Showing 156001 words to 159000 words out of 178828 words

Chapter 53 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt

18 Dec 2025

1460

ba a san inda ya faɗi ba.


Bayan sun shiga gidan suka zauna suna mayar da yadda aka yi, a nan Momi tana nunawa Meenal kuskurenta na yin maganar kuɗi a gaban wasu tun da ta lura maganar kuɗin ce ta ankarar da su akwai kuɗin a atare da su, shi ya sa ake so mutum ya kama bakinsa idan ya je wajen da bai san mutane ba, tun da ba a goshin mutum za a rubuta waye shi ba, idan mugu ne ko akasin hakan.


Ruwan zafi Momi ta dafa suka yi wanka sannan suka ci abinci suna maganar za su koma wajen bokan don cim ma manufarsu domin ba su daddara da abin da ya faru ba, hakan ya san Meenal ta ce akwai wasu kuɗaɗe da za su shigo mata da zarat sun shigo za su koma, Momi ma da yakr zuciyar a bushe take ta goya mata baya.

Sai da Nasir ya dawo daga kasuwa ta biya suka ya ɗakko ta. Tana shigowa gidan ganin Sadiya tana shanya kafa ta aika mata saƙon mugun kallo, abin mamaki sai Sadiya ta ji Nasir ya yi sallama, amsawa ta yi ta juyo tana masa sannunda zuwa ya amsa da fuska a sake, yana tambayar ta Kalifa ta ce yana ɗaki yana wasa, maimakon ya shige ɗakin Meenal sai Meenal ta ga ya juya da ledojin hannunsa ya nufi ɗakin Sadiyar.

Gaban Meenal ne ya faɗi a take ta shigar zargin ko dai da saka hannun Sadiya a rugujwar shirin da suka yi yau, wani ɓangarr na zuciyarta yana zargin ko dai Sadiya ta je tanyi wani abu ne da har Nasir ya kula ta yau.

Abin da Meenal ba ta sani ba shi ne wani maƙocin Nasir ne a kasuwa suke tattaunawa a kan yana gobe zai kai matansa kasuwa za su yi sayayya kowacce ta zaɓi abin da ranta yake so, a nan maƙocin yake cewa

"Ina tsoron shanyewar rabin jikina a ranar
ƙiyama shi ya sa ba na nuna bambanci a cikin matana, ko da a ce ba zan iya daidaita matsayi da soyayarsu a zuciyata ba tun da dama Allah ba ya amfani da fifikon soyayyar a zuciya kawai adalci ne na zahiri shi ya sa nake ƙoƙarin kiyayewa" Wannan furucin ne ya sa Nasir ya tuna rashin adalcin da yake yi wa Sadiya hakan ya sa ya ɗan sakko domin ya mata adalcin ko da kaɗan ne ba da yawa ba, sai dai ita Sadiya ganin abin da Nasir ya yi bai ba ta mamaki ba domin ta san tana kai kukan ta wajen ubangiji don haka ta san addu,ar ta ce ta fara karɓuwa.

Tana gama shanyar ta nufi ɗakinta. Meenal tun da ta ga ya kama hanyar ɗakin Sadiya sai ranta ya hau suya, dakyar ta yi yaƙi da zuciyarta ta shiga ɗakinta, shi ma don kar Sadiya ta gane ainihin ta razana da alamarin duk da an ce labarin zuciya a tamabayi fuska!.


Tana shiga ɗakin ta yi jifa da mayafin Momi wanda ta sako don hatta kayan jikinta na Momin ne har takalmi. Da sauri ta shiga leƙo tsakar gidan don ganin abin da yake wakana, ganin Sadiya ta nufi ɗakinta da turtsetsen cikin ta sai ta ji zuciyarta tana zafi. Safa da marwa ta fara a tsakar ɗakin tana son kiransa a waya ta tamabaye shi wannan sabon salon fa, sai dai tunowa da crwa ɓarayi sun yi sama da faɗi da wayar sai ta rungumi na annabawa.

Ta kasa zaune da tsaye gabaɗaya ba ta da nutsuwa tana ganin wannan raini ne yake ao ya ja mata. A ɓangaren Sadiya ko da ta shiga ɗakin ɗauke da sallamaa bakinta, tana shiga ta ganshi zaune a kusa da Kalifa ya buɗe masa biskit ɗin da ya fito da shi daga leda wanda dama shi ya siyowa, yaron sai murna yake yana ta taɓa jikin Nasir ɗin ganin yau bai kyamace shi ba, kuma bai dakatar da shi ba daga taɓa shi sannan bai haɗe masa fuska ba, uwa uba har da biskit ya siyo masa, sannan yana ta biya shi suna magana duk da gwarancin maganar ta shi ba komai ne ake fahimta ba.

Ranta ta ji ya yi wani sanyi, tana kallon Kalifa da tausaywa shi ma ga shi yau ya samu ƴanci irin na sauran yara da suke samu a wajen mahaifinsu, shi ma yau yana ta dariya da farinciki sai ta ji gabaɗaya laifukan Nasir sun wanke daga idanunta duk da dama ba ta sakawa a zuciyarta amma dai ta san yana mata laifi. A rayuwa tana so a ce ko da ita ba ta samu komai ana kulawa ba to tana son ƴaƴanta su samu hakan zai rage raɗaɗi.

Kalifa ya kalle ta ya ce

"Momma kalli Abba ya siyo mini biskit" Ya faɗa yana ɗago mata biskit ɗin fuskarsa a washe, har ƙwalla idanunta suka tara ganinncewa yaro ma ya san kyautatawa bare kuma babba.

Murmushi ta yi masa, sai ya taho yana ɗakko guda ɗaya ya nufi bakinta hakan ya sa ta buɗe bakin ta gutsuwa, shi kuma Nasir sai yake kallonsu yana murmushi. Allah kaɗai ya san yadda Sadiya take ji a ranta abu ne da suka rasa a iya zamansu a gidan amma yau rana ɗaya ga shi sun samu wannan yake nuni da cewa mahaƙurci mawadaci!.

Sannu da zuwa ta ƙara masa ya amsa yana murmushi, leda ɗaya ya ɗakko ya miƙa mata ta karma da hannu biyu. Kallonsa ta yi ta ce

"Za ka yi wanka?"

Ya ce

"Akwai ruwa mai ɗumi?"

,Ta ce

"Eh akwai" Ta faɗa masa don ta cika filas ɗin shayin, ruwan wanka ta je ta haɗa masa ya tashi ya je ya yi wanka ya yi alwala ya fito.
Bayan ya shafa mai dama kayan jikinsa ya mayar kasancewar babu kayansa a ɗakin duk suna ɗakin Meenal shi turakar tasa ma dama ba zama yake a ciki ba kawai ɗakin Meenal ne yake zuwa. Bai ce mata komai ba sai ta ga ya fito falon ya ɗauki ɗaya ledar da ya ajiye a gefe ya juya zai fita sai Kalifa ya bi bayansa abin mamaki sai ta ga ya kama hannun Kalifan sun fita.

Gabaɗaya ta yi ɗiff tana ta mamakin abun kamar a mafarki. Ɗakin Meenal ya nufa yana shiga lokacin tana banɗaki, ledar ya ajiye a kan madubi, ya buɗe drower kayansa ya ɗakko kayansa lodi guda ya fito Kalifan yana biye da shi, kayansa gogaggu wajen kala goma ya shigo ɗakin da su, yana shigowa ta tashi ta karɓa, ta nufi bedroom don saka masa a drower. Yana bata ya ƙara komawa hannunsa riƙe da na Kalifa jallabiyarsa ya ɗakko guda uku, har lokacin Meenal ba ta fito ba, ita kuma ta ji shigowarsa domin ta ji motsi sai dai ta san shi ne ya shigo tana son sai ta gama abin da take ta fito ta zo ta sauke masa ruwan masifa.


Ba ta zaci kaya yake ɗauka ba, lokacin da yake shirin fita daga ɗakin yana riƙe da kayan da hannu ɗaya ɗaya hannun ya riƙe Kalifa sai kawai ta buɗe banɗakin ta fito, tana fitowa ta yi mugun gani da sauri har tana neman faɗuwa ta nufo shi ta ce


"Nasir mene ne nake gani haka?" Ta faɗa ranta a ɓace.

Yana ɗan murmushi ya ce

"A ina fa?"
A gadarance ta ce

"Oh ni kake tambaya? Baka ga ko da muka shigo gidan nan ban sake saka ka a idanuna ba, sai yanzu ka shigo kuma yanzun ma kana shirin fita,wannan kayan fa ko na bayarwa ne"

Ɗan jim ya yi sai ya ce

"Yau a ɗakin Sadiya na sauka" Duk da ta san hakan amma yadda ya furta sai abin ya mata ciwo, hakan ya sa ta ce

"Mai kake nufi? Ba dai rabon kwana za ka fara mana ni da ita ba?"

Ya ce

"A,a kawai dai ita ma zan kwana a ɗakinnta ne...

Ta katse masa hanzari da faɗin

"Kar ma ka fara wallahi"

Bai jira cewar ta ba ya juya ya bar ra a tsaye kamar ta rafka ihu tsabar takaici haka ta ji, wani tsaki ta duka tana juyawa ta yi ido huɗu da ledar kan mudubin ba ta yi wata-wata ba ta ɗauka ta yi wurgi da ita kayan ciki suka tarwatse.

Ko da ya koma ɗakin bedroom ya shiganya sauya kayan jikinsa ya fito da jallabiya a jikinsa ya ce mata zai je masallaci ta ce masa sai ya dawo, yana fita Meenal ta jiyo rufowar ƙofar gida hakan ya ba ta tabbacin ya fita da sauri ta fito har tana tuntuɓe a barandar ƙofar ɗakinta, ta ji yadda yatsanta na ƙafa ya bugu amma ba ta damu da zugin da yake mata ba, burinta ta shiga ɗakin Sadiya.

Sadiya tana bedroom tana linke kayan da ya cire a lokacin Meenal ta faɗo falon ko sallama babu ta, Kalifa yana ganin shigowarta ya tashi yana riƙe da alrwar tsinkensa ya kama hanyar bedroom a kiɗime don shi tsoronta yake. Sadiya tana ganinsa ta hau faɗin mene ne hankali tashe don ta yi zaton Nasir ɗin ne ya dawo ya zare masa ido tun da Nasir ɗin ma da ba ya sakar masa fuska tsoronsa yake. Kafin ya bata amsa ya riƙe ta sai ta jiyo muryar Meenal tana faɗin

"Kai ina uwar taka take?" Sadiya ta gane da ita take kuma ta fahimci ita Kalifa ya gani ya gudo amma sai ta ba falon ajiyarta, hakan yansa abin ya ƙonawa Meenal rai ganin ta ƙi fitowa. Murya ta ɗage ta ce

"To baƙar munafuka idan ma wani ƙulle-ƙule kika yj kika shiga tsakanina da shi ki sani na fi ƙarfin zama bora a gidan miji" Jin haka sai Sadiya ta fito tsabar ma ta ƙonawa Meenal rai sai ta fito hannunta riƙe da gajeran wandon Nasir da take linkewa wanda ya cire ta ce


"Shiga tsakani kuma? Kin taɓa gani an shiga tsakanin mace da miji? Kenan ni da ba ya zuwa ɗakina shiga tsakanina kika yi da shi?" Tambayar rainin wayon nan ta ƙara hasala Meenal har ta fara tunanin yaushe Sadiya ta yi baki? Ganin gajeran wandonsa a hannunta ya yi wa Meenal zafi a zuciya, tana ganjn kenan har Sadiya ta fara samun ƴancin taɓa gajeran wandon Nasir bayan tin daga lokacin da ta zo gidan hatta suturarsa ta bar ɗakin nata.

Cike da kashedi ta ce

"Ki sani wannan abin da kika yi tamkar shuka ne a idon makwarwa, kuma ina sanar da ke ni da Nasir nan gani nan bari farar tumfafiya, da sannu zai dawo gareni yadda zai zamana sama ta yi wa yaro nisa sai dai ya tada kai ua yi kallo"

Baki Sadiya ta taɓe ta ce

"Kanki ake ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya" Tana faɗar hakan ta juya ta shige ɗaki, dana a can ta bar Kalifa don bai biyo ta ba, Meenal ganin Sadiya ta barta a faɗo wato ta mayat da ita kamar mahaukaciya, hakan ya sa ta ji takaici wata zuciyar tana raya mata cewa kamar ita wannan marar galihun za ta faɗawa magana ta tafi ta barta a tsaye a wajen.

Jiki babu ƙwari ta juya fuuuu ta fita suka ci karo da Nasir da shigowarsa gidan kenan ya mata kallon mamakin ganin ta daga ɗakin Sadiya ya ce

"Lafiya dai kika fito daga ɗakinta a fusace ni fa ba na son gutsiri tsoma ki kama kankj" Da yatsa ta nuna kanta tana faɗin

"Ni kake faɗawa hakan Nasir tabbas na yarda ba a hayyacinka kake ba an fi ƙarfika" ,Bai ce mata uffan ba ya raɓa ta ya shige ɗakin ya barta shanye a wajen, baki ta dantse da haƙori idanunta suna cikowa da ruwan takaici, tana kissima sai ta turbuɗe tauraron Sadiya da ya farw haske a zuciyar Nasir sai ta san yadda ta yi ta ƙwace komai ya dawo hannun ta fiye da baya.

Ko da ta koma ɗakinta dakyar da iya yin sallah tana ta tunanin Alhajin da ya mata alƙawarin kuɗi idan ya tura mata ma ta ina za ta gani ita ba da waya gare ta ba, duk sai ta ji ta raina kanta yau ɗaya rana da Nasir zai kwana ba a ɗakinta ba tana ganin hakan kaɓar gazawarta ne a ce mijinta ya koma hannun matar da take ganin ba ta da aji fa kimar da za ta yi gogayya da ita wajen haɗa miji, duk kuwa da cewar ita Sadiyar ita ce ta fara auren Nasir ɗin.

Sadiya wainar fulawa ya ce mata yana son ya ci haka ta masa ta kawo masa ya ci ya sha shayi mai kauri wanda Sadiyar ta haɗa masa da kayan shayinta da take saya.

Ganin yau a ɗakinta yake kuma bata shirya hakan ba duk da ita dama ba ta tsark da ruwan sanyi tun da ta san tsarki da ruwan zafi yana haɗe mace sannan yana hana ciwon sanyi infection samun wurin zama a wajen macen da take amfani da ruwan zafin wajen tsarki. Hakan yana sa mace ta kasance koyaushe a haɗe, saɓanin ruwan sanyj da yake buɗa mace sanann sanyi ya samu wajen zama inda shi kansa sanyi yakan saka mace ta zama a buɗe sannan ko da ta yi amfani da maganin mata ba ta ganin alfanu saboda cutar sanyin.

Yana nan zaune a falon yana danna waya Kalifa yana zaune a wajensa, ta ɗauki pure water ta shiga ɗakin da kofi da cokali ta tsakure dakan ni,ima na maman afrah ta zuba ta haɗa da madara ta ɗaga kofin ta shanye, wata ƴar roba ta ɗauka ta buɗe ta fito da ƙwallon dabino ta ɗauki guda huɗu ta rufe robar ta mayar ta fito daga ɗakin tana riƙe da kofin, kaskon turaren wuta ta ɗauka ta ɗakko gwarwashi ta haɗa kanamfari da ƙwallon dabinon ta je banɗaki ta zuba su a garwashin ta tsugunna. Sosai ta ji ya mayar da ita kamar sabuwar budurwa duk da dama Sadiya mace ce wacce tamkar ba ta haihu ba.


Bayan ya dawo daga masallacin isha,i lokacin Kalifa ya yi bacci, ya tarar ta masa shimfiɗa a falo ta ɗaura masa net, ita kuma tana sanye da wata figigiyar rigar bacci da bai taɓa ganinta da ita ba gabaɗaya rigar ta bi ilahirin jikinta ta manne kallo ɗaya ya mata ya luka duniyar ƙaunar kasancewa da ita.

Sun ƙule a ɗakin yana mata hira ƙasa ƙasa duk sai ta ji abun banbarakwai wai namiji da suna Hajara. A wannan lokacin ne Meenal ta zo ƙofar ɗakin da suka ryfe take bugawa tamkar za ta ɓalla, haka ya taso ya fito sanye da gajeran wando ko singlet babu ransa a matuƙar ɓace domin da kawo masa tsaiko a lamarinsa da Sadiya da yake jin tamkar yau ne ranar farko da zai kasance tare da ita ko don an daɗe ba a haɗu ba.

Ta windown ya tambaye ta ba,asin zuwanta da kiransa, ta ce magana take so ta yi da shi, shi kuma ya ce ba zai samu dama ba sai gobe, haka ta koma ranta yana ƙuna, tana kissma mummunan ƙuduri a zuciyarta.

Sosai ya ji sauyi game da Sadiya don shi kansa ya sani Sadiya ta da ban ce a cikin mata ta fita da ban ko da kuwa mata dubu ya tara!.

Washe gari ko da su Hibba suka zo girkin safe, ranar sun gama tsara yadda za a ke yi su da Hajiya cewa yanzu su daina bari sai abin da Meenal ta ɗauka musu suna zuwa suna zama da yunwa kawai suke ɗaukan dankalin a ɓoye, soai suka ji daɗin shawarar nan tun da suna ganin ai ɗan uwansu ne yake siya ba ita ba, kuma har mahaifiyarsa za a ci.

Lokacin da suka zo sun yi mamakin ganin yayan nasu ya fito daga ɓangaren Sadiya, sannan sai suka ga Meenal tana cika tana batsewa, ko da ta ɗauka musu ɗanyen dankalin ɗaki ta koma hakan ya sa suka samu damar ƙara ɗanyen dankalin a ɓoye suka ƙara fiƙewa suka yayyanka suka shiga kicin. Soyawa suka yi tare da soya wainar ƙwan. Ledar da Hajiya ta bayar Hibba ta fito da ita daga aljihun rigarta suka kwashi dankalin da wainar mai yawa sai ƴar dariya suke a ɓoye suna jin daɗin yau za su ci dankali ya ishe su. Bayan sun gama Husna ta je ƙofar falon Meenal ta ce sun gama ta daɗe kafin ta fito a shelaƙe tana wani taɓe baki tana shan ƙamshi.


Kicin ɗin ta je ta ɗauka musu dankalin ko waina ba ta saka musu ba haka kuma ta ƙi tsakura musu kayan shayin. Fulas ɗin ta kinkima don yau ita kaɗai za ta ci ba ta niyyar ba Nasir tun da ya kwana a ɗakin Sadiya. Sun fito za su tafi lokacin tana dab da hawa barandar ɗakin ta, kamar wanda aka ce ta juya haka ta juya sai kuwa idanunta suka sauka a kan aljihun doguwar rigar Hibba da ya yi tudu, hakan ya sa ta kafa ayar tambaya don ta san ita dai lokacin da suka zo ba ta ga wata alama ba a jikin ta.

Sai dai ba ta taɓa kawowa cewa dankali ba ne ita ta fara tunanin ko a kayan kicin ɗin ta ne suka ɗauki wani abun za su fara mata zari ɗai-ɗai. Murya ta buɗe ta ce

"Ke Hibba ku dakata!".

Cak!. Suka tsaya suna jiran tsamani domin ita Hibba har ta fara ƴar karkarwa don dama ƴan magana sun ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Fulas ɗin hannunta ta ajiye ta tunkaro su, tana zuwa ta ce


"Mai kika ɗauka min a kicin?"

Husna ce ta yi ƙarfin halin yin magana domin ta ga Hibba tana neman bayyana lamarin ta yanayinta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login