Showing 45001 words to 48000 words out of 178828 words
Chapter 16 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
fahimci mugun hali da mugun nufin da take da shi a kan Jidda ba.
Tana zuwa ta zauna a kan tabarmar kamar wata zautacciya sai baki take washewa don kar a gano jirginta, Jidda da Salama da suke tsaye daga can gefe suna magana Abba ya ce
"Salama zo ki buɗe min kayan na gani mana" Da to ta amsa ta taho tana raya yadda za ta turawa Umma haushi, Jidda kuma ɗaki ta nufa tana shiga Aliya ta ja wani uban tsakin da ya sa Jiddar kallonta babu shiri, dama ta san a rina wai an saci zanen mahaukaciya. Aliya wacce ganin screen ɗin wayarta ya yi raga-raga sanadin faɗuwar da ya yi ranta ya ɓaci tana tunanin wannan matsiyacin da ya kawo akwati biyu ina ma zai iya sauya mata sabuwar waya, duk da shi ya kawo mata wannan ɗin. Jidda kuma sai ta koma gefen katifarta ta zauna tana ɗaukan keypad ɗinta ta fara latsawa ganin miss call ɗin Ibrahim babu adadai ta ji duk ranta ya ɓaci domin ita yanzu tuhumarsa ma take a zuciyarta shin waye shi, kenan ba shi ne asalin Ibrahim ɗinta ba ne da take so da ƙauna mene ne manufarsa na ɓoye kansa mai ya sa bai bayyana mata waye shi ba tun asalin shin anya yana da gaskiya ma.
Aliya harara take ta aikwa Jidda da take danna waya, tana tunanin da a ce bata wulaƙanta Ibrahim ba da yanzu ita ce a wannan yanayin. Amma yanzu ta yi wa arziƙi dundu da gwiwar hannu ma ba wai da hannun ba.
A tsakar gida kuwa Salama sai ɗaga lesuna take suna ta walwalin tsada Umma ji take tamkar ta haɗiye zuciya ta mutu zai fi mata sauƙi a kan cewa lefen Jidda ne take gani wanda babu haɗinsa da na tilon ƴarta Aliya.
Cike da ƙarfin hali ta ce
"Kai ga wani leshi mai shefen kyau ai kayan nan babu na banza" Abba yana dariya ya ce
"Wallahi sun yi kaya kam shi ma mijin Aliya ai ya yi ƙoƙari a iya ƙarfinsa" A zuciyar Umma ta ce
'Indai akwati biyu da kit ne ƙoƙari Allah tsine ƙoƙari' A fili kuma sai ta ce
"Ai sun yi ƙoƙari matuƙa Allah sa abokan arziƙi ne"
Abba da Salama suka amsa da amin duk da Salama ta san addu'ar Umma iya fatar baki ne, haka Salama ta yi ta ɗaga kayan har suka ƙare kaf babu wanda bata ɗaga ba, kafin ta janye su gefe ta janyo akwatunan Aliya ta buɗe tana ɗagawa Umma ji take tamkar ta ce ta daina ɗagawa saboda haushin da take ji na Jidda kuwa ji take da za ta samu dama da ta babbaka musu ashana sun ƙone ƙurmus har akwatunan. Musamman a na Aliya da aka zo wajen kit ɗin nan aka fito da qur,ani da sallaya ta ji haushin Kasim kamar mai.
Umma gani take Salama da gayya take wani jujjuya atamfofin da basu da maraba da ƙanana. Bayan sun gama ta yi musu sallama ta ce za ta tafi haja suka fita da Jidda za ta taka mata zuwa waje.
Suna fita Salama ta sassauta murya ta yi ƴar guɗa yadda iya ita da Jidda ne za su ji ta ce
"Kai Allah abin godiya Allah ka ci gaba da ɗaukaka ƙawata aminiyata, yanzu dai na san jikin ta ƙaura ya yi la,asar tun yanzu an fara gane shayi ruwa ne, domin kuwa wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa!". Ta faɗa tana wani rawar kai Jidda wacce gabaɗaya damuwar da take ciki ta bayyana kanta ta dubi Salama cikin sanyjn murya ta ce
"Na lura ke farinciki kike, baki hango damuwar da zan shiga ba Salama, ni ba ma wannan ba Ibrahim ina ya samu kuɗi da ya yi wannan sayayyar sannan har ma da na kayan saka ranar da Abba bai bayyana ba?" Ta faɗa tana jingina da bangon gidan nasu da suke tsaye a kusa da shi tare da harɗe gabaɗaya hannayenta a ƙirji. Salama ta kalleta ta ce
"Tabbas ina yi masa kyakkyawan zato, na san ba sata ya yi ba kuma tabbas yana da tasa hujjar da ya yi hakan kuma dole ki karɓe shi da hannu biyu, sannan kuma ni murna yanzu na fara don da akwai ruwa a kusa da sai na zuba a ƙasa zan sha Jidda, duk iya ƙoƙarin mutanen nan na son ganinki a tsakiyar rana sai gashi Allah ya kai ki inuwa, a i uwar ma ya lulluɓe ki da bargon rahma" Shiru Jidda ta yi tana tuno irin kallon tsanar da Umma take jifanta da shi hatta yanayin kallon Aliya ya tsaye mata a rai, ita basu san ba bata da burin auren kyakkyawan miji bare kuma kuɗi wannan ba ya daga cikin burikanta, Ibrahim ma saboda karamcinsa ya sanya ta amince da shi bayan kasancewarsa kyakkyawa.
A kasalance ta ce
"Salama zan dakatar da Ibrahim domin na fasa aurensa!" Kallon mamaki Salama ta jefa mata, Jidda ta ɗauke idanunta daga kallon Salama tana kallon gefe guda tana tuno irin ƙaunar da take yi wa Ibrahim amma kuma ya zama dole ta haƙura da shi hakan ya sa ta ce
"Baki hangi abin da nake hanga ba Salama, baki san su waye Umma ba duk abin da nake baki labari kaɗan za ki fahimta da abubuwan da idanuna suke gani, zan jure rasa shi a rayuwata a kan na rayu a kan wani giɓi na tsantsar ƙiyayyar waɗanda su ne kaɗai nake kallo a matsayin dangi kuma ƴan uwa!"
Idanun Salama suka tara ruwa ta ciro hannayen Jidda daga ƙirjin Jiddar ta haɗe hannayensu a waje guda duk da akwai wayar Jidda a hannun nata suna kallon juna Salama ta ce
"Jidda!!!"
Amsawa Jiddar ta yi tana kallon Salama kamar yadsa take kallonta ita ma Salama ta ce
"Ina so ki sani abin da Allah ya rubuta ya daɗe da rubutawa, sannan Ibrahim bashi da mugun nufi a kanki don haka kar ki zarge shi ina so ki bashi dama, ya furta miki dalilansa a kan abin da ya yi, na sani ni shaida ce kina son sa kuma ban taɓa ganin kin so wani ɗa namini ba sama da Ibrahim idan kika ce za ki fasa aurensa tabbas zai cutu kuma ke ma za ki cutar da taki zuciyar. Abu na gaba ko ki aure mai kuɗi ko ki auri wanda ya fi mijin da Aliya za ta aura to fa ki sani ba za ta sauya zani ba, babu wani abu da zai sauya a lamarinsu ita kyakkyawar manufa saga zuciya take, duk abin da aka ce miki zuciyar mutum bata da kyau to har abada ba za a iya masa ba, ko da duniya za ka mallaka masa ke ko da za ka ciro zuciyarka ka damƙa masa a hannunsa" Sai da ta numfasa ta ɗora da faɗin
"Idan zuciya ta gyara to dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ta ɓaci dukkan jiki ya ɓaci, su Umma ci gabanki ne basa so don haka shi kuma ubangijin da ya fi kowa sonki yana son ki huta shi ya sa ya baki mijin da za ki aura nagartacce kuma kamili don haka kawai ki fawwalawa ubangiji lamuranki, ki dage da addu,a kamar yadda na sanki tabbas babu wani abu da zaj yi tasiri sai dai alkairi" Tana zuwa nan a maganarta ta damƙe hannun Jiddar da ƙarfi, su duka idanunsu sun cika da hawaye.
Bayanin da Salama ta mata ya sa ta ɗan ji wani ƙwarin gwiwa, shi ya sa take alfahri da ita kasancewarta ƙawar arziƙi a gare ta, duk ƙawar da za ta baka shawarar mai kyau ita ce ƙawa ta har abada, don haka yanzu ta ji tana da ɗamarar jin ta bakin Ibrahim in har bata samu akasin wani abu ba to za ta duba lamarin aurensa kuma ta shirya fuskantar duk wani ƙalubale da za ta tsinci kanta a sanadinsa, aon ta san muddin ta aure shi to bayan dara akwai wata caca!.
Sun daɗe suna magana Salama tana kwantar mata da hankali, kafin daga bisani suka yi sallama Salama ta kama hanya. Jidda kuea ganin Salama ta tafi sai ta ɗan tsaya tana nazarin maganganun tana kuma son kamo bakin zaren, kamar daga sama ta ga wata mota ta shigo layinsu a 360 yanayin yadda aka shigo da motar tuƙin ya yi kama da na ganganci ko dai babu lafiya. Ta gabanta motar da ta zo a guje ta sassauta gudun tana zuwa da ta gifta ta kaɗan sai ta tsaya, Jidda gabaɗaya ta tsorata ma ta fara tunanin ko dai mamallakin motar yana shaye-shaye kar ya je ya fito ya cutar da ita hakan ya sa ta fara ƙoƙarin shiga gida.
Ibrahim wanda ya hango Jidda tana shirin shiga gidan ya fito daga motar a sukwane, Jidda tana shirin shiga gidan sai ta ji muryarsa mai sanyi yana kiranta, gabanta ne ya harba da ƙarfi ta juyo cikin sauri da jajayen idanunta tana son ganin gaskiyar abin da kunnuwanta suka jiye mata, tana juyowa ta yi arba da shi gabaɗaya bashi da nutsuwa ta ga ko marfin motar bai rufe ba, daga gefen inda motar lefenta take ajiye, yana zuwa gabanta sai kawai ta ga ya zube a kan gwiwoyinsa, hawayen da ta gani kwance a saman fuskarsa sannan hannuwansa biyu a haɗe alamar roƙo, ba ya ma kunyar mutanen da suke wucewa jefi-jefi su ganshi durƙushe a gaban mace. Wani iri ta ji zuciyarta, gabaɗaya sai ta ji hankalinta ya tashi kafin ta samu damar furta wasu kalmomi ya buɗe baki cikin dashshshiyar muryarsa ya ce
"Jidda, don Allah da manzonsa karki gujeni Jidda, ke kaɗai ce farincikin ruhina wallahi ina ƙaunarki fisabililillahi, ki sani ban yi komai ba sai don gudun ki suɓuce mini" Tun da ya fara maganar tamkar an ƙara gudun hawayensa kuka yake haiƙan abin da ya ƙara saka jikinta ya yi sanyi.
Jin bata ce komai ba ya ɗora da faɗin
"Tun ranar da na fara ganinki kyakkyawar alaƙar ki da direbana da ya watsa miki ruwa shi ne abin da ya kwaɗaitar da zuciyata ta wuni da ke a ranar, tun daga wannan lokaci ta hanani sukuni Jidda koyaushe ki take ambato!. Na bibiyeki ban samu ganinki ba har dai Allah ya sa a watarana na ganki ke da ƙawarki Salama a inda kuka tsaya kuna tattaunawa a jikin motar da nake ciki, a cikin kalamanki Jidda na samu abin da kike so da wanda bakya so wato kyakkyawan namiji kuma mai kuɗin, wannan furucin ya sa na fara sauya taku ba don na yaudareki ba don yaudara bata cikin tsarina, sai dai kyaun da nake da shi bai ɓuya ba kuma sai Allah ya sa baki gujeni ba, Jidda ki min hukuncin komai amma karki rabo da ni, rabuwarki da ni zai jefani cikin damuwa kuma kin san da hakan, don Allah ba don no ba ki tausayawa wanda ya ƙaunace ki domin Allah" Kallonsa kawai take yadda yake rarraba hannuwa yana roƙonta gashi kalamansa masu kashe jiki domin kalamai ne da wanda ake yi wa su zuciyarsa za ta raunatu!.
Jin bata ce komai ba ya ce
"Idan har za ki yarda ki rayu da ni na yarda zan rabu da duk wani abu da na mallaka wani yake alaƙa da dukiya, in har hakan zai saka ki farinciki Jidda!."
Yanayin yadda yake mata magiya sai ta ji duk tausayinsa ya kamata, a kanta ita Jidda har zai iya sadaukar da komai nasa lallai ƙaunar da yake mata ba ƙarama ba ce. Zuciyarta ce ta mata jagora wajen tsugunnawa a gabansa sai dai ita bata saka gwiyoyinta a ƙasa ba. Tamkar an masa albishir da kujerar makka haka ya ji tun da ganinta tsugunne ya tunatar da shi cewa ba za ta rabu da shi ba amma ganin da yana ta kiranta a waya bata ɗauka ba sai zuciyarsa take ta masa zulumin cewa za ta rabu da shi.
Idanunsa jajaye ya kafe ta da su yana duba nata idanun inda ya ga alamun ta sha kuka duk da ya san kukan ba ya rasa nasaba da gano waye shi amma sai ya ji tausayinta ya kama shi shi ji yake da yana da iko Jidda ba za ta taɓa shiga ƙunci ba a rayuwa ya gwammace duk wata damuwarta ya haɗa da tasa damuwar ya saka a zuciyarsa ita ta rayu cikin salama.
Cikin sanyin murya ta ce
"Na gamsu da jawabinka kuma ko a mafarki ban taɓa tunanin za ka taɓa cutar da ni ba, ina so ka sani ni Jidda ina sonka, kuma zan rayu da kai daɗi ko wuya ina tare da kai, sai dai inaso na ci gaba da kasancewa cikin addu'o,inka kamar yadda kake min a kullum!" Tana gama faɗar hakan bata jira cewarsa ba ta miƙe tsaye kafin ta dawo daga mamakin da ta shayar da shi wuff ya ga ta shige cikin gida.
Tamkar an saka masa daskararriyar ƙanƙara a saitin zuciyarsa haka ya ji, wani sanyi ya baibaye ta haɗe da wani farinciki marar misali a take ya tafi ƙasa ya kai goshinsa ya yi sujada yana miƙa godiyarsa ga mahaliccin da bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, don ya san shi ne ya bashi komai kuma shi yake masa komai. Yana ɗagowa daga sujadar ya tashi ransa fari ƙal ya koma ya shiga mota ya tada ya bar unguwar cikin tuƙi na hankali ba kamar yadda ya zo a kiɗime ba.
Ko da ta shiga gida Abba har ya shige ɗaki sallamar da ta yi ma Umma bata amsa ba sannan akwatunan babu ko ɗaya a tsakar gidan da alama suna ɗakin Abba.
Aliya tun bayan fitar Jidda wayarta ta shiga neman ɗauki wanda ba kowa ba ne sai Kasim wanda ta wa laƙabi da sabon suna wato faƙiri ɗan anace. Ya daɗe yana kiranta kafin ta ɗauka a kufule ta farfaɗa masa maganganu mararsa daɗi wanda suka sosa masa zuciya a ƙarshe ta ce ya aiko a kwashe wannan akwatunan bata so kuma kar ya ƙara tunkarar ƙofar gidansu. Hankalinsa ya tashi amma ya san ɓacin rai ne yana fatan zuciyarta ta sasauto. Haka suka kwana suƙuƙu, don Jidda ta lura Aliya bata runtsa ba a ranar sai tunane tunane sai dai bacci ɓarawo, don ko da ta tashi sallar dare ma Aliya idonta biyu ko alamar bacci amma kuma ba za ta yi nafila na yi addu'a ba tana dai kwance kamar an soya idanunta amma zuciyarta tsanar Jidda ce fal kuma ta ci alwashin warware duk wani abu wanda zai kawo mata damuwa a zamantakewarta wanda Jidda za ta samu ita bata samu ba, don ta ci alwashin ko mene ne Jidda ta mallaka a rayuwa sai ta dawo da shi gareta ko mene kuwa ta ƙudurta hakan a rai da zuciyarta.
Yadda Umma ta ga rana haka ta ga dare bata runtsa ba, zuciyarta kamar ta buga.
Washe gari da wuri Abba ya tafi kasuwa, don haka Umma da Aliya suna ɗakin Aliya suna ta shirya yadda abubuwa za au kasance ba tare sa sun kunyata ba.
Aliya ta ce
"Umma tun jiya da wani zazzaɓi ya rufe ni har yanzu bai sauka ba, ni fa akwatunan nan na gama yin status ɗinsu haka ma ƙawayena hatta grp ɗinmu na makaranta da muke ciki da wanda muka yi karatu na tura musu hoton da kuma hoton akwati biyu da kit ina cewa na Jidda ne yanzu kuma ido ya juye da mujiya?" Umma ta sauke wata nannuyar ajiyar zuciya tana tuno yadda ta yi ta alfahri a idanun mutanen unguwa jiya da kuma ƴan uwa a kan lefen yanzu ya zan ce da mutane wallahi dariya za a yi mana"
Aliya ta ce
"Ni tunanina ma gidan da za a kai Jidda da kuma inda za a kaini ai juma,ar da za ta yi kyau saga laraba ake ganeta wallahi Kasim ya cuceni!"
Umma ta yi shiru tana nazari ta ce..
"Na samo mafita, tun da Abbanku ne kaɗai ya san maganar akwatunan ba naki ba ne, shi kuma ba mazaunin gidan ba ne, ita kuma Jidda ko a gabanta aka ce naki ne ba za ta ce komai ba, kawai yanzu a barshi a mazaunin duk wanda ya zo ganin kaya akwati ashirin da huɗu da mota naki ne, akwati biyu da kit na Jidda" Wani daɗi ya ziyarci Aliya jin an rufe mata wani asirin, sai kuma ta ce
"Umma idan kuma aka kaimu gidajenmu fa ai ƙawaye da mutane ba mahaukata ba ne da za su yarda cewa wanda ya yi akwatuna da mota zai kai ni gidan matsiyatan da Kasim zai kaini"
Umma ta ce
"Dole zan zage dantse a komai Aliya, ba zai iyu ƴar karo ta fi ƴar gida, wato mummuna ta fi kyakkyawa samun gidan hutu da arziƙi"
MAMAN AFRAH
09025576222
[10/22, 4:33 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/DNhoKsIb9qP8PlVQdpQ4BW?mode=ems_copy_c
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 1️⃣1️⃣
*ZALIKA*
Rayuwar gidansu ta ci gaba da kasancewa a ƙunci sanadin takurewar da mahaifinsu yake musu, rashin walwala da kuma damuwa da al'amuransu sakin fuska ko yin hira da su matsayinsa na