Showing 174001 words to 177000 words out of 178828 words

Chapter 59 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt

18 Dec 2025

1457

yi saurin dafe ƙirji tana dogon wiya alamar babu wanda yake jinsu ta sassauta murya ta ce

"Haba Aliya ke baki iya sirri ba yanzu idan akwai wani a laɓe ai shikenan ya gama jinmu, sai asirinmu ya tonu, sannan kuma idan kika je kika kwaso set ai ganewa za a yi kawai dai ki samu ko ɗan zobe ne ki ɗakko na san za mu samu biyan buƙata a iya zoben ma"

Murmushi Alia ta yi ta ce

"Shi ya sa nake son ki Umma ke mikiya ce mai hangen nesa"

Sun gama tsara komai bayan kwana biyun Aliya tana zaune a falonta tana kallon daɗin kowa an yanka ta tashi sai kiran Jidda ya shigo amma har ya katse ba ta ɗauka ba sai saƙon harara da ta kake aikawa lamba da sunan Jidda da ya fito a jiki tamkat dai Jiddar ce sai da kiran ya ɗauke sannan ta saki wani gajeran tsaki. Sai da Jidda ta yi sau uku na ukun yana dab da yankewa sannan ta ɗauka cike da fara,a ta amsawa Jidda nan Aliya ta ce mata tana kicin tana aiki yanzu ta shigi falon ta tarar da wayar tana yi. Sun ɗan gaisa sai Jidda take faɗa mata gobe za ta zo gurinta ta wuni gaban Aliya ne ya buga ta fara tunanin ko dai Jidda ta gano gaskiya cewa gobe za ta je gidan ta zuwa na baza ta don aiwatar da aiki amma yanzu tana shirin fitowa.
Har sai da Jidda ta ƙara magana a kan ta yu shiru Aliya ta marairaice murya ta ce
"Allah sarki ƴar uwata rabin jiki wato na yarda da aka ce jinin ƴan uwa a haɗe yake tun da ga shi nima una shirin zuwa gobe domin har na tambayi mai gidan ya ce ya barni" Shiru Jidda ta yi ta ce

"To sai kin zo ƴar uwa ni dama cewa na yi bari na sanar dake amma tun da har kina da shirin zuwa to na yi maraba da hakan" Sun jima suna magana kafin daga bisami suka yi sallama kowa ya kama sha,anin gabansa.

Washe gari Aliya ta wanki ƙafa da yamma ne ma sai gidan Jidda ko da ta zo ta shiga gidan sai ta tarar babu Jidda a dalon ƙasan sai take tambaya nan Saude ta ce.mata ai tana wajen wasan motsa jiki, Saude ta saka ta nuna mata hanyar da za ta bi don ta sada ta da wajen saboda tana kiran wayar Jidda ba a ɗauka kuɓa ta ganta a kan kujara. Tana tahowa tun daba ɗan nesa ta fara hangen ya filin wasan da yake a zagaye, sanye suke da kayan ƴan ball riga mai dogon hannu wandon ma dogo kanta da hula saɓanin shi da ba shi da hula yellow ne kayan sai ratsin fari a jiki kala iri ɗaya Jidda ce da Ibrahim yana riƙe da ball ɗin ya ɗaga ta sama ita kuma tana ta ƙoƙarin sai ta karɓa idan ya riƙe a hannun dama tana zuwa wajen hannun dama sai ya ga ta raja,a da hannun damar ta kusa kamowa sai ya yi saurin mayarwa hannu dama suna ta yin abin cikin nishaɗi. Sosai ran Aliya ya hau ɓaci domin da ta ga inda ake soyayya ruwa ruwa mai cike da tsantsar kulawa, amma ita ta kasa nutsuwa ma bare ta zauna a nata gidan kullum cikinnya za ta rusa rayuwar wasu ta gina tata.

Ta jima tana kallonsu ganin Ibrahim ya ɗago zai kalli inda take da sauri ta laɓe ta ci gaba da leƙo su. Sai da aka jima sai ga su sun taho hannunsu cikin na juna, sai dai wannan lokacin Jidda ta ɗorw hijabi a kan kayan. Kasancewar ba ta son fitar da jiki kuma gidan yana da ma,aikata maza duk da inda suke idan har suna can babu ma mai yin hanyar wajen sannan ta inda suke bi ma ta can cikin gidan ne. Ta gaban Aliya da take laɓe a korido suka wuce wani irin ni,imtaccen ƙamshi ya bugi hancin ta, suna wucewa ta doka uban tsaki dama su ba su ma lira da ita ba. Jim kaɗan ta biyo bayansu lokacin da ta zo falon sun haye sama Jiddar ta haɗa masa ruwan wanka sai ta sakko za ta je ɗakinta a nan ne ta samu Aliya. Da sauri ta rungume Aliya tana mata oyoyi iya ma Aliyar tana mayar mata da mrtanin dariyat da iyakarsa fatar baki.

Bayan sun gaisa ta ce za ta je ta watsa ruwa kasancewar wasan motsa jikin fa suka yi, nan take taɓbayar Aliyar ma ya aka yi ba ta mata waya ba da ta zo sai ta ce ai ta kora wayar ba a ɗauka ba sai dai ba ta faɗa mata cewa ta je ta gansu suna cikin wasa suna nishaɗi ba.

Ɗakin da ta shiga yin wankan ba a can ne Aliya za ta yi nata aikin ba, don haka jim kaɗan ta tashi ta ajiye jakarta tana fatan wanna Sauden mai shegen rawar kai kar ta dawo ɓangaren har ta gama abin da za ta yi. Ko da ta je ta buɗe ƙofar ɗakin cikin sanɗa ta tabbatar Jiddar tana wankan domin ta ji ƙaran ruwa da sauri ta rufo mata ƙofar ta fito tana waige-waige irin na marar gaskiya. Ta buɗe ɗakin ɗaya ta shige ta rufo ganamta yana faɗuwa tana fatan dacewa da abin da ta je nema.

Aliya zuciyarta ba ta huta ba tana ta kai kawo wajen buga mata gabanta yana faɗuwa, zuciyarta cike da ƙiyayya da hassadata buɗe drower ta shiga dubawa amma ba ta gani ba.

A zuciyarta ta ce

'Wannan karon Jidda har dukiyarki sai ƙiyayyata ta taɓa ta wato ke mai son rai ba za ki iya ba mahaifiyata kuɗi ba saboda ba uwar da ta haifeki ba ce, to ai in laila ta ƙiya sai a koma caca' Ɗayar drower ta buɗe nan ma babu sai da ta buɗe ƙaramar lokar ƙasan drower ta can ƙasa sannan ta ga abin da take neman domin Jidda ranar nan suna hira a kan tanadi Aliya tana cewa ita ba ta da tanadi Jiddar ta fi ta, sai Jiddar take cewa ni kam ina da tanadi yanzu duk abu mai muhimmanci wajen da nake ajiyarsa da ban, komai wajensa nake ware masa ke hatta ɗankunnenayena ma,ajinsu daban. Wannan ya sa Aliya yjn dogon nazari tana buɗe lokar sai ga wani ƙaramin akwati mai kyau yana sheƙi da sauri ta buɗe sai ga sarƙoƙin Jidda.


Shagala ta yi da kallonsu tana tunanin ba don Umma ta ce kar a ɗauki set ba da babu abin da zai sanya ta ɗauki zobe kaɗai. Sai da ta duba wani mai ɗan girma yana ɗauki da harafin J a jiki wayo farkon sunan Jidda ta ɗauka da sauti ta mayar da ɗan kir ɗin ta rufe lokar ta ɓoye zoben, da sauri ta shiga banɗaki ta ɗan taɓa tuwa alamar ta shiga banɗaki, sannan ta daidaita nutsuwarta ta fito, a daidai nan Ibrahim yana sakkowa daga saman sanye da ƙananan kaya.

Haɗe rai ya yi ota kuma ta sha jinin jikinta har tana rayawa a ranta ko ya gane ta yi wani abi a ɗakin Jiffar na rashin gaskiya, haka dai ta dauri tana ɗan ƙirƙirar murmushi ta gaishe shi kamar ba zai amsa ba sai kuma ya amsa yana mai buɗe ƙofa ya fita. Bayansa ta bi da kallo tana sauke ajiyar zuciya a fili tabbas ba ƙarya Ibrahim ga haɗu a duk lokacin da za ta yi tozali da shi sai ta ji wani itin sonsa da ƙaunarsa. Yana fita kamar haɗin baki Jidda tana fitowa sanye da wata abaya mai kyau.

Lemo da kofi ta ɗakkowa Aliya wacce ba ta da nutsuwar shan wani lemo ma kawai so take ta tafi sai dai ba zai yiwu ba tun da dai yanzu tana fita sai an ɗarsa zargi a kanta duk da ta san Jidda ba za ta zarge ta ba amma dai maganin kar a yi kar a fara. Tana shan lemo suna gaisawa lokacib ne Saude da Jidda ta kira a waya ta zo ɗaiki da tire da aka jera kwanuka a ka ta ajiye tare da gaishe da Aliyar a raine sai dai Jidda ba ta lura ba tun da tana latsa waya lokacin ita kuma da ido ta mata kallon rainin tana taɓe baki, sosai abin ya yi wa Aliya ciwo sai dai ta zargi ko dai Sauden ta san abin da take aikatawa ne sai kuma ta kawar da zargin. Tana rayawa a ranta akwai ranar ramuwar gayya wacce ta fi ta gayya zafi.

Ta ɗaga kofin lemon za ta kurɓa lokacin ne Jidda ta ce

",Ƴar uwa albishirinki" Aliya ta ce

"Goro" A takaice, Jidda cike da fara,a ta ce

"Allah ya yi zan taka ƙasa mai tsarki" Ƙwaruwa Aliya ta yi saboda baƙinciki domin maganar ta zo mata a bazata, sai da Jidda take buga mata bayanta tana kera mata sannu sannn ta samu tarin ya lafa zuciyarta ta cika da baƙincikin da har ta kasa yin furucin komai, tana jin wani tuƙuƙin baƙincikin wai Jidda ce za ta shiga jirgi ta bar ƙasa ta je makka.

Dakyar ta taushi zuciyarta ta nuna mata farincikin da iyakarsa fatar baki, amma zuciyartw baƙiƙƙirin. Nan Jiddar take faɗa mata har sun jr an yi mata passport amma umra ce za su je ita da mahaifan Ibrahim dama Daddy ne da Mummy za su je, sai Mummy ta ce sai an tafi da ita domin shi Ibrahim yana da aiki a office ban da shi za a je shi sai hajji za su je tare da Jiddar. Shi sai ba ya ma son tafiyar nan don sai ya ji ko kaɗan ba ya son Jidda ta yi nesa da shi, ga shi da yawan buƙata iya kuma ba ta gajiyawa da biya masa buƙatarsa.


Sosai Aliyar ta nuna rashin jin daɗin rashin faɗa musu da Jidda ba ta yi ba sai lokacin take faɗa mata dama yau zuwan da za ta yi gidanta don ta faɗa mata ne ba ta zo ta faɗa mata a waya, nan take cewa sai da dare ma za ta je gidan Ibrahjm zai kaita ta faɗawa su Abba.


Sai dab da magriba ta tafi shi ma dakyar ta daure saboda ba ta son ta tafi da wuri kawai sai take ganin kamar dai za a gane akwai wani abun kuma kawai zarguwa ne, dama bahaushe ya ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Jidda shiryawa ta yi da suka yi sallar magriba suka tafi ya kaita gida don faɗawa su Abba domin saura kwana huɗu su tafi.



Umma ta yi baƙinciki sai dai haka ta daure tana ta sakin dariyar yaƙe Abba kuwa sai godiya yake jerawa Ibrahim ɗin don ya ji matuƙar farinciki. Umma dama da Aliya ta kira ta ta faɗa mata don ba ta bi ta gida ba da ta dawo daga gidan Jiddar saboda magriba ta gabatota san dole za su haɗu da Abba.


Washe gari da Umma da Aliya suka tafi kasuwa bayan Abba ya tafi kasuwa hala shi ma Kasim. Ko da suka kai zoben ba a saya ba duk inda suka je sai a ce sai sun kawo risit ɗin. Sun taka waje kusan bakwai amma duk inda suka je amsar ɗaya ce don kpwa sai ya ce ba zai saya ba in babu shaida domin kar su saya abin sata, duk da rantse rantse da su Umma suka sha yi a wurare da dama kan cewar gobara suka yj da daɗewa ya ƙone risit ɗin, amma sai a ce musu ai da sun koma wajen wanda suka saya sun masa bayani ya rubuta musu wani.


Haka suka gaji da yawo suka koma gida rai babu daɗi .Washe gari ma haka, sai da suka gaji da yawo a kasuwa har wajen ƙarfe ɗaya sannan suka haɗu da wata mata ta ce ita ta san inda za ta raka su a saya don shi mutum hatta kayan sata saya yake kua har yau dubunsa ba ta cika an kama shi ba, tashin farko da suka ji kuɗin sun tsorata domin cewa ya yi miliyan biyu da dubu ɗari da naira dubu uku. Haka ya karɓa ya transper suka tafi suna murna da sharaɗin ko da wani abu ya ka je ya zo karki su kuskura su ambaci sunansa don ya gane alamomin rashin gaskiya a tare da su daga ganin yadda suka razana da kuɗin zoben ya fahimci ba mallakinsu ba ne. Kuma shi ma a hakan ma ya musu zururun dubu ɗari biyar.

Cike da farinciki suka koma Umma ta wuce gida ita ma Aliya ta wuce nata gidan, suka ce sa ƙarasa maganar a waya don dama a akawun ɗin Aliya aka tura kuɗin.


A ranar da su Jidda suka tashi a ranat nr su Umma suka samu labarin wani hamshaƙin boka da ƙawar Umma ta musu jagora. Sun sha baƙar wahala wajen zuwa kasancewar a cikin surƙuƙin daji yake sannan gidansa a kan wani dutse.Bayan an basu izini sun shiga nan ya kwashe abin da yake tafe da su ya faɗa musu ya ce domin an sanar da shi zuwansu da kuma abin da yake tafe da su.

Ya ce zai yi aikin amma da sharaɗin Aliya za ta bashi kanta, sun razana da lamarin buƙatar bokan, sai ƙawar Ummar take mata alama ta amince domin hakan zai sa burinsu ya cika. Sai Umma ta ce sai dai ita ta bashi kanta amma boka ya ce ai sharaɗin a kan Aliya yake don ita ce wacce za a yi wa aikin idan kuma ba za su amince ba su ɗauki takalmansa su bar masa gida. Aliya jin an cr aikinsa kamar yankan wuƙa yake hakan ya sa ta ce kawai ta amince don a neman duniyar da take zuciyarta ta ƙeƙashe ji take komai ma za ta iya sannan tana ganin cewa ba kanta farau ba kuma ba za a ƙare a kanta ba, ta sha jin ana cewa mata da dama sai sun bada jikinsu a wajen boka wa,iyazubillah. Ita kanta zina ba a ɗauke ta a bakin komai ba yanzu a wannan zamanin ba ga ƴanmata ba, ba ga matan auren ba ba ga mazan auren ba sai wanda Allah ya tsallakar amma akwai wanda ko yatsunsu ba sa bari wanda ba muharraminsu ba ya taɓa kuma duk lalaewat zamani ba za su saɓaw Allah ba.


Umma da ƙawarta waje suka fita Aliya suka shiga can cikin ɗakin da bokan yana faɗin aikin da za a yi yana daga cikin wannan sharaɗin in har ta yarda a lokacin da yake tarayya da ita ne zai fara aikinsa. Haka suka yarda da ƙaryarsa ba su san cewa babu wano aiki da zai yi da wannan tarayyar ba kawai ƙishirwarsa yake kashewa da mata mararsa kamun kai masu neman duniyar wanda suka manta cewa komai suka samu a duniyar za su bar shi, hatta ɗankunne ko zobe ba za su shiga kabari da shi ba daga su sai likkafani sannan duk abin da suka saɓawa Allah sai an azabtar da su, da yawa ana mantawa da makoma ne.

Sai da ya gama watsewarsa da Aliya wacce ta manta matsayinta na matar aure, sannan ita kanta zina ko baka da aure haramun ce kusantar ta ma Allah cewa ya yi kar a yi. Sun dawo yana ta washe bakin garaɓasar da ya samu. Ya ce sai bayan kwana bakwai za su dawo. Sai da aka yi kwana bakwai sannan suka kwaso ƙafa suka zo, sai dai ranar su biyu suma zo babi waccrn ƙawar ta Umma da ta rako su, dama ƙawarta ce da suka zauna unguwa ɗaya malotan gidan su Umma ce. A ranar da suka dawo ranar ne ta cika kwana biyar da mutuwa kuma lafiya ƙalau kawai ƙarar kwana ta yanke jiki ya faɗi sai gawarta. Wannan kaɗai bai fahimtar da su cewa duniyar ba za a tabbata a cikinta ba.


A waje ya ce Umma ta dakata zai yi wa Aliyar bayani nan Umma ta fita ta zauna saga gefen dandazon mstan da suke zaune dodo guda suna jiran zuwan layinsu, don su kaiwa boka buƙatarsu zuciyoyinsu sun karkata ga kaiwa wanin Allah buƙatarsu da faɗa masa damuwarsu sun manta Allah kaɗai yake maganin matsala da damuwa wajensa kaɗai ake samun biyan buƙata.

Yana fita boka ya ɗakko wata ƴar kwalba ya ce

"Wannan kwalbar maganin ciki za ki samu abinci ko na sha ki zuba masa a ciki" Idanu Aliya ta zaro jin wani baban lamati don ba ta manta tababar da ta sha wajen sauya cokali ba, amma sai ta amsa da cewa to.

Ya ci gaba da faɗin
"Wannan maganin idan kin tabbatar ya cj abin da kika saka maganin ko ya sha sai ki saka a ƙasanki sannan ki shafa wannan turaren " Ya faɗa yana miƙa mata. Karɓa ta yi tana jiran ƙarin bayani ya ce

"Idan ya sha abin shan duk inda mace take burinsa ya yi tarayya da ita kinnga ke kuma kina nan to za ki yi duk yadda za ki yi tun da kin ce matarsa ba ta ƙasar ma"

Aliya cike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login