɗi, ya jima a tsaye yana ta tunani don gano laifin da ya yi, sai daj a rai da rubinsa yana tunani da fatan Allah ya sa kar Meenal ɗin ta ce ta fasa aurensa. Da na sani ne ya lulluɓe shi da ya tuno ko dai don saboda abin da ya yi wa Sadiya ne Meenal ta ji haushi, a take ya ji wani haushin Sadiyar yana ta sakin tsaki a kai-a kai shi bai ma san dalilin da ya saka ya sakarwa Sadiyar fuska a gabansu ba sannan kuma ai ya rasa yaushe na Sadiya ta san cewa wai Meenal za ta zo tun da shi dai a iya saninsa bai faɗa mata ba. Ya fara tunanin ko dai wani makirci ne Sadiyar ta yi a ƙufule ya juya ya dawo, a wajen motarsa ya tsaya ya ɗakko wayarsa a aljihu ya shiga kiran Meenal har ta katse bata ɗauka ba hakan ya sa ya ƙara hawa tamfa, sake kiranta ya yi ta ɗaga yana jin yadda ta hayayyaƙo masa har sai da gabansa ya faɗi, a ransa yana raya anya wannan za a yi abin arziƙi da ita daman yana ganinta shiru -shiru ashe dai a she dai sai kuma wani sashe na zuciyarsa ya ce wataƙila ɓacin rai ne kawai ba wai halinta ba ne.
Haƙuri ya shiga bata sai dai da alama ta yi nisan da jin kira zai mata wuya, sai faɗin ya disga ta a gaban Sadiya take, har tana cewa dama ya kawo ta ne ya nuna mata iyakarta don ta ga Sadiyar ma har wani harararta take tana mata gwalo a fakaice bai gani ba. Haƙuri ya shiga bata yana faɗin zai ɗauki mataki kafin ya ƙarasa ta kashe wayar. Mota ya shiga ya bi bayansu zuwa gidansu, ko da ya je dakyar suka saurare shi ita da ƙawarta sai dai a ƙarshe ta nuna ita ba za ta zauna da kishiya ba sai dai ya zaɓa ko ita ko Sadiya!.
Nan ya shiga faɗa mata shi da a ce don ta shi ne da tuni ya daɗe da tsinke igiyar aurensa da Sadiya, don dai ita ce da ƙwawa sannan da a ce tana da zuciya da tuni abubuwan da yake mata ma ta nemi sakin auren ko da kuwa a kotu ne!. Ita dai ta nuna babu ruwanta yanzu zaɓi ya rage gare shi, tana gama faɗar hakan sula shige gidannsula barshi ita da Huzaifa. Ko da ya jima yana tunanin mafita a ƙarshe ya juya ya shiga mota ko gidan Hajiya bai je ba bare ya shawarce ta don ya san ƙarshen aleewa ƙasa ne, kuma dai ko ya shawarce ta ko dai ya ranke hukunci da kansa to tabbas ba wani abu za ta ce ba tun da ya san ita ma dai daga ita har ƴan uwansa ba ƙaunar Sadiya suke ba.
Sadiya tana haɗawa Kalifa kunu wanda ta dama masa take zuba madara don yanzu madara ma ƴar aune take siya kwata sai take musu amfani da ita, don sana'ar ta ta rufa mata asiri sosai, ana cikin hakan ta ji tsayuwar motarsa da yake ɗazu bai rufe ƙofar gidan ba shi ma yaron da ya fita bai rufe ba, don haka shigowarsa ta ji kamar an jefo shi. Sai da ya shigo ya tuna dole ya yi takatsan tsan don kar ta gane manufarsa. Fuskarsa ya gyara tare da saita yayinsa yana ƙirƙirar murmushin yaƙeyana shigowa ya zauna ya ce
"Sadiya manyan ƙasa ni kam ya aka yi kika san Meenal za ta zo ko in ce yaushe na faɗa miki da dare za su zo?" Ya faɗa a zahiri bai nuna komai ba amma a baɗini kamar ya wanke ta da mari don ta rusa masa komai, bata san cewa zaman alaƙaƙai yake da ita ba.
Ɗan murmusawa ta yi sai kuma cike da kissa irin ta mata ta ce
"Ayya Abban Kalifa dama na yj hakan ne don kar su ɗauka baka sanar da zuwansu ba, na yi haka ne don in wanke ka" Jim ya ɗan yi sai kuma ya ce
"Amma kin yi dogon tunani gaskiya irinku basu da yawa a cikin mata" Tana ba Kalifa kunun ta yi dariya ba tare da ta ce komai ba amma da a farko ta ji faɗuwar gaba gudun kar dai laifi ne hakan. Ya jima bai ce komai ba sai ƴar magana da yake kiran Kalifa da ita sai kuma ya ce
"Abin nan da kika yi kin birgeni shi ya sa na ce ki tashi mu je gidan Baba mu gaishe da su" Da sauri ta ɗago fuskarta tana bayyana tsantsar mamaki, don abu ne da bai taɓa faruwa ba wai a ce ya je gaishe da iyayenta daɗin daɗawar ma har da ita. Cike da zumuɗi bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba tana cewa Kalifa sai mun dawo ka sha kunun. Shi kuwa Nasir yana mata kallon baki da hankal.
Hijabi ta saka dogo har ƙasa ta ɗauki Kalifa tana cewa gidan Baba za su je, saboda kissa har da buɗe mata mota, a take ta fara jin lallai addua,arta ta fara karɓuwa ta samun ƴanci a gidan miji!. A ƙofar gidan su ya yi parking tana ta washe baki ya ce
"Ki min sallama da Baban idan yana nan sai na gaishe da su" Ranta fari ƙal tana jin kanta ita ma kamar kowace mace, yau dai ta zo gidansu cikin kwanciyar hankali ba za a kore ta ba ko a kyare ta cewar ta koma tun da yau mai kankat aka yi wato har da mijin. Da sallama ya shiga gidan, kowa yana hada-hadarsa Baba yana zaune a kan dutsi yana alwalar magriba don wasu masallatan sun fara kira. Yana ganinta ya dangwarar da butar ya ce
"Sadiya wace jarabar ce ta kawo ki gida da gabannin magribar wannan? " Ya faɗa don tunaninsa laifi ta yi suka yi faɗa ko kuma ƙara ta kawo da sauri ta ce
"Baba tare da Abban Kalifan muke shi ya kawo mu a mota yana waje ya ce ka je ku gaisa" Wani irin washe baki Baba ya yi tuni ya tashi yana saɓa babbar rigarsa tare da gyara zaman hularsa matan gida da aka fara ƙusƙus jin abin da Sadiyar ta faɗa, Baba a zaure har tuntuɓe ya yi da wani dutse yana jin kansa wai yau shi ne sirikinsa ya zo har ƙofar gidansa gaishe da shi kuma a motar da akam ce sabuwa ce ma, ya san yau kam Nasir zai masa sha tara ta arziƙi, sai dai kash!. Yana fitowa bai ga komai ba sai sawun motar Nasir don tuni ya cikawa rigarsa iska!.
ALIYA
Ranta yana ƙuna ta ji Umma ta ce
"Tsakaninki da Allah Aliya ko dai don kin daina ra,ayinsa kika faɗi haka Aliya ban da sharri" Umma ta faɗa tana yin ƙasa da murya don tuni idanunta sun raina fata sun yi jawur kamar ta sha ƙwayar da ta fi ƙarfin kanta.
Aliya tana kuka ƙasa-ƙasa ta ce
"Umma wallahi ganin idona Kasim ba asalin namiji ba ne" Umma cike da ruɗu ta ce
"Ya aka yi kika gane Aliya kar fa ki yi abu da ka" Aliya tana jin tamkar dai ta shiga kwakwalwar Umma ta cusa mata abinnda take so ta fahimta. Ta ce
"Umma idan baki yarda ba in koma ɗakin in ɗakko miki hotonsa ki ga zahir... Tun bata ƙarasa ba Umma ta ce
"Kina da hankali Aliya ina ni ina ganin gaban siriki tsakani da Allah wannan ai mugun ji ne, to ke in ban da ma tonon silili Aliya amarya tana langwaɓewa namiji ya mata bauta a daren farko amma ke kin... Aliya ta katse Umma da faɗin
"Umma ana ga yaƙi kina ga ƙura Umma ba zan taɓa zama da mata maza a matsayin miji ba" Umma tana ƙara da murya ta ce
"Aliya kar fa kisa in ke ɗaga murya kin san dai akwai sauran ƴan biki da basu tafi ba suna ɗakinku ku, dama jiyaa ana ta batun kyawun gidan Jidda ke babu ma wanda yake batun ki in dai aka sako maganar gidanki sai dai in zancen mutuwar inji za a yi haka jiya na sha ƙunsar takaici, dakyae bacci ɓarawo ya sureni wallahi cikin baccina na yi mafarki ke kin koma gidan Jidda matsayin matar Ibrahim ita kuma ta koma gidan Kasim matsayin matarsa " Aliya ta ce
"Ai haka ne ma Umma wannan ba gidan zamana ba ne babu wani kyau da armashi ga miji yana ɗauke da baƙar ƙaddara, ni dai Umma ki faɗawa Abba ana jimawa daga gari ya waye zan taho gi.. Umma ta katse mata hanzari da faɗin
"Aliya ki rufa min asiri wallahi kinnsan dai halin Abbanku, sannan tonuwar asiri ne a ce kin fito a ranar da kika yi kwana ɗaya da tarewa a gidan miji, ƙaramar bazawara kike son zama?" Aliya ta rushe da kuka ta ce
"Ni dai ba zan zauna in haifi mata maza ba" Umma ta ce
"Aliya wa ya faɗa miki ana gadon haihuwar mata maza? Ai baba gadon haihuwar kawai dai halitta ce amma ba a gado" Umma ta faɗa cike da son ganin ra lallaɓa ta duk da ta san tabbas gaskiya ta faɗa ba a gadon haihuwar amma dai ita yanzu duk ta rasa nutsuwa in ta tuno Jidda tana can maƙure da nata mijin a gidan daula cikin kwanciyar hankali sai ta yi ta tsine mata a zuciyarta.
Sun jima suna waya Aliya tana kuka Umma tana lallashin ta duk da ita ma kaɗan ya rage ta rushe da kukan, amma ta bari sai bayan sun gama wayar ta keɓe ta sharɓi kukanta son ranta, suna cikin wayar Abba ya shigo da sallama da sauri Umma ta danne makunnar wayar har sai da wayar ta mutu, tana kirkirar murmushi tare da ɗauke kai kar ya ga fuskarta.
Aliya kuwa ko da ta ji wayar ta ɗauke ta sauke ta daga kunnenta ta duba aai ta ga kiran ne ya katse, ƙara kiran Umma ta yi amma sai ta ji wayar a kashe, hakan ya sa ta fito daga kicin ɗin har wani duhu take gani tsabar ɓacin rai ta nufi ɗakin tana tuna irin uƙubar da za ta shayar da Kasim a zaman ta d shi a gidan, tun da har shi ya ga ya ji ya gani.
Tana shiga ɗakin ta ɗauki riga ta saka har lokacin yana bacci sai jan munshari yake, wani haushinsa ya turnuƙe Aliya ta tsaya tana ƙare masa kallo, Kasim bawan Allah kamar ya san mai take ya ɗan yi juyi kaɗan, sai kuwa ya ɗan yamutsa fuska kafin ya buɗe idanunsa tarrr a kan Aliya wacce take tsaye riƙe da ƙugu tana jifansa da mugun kallo hawaye yana zuba kamar an buɗe famfo. Sai lokacin ma ya gama wartsakewa da sauri ya lura da babu kaya jikinsa faɗuwar gabansa ya tsananta tunowa da ya yi cewa akwai ɓoyayyan al,amarin da yake tare da shi wanda Aliya bata sani ba.
A kiɗime ya tashi zaune tare da rarumo gefen zanin gadon ya rufa a gabansa...
MAMAN AFRAH
09015576222
https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=wwt
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 1️⃣5️⃣
SADIYA
Tun da Baba ya fita ta fara zuwa tana gaishe da matan gidan cike da girmamawa, duk cikin ƴaƴan gidan babu mai haƙuri da ladabi da biyayyar Sadiya tamkar dai ba a gidan take ba, don Sadiya daban ce a cikin ƴaƴan gidan ta kowane fanni. Lokacin sa ta je ta gaishe da Mama Habiba har za ta tafi Mama wacce ta ɗauki Kalifa ta ɗora cinya tana cewa
"Tun da dai baka son in ɗauke ka to zan maka saki uku"Ta faɗa tana dariya shi ma dariyar yake duk da bai san manufar maganar tata ba amma dai ya gane wasa take masa. Mama Habiba ta kalli Sadiya da take zaune kusa da ita ta ce
"Sadiya ki ci gaba da haƙuri a gidan aurenki, ki sani aljanna kike nema duk wani abu da namiji zai ƙunsa miki na baƙin ciki da ɓacin rai to ki sani wannan ɗacin da za ki ji a zuciyarki idan kika danne Allah zai baki ladan haƙuri sannan shi aure dama ɗan haƙuri ne, ita aljanna ba a samunta ta sauƙi, kuma duk ko da a ce mutum ya tauye maka haƙƙi ko yana maka abubuwa da gangan idan ka yi haƙuri wataran za ka ci riba. Na sanki da haƙuri to ki ci gaba wataran in har muna raye za ki ce na faɗa miki domin sai kin ga sakamakon haƙuri da juriyar da kika yi" Sadiya ta ɗago kai ta kalli Mama Habiba idanun Sadiya suka cika da ƙwalla tana jin Mama Habiba tamkar dai mahaifiyarta Mama Habiba tana mata abin da Mamarta bata mata, tana nusar da ita abubuwa masu yawa. Cike da rawar murya ta ce
"In sha Allahu Mama, na gode sosai ina alfahri da ke" Hannu Mama ta kai ta dafa kafaɗar Sadiya ra ce
"Babu komai Sadiya haƙuri ba ya taɓa yin tawa ko kuma a ce ya ƙare ita dama rayuwar cike take da ƙalubale, kowa da jarawabarsa haka kowa da ƙaddararsa wata ƙaddararta rashin samun mijin auren, wata kuma ta samu amma kuma babu kwanciyar hankali, wata kuma kishiya ce matsalarta ta hana ta sakat ta hana ta zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta kange komai ta hana ƴaƴanta su wayata" Sadiya kai kawai take gyaɗawa kamar ƙadangaruwa don ta san duk abin da Mama take faɗa haka yake!.
Suna cikin hakan ta ce ta je ta yi alwala, alwalar ta yi ta dawo ɗakin ita ma Mama ta yi suka tada sallah shi kuma Kalifa yana zaune yana cin biskit ɗin da Mama Habiba ta ɗakko ta ɓarw ta bashi. Bayan sun idar Mamar ta ci gaba da mata nasiha a kan kishiyar da za a mata tana ta nuna mata yadda za ta yi ta zauna lafiya duk da ta san Sadiya bata da hayaniya kuma tana da kawar da kai amma dai dole ta ƙara koyawa kanta juriya kasancewar yanzu abubuwa za au sauya idan da mijinta ne matsalarta yanzu kuma wata za ta shigo gidan kuma ba a san da mai za ta shigo ba, galibi ko yawanci mata ba wai suna tsoron kishiya ba ne sai dai suna tsorob da mai za ta shigo? Shin zaman lafiya ne zai kawo ta ko kuma kawai zuwa za ta yi ta hargitsa gidan, wata sai ta fitar da matar gidan kuma ta zo ta bar gidan, shi ya sa kishiya kala-kala ce wata ta zaman lafiya wata akasin haka.
Sadiya ji take tamkar a cikin ƙwaƙwalwarta Mama take kissima maganganun, don sosai suke shigarta, duk da kasancewarta wacce ta taso a gidan kishiyoyi har huɗu amma dai shi zaman aure makaranta ce mai zaman kanta da babu wacce za ta fane sai wacce ta yi auren, kazalika kishiya ma abu ce mai zaman kanta da babu wacce za ta fahimci zama da ita sai wacce aka yi wa duk da ba a taru zan zama ɗaya ba, tun da ita Sadiyar shaida ce tun da gashi yanzu kishiyar mahaifiyartw ce take nusantar da ita. Ba wai don tata mahaifiyar bata gidan ba, tun da da ta gaishe da Mamar ta je wajen Mama Habibar.
A ɓangaren Baba tun da ya yi turus ganin babu motar Nasir sai abubuwa da dama suka shiga masa gizo a ƙwaƙwalwa ya shiga saƙa da warwara sai dai idan zuciyarsa ta kissima masa abu marar kyau dangane da kawo Sadiya gida da Nasir ya yi sai ya yi saurin kawar da hakan, yana ƙara faɗawa kansa cewa ba da wata manufa Nasir ɗin ya kawo ta ba, tun da idan ya tuna fuskar Sadiya ai ya ga babu wata damuwa ko alamar ɓacin rai sannan ya ga Sadiyar ta murmure ta yi kyau abin ta babu wata rama ko yanayin da ya saba ganinta a can baya, ya ƙara haɗa hakan da cewa Nasir ne yake vata kulawa bai san cewa ita ce ta samarwa kanta mafita ba da taimakon Kaka, duk da ya san da maganar amma dai bai san