Showing 87001 words to 90000 words out of 178828 words

Chapter 30 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt

18 Dec 2025

1450

ya shiga kiran Kasim don jin ba a sin yadda aka yi ya bar matarsa sabuwar amaryar kwana ɗaya tak ta tafi gida, tun da wannan abu ko shi ne aka yi wa ƴarsa hakan ba zai ji daɗi ba don wannan abin kunya ne abin takaici ka kai ƴa ɗakin miji ta dawo gida.

Kasim da yake shirin fitowa daga shagon nan kiran Babansa ya katse masa hanzari yana ɗagawa Babansa ya ce

"Kasim mene ne dalilin da ya sa ka bar matarka ta taho gida? Kai baka mata bayanin cewa tun kana ƙarami aka maka tiyata cewa kai ba mata maza ba ne kuma mata maza suna iya rayuwa kamar kowa su haihu kamar kowa, sannan suna da dama kamar kowa ba?" Baban Kasim da ya katse gaisuwar da Kasim yake kawo masa ya faɗa cike fa hargagi har Babar Kasim da take kicin ta jiyo abin da yake faɗa, hakan ya sa gabanta yankewa fa faɗi a nata ganin ta aurar da ɗan nata amma kuma wata wutar tashin hankali yana tunkaro su. Kasim a take ya ji bakinsa ya bushe wani tashin hankali ya saukar masa maimakon ya ba Babansa amsar tambayar da ya masa sai ya ce

"Gani nan zuwa Baba" Baban nasa kuwa ya yanke kiran, shi kuma Kasim ya yi hakan ne son kawo ƙarshen maganar saboda yana mamaki da tantamar anya Aliya ta tafi gida kuwa? Tun da ya san a gidan ya barta.

A rikice ya yi cikin gidan yana ƙwala mata kira, amma shiru ko ƙutarta bai gani ba banɗaki ya nufa amma bai ganta ba, kicin ma haka duk da ba ya saka ran ganin ta a kicin ɗin saboda ya san babu abin da za ta je yi, yana komawa ɗaki da ya je bedroom a nan ya tabbatar da maganar Babansa don ya ga alamar hargitsa kaya da Aliya ta yi.

Bai yi wata-wata ba ya fito daga gidan sai da ya zo ƙofar gida ya tuna bai ɗakko mukulli ba ya koma ya ɗakko ya fito yana cikin datsewa ya ji wani yana cewa
"Ango ka sha ƙamshi" Yana juyawa ya ga wani abokinsa ne, hannu kawai ya iya ɗaga masa ya tsare mashin ya hau don ya lura idan ya tsaya zai iya gane ba ya cikin hayyacinsa. Suna cikin tafiya kiran Babansa ya shigo yana ɗagawa Baban nasa ya ce

"Kasim ka zo gidan Abba muna can" Gabansa ne ya hau dakan lugude yana fatan kar wannan zaman da za a yi a saka ya warware igiyar aurensa da Aliya.





SADIYA
Da kamar ta nufi gidan Kaka amma sai ta daure ta ƙarasa gidan, tana zuwa sai ta ga babu mukulli a ƙofar gidan mamaki ya kama ta kenan mai yake a gidan bai fita ba ko dai ya dawo daga kasuwar ne ko kuma mene ne dalili da wannan saƙe-saƙe ta shiga gidan tana jin babu daɗi a ranta na wunin ranar yau bata sayar da kayan sana'ar ta ba bayan ta saba kama kuɗaɗenta. Tana shigowa ta fara sallama amma shiru ba a amsa ba sai dai ta ga takalminsa a ƙofar ɗakin sai da ta yi sau uku amma babu alamar zai amsa haka ta shigo ta ɗaga labaulen falon ta shigo dama Kalifa bacci yake a bayanta a ranta tana raya ko ina motar tasa kuma tub da baya ganta a ƙofar gida ba.

Ko da ta shiga ɗakin yana gaban madubi yana idaidaita hula a kansa amma ko kallo bata isheksa ba, kamar dai ba a yi ruwanta a wajen ba. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi wanda take fatan hakan ya narkar da takaicin da yake danƙare a ƙirjinta. Ta ɗan daure ta ce

"Barka da yamma" Bai amsa ba illa ya saki hular tasa ya riƙe ta da hannu ɗaya saɓanin lokacin da ta shigo hannuwansa biyu suka riƙe suke da hular, ɗaya hannun marar hular ya yi amfani da shi wajen ɗaga mata hannu alamar ta dakata hakan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru tana kallon ikon Allah duk da bata san dalilin dakatar da ita ɗin ba. Ya kusa minti huɗu yana daidaita hular har sai da ya ga ta masa yadda yake so ita kuma tana jira ta ji abin da zai ce. Da ya gama gyara hulae bai juyo ba yana kallon madubi sai da suka hala ido ta cikin madubin ta ji ya ce

"Ki daina kalle mata kwalliyar" Cike da mamakin furucinta da kuma rashin sanin inda maganar ta dosa sai kuma ya ce

"Na ji kina mini barka da yamma ke ai ya kamata a yi wa barka ko?" Da nuna alamar tambaya a fuskaryta ta ce


"Ban gane ba barkar mai?" Ya ce

"Barkar dawowa ɗakin ki mana, ai nan Baba ya kirani a waya yana ta bani haƙuri, na ce bari na tambayi Meenal ɗin in ta haƙura sai ki dawo" Har sai da idanunta suka ciko da ƙwallah tsabar ɗacin da maganar ta mata wato dai Baba ya zubar mata da mutunci da kima a ce ya kaita gida amma saboda ta zauna a gidan aure yake bada haƙuri gashi yanzu ya ja mata raini har ana mata barka da dawowa ɗakinta, wato ta ga samu da ta rashi ɗan kawar da kai gefe ta yi tana danne abin da ta ji ta ce

"Allah sarki Baba yana son ƴaƴansa su yi zaman aure ne ai sannan mutum ne mai son zaman lafiya ba ya son tashin hankali shi ya sa ya zaɓi ya bada haƙuri a kan ciccira magana" Ta ce tana jin kamar mai.

Wata ƴar dariya ya yi wacce ta yi kama sa ta yi kama da ta raninin hankali ya ce

"Allah ko?" Bata tanka masa ba ta zaɓi ta bar ɗakin don ta ga abin cin fuska ne. Tana dab da fita daga ɗakin ya ce

"Da farko na dakatar da ke ne da kika min mafana saboda ina saka hula bana so ta karkarce kin san idan za a yi wa amarya kwalliya abin a tsara ne don a birge ta" Murmushi ta yi ta ce

"Wannan gaskiya ne" Bai jira ta ce wani abu ba ya ce

"Na ce kina kalle mata kwalliyae ne saboda ta ce mini kar in bar ƴan mata su kalle mata ni" Maganar ta ɓata mata rai amma sai ta zaɓi mayar da martani cikin ruwan sanyi ta ce

"To ai ƴanmata ta ce ka ga bata ce har matarka ba kenan matarka ta fi damar ta kalle ka don halaliyarka ce" Tana faɗa ta juya ta fita. Shi kuma ya murmusa don yana ganin Baba ya ƙara bashi damar wulaƙanta ta tun da yana nuna dole sai ta zauna a gidan, tun da yana faɗa masa sauran ƙannenanta suna nan babu mashinshi ni.

Tana zuwa falon ta sauke Kalifa ta ɗora a kan kujera ta fara shirin gyara gidan, sallamar wata yarinya da ta zo siyan manja ya sa ta fito daga ɗakin ta je ta bata ta dawo, tsintsiya ta ɗakko bayan ta kunna gawayi don yin tuwon dare. Fitowarsa daga ɗaki yana buɗaɗa ƙamshi ita shaddar ma kanta aabuwa ce dal yau ya fara sakawa hatta hula da agogon duk sabbi ne yadda kayan ya masa kyau tamkar ranar ɗaurin aure kamar abin arziƙi ya ce

"Sadiya baki tambaye ni ina mota ta ba" Murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce

"Na ga bata waje to tunanina ko ka ba wani ne ɗani" Ta faɗa cikin zolaya. Washe baki ya yi ya ce

"Kamar kin sani kuwa ai Meenal ce suka karɓa aro ita da ƙawarta za a koyawa Meenal ɗin mota" Ɗan jim ta yi tana tunanin ba ya ma gudun matsala sai ta ce

"Ma sha Allah, Allah ya tsare ya sa a koya a sa'a" Da amib ya amsa yana saka takalmi ya fita a daidai lokacin kuma suka ji ƙaran tsayuwar motar ya waiwayo yana cewa

"Kin ji ƴan halak suna dawo" Ita dai bata amsa masa ba ganin ya zama wani sauna a kan mace duk don ya ga bata nuna damuwa a kan lamuransa shi ya sa har yake faɗa mata komai ya zo bakinsa yana ganin ba za ta ji ciwo ba.


Yana fita ya rufo ƙofar Sadiya ta cire takalmi ta yi saɗaf-saɗaf ta je zauren ta shiga leƙawa daga wata ƙaranar tulla da take jikin ƙofar, tana ganin lokacin da suka fito daga motar wata farar budurwa wacce fuskarta har wani jaja take saboda bikicin ita ce ta fito daga mazaunin direba ita kuma Meenal ɗin daga mazaunan mai zamana banza. Suna ta dariya shi kuma ya harɗe hannu a ƙirji yana ta kallonsu, Meenal ta zunɓura baki tana magana cikin ɓaci ta ce


"Ka ga ko, ta kusa jefa maka ni a kwata" Ƙawar tana dariya ta ce

"Ka ji ni da mata za ta min sharri wai ni ce ma zan jefa ta a kwata to ita ce ta kusa jefa mu a wata ƙatuwar kwata, ɗazu ma kaɗan ta kaɗe wani tsoho" Gabaɗaya aka yi dariya, kafin ita ƙawar ta shiga baya ita kuma Meenal ta shiga gaba shi kuma ya shiga ya tada motar da yake a jiki ta bar mukullin, haka suka bar layin duk abin da suke a kan idanun Sadiya sai da suka tafi ta juyo ta dawo cikin gidan ta fara aikin gabanta.



Yau saura sati ɗaya biki Nasir duk ya mayar da hankaki kwacakwam kan lamarin bikinsa sai hidima yake daga shi har su Hajiya da ƙannensa tamkar dai wannan ne karon farko da zai taɓa aure. Duk da Hajiyar ta faɗawa Sadiya cewa su a wurinsu wannan ne auren fari da Nasir ɗin zai yi, kuma wannan ne auren da suke gani za su yi biki na kece raini, maganganu maarar sa kai da ƙafa dai Sadiya ta ji su sai dai tana toshe kunnuwanta ta yi kamar ba ta ji ba, saboda Hajiya ita tana ikirarin biki biyu za ta yi wato ɓangaren amarya da na ango abin ta tuwona maina.

Tun da aka zo aka yi jere ake ta kulle ƙofofin ɓangaren amarya, sannan duk wanda zai shigo gidan cikin nuna halin ko in kuka yake ga Sadiya hatta gogan yanzu ta rasa kansa da ƙafarsa babu wani abu da yake shiga tsakaninsu ba ya cin abincin gidan kwata-kwata sannan idan ya fita ma wani lokacin sai dare. Ita yanzu ko ya zo ma baya yake juya mata a kan gadon, domin ta lura gabaɗaya zumuɗin son kasancewa da sabuwar amarya yake ɗibansa, komai ya mayar da shi ga amarya, ana saura kwana biyu ɗaurin aure ya haɗa kayayyakinsa ya kwashe rabi da kwata ya kai ɗakin amarya, duk wasu abubuwa na amfaninsa to ya mayar ɗakin amarya, tamkar dai cewa aka yi ita Sadiyar ba matarsa ba ce duk da ayyukansa ya nuna cewa da alamar hakan amma dai ita ta bashi lokaci.


Ko naira biyar bai bata ba a matsayinta na uwar gida bare ta saka ran wani kayan da ake yi wa uwar gidan duk da malamai suna ganin hakan ba wajabci ba ne sai dai sun faɗa hakan kyautatawa ce sannan kowace rai tana son a kyautata mata amma Sadiya bata samu hakan ba. Ita ma ganin da kuɗinta hakan bai wani dame ta ba, tun gabatowar bikin a littafin maman afrah ruɓaɓɓiyar igiya ta ɗauki lambarta ta kira ta ta faɗa mata tana son atamfofi lokacin ana saura kwana biyar biki ne. Nana maman afrah ta ce ta mata magana ta whatsapp ta tura mata atamfa da les da takalmi da jaka, sai kayan Kalifa kala biyu ta bata acc no ta saka kuɗi sai ga mai napep ya kira ta a waya ya ta faɗa masa unguwar ya kawo mata, sun yi kyau sosai kamar yadda ta gansu a hoto haka suke shi ne ta bayar aka mata ɗinki. Sai aka mata buɗaɗɗe kasancewar tsufan da cikinta ya yi.


Ko bayan ya kwashe kayansa daga ɗakin tana gyara masa drowersa ta ga ya ajiye wasu magunguna na maza hakan ya sa ta gane tanadin amarya ne murmushi ta yi abinta tana musu fatan wanyewa lafiya.


A ɓangaren amarya Meenal kuwa ta saya magungunan mata ciki kuwa har da wani na matsi mai suna gamgam wanda take fatan ma dawo mata da budurcinta ba tare da angon nata ya farga cewar ta yi fatali da mutuncin da ake fata da burin kowace mace ta kai gidan miji.


Yau za a kawo amarya bayan an yi gagarumin bikin kece raini kamar yadda Hajiya ta buƙata, Sadiya ma ta yi ɗan taro na maƙota da ƙwayenta, ta saka atamfarta poplin da ta ɗinka da yake ɗinkin doguwar riga ne sai ya mata cif abinta. Dirin tsayuwar motoci a ƙofar gidan ya ankarar da kowa ƙarasowar amarya, kasancewar akwai nepa, ife-ifen yara da guɗar manya ita ce ta karaɗe unguwar, sai yi suke suna maimaitawa Sadiya da ta fara jin faɗuwar gaba ta shiga ambaton hasbunallahu wa ni'imal wakil, ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagisu aslihli sha,ani kullahu wala takilni ila nafsi ɗarfata ain.


Haka suka shigo kamar da gayya suna ƙara guɗa, su kuma maƙoa suka shiga musu sannu da zuwa amma sai suke yi wa Sadiya da mutanenta kallon ƙasƙanci. Babu wansa ya ƙara tanka musu, suka nufi sashen amarya. Bayan kowa ya watse an yi wa Sadiya sallama tare da bata haƙuri hatta wasu saga cikin ƙannenta ma sun zo.

Zaune take a falo da kankana a gabanta wacce ta ɗakko daga frige lokacin Kalifa ya yi bacci, tana cikin sha ta ji tsayuwar mota jim kaɗan ta ji shigowar Nasir da abokansa suna sallama, ita ce ta amsa kasancewar part ɗinta ya fi kusa da ƙofae gidan. Sai dai da suka shigo babu wanda ya nufi inda take suka yi ɓangaren amarya. Zuwa can ta ji fitowarsu tana jin tashin muryoyin ƴanmata hakan ya bata tabbacin ƙawayen amarya ne. Bayan sun fita sai kuma ta ji dawowar Nasir shi kaɗai don ta ji lokacin da ya garƙama sakata a gidan, sannan kuma da safe da ta je gyara masa drower ta ga duk ya kwashe magungunnsa, hakan ya bata tabbacin za a kwashi amarci a daren yau!.

Shiru-shiru ko zai shigo ya mata sallama, ko kuma ya kawo mata ɗan abin taɓawa da wasu mazan suke siyowa har uwar gida, duk da bata saka rai ba amma bai kai mata komai ba, sannan bai kawo amarya ya haɗa su ba, wannan ya ƙara tabbatar mata za a yi wani zama a cikin gidan. Babu zato da tsammani sai jin ƙaran rufo ƙofar falon amarya ta yi.

*Ga link nan wansa yakemson shiga adashen kayan sallah ya shiga zubi duk sati 3k idan ka gama zubi sai ka karɓi kayan da ka zaɓa, in kin san ba yi za ki yi ba karki shiga min grp*

Ko a shiga grp ko min magana ta wtsapp


MAMAN AFRAH
09025576222






[11/15, 12:55 PM] 😍: *RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)


NA


MAMAN AFRAH


. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 1️⃣8️⃣


AMARYA MEENAL

Tun da aka watse gabanta yake ta faman dukan tara -tara domin abin ya ma zarce dukan uku-uku tunaninta guda ɗaya shi ne, kar a je Nasir ya fahimci sirrin da take ganin ta haƙa rami ta binne wato ya gane ɗanyen aiki da ta yi wa tinƙahon kowacce mace wanda ake fata da burin ta kai ga mijinta na sunna amma ita tuni ta ɓarar da wannan damar a titi. Sannan fargabar ma bata wuce cewa shi Nasir yana mata kallon mutuniyar kirki sannan mahaifiyarsa tana mata kallin mai ladabi da biyayyar da har suke ganin ta zarta uwar gidansa Sadiya bayan duk abin da suke zato ba haka ba ne.
Yanzu ta fi mayar da hankali ga cewar an ƙare lafiya ita da Nasir a daren faekon nan ba tare da ya fahimci cewa an masa riga malam masallaci a abin da yake ɗoki da zumuɗin samun a daren farko a wajen amaryarsa. Duk da ta san da wuya gyara ya yi kamar sabo amma dai an bata tabbacin abubuwan da ta yi amfani da su Nasir ba zai taɓa gane ita ba cikakkiyar budurwa ba ce, sannan uwa uba wani magani da za ta yi amfanu da shi wajwn daƙile masa wannan tunanin duk ƙwawa da ƙwaƙwarsa bai isa ya yi wannan tunanin ba, dole ko ya yi yunƙurin hakan abin ba zai yi ba. Tana zaune bakin gado abin duniya goma da ashirin ya kwaɓe mata sai saƙa da warwara take, jin lokacin da ya turo ƙofar falon tare da mayarwa ya rufe, tabbas gabanta ya bada sautin rasss ta yadda daƙyar ta iya saita kanta yadda ba zai fahimci yadda jikinta take karkarwa ba,duk da an ce marar gaskiya ko a cikin ruwa gumi yake amma dai za ta yi ƙoƙarin wajen daƙile wannan karin maganr na bahaushe ba tare da hakan ya faru ba don ba za ta taɓa barin Nasir ya gane ba.

Yanayin sallamarsa da ya yi zuwa bedroom ɗin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login