Showing 150001 words to 153000 words out of 178828 words

Chapter 51 - RUWA CIKIN COKALI COMPELET BOOK BY MAMAN AFRAH.txt

18 Dec 2025

1464

ta ga ledar ma iska ta matsar da ita daga kusa da ita ta yi can gefe guda. Kukan takaici ne na zuci wannn da ya fi na fili ciwo ya kufce mata, don tabbatar an kuma mace ta haifi mace wato asara dai ta wannan aikin ma an yi ta kamar yadda aka yi asarar aikin cokali, yanzu abu ɗaya ya rage mata yadda gawar za ta sake ta.

Addu,a ta fara son karantowa don ta ga yanzu ita kaɗaice ta rage mata amma addu,ar ta kasa ambatawa ko da a zuciya ne domin dama ba ta da ƙarfin gwiwar furtawa a fili.




BABA

Hankali tashe yake kallon yadda hayaƙi yake biyowa daga cikin store ɗin nasa wanda ya tabbatar da cewa karkaf kayan amfanjnsa ne a cikin ɗakin wannan abin daidai yake da karayar arziƙinsa a cewarsa kenan hakan ya sa ya takarkare ya zandama ihun da kowa na gidan sai da ya fito a sukwane domin yanayin yadda ya yi ihun tamkar wanda aka daɓawa wuƙa a ƙirji.

Ganin abin da yake faruwa sai kowa ya yi turus suna ganin wuta tana ci tamkar wanda aka kunna ta, Baba kuma sai miƙa hannu yake kamar mai neman sadaka duk ya gigice dama ga shi mai sarewa a kan abu barw kuma wannan yana gani ƙiri-ƙiri wuta tana cin store ɗin nashi da yake ji da shi wanda hatta iyalansa yana musu ƙauro. Zaman dirshan ya yi yana kuka wiwi tamkar an ce masa Kaka ce mahaifiyarsa ta mutu. Hafsat ce ta yi waje tana cewa.

"Gobara jama,a a kawo ɗauki" Lokacin har Mama Habiba da Mamar Sadiya sun fara ɗakko ruwa suna watsawa don yanzu hatta ƙofar ɗakin ta cinye. Samari ne suka shigo gidan wanda suke zaune a ƙofar gidan aka shigo ana ta zubawa wutar ruwa dakyar aka samu ta mutu, sai dai gabaɗaya ta ƙone komai na ɗakin ƙurmus. Samarin nan suna ta jajantawa Baba gobarar amma sai faɗi yake

"Ku kawo ɗauki jama,a na taiyace na talauce wayyo ni" Ganin kamar ba a hayyacjnsa ba y a yake suka jajantawa matan gidan suka tafi sama gabaɗaya cikin ƴaƴan babu wacce ta taimaka wajen kashe wutae kafin samarin su zo su ma matan daga Mama Habiba saj Mamar Sadiya ne kawai suka kaiwa wutar ɗauki.

Mamar Sadiya da Mama Habiba ya ce

"Habiba ke da Talatuwa ku zo ku kamani ku kaini ɗaki, na ga ku ne kuka fi tausayina ku ne kaɗai kuka kaiwa wutar nan ɗauki, sauran kamar ma farinciki suke da faruwar hakan" Haka suka zo suna masa kama-kama duk ya saki jiki sai sharɓar kuka yake, sai da suna dab da shiga ɗakinsa kawai sai ya zauna kamar wanda aka turo ya kifa uban tagumi yana cewa

"Wayyo hatsina wayyo shinkafata da na san wannan ƙaddarar za fa faɗa musu da na daɗe da kaiku kasuwa na karɓi kuɗina" ,Ya faɗa yana face hanci.

Mama Habiba ta ce

"Haba Malam ina kake so ka kai imaninka ne ai baka da tsumi ko dabara a kan hakan, tun da Allah ne kaɗai ya san abin da zai faru haka za ka rungumi ƙaddara...

Ko ƙarasawa bata yi ba ya hayayyaƙo ta da masifa yana faɗin


"Saboda ba kayanki ba ne ko, shi ya sa ma kuke nuna bai dame ku ba, na lura kamar ma ni kaɗai abin ya dama ban da lalacewar zamani a ce mace kadarar mijinki ta ƙone amma babu wacce cikin ku ta matse hawaye ko da ba na gaskiya ba ne, a ƙalla a kowacce ko da kukan kissa ne ta yi na ƙarya ai na ɗan ji daɗi amma kowacce fuskarta washe kamar gonar auduga ni kaɗai nake shan kuka da takaicina" Kallon kallo aka shiga tsakanin Mama Talatuwa da Mama Habiba ganin shi tsaninsa da Allah yana so su taya shi kuka a kan kayan abincin da sai ranar da ya ga dama yake ciyar da su, Mama Sa,ade da Mama Bilki kuwa dama tuni suka ba banza ajiyarsa kowacce tana ɗakinta haka ma ƴaƴan.


Mama Talatuwa ta ce

"Malam ko mu yi kuka ko kar mu yi wannan ƙaddarar ba mu isa mu kankar ta ba, kai da Allah ya tseratar da kai da iyalanka babu wanda wutar ta ƙone ai an ci ta varka, baka ga ko gidan jaje aka je ba idan iya dukiya ko amfani wuta ta ci ba har barka ake yi wa mutum saboda ba ƙaramar ni,ima ba ce saboda ubangiji yana iya yin komai amma ya tsayar iya haka wato ya taƙaita"

Yana kallon ta da jajayen idanunsa ya ce

"Barka fa? Kika ce a yi barka to duk wanda ya tako gidan nan ya yi mini barka sai ya cire masa ƙafa" Mama Habiba ta ce

" Kenan baka godewa Allah da wannan abin da ya maka ba, da ka gode masa sai ya dawo maka da abin da ka rasa ta inda baka yi zato b... Kafin ta ƙarasa ya ce

",Rufe mini baki Habiba ai ina ga ma ke ce kika mini baki, da kika zo riƙona in bada abinci a dafa baki da kuɗin da za ki sayi abin da za ki ce wataƙila ma sanadinki ne gobaear ta kama, ni ban san ma wace jarabar ce ta sa nae zaune da ke ba har yau Habiba, to mace ke dai ba haihuwa kike ba sannan kawai dai ni ne nake ciyar da ke don haka kawai ina ga zan hukunta ki...

Mama Talatuwa ta katse shi da sauri da faɗin

"Haba Malam kaima ka san wannan dai son zuciya ne kawai ka yarda da ƙaddara saj ka samu sauƙi a zuciyarka, amma wannan zargi ne kake hakan kuma zai saka maka kokwanto a zuciyarka baka yarda da ƙaddarar da Allah ya aiko...

Ƙasa ya dafa ya miƙe tsaye duk da ƙafafunsa karkarwa suke saboda gabaɗaya abin da ya faru ya ruɗa shi.

Da yatsa ya nuna Mama Talatuwa ya ce

"Idan akwai shegen da zai faɗa min yadda zan yi a rayuwata sai in gani, don haka ni nake da damar yin abin da na so a lokacib da na so"

Mama Habiba tun maganar da ya faɗa ta gorin da ya mata hawaye ya daɗe da wanke mata fuska a zuciyarta tana addu,ar Allah ya bata haihuwa watarana, Baba ya kalle ta ya ce

"Habiba ki je na yanke igiya ɗaya daga cikin igiyoyin da suke tsakanina da ke" Mama Habiba ta ɗago fuskarta sharkaf da hawaye ta ce

"Tohm Malam ina roƙon Allah ya sa haka ya zama mafi alkairi a garemu" ,Bai tanka mata ba sai Mama Talatuwa da tar rafka salati, ita kuma Mama Bilki da take jiyo abin da suke daga ɗakinta ta leƙo ta tsaya a ƙofar ɗakinta ta kama tsantsa ta ce

",Allah ya yanke miki wahala Habiba, yo ai ke gaba ta kaiki gobarar titi, zaman gidan nan ai jarabawa ne, duk lokacin da Allah ya yanke maka sai ka gode wataƙila gaba ta fi ba ya yawa!" ,


Baba ya ce

",To mai bakin reza, wato ke ishashshiya da mai to ai hausawa sun ce riƙon mahaukaci sai sarki, kuma wallahi kika cika baki kafin ta isa gidansu ke ma kin kama hanyar naku gidan" Baki sake take kallonsa.

Mama Habiba ba ta tanka musu ba ya wuce ɗakinta jiki sanyi ƙalau ranta duk bau daɗi tana tunanin ashe dama shi ya sa ubangiji ba ya son saki duk da abu ne halactacce, saboda gabaɗaya ta ji wani ɗaci a ranta lallai ta tabbata saki ba shi da daɗi.

Kayanta ta haɗo a jaka ta fito ta zo ta yi wa matan da yaran gidan da suka fito sallama ta kama hanya ta fita.

Tana fita Baba ya ce

"Yawwa yanzu kuma na ragewa kaina wahala amma dai ba zan gushe ba ina son ɗa namiji ko kan gararre ne sai ranar da na haifi ɗa namiji dole ne ma yanzu in samu budurwa ko sakin wawa in auro" ,Yana faɗar hakan ya ja ƙafafunsa yana yin ɗan kukan takaicin ƙonewar kayan abincin sa. A tsakar gidan kuwa Mama Talatuwa ce kaɗai take cike da jimamin barin gidan da Mama Habiba ta yi sai dai tana fatan ta samu sauyi mafi alkairi tun da ta lura rashin haihuwar ne kaɗai yake saka Baba yake mata yadda ya so.

Washe gati da maƙota suka riƙa shigowa gidan suna jajantawa Baba. Duk magidancin da ya shigo sai Baba ya ce

",Kun ga dai yadda Allah ya jarafceni da ƙonewar kayan abincin, wannan lamari ne da yake buƙatar taimako da tallafin jama,a sannan kamata ya yi mutanen unguwa su yi gangami a yi meeting a sanar a masallaci ake haɗa kuɗin tainakon da za a bani wataƙila kuɗin su zama silar warakata dagaa baƙin talaucin nan" ,Duk wanda Baba ya faɗawa haka sai ya nuna ya yi na,am kuma hakan abu ne mai kyau sai dai babu wanda ya zauna ya ce a yi shawarar haɗa masa kuɗin domin Baba bai san cewa kaf unguwa babu wanda bai san halin da gidansa yake ciki ba, ya manta cewa yanzu kiwo na mutum ake yi ba dabba ba.

Ko da Mama Talatuwa ta kira Sadiya a waya ta sanar da ita abin da yake faruwa ta yi jimami sosai kafin daga bisani ta fawwalawa Allah komai dama ai ta san halin mahaifinsu na rashin wadata iyali wanda bai san hakan cewa ba iyalinsa kaɗai yake tauyewa ba hsr da kansa yake tauyewa domin sai ya sauke nauyin haƙƙinsu ne Allah zai ƙara buɗa masa, sai dai shi ya kasa fahimtar hakan gani yake rashin wadatarwar shi ne zai haɓaka arziƙinsa.

Ko da ta je gidan ta jajanta masa sai da ya ce

"Sadiya kin faɗawa Nasir ɗin na samu gobara komai na kayana abincina ya ƙone? Na kira wayarsa sau biyu bai ɗaga ba kuma bai biyo kiran ba, ai kin ga a matsayinsa na surukina ɗaya ƙwallin ƙwal ya kamata ya kawo ɗan wani abu mana, don na ga jama,ar unguwar nan babu niyya ango ya kwana da wando, tun jiya an gagara kawo ko ƙwayar gero bare a saka ran kawo shinkafa, ni wallahi na ɗauka zuwa yanzu an tara buhun shinkafa ƴar gwammani buhu bakwai a lalace na hatsi biyar dawa huɗu amma har yanzu shiru maƙatau, ko dah taimakon ƴan siyasa zan nema ne?"

Sadiya ta danne takaicin da ta ji ta ce

"Baba wataƙila ko yana kasuwa lokacin da ka kira shi, amma dai maganar kawo tallafi dama ba lallai ba ne tun da yanzu rayuwar ce sai a hankali kowa ta kansa yake...

Hannu ya ɗaga mata ya ce


"Ke dalla rufewa mutane baki, ba ta kai ba idan ma ta ƙafa ake ai ba za su rasa amfanin abinci a gidansu ba a lalace ko kwano biyar biyar ce mutum in zai zo jaje sai ya taho da shi, amma don asara sai su taho babu komai kowa haka zai shigo hannu yana dukan cinya su zo su ishi mutane da cewa, ka yi haƙuri malam Bala haka Allah ya ƙaddara Allah mayar da alheri" ,Ya faɗa yana kwaikwayon yadda mutanen suke faɗa in sun zo masa jajan tare da jan wani dogon tsaki yana muzurai. Haƙuri ta shiga bashi ta ɗakko dubu goma ta ba shi, ya karɓa ko godiya bai mata ba bare ya saka albarka, saboda shi yanzu wasu kuɗaɗe masu kauri yake so su faɗo masa.

Kamar zai yi kuka ya ce

"Wllahi shi ma limamin nan na masallacin nan ba shi da tausayi ina ga ma in daina sallah a masallacjn nan in koma wani, mutumin nan yana kallo tun kan ladan ya kira assalatu na fita na je masallacin nan na ringa sallar nafila ina ɗaga hannuwa sama idan na idar ina ta addu,a amma na ɗauka da aka idar da sallar asubar zai yi sanarwa a lasifika cewa a taimaka mini amma shiru maye ya ci shirwa, haka da aka idar da sallar azzahar na kifa kaina da gwiwoyin ƙafata wai duk don a fahimci ina cikin damuwa da halin ƙaƙanika yi amma babu wanda ya bi ta kaina"

Haƙuri dai Sadiya take ta ba shi, bayan ta jo sallamar mutane a zaure ta amsa suka shigo don Baba yana jin sallamar ma ya ƙi amsawa ya rage murya ya ce

"Sadiya da kin ƙyale su, don ba wata tsiyar suka kawo ba in banda zance" Ita dai ba ta amsa ba haka suka shigo Baba kuwa ya haɗe fuska yana muzurai don dakyar yake amsa jajan da ake masa.

Sadiya sai da suka keɓe da Mama Talatuwa take faɗa mata sakin da Baba ya yi wa Mama Habiba, salati ta yi hankali tashe tana jimanta abin, don ita da ta shigo ta ga ɗakin Mmar a rufe ta ɗauka ko unguwa ta tafi cike da damuwa a fuskarta ta ce

"Mama wai su maza haka suke ne?"

Mama ta ce

",Kamar yaya?"

Sadiya ta ce

"A yadda na fahimta yawancinsu ba su da uzuri, sannan duk daren daɗewa suna manta halacci, kuma su babu ruwansu da daɗewar da mace ta yi tare da su da sadaukarwa da taimakonsu da ta yi a rayuwa, haka kawai wani namijin sai ki ga an ce sun kwashe shekaru da matarsa tun ba shi da komai tun suna gidan haya, wani ma ko aikin yi ba shi da shi, sai ya fita ya nemo za a samu a ci watarana ma a haƙura idan bai samo ba, wani kuma matar ce za ta ciru ta ƙullu ta ciyar da gidan wata rana, wata ma bashi za ta ci, wata kuma ta haka jarinta da take juyawa zai salwanta a wajen taimaka masa, amma daga ya samu dama sai ya manta da duk abubuwan da suka faru a baya, sai ki ga bai mata halacci ba, sai ki ga tukucin da zai mata shi ne rabuwa da ita sai ya sake ta, ya auri wata ya ci gaba da rayuwa da waccan ɗin wacce ta zo ta samr shi cikin arziƙinsa wacce ba ta san wahalarsa ba amma ita za ta ji daɗin ita wacce ta sha wahalar sai ki ba ba ta da darajar da za ta zauna a gidan nasa ma mai ɗan mutunci shi ne wanda zai zauna da matar bai sake ta ba, amma dai wata duj da tana gidan sai ki ga wulaƙanci yana biyowa baya" Cewar Sadiya tana hawaye.

Mama ta ce

"Eh maganrki tana kan hanya Sadiya duk da ba duka aka taru aka zama ɗaya ba"

Sadiya tw ce

"Ni ma ai wasu na ce Mama, dimin wasu sun san halacci wani ba ya taɓa mantawa da halaccin, wani yana darajawa da mutunta matar ko da a ce ya auri wata matar to fa ya san darajar waccan da suka sha wahalar tare"

Mama ta ce

"Ai wasu mazan sai addu,a domin wani namijin a ya riƙe alƙawari amma mafi yawanci ƴa mace ta fi yin halaccia a kan ɗa namiji, mace ta fi riƙe alƙawari duk da su ma mazan akwai masu tsananin riƙe alƙawari"

Sadiya ta ce

"Mai ya sa?"

Mama ta ce
"Saboda za ki ga ƴa mace ko mijinta ne ba shi da lafiya wato duk tsananin jinya za ta zauna ta kula da shi, sannn ko da nakasa ya samu sai ki ga ta ƙarar da ƙuruciyarta wajen kula da shi, babu ruwanta da sai ta je ta auti wani ta ci gaba da rayuwa da wanin, amma ita kuma macen idan bata da lafiya ko zazzaɓi ne ya yi tsananin sai dai a kaita gidansu iyayenta su yi jinya, idan ta warke sai ta dawo gidan mijin"

Sadiya ta ce

"Kenan lafiyarta ce a bar amfana?"

Mama ta ce

"A,a ina faɗa miki yawancin abin da yake faruwa amma akwai wasu mazan da suke kula da matansu fiye da tunaninki" Ajiyar zuciya Sadiya ta sauke amma dai ta ji ɗacin sakin da Baba ya yi wa Mama Habiba.

Ko kiran magriba ba a yi ba ya ringa ƙwala mata kira yana faɗin ta ɗakko Kalifa su zo su tafi gida.


ZALIKA


Tana karkarea take kallon kwalin duk ta diririce tunanin ta ya tsaya cak sai faman haɗo tunanin take amma hakan ya gagara, ta ma rasa abin da za ta shirya don ta kare kanta don ta ji ƙwaƙwalwar ta da kuma yanayin da jikinta ya nuna suna neman ƙin bata haɗin kan da zai taimake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login