Showing 117001 words to 120000 words out of 178828 words

Chapter 40 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt

18 Dec 2025

1443

abin da take lokacin da ta kawo kai kicjn ɗin, mamaki ne ya kama Saude dalilin murna da kuma dariyar a kan ganin cokali Aliya kuma da ta ga mutum sai kawai gabanta ya faɗi don bata ma gama tantancewa cewa Saude ba ce duk tunaninta Jidda ce ta dawo bata san lokacin da ta ɓoye cokalin a baynta ba wanna ya sanya wani abu ya ɗarsu a zuciyar Saudr tun da ba yarinya ba ce budurwa cenza ta yi shekara sha buyar zuwa sha shida.


Aliya kuma da ta dawo hayyacjnta daga duniyar tsoron ta ga Saude ce ta doke tsaki ta ce

"Wai uban mene ne kike diddiftu a kicin ɗin nan?" Saude ta ce

Dama Baba Kuluwa ce ta ce mura take ba za ta iya shan ruwa mai sanyi ba na canjo mata" Aliya ta ce

"Aikin banza da wofi duk samun wuri kuka yi wallahi da wasu ƴan aiki ne za a ba ruwan roba in ban da asarar abu bakwa shan ruwan famfo, ai duk laifin Jidda ne ni akwai wani ɗan aiki da zai saki jiki in na dawo gidan nan" Sai da ta yi furucin ta gane wautar da ta yi don dama tana nufin idan ta dawo gidan da aure wato bayan ta auri Ibrahim, ita kum Saude sai ta fara tunanin in ta dawo gidan yaushe? Maganar da Aliya ta yi ta cire mata shakkun tunani ta hanyar faɗin

,"Idan na dawo gidan nan watarana in Jidda ta haihu na zo zaman wanka" Tana faɗar hakan Saude ta mayar da ruwan ta ɗauki marar sanyi ta yi tafiyar ta ita kuma Aliya ta fito da sauri ta dawo falon ta bule jakarta ta saka cokalin.

Ranta fari ƙal har ta fara hango ta a wannan haɗaɗɗan gidan tana baza capacity tana zuba tashin mutunci don daga dangi har sangin dangiro sai sun san bata da mutunci musamman mutane makwaɗaita za su ɗanɗana kuɗarsu.

Jiida kuwa dakyar ta samu ya yi cokali biyu ta bashi maganin da ya sha sai bacci ya ɗauke shi plates ɗin abincin ta ɗakko ta fito ta rufe masa ƙofa ta sauko ƙasa. Nan suka zauna suna hira sai Aliya take cewa Umma ta kira a waya ta ce a bata lokacin tana sama, kiran Ummar Jidda ta yi Umma cike da fara,a amma ta ciki na ciki ya hau magana da Jidda cike da nuna soyayya ta ƙarya. Bayan sun gama ta ce ta gaishe da Abba suka yj samma Umma tana jin kamar ta shaƙo Jiddar daba cikin wayar.

Wajen ƙarfe biyu da wani abu Aliya ta ce tafiya za ta yi Jidda ta ce ta bari a yi la,asar amma ta ce tana so ta je ta yi girki saboda Kasim ya kira ta ya ce da wuri zai zo nan Jidda ta ma rasa mai za ta bata don daɗi haka ta je ta samu lece da atamfa ta zuba mata a leda Aliya sai godiya take haka ta rako ta bakin ƙofa sai Aliya ta ce

"Kai jama,a talaka ya shiga uku wallahi aka bar mutum da kuɗin adaidaita sahu kaɗai ma sai ya kashewa mutum gwiwar zumunci" Jidda cike da tausayawa ta ce

"Ayya karki karaya ai shi zumunci hanya ce ra shiga aljanna sannan duk wanda ya yanke shi Allah zai yanke shi daga rahmarsa, bari na saka direba ya kaiki gidan...

Tun kafin ta kai ƙarshen zancen Aliya ta ce

"Lah ki bari kawai na biya adaidaitan" Ta faɗa tana juyawa za ta tafi sai Jidda ta ce

"Bari na saka miki a acc sai ki biya shi" Ta faɗa tana komawa ta ɗakko wayar sai ta tura mata dubu ashirin ta ce ta yi wani abu da canjin tun da ko jiya Mummy dubu ɗari biyu ta turo mata. Godiya Aliya ta yi suka yi sallama ta zo ta wuce mai gadi yana mata a sauka lafiya ko kallonsa bata yi ba ta buɗe ƙofa ta fice a zuciyarta ta ce

'Duk ranar da na auri Ibrahim ka tabbata ruwan shanka ya ƙare!' Ta faɗa tana duba alert ɗin da Jidda ta mata na dubu ashirin tana cewa a fili

"Matsiyaciya kin biya kuɗin aikin da za a yi a fatattka tsakaninki da mijin naki a sama mini gurbin zama"


Ko da ta dawo gida ta shiga kiran Amatullahi tana bata labari sai dai Amatullahi ta ce gobe su je su kai cokalin amma kuma ba a gobe za a kai cokalin gidan Jiddar ba saboda kar ta zargin wani abu na zuwa gidan a jere a kwana kusa. Bayan sun gama ta kira Umma tana zayyana mata ƙusurinsu na fitar da Jidda daga gidan da kuma samawa Aliya gurbin zama Ibrahim ya auri ta. Buɗar bakin Umma ta ce


"Kun yi min daidai ƴan albarka ubangiji ya muku albarka ke da Amatullahi ƙawar arziƙi, ai duk wanda ya ci tuwo da mu miya ya sha dole a fitar da Jidda daga gidan wannan idan ma har hakan ba zai iyu ba sai dai ke ki shiga a rufewa kowa baki hatta uban naku sai an rufe masa baki ruff in ya so sai ta rayu cikin uƙuba a gidan ta zama da ita da babu duk ɗaya da samuwarta da rashinta duk ɗaya!" Umma ta faɗa tana tunano irin yadda za ta baza capacity idan ta zama sirikar Ibrahim babu abin da take so irin ta ga Aliya a gidan nan da ake ta bada labari.

Bata ƙara bi ta kan Ibrahim ba sai ta tattara shi ta ajiye bata sake kiransa a waya ko masa saƙon whatsapp ba, tun da dai tana ganin aski ya zo gaban goshi, saura ƙiris ta koma gidansa sannan a matsayin matarsa.

Washe gari bata tambayi Kasim fita ba sai kawai ta bari da ya fita Amatullahi ta kira a waya ta faɗa mata su haɗu a marabar bamin titin suna haɗuwa suka tafi, ko da suka kai wa bokanya cokalin ta shafa wani magani ta ringa wani siddabaro tana ambaton sunan Ibrahim. Da ta gama ta ɗakko wani jan ƙyalle da baƙi ta ajiye a gefe ta shafa wani magani da mai sai kuma ta saka baƙin ƙyallan ta goge cokalin sannan ta saka jan ta ƙara gogewa sai da ya dawo tass sannan ta miƙawa Aliya ta ce

"Karɓi da ƙafarki ta hagu" Haka Aliya gabanta yana faɗuwa ta miƙa ƙafar hagu bokanya ta saƙala mata cokali ta ce

"Sai kuma ki ɗauke shi daga ƙafar taki da hannun dama" Haka Aliya ta aikata sai bokanya ta ce


"Kamar yadda ƙafar hagu take a gefe hannun dama a gefe basu haɗa hanya ba to idan Ibrahim ya ci abinci da cokalin nan haka zai yi gabas Jidda ta yi yamma, ba zai sake kallonta da idon soyayya ko idon rahma ba babu wacce zai so sai ke kaɗai!". Bakin Aliya kamar ƙofar gari wani daɗi da sanyi ya ziyarce ta har ta fara hango yadda za ta yi idan ta shiga gidan naira saboda da butulci ma ko da ta sauke idanunta a kan Amatullahi a zuciyarta ta ce

'Sai dai ki yi haƙuri Amatullahi idan na shiga daula zan sallame ki da kuɗi masu kauri sai dai dole na sauyaki a matsayin ƙawa don babu ni babu ƙawa da talaka ko hanya ba za mu haɗa ba, sai dai na samu matan masu kuɗi kuma mata masu aji, sannan ma ke barazana ce ga shiga ta gidan Ibrahim kar watarana faɗa ya haɗomu ki tona mini asiri!'


Aliya ta ce

"Bokanya kuma batun toshiyar baki fa mahaifina ba zai taɓa bari na auri mijin Jidda ba, sannan mutanen gari za su zargi wani abu uwa uba mijin Kasim ban san ya zai sake ni ba!" Da wata dariya bokanya ta bushe mai ban haushi ta jima tana dariyar kafin daga bisani ta haɗe rai tamkar bata taɓa yin dariya ba ta ce

"Wannan aikin da aka miki na cokali ya haɗa komai da kowa, babu wanda zai buɗi baki ya ce din me, babu wanda zai yi musu kuma Kasim a take kina ambata takardar saki zai baki shi ma mahaifinki ba zai tambayi dalilin wani auren ba ko dalilin mutuwar auren naki, sannan ruwanki ne ki bari ki yi idda kuma ruwanki ne ki yarda a ɗaura auren a ranar da aikin ya afku, sannan Jidda in kin ce ya sake ta ba zai yi musu ba kuma in kin ga dama zaki iya barinta a gidan kike gana mata uƙuba!" Sosai ta ji daɗi sai murmushi suke dokawa ita da Amatullahi don sun dara jin ƙamshian nasara.

Sun sanar da ita saboda taka tsantsan za su bari sai bayan kwana biyu Aliyar ta je gidan Jidda saboda kar su zargi wani abu, bokanya ta ce ko shekara ɗari za su yi babu matsala kawai dai a tabbatar Ibrahim ya yi amfani da cokalin. Dubu sha biyar ta karɓa kuɗin aiki Aliya tana jaddada mata sai sun dawo kawo mata gagarumar kyauta idan aiki ya ci!. Daga nan basu zame ko ina ba sai ƙyamis ta saya ƙwayar hana haihuwa pills don ta ce kar tsautsayi ya sa cikin Kasim ya shiga gwara ta fara planning don haihuwa sai a gidan Ibrahim.

Ko da ta dawo gida Kasim bai dawo ba don haka ta samu waje ta ɓoye cokalin da take jin tamkar da bugun numfashinta yake rayuwa!.

Bayan kwana biyu ta kira Jidda ta ce gata nan za ta kawo mata ziyara wai Kasim ne ya yi tafiya zai raka abokinsa wani gari ɗaurin auren yayan abokin kuma yance kwana zai yi don garin da nisa hakan ya sa ta ji kaɗaici ya ishe ta za ta je ta wuni, Jidda ta ji daɗi kuma bata kawo komai a ranta ba.

Bayan ta je gidan Jidda wajen sha biyu na rana, suna ta hidimar girki tare Aliya tana maƙale da jakarta mai ɗauki da cokalin siddabaru. Har aka gama abinci bata ga Jidda ta zuba na Kasim ba kawai su Saude ta kwasawa a ƙaton fulas, ta ɗauka musu ita da Aliya. Suna cin abinci ta ce

"Ni ina mai gidan kuwa" Ta tambaya gudun kar ta ce ina abincin sa din marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, nan Jidda ta sanar da ita yana office yance yana da aiki da yawa ba zai dawo ba sai ƙarfe biyar.

Bayan sun yi sallar la,asar Jidda ta zauna ta yi azkar ɗin maraice kamar yadda take yj kullum safe da yamma domin kariya daga dukkan sharri. Bayan ta idar ta shiga kicin ta fara ɗora tukunyar tuwon shinkafa da mai gidan ya ce ta masa da miyar agushi Aliya tana falo a kwance tana ta charting ita kuma Jidda suna kicin ita da Saude sai Baba Kulu da ta zo ta yi goge -goge ta fita.

Sai da ta kammala komai Saude tana taimaka mata da miƙa mata abin da ta buƙata na amfani. Bayan sun gama ta ɗora masa a kan dinning ta ɗakko plate da cokali ta ajiye da saving spoon ta bar Saude tana gyara kicin ɗin tare da wanke abubuwan da suka ɓata. Aliya ta ce a ƙoshr take ba za ta ci tuwon ba tun da basu daɗe da cin abincin ba, ranta dai fari ƙal tana murna don ta je ɗakko ruwa a frige ta hangi cokalin da aka ajiye masa sak wanda aka mata magani a jiki kenan ko ta sauya ba za a gane ba.


Hatta Jidda sai da ta fahimci Aliya tana cikin farinciki.

Lokacin da ya dawo Aliya ta gaishe shi ya amsa cikin sakin fuska har yana tambayar Aliya mai gidan nata, ba komai ya sa ta saki fuska ba sai Jidda da ta masa magana ranar nan ta ce bata ji daɗin yadda ya amsawa ƴarnuwarta gaisuwa a daƙile ba, hakan ya sa ya karɓi kuskurensa shi kuma kawai ra,ayin Aliya ne ba ya yi.

Sai da ya yi wanka ya shirya da kayan da ta fitar masa sannan ya ce ta zo ta ɗakko masa abincin a sama zai ci, a daidai lokacin Aliya kuma ta fito da cokalin tana shirin zuwa ta sauya sai kawai ta ga Jidda kamar an jefo ta hakan ya sa ta wayince bata sanin bata taki sa,a ba sai da ta ga Jidda ta ɗauki kwanon miya da plate mai ɗauke da cokolan ta haura sama da su.

Har sai da ta yi ƙwallah don takaici, jim kaɗai sai ga Jidda ta sakko tana cewa bari ta watsa ruwa tana sanar da ita yanzu za ta fito sai ta fito ma za ta zubawa Ibrahim abinci hakan yana nuni da ba za ta daɗe a banɗakin ba. A can sama kuma bayan ta kai masa abincin sai ta samu ya buɗe system yana ɗan wani abu hakan ya sa ya ce kar ta zuba abincin bari ya ɗan kammala sai ta ce za ta sauka ta watsa ruwa sannan ya gama sai ta zo ta zuba masa. Aliya tana zaune jugum abin duniya ya haɗe mata goma da ashirin sai kawai ta hangi Ibrahim ya sakko da waya a kare a kunnensa yana cewa

"Wallahi na manta shi gani yanzu zan duba amma dai kamar na taho da shi daga office, yana buɗe ƙofa ya fita Aliya ta tsam ta tashi tsaye gabanta yana tsananta faɗuwa da sauri ta yi hanyar bedroom ɗin da Jidda ta shiga ta je ta kara kunne a jikin ƙkfar ɗakin tana iya jiyo ƙaran ruwan da take wankan, da sassafa ta fara haura saman tana haɗa matakala biyu, don ta saka a ranta sai ta sauya cokalin nan a yau!


Idan kuna comment tabbas za a ke posting a kan lokaci amma ku ci gaba da karantawa wasu suna yi wasu suna yin ɗifffff ni ma sai in ke ɗiɗifffff😃

MAMAN AFRAH
. 09025576222







https://chat.whatsapp.com/DsxFGh957C5EvfrSjJDdgO?mode=wwt



*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)


NA


MAMAN AFRAH


. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 2️⃣2️⃣



ALIYA

Da tsananin faɗuwar gaba ta ƙarasa hawa saman benen ko fargabar ɗaya daga cikinsu bata yi ya zo ya ganta. Sai da ta gama hawa ta je ta rasa ma wace ƙofa ce za ta buɗe inda za ta ga inda aka ajiye abincin ta canja cokalin tana rarraba ido duk ta rikice burinta kawai ta aikata abin da fa kawo ta sai dai bata san ya za ya yi abin ya tabbata ba tare da wata matsala ta biyo bayan hakan ba.
A hanzarce ta yi hanyar ƙofar ɗaya ta tura ta shige saboda ƙarfin hali har da karo ƙofar sai dai kash sai bayan ta shiga ta gane ba ɗakin da take nema ba ne don babu alamar wani abinci a ɗakin.Da sauri ta fito tana ta tunanin rashin nuysuwar da take da shi wanda ya sa bata gane inda za ta shiga ba sai dai ta san dama ba za ta samu nutsuwa ba saboda kawai tunaninta ya ta,allaƙa ne ga samun cikar burinta wato canja cokalin ne kawai a gabanta wanda take tunanin daga shi burinta na duniya ya cika.

Ɗaya ƙofar ta tura a nan ne wani farinciki ya baibaye zuciyarte, domin tana buɗewa ta yi arba da system da kayan abincin da Jidda ta kai sannan uwa uba cokalin da yake kan plate ɗin tabbas shi ne dai wanda bokanyan ta yi aiki a kansa, wani daɗi ne ya ziyarci zuciyar Aliya maimakon ma ta yi abin da ya kaita sai ta tsaya ta ƙarea ɗakin kallo tana ƙiyasta nan da wasu kwanaki da basu taka kara sun karya ba ɗakin zai zama ya dawo ƙarƙashinta wato ita take iko da shi.
Ƙarasawa ta yi ta tsugunna a gaban plate ɗin ta saka hannu ta ɗauke cokalin kan plate ɗin ta ɗora na hannunta wanda ta zo da shi, sannan sai ta ɗaga bra ɗinta ta saka wanda ta ɗauke wancan ɗin. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta samun nasara.

Baki ta taɓe tana tashi tsaye har hango ta take yi tana zuba ƙasaita sai motar da ta ga dama kuma ta yi ra,ayi za a ta shiga hatta dangi da ƴan uwan Ibrahim ɗin ma kansa sai sun dawo ƙarƙashinta. Dama Abba ne matsalarta to gashi an ce aikin da aka yi mai gabaɗaya ne wato kowa da kowa.

A zuciyarta ta ce

"Uhmm Aliya rufawa kanki asiri ki koma ƙasa ki zauna ki naɗe ƙafa kamar baki motsa daga wajen ba, tun da dai Allah ya ida nufi kin canja cokalin' Ta faɗa tana zuwa ta miƙa hannu za ta buɗe ƙofar, kamar abin almara kawai sai ta fara jiyo ƙaran takun takalmi alamar ana hayowa saman, idanu ta zaro ƙirjinta yana fatfat waiga bayanta ta yi tana jin faɗuwar gabanta yana tsananta a take ta shiga tunanin waye a cikinsu yake ƙoƙarin hayowa saman shin Jidda ce ko kuma shi mai gabaɗayan ne wato Ibrahim.

A fili kuma a hankali ta furta
"Na shiga uku asirina yana dab da tonuwa" Ta faɗa tana haɗiye wani yawu muƙut.
Tunani ta fara shin idan Ibrahim ne ya same ta a ɗakin nan wane zargi zai yi mata da wane idon ma za ta kalle shi ko da a ce a saman ya same ta ba ma a ɗakin ba mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login