Showing 90001 words to 93000 words out of 178828 words
Chapter 31 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt
sa ta fahimci tana cikin farinciki sannan a muryarsa ta gane yana cike da ɗoki, dunƙulallan maganin hannunta wanda shi ne zai gusar da tunaninsa wajen gane an ci da rabinsa tun a waje, shi ta yi dabarar sokewa a ƙugugunta kasancewar laffaya ta ɗaura a saman kayan jikinta. Tana zaunen tana ɗan qasa da yatsunta ya ƙaraso gaban gadon yan daɗin
"Amarya kin sha ƙamshi" Kamar yadda bata amsa sallamar tasa ba haka nan bata amsa kirarin amaren da ya mata ba tana son ƙara tabbatar masa da cewa ita mace ce mai kunya, wannan abin da ta yi na sunkuyar da kai ba tare da ta furta komai ba shi ya farantawa Nasir yana ji a ransa burinsa ya cika ya auri wacce yake so mace mai kunya da ladabi haɗe da biyayya ba irin Sadiya ba da yake ganin bata masa biyayya, sannan yana murnar zai ɓarje amarci sa sabuwar amarya tun da a nasa tunanin Sadiya ta zama tsohon yayi yanzu domin yana ganin ma ai an daɗe da cin moriyar ganga dole a yada korenta.
Babbar rigarsa ya cire ya samu wuri ya ajiye, ya ƙaraso gaban gadon ya tsaya a gabanta hannu biyu ya saka ya ɗaga mayafin laffayar da take kanta, ya kai hannu ya ɗago haɓarta sai ya ga ta rufe idanunta wani irin daɗi da farin ciki yake ji a ransa tabbas ka auri wanda t
kake fata da buri shi kaɗai ma abin alfahri ne. Saɓanin a zuciyar Meenal ba haka ba ne illa fargaba sai yanzu take tunanin dama haka ƴanmtan da suka watsar da mutuncinsu a waje suke tsintar kansu a fargaba da tashin hankali idan an kai su gidan miji.
Bata ankara ba ta ji hannunsa cikin nata, ya kama ta ya tada ita tsaye tana wani kauda kai ita ala dole kunya cike da wata murya da bata san ma yana magana da irinta ba, duk da ta san yau amarya take kuma a ranar farko don haka yana iya mata magana da kowane lafazai mai daɗi ji ta yi ya.ce
"Duk kunyar nan yau zan cire miki ita" Ƙara sadda kai ta yi a haka ya kamata ya kai ta ƙofar banɗakin bedroom ɗin, ya tsaya ya ce
"Za ki iya yin alwala mu gabatar da sallah ko ni zan miki da kaina" Kafaɗa ta ɗaga masa alamar a,a wato bata son fa mata alwala, hakan ya sa ya ɗan yi murmushi don ya gane kunya take ji. Nan ta bar shi tsaye ta shige banɗakin ta rufe ƙofar ya saki wani murmushi don shi ma ya mata uzurin ba zii bita ba don ya san dama yau dole a rina wai an saci zanen mahaukaciya wato dole kunya ta lulluɓe ta.
Meenal tana shiga banɗakin ta ɗakko wannn dunƙulallan abun ta tura a matancin ta, ta ɗan ji sawaba a zuciyarta jin da za ta saka abin ya shiga dakyar alama ce ta matain ya yi sai dai tana ta wasi-wasin anya hakan ya yi kuwa. Ruwa ta kama ta ɗaura alwala ta gyara laffayar ta, ta buɗe ƙofa ta fito sai da ya kama hannunta ya kaita har falo ya zaunar a akan kujera kafin ya koma yana cewa ta bashi mintina kaɗan yanzu zai ɗauro tashi alwalar, jim kaɗan sai gashi ya dawo ko sallaya basu shimfiɗa ba suka yi sallar kasancewar komai sabo ne wato wajen yana da tsafta tun da kafet ne. Bayan sun idar suka ɗan taɓa kayan maƙulashen su duka babu wanda ya ci abin kirki shi yana zumunɗin amarci ita kuma tana fargabar ya ji ba daidai ba, don ta san muddin ya gane akwai matsala saboda komai ya kwance mata duk wani ƙuduri da za ta aiwatar a gidan ba za ta samu dama ba komai zai ɓalɓalce wanda bata fatan hakan.
Suna gamawa bai bari ta taka da ƙarfarta ba ya sungume ta gabanta yana dak-dak-dak bayan sun yi shirin kwanciya ya kashe wutar ɗakin, daga nan kuma abubuwan da suke da wuyar durtawa a baki suka fara faruwa, shi dai Nasir a hankalce tun da ya kai ziyarara wannan waje ya so dai ya fahimci wani abu sai dai ya kasa gane mene ne sai ya ji kamar ya manta mai yake so ya gane wanda kamar dai akwai matsala amma ba zai ce ga matsalar ba. Ko da komai ya lafa Meenal ta ga bai nuna komai ba hakan ya sa ta gane maganin da ta karɓa wajen malamin nan ya yi aiki duk da ta san ya ce mata abun zai iya warwarewa amma dai ta san in aka wuce wannan ranar to ita bata da wata damuwa.
Ko da safe haka ta narke ta ƙi fita ko falo wai ita ala dole ƙafafunta basa haɗuwa, ko banɗaki za ta shiga kamar ƴar shayi haka take tafiya tana son nuna masa cewar shi ne dai farkon wanda ya fara saninta a mace. Abu kaɗan za ta hau raki shi dai duk ya kasa ganewa.
A ɓangaren Sadiya tun da ta sha kankanar nan duk da bata wani sha da yawa ba, sai ta mayar frige ta je ta yi shirin kwanciya, bayan ta kwanta sai ta ji zuciyarta ta mata ƙunci, tana ta mata saƙe-saƙe cewa yau ce ranar farko da za ta kwana ita kaɗai a ɗakin sannan ita kaɗai a gadon ba tare da Naair ba. Zuciyarta tana azalzalarta a kan cewa yanzu yana can tare da wata matar da ita ba, yanzu haka suna kaza da kaza sun yi kaza jin dai shaiɗan yana neman haddasa mata baƙinciki haɗe da rashin bacci sai ta shiga karanto addu'o,in a take ta ji duk wani ƙunci da baƙinciki ya yaye tamkar bata da wata damuwa. Bata ma san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ita ba.
Bata tashi ba sai da asuba, dakyar ta sakko daga gadon saboda jikinta ya mata nauyi cikinta yana ƙara girma sosai. Bayan ta idar da nafila raka,atainil fajr ta yi sallar asubar sannan ta zauna ta yi ta addu,oi haɗe da karatun qur'ani. Bayan ta gama ta ɗan jingina da jikin gado bayan ta miƙe ƙafafunta da ta ga yau sun kumbura bacci ɓarawo ya sace ta. Ko da ta tashi daga baccin wanka kawai ta shiga ta saka wata doguwar riga marar nauyi, Kalifa har lokacin bacci yake, madara da ta bayar aka auno mata kwata da milo sacet guda ta haɗa shayi mai kauri ta sha domin har lokacin akwai nepa hakan ya sa ta jona ruwan, jin yunwa abin cikinta sai motsi yake.
Ɗakinra ta gyara tass ta kunna turaren wuta ɗan tsinke, lokacin Kalifa ya tashi ta wanke masa baki ta masa wanka sannan ta haɗa masa shayi ta bashi da biredi ya cinya ƙoshi tun da jiya ana taro bata yi tuwo ba.
Har ƙarfe goma babu alamar amarya da ango, wajen goma da kwata Sadiya tana wanke-wanken ƴan kwanuka da suka rage babu wanki don jiya sai da aka wanke duk kwanukan da aka ɓata. Nocking ɗin gidan aka shiga yi, ta tashi tana ɗan jin yadda bayanta yake riƙe mata, Kalifa kuwa yana ta wasan sa, tana zuwa zauren ta ce
"A nan ne? Waye?" Ta tsinkayi muryar Husna cike da gadara ta ce
"To sarkin ƴan ƙarfin hali ɓarawonda sallama, ki buɗe mana gidan tun da yanzu dai ya zama mallakin ku, ku biyu" ,Bata ce komai ba ta buɗe, ko tsayawa bata yi ba ta juya su kuma Husna da Hibba suka shigo sai da suka zo ƙofar ɗakinta sannan suka yi sallama a daƙile amsa musu ta yi ba tare da ta ƙara bi ta kansu ba ta wuce wajen da take wanke-wanke Hibba ta kalli Kalifa don ganin ta ƙular da Sadiya ta ce
"Yaro ɗan sabuwar amarya yau babanka ya kwana yana shan amarci ko?" Shi kuma kawai kallonsu yake don ba wani sabawa da su ya yi ba.
Sadiya ko kallo basu ishe ta ba ta cigaba da ɗaukan kaya tana shiga da su kicin ta baiwa banza ajiyarsu, ta fito ta sunkuya dakyar tana wanke wajen sai Husna ta yi karaf ta ce
"Sadiya ba sai kin mana banza a gidan ɗan uwanmu ba, mu ai mun isa mu saka ƙafarmu a ko ina a gidan nan ba tare da shamaki ma ko kin manta shi ne ya sha nono ya bar mana?" Hibba ta karɓi maganar ta ce
"Ke kika kula ta ma, bata san zamanta a gidan nan ɗorin ɗosano ba ne" Husna ta ce
"Wallahi kuwa ai kawai saboda Kalifan nan ne amma ai da wannan cikin ma saj dai a haife a gidan tsohon...
Kafin ta ƙarasa faɗa Sadiya ta miƙe tsaye a zuciye ta saka hannu ta finciko mayafin Husna rai a ɓace ta ce
"Husna duk abin da za ki yi ya tsaya iya kaina amma karki kuskura rawar kanki ya kai ga mahaifina wallahi za ki yi nadamar hakan" Husna duk da ta tsorata da yanayin da ta ga Sadiyar amma sai ta yi ƙarfin halin cewa
"Dalla malama saka min mayafina" Gamgam Sadiya ta riƙe bata saki ba sai da Husnar ta fisge sannan Sadiyar ta sakar mata Hibba kuwa bata furta koɓai ba ta yi ɗiff sai da suka yi hanyar ɓangaren Meenal Hibba ta ce
"Kyaji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa, wato wutar kishi tana nuƙurƙusar zuciyarki shi ne za ki sauke a kanmu" Ko kallonsu bata yi ba suka nufi ƙofar ɗakin Meenal dama ɗauke suke da kwando mai food flask masu kyau da alama abinci suka kawo. Ƙwanƙwasawa suka yi amma shiru waya Husna ta duba lokacin goma har da rabi hakan ya sa suka kalli juna suna danne dariyarsu.
A can cikin ɗaki Meenal da ta narke tana zuba shagwaɓa ce jin ana bugawa sai Naair ya ce zai je ya buɗe buɗar bakinta sai ta ce
"Ka rabu da ita Sadiya cw kishi yake cinta take son rabamu fa" Murmushin yaƙe ya yi shi dai ya san yau ranar farin ciki ce amma kuma ya kasa gane ta ina walwalarsa ta samu naƙasu, kawai dai ya rasa ma mene ne yake damunsa. Kamar raƙumi da akala haka ya tsinci kansa da bin umarninta, ya koma ya hau gadon tare da kwantawa ita kuma ta mayar da kanta ta ɗora a cinyarsa yake shafa gashin kanta. Sun jima suna bugawa amma babu alamar za a buɗe Hibba ta buɗe baki ta ce
"Yaya!" Jin muryar Hibba sai ya yi karaf ya ce
"Kin ji ashe ma Hibba ce ba Sadiya ba" Ya faɗa yana washe baki, tamkar ya sanar da ita mutuwa haka ya haɗe rai ta ce
"To mene ne idan su ne, shin basu san yau ranar mu ba ce ba ma buƙatar hayaniya?" Wani abu mai kama da mamaki ya ɗarsu a zuciyarsa duk yadda ya ga tana haba-haba da su amma kuma yau sai ta canja fuska sai dai ya yi tunanin ko dai don tana cikin raɗaɗin amarcin ne bata ware ba.
Idan Hibba ta ƙwala masa kira sai Husna ma ta kira shi amma Meenal ko amsawa ta hana shi ya yi. Sadiya tana jin su tana danne dariyarta, har suka gaji da tsayuwa suka zauna a ƙofar ɗakin suna zaman jiran tsammani saboda zuciyarsu ta faɗa musu cewa ko suna cikin halin da ba za a iya ganinsu ba.
Tana ganin yanayinsa ya canja ta san kuwa saboda ta hana shi zuwa wajen ƙannensa ne saboda ta san son su yake kamar mai amma dai ta yi alƙawarin takawa wannan alaƙar tasu birki. Wayarsa ce ta shiga ruri bata masa magana ba ya ɗ kko a kan bedside drower yana ganin sunan Hibba da sauri ya ɗauka cike da shagwaɓa ta ce
"Yaya mun jima a ƙofar ɗakin amarya muna jiranka, Hajiya ce da kanta ta tashi tun asuba ta muku girki, abin da ya sa ma bamu ƙaraso da wuri ba saboda cewa ta yi mu bari rana ta ɗan yi kar mu yi sakko baku tashi ba" Ba tare da ya kashe yana cewa Meenal
"Bari na karɓo abinci ne suka kawo in ji Hajiya" Baki ta taɓe ta juya ta kwanta tana rayawa a ranta cewa kwa ji da shi ciwon ajali a yatsa. Yana fita ya karɓo, su kuma sai suka yi ƙoƙarin bin bayansa wai za su gaisa da Meenal tun da a tunaninsu babu wani abu domin ya fito sannan tun da gidan ba su kaɗai ba ne a ganinsu ai ba sa zauna suna ta yin abu ɗaya ba. Samun kansa ya yi da kasa dakatar da su, suka shigo falon suka zauna suna ganin falon sai wani daɗi suke ji Meenal matar yayansu.. A falo ya ajiye kwandon suna ta hayaniya ya shiga ɗakin gar lokacin tana kwance ta juya baya yana ɗan washe baki ya ce
"Abinci ya hallara ranjki ya daɗe sannan kin yi baƙi" Juyowa ta yi ta ɗan yatsiina fuska ta ce
"Baƙi kuma? Daga ina aka samu baƙi da sassafe" Ya ji abin da ya ɗaure masa kai ɗan ƙara washe bakin ya ya yi ya ce
"Ƙannenki ne fa, kuma yanzu maganar ƙarfe sha ɗaya ake kin ga kuwa ai ya fi sassafe" Bata bashi amsa ba yake tsaye kamar wani itace duk abin da ake a kan kunnen su Husna sai dai basa gane mai ake cewa amma tabbas suna jin alamun magana. Sai da ya sake maimaita mata ta ɗan yatsina fuska haɗe da karyar da kai yadda ba zai fahimci da gangan za ta yi abin da take shirin faɗa ba ta ce
"Ka ce musu su dawo an jima" Sheƙeƙe yake kallonta saj ta yi abin tausayi na kissa ta ce
"Ƙafafuna ne suke cewa kuma fa ka san duk kaine ka yi wannn aika-aikar ina fita za su fahimci wani abu" Wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauke don furucin nan nata na ƙarshe ya kauda duk wani zargi da ya ɗarsu a zuciyarsa da farko ya ɗauka dai zaɓen tumun dare ya yi ma,ana bata ƙaunar ma ƴan uwansa tun da abu ne sabo da bai saba da shi ba daga wajen Sadiya wato wofintar masa d ƴan uwa ya san Sadiya ba kallon ƴan uwansa ba duk wanda zai sako ƙafarsa gidan ba zai yi kuka da ita ba. Yana nuna tausayawa don shi ma ya san tana tafiya kamar ta sabbin ƴan shayi sai ya karɓi uzurinta.
Fitowa ya yi ya same suka zuba masa na mujiya don tunaninsu a yadda suka saba da ita za ta fito daga ta ji shigowarsu amma sain gashi da har da aike ta gagata fitowa kamar wata sarauniya. Shi sai da ya zo falon ma ya tuna bai tanadi abin faɗa musu ba sosa ƙeya ya yi ya ce
"Bacci take" Junansu suka kalla da mamaki din sun san sun ji muryarta sai kumamsuka kalle shi, sai lokacin ma ya gane ɓaran ɓaramar da ya yi don ga san za su iya jin dirin muryoyinsu Hibba ce ta ce
"Baccj kuma yaya? Ko dai ba za ta samu ganinmu ba?" Saurin ɗaure fuska ya yi ya ce
"Ƙarya zan muku kenan?"Kai suka shiga kaɗawa kamar ƙadangaru sai ya ce
"Ku tashi ku wuce gida an jima kwa dawo" Sum-sum suka tashi kowacce tana gungune sula fita, bayansu ya bi ya rufe ƙofar, lokacin Sadiya tana tsaye jikin windon falonta daga wajen tana gogewa, kallo ɗaya ta musu ta gane a jone suke wato ransu a ɓace ko kallo bata ishe su ba, suka fita fuuuu.
Tun da suka fita a hanya suke ta mita suna mamakin faruwar hakan, ko da suka je gida suka faɗawa Hajiya sai ta musa tana faɗin ai ƴarta Meenal ba za ta yi haka ba wataƙila ma tana cikin yanayin farkon amarci abinka da sabuwar rayuwar da ba a saba ba. Haka dai suka haƙura amma ba don sun yarda ba suna da mamaki kawai!.
Sai sha biyu ta sako ƙafafunta daga kan gadon lokacin har an maimaita abin da aka gabayar jiya na amarci, abin da ya ɗaurewa Nasir kashi ne kamar wanda ya kai zicyara ƙofar gari haka ya ji hanyar zurum babu wani birki, don lamarin ya fi ƙarfin na darw har gwara da dare da sauƙi. Sai dai abin mamakin daga ya gama aikata sunnar sai dai abin ya tsaye masa a rai ga abu na damuwa amma ya kasa tuna mene ne. Sannan yadda take raki bashi da banbanci da farin shiga bai sai duk ana yin hakan don a kawar masa da zargi duk da ta san maganin da ta yi amfani da shi jiya da dare sai ya fi aikinngusar masa da mummunan zato fiye da kissa da kisisinar da take yi . Shi ya jona tuwan kamar dai wanda ya jona musu na farko ya kai ya haɗa ta shiga tana mita irin ta sabbin